Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Me ya sa 2 Sama’ila 21:7-9 suka ce Dauda “bai yarda ya ba da Mefiboshet” ba, amma daga baya sai ya ba da Mefiboshet a kashe shi?

▪ Wasu da suka karanta wannan labarin cikin hanzari sun yi wannan tambayar. Amma wannan labarin yana magana game da mutane biyu ne da sunansu Mefiboshet kuma za mu iya koyan darasi daga bincika abin da ya faru.

An haifa wa Shawulu sarkin Isra’ila ’ya’ya maza bakwai da kuma ’yan mata biyu. Ɗan farin Shawulu shi ne Jonathan. Daga baya, Rizpa matar da Shawulu ya ajiye ta haifa masa ɗa, wanda sunansa Mefiboshet ne. Amma Jonathan ɗan Shawulu ma ya ba ɗansa suna Mefiboshet. Saboda haka, Sarki Shawulu yana da ɗa mai suna Mefiboshet da kuma jika mai suna Mefiboshet.

Akwai lokacin da Sarki Shawulu ya yi ƙoƙarin kakkashe dukan Gibeyonawan da suke zama a ƙasar Isra’ila. Da alama ya kashe da yawa daga cikinsu. Hakan babban zunubi ne. Me ya sa? Domin a zamanin Joshua, shugabannin Isra’ilawa sun yi yarjejeniyar zaman lafiya tare da Gibeyonawan.—Yosh. 9:3-27.

Yarjejeniyar ta ci gaba da aiki har a zamanin Shawulu. Amma sarkin ya saba wa wannan yarjejeniyar ta wajen yunƙurin kakkashe Gibeyonawan. Wannan abin da Shawulu ya yi ya kawo “alhakin jini a kan Shawulu da gidansa.” (2 Sam. 21:1) Daga baya, Dauda ya zama sarki. Gibeyonawan da suka tsira sun kai kuka wurin Dauda domin abin da Shawulu ya yi musu. Dauda ya tambaye su yadda suke so a biya musu hakkinsu domin muguntar da Shawulu ya yi musu. Ta hakan ne Jehobah zai yi wa ƙasar Isra’ila albarka. Maimakon Gibeyonawan su ce a biya su kuɗi, sai suka ce a miƙa musu ’ya’ya bakwai na mutumin da ya so ya halaka su don su kakkashe su. (L. Ƙid. 35:30, 31) Sai Dauda ya yarda da hakan.—2 Sam. 21:2-6.

A lokacin, Shawulu da Jonathan sun riga sun mutu a yaƙi. Amma Mefiboshet ɗan Jonathan yana da rai har ila. Shi gurgu ne domin ya yi hatsari a lokacin da yake ƙarami kuma ba ruwansa da harin da kakansa ya kai wa Gibeyonawan. Tun kafin lokacin, Dauda ya riga ya yi yarjejeniya da Jonathan cewa za su zama abokai kuma hakan ya shafi zuriyarsu har da Mefiboshet, ɗan Jonathan. (1 Sam. 18:1; 20:42) Ayar ta ce: “Saboda rantsuwar da Dawuda ya yi da Yonatan ɗan Shawulu a gaban Yahweh, bai yarda ya ba da Mefiboshet ɗan Yonatan jikan Shawulu ba.”—2 Sam. 21:7.

Duk da haka, Dauda ya yarda ya yi abin da Gibeyonawan suka ce ya yi. Sai ya ba da ’ya’yan Shawulu guda biyu; ɗaya daga cikin su sunansa Mefiboshet ne, da kuma jikokin Shawulu guda biyar. (2 Sam. 21:8, 9) Abin da Dauda ya yi ya ɗauke alhakin jini daga ƙasar.

Wannan labarin ba tarihi ba ne kawai. Dokar da Allah ya bayar a bayyane take. Ta ce: “Ba za a kashe . . . ’ya’ya saboda zunubin iyayensu ba.” (M. Sha. 24:16) Da a ce ’ya’yan Shawulu biyu da kuma jikokinsa biyar ba su da hannu a cikin abin da Shawulu ya yi, da Jehobah bai bari a kashe su ba. Dokar ta ƙara da cewa: “Duk mutumin da ya yi zunubi, shi za a kashe.” Da alama cewa ’ya’yan Shawulu da jikokinsa da aka kashe suna da hannu a abin da ya yi. A sakamakon haka, an kashe su don zunubinsu.

Wannan labarin ya nuna cewa mutum ba zai iya yin zunubi sa’an nan ya ba da hujja cewa ya bi umurni ne da aka ba shi ba. Wani ƙarin magana ya ce: “Ka tabbata ka san abin da kake yi, duk abin da kake yi kuma zai zama daidai.”—K. Mag. 4:24-27; Afis. 5:15, Mai Makamantu Ayoyi.