Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 39

Abin da Za Ka Yi Idan Wani a Iyalinku Ya Bar Jehobah

Abin da Za Ka Yi Idan Wani a Iyalinku Ya Bar Jehobah

“Sau nawa suka  . . . sa shi baƙin ciki.”​—ZAB. 78:40.

WAƘA TA 102 “Mu Taimaki Marasa Ƙarfi”

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Idan aka yi ma wani yankan zumunci, ta yaya hakan zai shafi iyalinsa?

AN TAƁA yi ma wani a iyalinku yankan zumunci? Hakan yana jawo baƙin ciki sosai! Wata ’yar’uwa mai suna Hilda ta ce: “A lokacin da mijina ya rasu bayan mun yi shekara 41 da aure, na ɗauka babu abin da zai taɓa sa ni baƙin ciki kamar hakan. * Amma lokacin da ɗana ya daina bauta wa Jehobah kuma ya bar matarsa da yara, hakan ya ci mini rai fiye da mutuwar maigidana.”

Jehobah ya san irin baƙin cikin da za ka yi idan wani a iyalinku ya daina bauta masa (Ka duba sakin layi na 2-3) *

2-3. Bisa ga Zabura 78:40, 41, yaya Jehobah yake ji idan bayinsa suka daina bauta masa?

2 Ka yi tunanin irin baƙin cikin da Jehobah ya yi a lokacin da wasu daga cikin ’ya’yansa mala’iku suka yi masa tawaye! (Yahu. 6) Ban da haka, ka yi tunanin yadda ya yi baƙin ciki sa’ad da mutanensa da yake ƙauna, wato Isra’ilawa, suka yi masa tawaye sau da yawa. (Karanta Zabura 78:40, 41.) Ka kasance da tabbaci cewa Ubanmu na sama mai ƙauna yana baƙin ciki sosai a duk lokacin da wani da kake ƙauna ya daina bauta masa. Ya san irin baƙin cikin da kake yi. Zai ƙarfafa ka kuma ya taimaka maka.

3 A wannan talifin, za mu tattauna abin da za mu iya yi domin Jehobah ya taimaka mana idan muna cikin irin yanayin nan. Ƙari ga haka, za mu ga yadda za mu iya taimaka wa ’yan’uwan da aka yi ma wani a iyalinsu yankan zumunci. Amma da farko, bari mu tattauna irin tunanin da muke bukatar mu guje wa.

KADA KA ƊORA WA KANKA LAIFI

4. Yaya iyaye suke ji idan ɗansu ko ’yarsu ta daina bauta wa Jehobah?

4 Idan yara suka daina bauta wa Jehobah, iyayen za su iya ɗauka cewa akwai abin da ya kamata su yi da ba su yi ba don su taimaka wa yaran kada su bar Jehobah. Akwai wani ɗan’uwa mai suna Luke da aka yi wa yaronsa yankan zumunci. Ɗan’uwan ya ce: “Na ɗora wa kaina laifi. Har na yi ta yin munanan mafarki game da abin da ya faru. A wasu lokuta, nakan yi kuka har in ji kamar zuciyata za ta rabu biyu.” Wata ’yar’uwa mai suna Elizabeth da ta fuskanci irin yanayin nan ma ta ce: “Mai yiwuwa na yi kurakurai da yawa a matsayin mahaifiya. Na ji kamar ban yi iya ƙoƙarina ba yayin da nake koya wa ɗana game da Jehobah.”

5. Waye ne yake da laifi idan wani ya daina bauta wa Jehobah?

5 Muna bukatar mu tuna cewa Jehobah ya ba kowannenmu ’yancin yin zaɓi. Hakan yana nufin cewa za mu iya zaɓa mu yi masa biyayya ko a’a. Akwai yaran da iyayensu ba su kafa musu misali mai kyau ba. Duk da haka, yaran sun zaɓa su bauta wa Jehobah kuma sun riƙe amincinsu. Wasu yaran kuma, iyayensu sun yi iya ƙoƙarinsu su koya musu game da Jehobah, amma da yaran suka yi girma, sai suka daina bauta wa Jehobah. Don haka, kowannenmu ne zai zaɓa da kansa ko zai bauta wa Jehobah. (Yosh. 24:15) Saboda haka, iyaye, idan kuna baƙin ciki domin ɗanku ko ’yarku ta daina bauta wa Jehobah, kada ku ɗauka cewa laifinku ne!

6. Yaya matashi zai iya ji idan iyayensa suka daina bauta wa Allah?

6 A wasu lokuta, iyaye za su iya daina bauta wa Jehobah har ma su bar iyalinsu. (Zab. 27:10) Hakan zai iya jawo baƙin ciki mai tsanani ga yaran da suke daraja iyayensu sosai. Wata mai suna Esther da aka yi wa mahaifinta yankan zumunci ta ce: “Na yi kuka sosai domin na gano cewa ba sanyin gwiwa ne kawai ya yi ba. Amma ya zaɓa ne ya daina bauta wa Jehobah. Ina ƙaunar mahaifina, saboda haka, a lokacin da aka yi masa yankan zumunci, na damu sosai da yadda yake. A wasu lokuta, zuciyata takan tsinke.”

7. Yaya Jehobah yake ji game da matashin da aka yi wa iyayensa yankan zumunci?

7 Matasa, idan an yi wa babanku ko mamarku yankan zumunci, muna baƙin ciki tare da ku! Ku kasance da tabbaci cewa Jehobah ya san irin baƙin cikin da kuke yi. Yana ƙaunar ku kuma yana farin ciki cewa kuna bauta masa da aminci. Mu ’yan’uwanku ma muna ƙaunar ku. Ku tuna cewa shawarar da iyayenku suka yanke ba laifinku ba ne. Kamar yadda aka ambata a baya, Jehobah ya ba kowane mutum ’yancin yin zaɓi. Duk wanda ya yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ya yi baftisma, zai “ɗauki kayan kansa.”​—Gal. 6:5.

8. Mene ne waɗanda suke bauta wa Jehobah za su iya yi yayin da suke jiran wanda aka yi wa yankan zumunci ya dawo? (Ka duba akwatin nan “ Ka Komo ga Jehobah.”)

8 Idan wani da kake ƙauna ya daina bauta wa Jehobah, babu shakka, za ka yi ta sa rai cewa wata rana mutumin zai dawo. Mene ne za ka yi yayin da kake jira ya dawo? Ka yi iya ƙoƙarinka ka ƙarfafa bangaskiyarka. Ta yin hakan, za ka kafa misali mai kyau wa sauran ’yan’uwanka, mai yiwuwa har da wanda aka yi wa yankan zumuncin. Ƙari ga haka, za ka sami ƙarfin jimre yanayin. Bari mu tattauna wasu abubuwa da za ka iya yi domin ka ƙarfafa bangaskiyarka.

ABIN DA ZA KA IYA YI DON KA ƘARFAFA BANGASKIYARKA

9. Mene ne za ka iya yi don ka ƙarfafa bangaskiyarka? (Ka duba akwatin nan “ Nassosin da Za Su Ƙarfafa Ka Idan Wani a Iyalinku Ya Daina Bauta wa Jehobah.”)

9 Ka yi iya ƙoƙarinka don ka ƙarfafa bangaskiyarka. Yana da muhimmanci ka ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarka da kuma na sauran membobin iyalinka. Ta yaya za ka yi hakan? Ka karanta Littafi Mai Tsarki a kullum, ka yi tunani a kan abin da ka karanta kuma ka halarci taro a kai a kai. Yin waɗannan abubuwan zai taimake ka. Wata ’yar’uwa mai suna Joanna wadda mahaifinta da ’yar’uwarta suka daina bauta wa Jehobah ta ce: “Hankalina yakan kwanta a duk lokacin da na karanta labarin Abigail da Esther da Ayuba da Yusufu da kuma Yesu. Misalinsu yana ƙarfafa ni kuma yana taimaka mini in kasance da ra’ayin da ya dace. Waƙoƙinmu na JW ma suna ƙarfafa ni sosai.”

10. Bisa ga Zabura 32:6-8, mene ne za mu iya yi idan muna baƙin ciki?

10 Ka gaya wa Jehobah dukan abubuwan da ke damunka. Idan kana baƙin ciki, kada ka daina yin addu’a. Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka bi da yanayin yadda yake so kuma ya ‘koya maka ya kuma nuna maka hanyar da za ka bi.’ (Karanta Zabura 32:6-8.) Hakika, zai iya yi maka wuya ka gaya wa Jehobah ainihin yadda kake ji. Amma Jehobah ya san yadda kake ji. Yana ƙaunar ka sosai kuma yana ƙarfafa ka ka gaya masa abin da ke zuciyarka.​—Fit. 34:6; Zab. 62:7, 8.

11. Kamar yadda Ibraniyawa 12:11 ta nuna, me ya sa ya kamata mu amince cewa horon da Jehobah ya yi daidai ne? (Ka duba akwatin nan “ Yankan Zumunci Hanya Ce da Jehobah Yake Yin Horo da Ƙauna.”)

11 Ka goyi bayan matakin da dattawa suka ɗauka. Jehobah ne ya tsara cewa a yi ma duk mai zunubin da ya ƙi tuba yankan zumunci. Ƙauna ce take sa Jehobah ya yi wa mutum horo. Kuma horon yana taimaka wa mai zunubin da ma kowa. (Karanta Ibraniyawa 12:11.) Wasu a ikilisiya suna iya cewa dattawa ba su yanke hukuncin da ya dace ba. Amma ka tuna cewa irin ’yan’uwan nan ba sa faɗan laifin da mutumin ya yi. Gaskiyar ita ce, ba mu san kome da kome game da batun ba. Saboda haka, ya kamata mu gaskata cewa dattawan da suka yanke hukuncin, sun yi iya ƙoƙarinsu su bi abin da ke Littafi Mai Tsarki kuma sun yi shari’a a madadin Jehobah.​—2 Tar. 19:6.

12. Wace albarka ce wasu suka samu domin sun goyi bayan tsarin da Jehobah ya yi na yankan zumunci?

12 Idan ka goyi bayan hukuncin da dattawa suka yanke na yi ma wani a iyalinku yankan zumunci, hakan zai iya taimaka wa mutumin ya dawo ga Jehobah. Elizabeth wadda aka ambata ɗazu ta ce: “Ƙin yin mu’amala da ɗanmu bai zo mana da sauƙi ba. Amma da ya komo ga Jehobah, sai ya ce ya dace da aka yi masa yankan zumunci. Daga baya, ya ce ya koyi darussa da yawa masu kyau. Yanzu na gane cewa duk horon da Jehobah yake bayarwa daidai ne.” Mijinta mai suna Mark ya ce: “Daga baya, ɗanmu ya gaya mini cewa ɗaya daga cikin dalilai da suka sa ya dawo shi ne domin mun daina mu’amala da shi. Ina farin ciki cewa Jehobah ya taimaka mana mu yi masa biyayya.”

13. Mene ne zai taimaka maka idan kana baƙin ciki sosai?

13 Ka tattauna da abokanka da suka fahimci yadda kake ji. Ka riƙa yin cuɗanya da ’yan’uwa da suka manyanta da za su iya taimaka maka kada ka fid da rai. (K. Mag. 12:25; 17:17) Joanna wadda aka ambata ɗazu ta ce: “Na kaɗaita. Amma tattaunawa da abokan da na yarda da su ya taimaka mini.” Mene ne za ka yi idan wasu a ikilisiya suka faɗi abin da ya daɗa sa ka baƙin ciki?

14. Me ya sa ya kamata mu yi ‘ta yin haƙuri da juna’ da kuma gafarta wa juna?

14 Ka riƙa yin haƙuri da ’yan’uwanka. Bai kamata mu yi tsammani cewa kowa zai faɗi abin da ya dace a kowane lokaci ba. (Yak. 3:2) Dukanmu ajizai ne, saboda haka, kada ka yi mamaki idan wasu suka rasa abin da za su faɗa maka, ko kuma suka faɗi abin da ya ɓata maka rai a cikin rashin sani. Ka tuna shawarar da manzo Bulus ya bayar cewa: “Kuna ta yin haƙuri da juna. Idan kuma wani a cikinku ya yi wa wani laifi, ku gafarta masa.” (Kol. 3:13) Wata ’yar’uwa da aka yi wa ɗanta yankan zumunci, ta ce: “Jehobah ya taimaka mini in gafarta wa ’yan’uwa da suka ɓata mini rai, ko da yake sun so su ƙarfafa ni ne.” Mene ne ’yan’uwa a ikilisiya za su iya yi domin su taimaka wa iyalin da aka yi ma wani a cikinsu yankan zumunci?

‘YAN’UWA A IKILISIYA ZA SU IYA TAIMAKAWA

15. Me zai taimaka wa ’yan’uwan da bai jima da aka yi ma wani a iyalinsu yankan zumunci ba?

15 Ku nuna alheri ga ’yan’uwa masu aminci da aka yi ma wani a iyalinsu yankan zumunci. Wata ’yar’uwa mai suna Miriam ta ce ta ji tsoron halartan taro bayan an yi wa ɗan’uwanta yankan zumunci. Ta ce: “Ban san abin da ’yan’uwa za su faɗa ba. Amma akwai abokai da suka ƙarfafa ni ba tare da yin baƙar magana game da ɗan’uwana da aka yi wa yankan zumunci ba. Saboda yadda suka nuna sun damu da ni, na sami ƙarfafa sosai.” Wata ’yar’uwa ta tuna abin da ya faru kuma ta ce: “Bayan an yi wa ɗanmu yankan zumunci, abokanmu sun zo su ƙarfafa mu. Wasu a cikinsu sun ce ba su san abin da za su faɗa ba. Wasunsu sun yi kuka, wasu kuma suka turo mini wasiƙa. Abin da suka yi ya taimaka mini sosai!”

16. Ta yaya ’yan’uwa a ikilisiya za su riƙa taimaka ma waɗanda aka yi ma wani a iyalinsu yankan zumunci?

16 Ka ci gaba da taimaka wa iyalin waɗanda aka yi wa yankan zumunci da suke bauta wa Jehobah da aminci. A yanzu ne suka fi bukatar ka nuna kana ƙaunar su kuma ka ƙarfafa su. (Ibran. 10:24, 25) A wasu lokuta, ’yan’uwan waɗanda aka yi wa yankan zumunci sun lura cewa, wasu ’yan’uwa a ikilisiya sun daina cuɗanya da su sai ka ce su ma an yi musu yankan zumunci. Ba zai dace mu sa su ji hakan ba! Matasa musamman waɗanda iyayensu suka daina bauta wa Jehobah suna bukatar a riƙa yaba musu da kuma ƙarfafa su. Wata ’yar’uwa mai suna Maria da aka yi wa mijinta yankan zumunci kuma ya bar ta da yaransu, ta ce: “Wasu a cikin abokaina sun zo gidanmu, suka dafa mana abinci kuma suka yi nazari da yarana. Sun nuna sun damu da ni kuma sun yi kuka tare da ni. Sun kāre ni sa’ad da mutane suka soma faɗan abubuwan da ba gaskiya ba game da ni. Hakika, sun ƙarfafa ni sosai!”​—Rom. 12:13, 15.

’Yan’uwa a ikilisiya za su iya ƙarfafa waɗanda wani a iyalinsu ya daina bauta wa Jehobah (Ka duba sakin layi na 17) *

17. Me ya kamata dattawa su yi don su ƙarfafa waɗanda suke baƙin ciki?

17 Dattawa, ku yi amfani da kowace dama da kuka samu domin ku ƙarfafa waɗanda aka yi ma wani a iyalinsu yankan zumunci. Kuna da hakkin ƙarfafa ’yan’uwan da wani a iyalinsu ya daina bauta wa Jehobah. (1 Tas. 5:14) Ku tattauna da su kafin taro da kuma bayan taron don ku ƙarfafa su. Ku ziyarce su kuma ku yi addu’a tare da su. Ku fita wa’azi tare da su, ko kuma a wasu lokuta ku gayyace su su yi ibada ta iyali tare da ku. Dattawa suna bukatar su kula da waɗanda suke baƙin ciki kuma su nuna musu ƙauna da tausayi.​—1 Tas. 2:7, 8.

KADA KA FID DA RAI KUMA KA CI GABA DA DOGARA GA JEHOBAH

18. Kamar yadda 2 Bitrus 3:9 ta nuna, mene ne Allah yake so waɗanda suka daina bauta masa su yi?

18 Jehobah “ba ya so wani ya halaka, sai dai kowa ya zo ya tuba.” (Karanta 2 Bitrus 3:⁠9.) Ko da mutum ya yi zunubi mai tsanani, Jehobah ba ya so ya hallaka. Ka tuna cewa Jehobah ya ba da abu mai daraja domin ya fanshe mu, wato ran Ɗansa da yake ƙauna. Jehobah yana ƙoƙarin taimaka ma waɗanda suka daina bauta masa su komo gare shi. Yana fatan cewa za su zaɓi su yi hakan, kamar yadda kwatancin Yesu na mubazzari ya nuna. (Luk. 15:11-32) Mutane da yawa da suka daina bauta wa Jehobah daga baya sun komo ga Ubanmu na sama mai ƙauna. Kuma ’yan’uwa a ikilisiya sun marabce su sosai. Elizabeth da aka ambata ɗazu ta yi farin ciki sa’ad da ɗanta ya komo ga Jehobah. Ta ce: “Na yi farin ciki sosai cewa ’yan’uwa da yawa sun ƙarfafa mu kada mu fid da rai.”

19. Me ya sa za mu iya ci gaba da dogara ga Jehobah?

19 Jehobah ba zai taɓa ba mu shawarar da za ta sa mu cikin matsala ba, don haka, za mu iya dogara gare shi a koyaushe. Shi Uba ne mai tausayi, mai bayarwa hannu sake. Yana ƙaunar waɗanda suke ƙaunar shi kuma suke bauta masa. Ka kasance da tabbaci cewa Jehobah ba zai taɓa yin watsi da kai a lokacin da kake baƙin ciki ba. (Ibran. 13:5, 6) Mark da aka ambata ɗazu ya ce: “Jehobah bai taɓa yin watsi da mu ba. Yana taimaka mana a duk lokacin da muke cikin matsala.” Jehobah zai ci gaba da ba ka “cikakken ikon da ya fi” kowanne. (2 Kor. 4:7) Hakika, za ka iya riƙe amincinka kuma ka ci gaba da sa rai cewa wanda ya daina bauta wa Jehobah a iyalinku zai iya dawowa.

WAƘA TA 44 Addu’ar Wanda Ke Cikin Wahala

^ sakin layi na 5 Za mu yi baƙin ciki sosai idan wani da muke ƙauna ya daina bauta wa Jehobah! A wannan talifin, za mu tattauna yadda Allahnmu yake ji idan hakan ya faru. Za mu tattauna abubuwan da iyalin wanda aka yi wa yankan zumunci za su iya yi domin su sami ƙarfafa kuma su ci gaba da kasancewa da bangaskiya. Ƙari ga haka, a wannan talifin, za a tattauna yadda kowa a ikilisiya zai iya ƙarfafa iyalin kuma ya taimaka musu.

^ sakin layi na 1 An canja wasu sunaye a wannan talifin.

^ sakin layi na 79 BAYANI A KAN HOTO: Idan wani ɗan’uwa ya daina bauta wa Jehobah kuma ya yasar da iyalinsa, matarsa da yaransu za su sha wahala.

^ sakin layi na 81 BAYANI A KAN HOTO: Dattawa biyu sun zo su ƙarfafa wata ’yar’uwa da yaranta.