Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 38

Ka Kusaci Jehobah da Kuma ’Yan’uwa

Ka Kusaci Jehobah da Kuma ’Yan’uwa

“Zan koma wurin Ubana kuma Ubanku.”​—YOH. 20:17.

WAƘA TA 3 Ƙarfinmu, Begenmu da Makiyayinmu

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Me za mu iya kiran Jehobah?

IYALIN Jehobah ta ƙunshi Yesu wanda “shi ne Ɗan fari gaban dukan halitta,” da kuma miliyoyin mala’iku. (Kol. 1:15; Zab. 103:20) A lokacin da Yesu yake duniya, ya nuna cewa mutane masu aminci za su iya kiran Jehobah Uba. Ga abin da Yesu ya gaya wa mabiyansa sa’ad da yake magana game da Allah, ya ce da shi “Ubana [da] kuma Ubanku.” (Yoh. 20:17) Sa’ad da muka yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma muka yi baftisma, mun sami ’yan’uwa maza da mata.​—Mar. 10:29, 30.

2. Me za mu tattauna a wannan talifin?

2 Yana yi ma wasu wuya su ɗauki Jehobah a matsayin Uba mai ƙauna. Wasu kuma yakan yi musu wuya su nuna wa ’yan’uwa cewa suna ƙaunar su. A wannan talifin, za mu tattauna yadda Yesu ya taimaka mana mu ɗauki Jehobah a matsayin Uba mai ƙauna da za mu iya kusantar sa. Kuma za mu ga hanyoyin da za mu iya bin misalin Jehobah a yadda muke bi da ’yan’uwanmu.

JEHOBAH YANA SO KA KUSACE SHI

3. Ta yaya addu’ar Ubangiji da Yesu ya koya mana take sa mu kusaci Jehobah?

3 Jehobah Uba ne mai ƙauna. Yesu yana so mu ɗauki Jehobah a matsayin Uba mai ƙauna da alheri, wanda za mu iya magana da shi a kowane lokaci, ba kamar wanda damuwarsa ita ce mu bi dokokinsa kawai ba. Mun ga tabbacin hakan a addu’ar da Yesu ya koya wa mabiyansa. Ya soma addu’ar da kalmar nan: “Ubanmu.” (Mat. 6:9) A cikin addu’ar, Yesu bai koya mana cewa mu kira Jehobah “Mafi Iko Duka” ko ‘Mahalicci’ ko kuma “Sarkin zamanai” ba. Kiran Allah da waɗannan laƙabin ba laifi ba ne domin an yi amfani da dukansu a Littafi Mai Tsarki. (Far. 49:25; Isha. 45:18; 1 Tim. 1:17) A maimakon haka, Yesu ya ce mana mu kira Jehobah “Uba.”

4. Ta yaya muka san cewa Jehobah yana so mu kusace shi?

4 Yana maka wuya ka ɗauki Jehobah a matsayin Uba mai ƙauna? Hakan yana ma wasu a cikinmu wuya. Idan mahaifinmu bai nuna mana ƙauna ba, zai iya yi mana wuya mu fahimci yadda uba yake nuna ƙauna. Sanin cewa Jehobah ya san yadda muke ji da abin da yake sa mu ji hakan, yana da ban ƙarfafa sosai! Yana so ya kusace mu. Shi ya sa Kalmarsa ta gaya mana cewa: “Ku yi kusa da Allah, shi kuwa zai yi kusa da ku.” (Yak. 4:8) Jehobah yana ƙaunar mu, kuma ya yi mana alkawari cewa zai zama mana Uba da babu kamar sa.

5. Bisa ga Luka 10:22, ta yaya Yesu zai taimaka mana mu kusaci Jehobah?

5 Yesu zai iya taimaka mana mu kusace Jehobah. Yesu ya san Jehobah kuma yana koyi da halayensa sosai. Shi ya sa ya ce: “Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban.” (Yoh. 14:9) Kamar yadda babban yaya yake yi, Yesu yana koya mana yadda za mu daraja Ubanmu kuma mu yi masa biyayya, da yadda za mu guji ɓata masa rai don mu sami amincewarsa. Amma abu mafi muhimmanci da Yesu ya koya mana shi ne cewa Jehobah Allah ne mai ƙauna sosai da kuma alheri. (Karanta Luka 10:22.) Bari mu ga wasu misalai.

Jehobah Uba ne mai ƙauna, shi ya sa ya aiki mala’ika ya ƙarfafa Ɗansa (Ka duba sakin layi na 6) *

6. Ta yaya Jehobah ya amsa addu’ar Yesu? Ka ba da misali.

6 Jehobah yana jin addu’ar ’ya’yansa. Ka yi tunani a kan yadda Jehobah ya saurari Ɗan farinsa. Jehobah ya amsa addu’o’in Ɗansa da yawa sa’ad da Ɗan yake duniya. (Luk. 5:16) Sa’ad da Yesu ya yi addu’a ga Jehobah a kan mataki mai muhimmanci da yake so ya ɗauka, Jehobah ya amsa. Alal misali, ya taimaka masa a lokacin da yake so ya zaɓi manzanninsa 12. (Luk. 6:12, 13) Jehobah ya kuma amsa addu’ar Yesu sa’ad da Yesu yake baƙin ciki. Dab da lokacin da za a ci amanar Yesu, ya yi addu’a ga Jehobah sosai game da abubuwan da za su faru da shi. Jehobah bai ji addu’ar Yesu kawai ba, ya tura mala’ika ya ƙarfafa Ɗansa da yake ƙauna.​—Luk. 22:41-44.

7. Yaya kake ji a duk lokacin da ka yi tunanin yadda Jehobah yake amsa addu’o’in bayinsa?

7 A yau ma Jehobah yana jin addu’o’in bayinsa, kuma yana taimakon su a lokaci da kuma hanyar da ta fi kyau. (Zab. 116:1, 2) Wata ’yar’uwa a Indiya ta ga yadda Jehobah ya amsa addu’arta. Ta daɗe tana fama da ciwon damuwa, sai ta roƙi Jehobah ya taimake ta. Ta ce: “Shirin Tashar JW na watan Mayu 2019 da ya yi magana a kan yadda za mu daina yawan damuwa, ya taimake ni sosai. Jehobah ya yi amfani da shirin ya amsa addu’ata.”

8. A wace hanya ce Jehobah ya nuna cewa yana ƙaunar Yesu?

8 Kamar yadda Jehobah ya yi wa Yesu, mu ma yana ƙaunar mu kuma yana kula da mu. (Yoh. 5:20) Jehobah ya taimaka masa ya kasance da bangaskiya mai ƙarfi, ya ƙarfafa shi sa’ad da yake baƙin ciki, kuma ya ba shi abubuwan da yake bukata. Jehobah ya gaya wa Ɗansa cewa yana ƙaunar shi kuma ya amince da shi. (Mat. 3:16, 17) Da yake Yesu ya san cewa Ubansa yana tare da shi, bai kaɗaita ba.​—Yoh. 8:16.

9. Mene ne ya tabbatar mana cewa Jehobah yana ƙaunar mu?

9 Dukanmu muna ganin yadda Jehobah yake nuna mana ƙauna, kamar yadda ya yi wa Yesu. Ka yi tunanin wannan: Allah ya ba mu damar zama abokansa, kuma ya ba mu ’yan’uwa da suke sa mu farin ciki da kuma ƙarfafa mu sa’ad da muke baƙin ciki. (Yoh. 6:44) Jehobah yana ba mu abubuwan da za su ƙarfafa bangaskiyarmu. Kuma yana ba mu abubuwan biyan bukata. (Mat. 6:31, 32) Idan muna tunanin yadda Jehobah yake ƙaunar mu, za mu daɗa ƙaunar sa.

KA BI DA ’YAN’UWA YADDA JEHOBAH YAKE BI DA SU

10. Mene ne za mu iya koya daga yadda Jehobah yake bi da ’yan’uwanmu?

10 Jehobah yana ƙaunar ’yan’uwanmu Kiristoci. Amma, a wasu lokuta zai iya yi mana wuya mu ƙaunace su ko mu nuna musu cewa muna ƙaunarsu. Hakan yana iya faruwa domin al’adunmu ba ɗaya ba ne, kuma mun taso a yanayi dabam-dabam. Ƙari ga haka, mu ajizai ne kuma abubuwan da muke yi za su iya ɓata wa ’yan’uwanmu rai. Duk da haka, za mu iya ci gaba da nuna ma ’yan’uwanmu ƙauna. Ta yaya? Ta wajen bin misalin Ubanmu na sama yayin da muke nuna ƙauna ga ’yan’uwanmu. (Afis. 5:1, 2; 1 Yoh. 4:19) Bari mu ga abin da za mu iya koya daga misalin Jehobah.

11. Ta yaya Yesu ya nuna cewa Jehobah mai ‘yawan jinƙai’ ne?

11 Jehobah mai ‘yawan jinƙai’ ko kuma tausayi ne. (Luk. 1:78) Mutum mai tausayi yakan damu idan ya ga wasu suna shan wahala, kuma yakan nemi hanyoyin da zai taimaka da kuma ƙarfafa su. Yadda Yesu ya bi da mutane ya nuna musu cewa Jehobah ya damu da su. (Yoh. 5:19) Akwai lokacin da Yesu ya ga taron jama’a kuma ya “ji tausayinsu, gama suna shan wahala kuma ba mai taimako, kamar tumakin da ba su da makiyayi.” (Mat. 9:36) Yesu bai ji tausayin su kawai ba, amma ya taimaka musu. Ya warkar da marasa lafiya, kuma ya sa waɗanda suke “fama da kaya masu nauyi” su huta.​—Mat. 11:28-30; 14:14.

Ka yi koyi da Jehobah ta wajen tausaya wa ’yan’uwanka da kuma taimaka musu (Ka duba sakin layi na 12-14) *

12. Ka ba da misalin yadda za mu iya nuna tausayi.

12 Idan muna tunanin matsalolin da ’yan’uwanmu suke fuskanta, za mu iya tausaya musu. Alal misali, a ce wata ’yar’uwa tana fama da rashin lafiya mai tsanani kuma ba ta magana a kan matsalarta. Idan wani ya taimaka mata, za ta yi farin ciki sosai. Ta yaya take biyan bukatun iyalinta? Shin za ta bukaci wani ya taimaka mata da dafa abinci ko kuma shara? Mai yiwuwa akwai wani ɗan’uwa da aka kore shi daga wurin aiki. Za mu iya ba shi ɗan kuɗi ba tare da mun gaya masa wanda ya ba shi kuɗin ba. Hakan zai taimaka masa har sai ya sami aiki.

13-14. Ta yaya za mu zama masu bayarwa hannu sake kamar Jehobah?

13 Jehobah mai bayarwa ne hannu sake. (Mat. 5:45 ) Kada mu jira sai ’yan’uwanmu sun nemi taimakonmu kafin mu taimaka musu. Za mu iya taimaka musu ko da ba su ce mu yi hakan ba kamar yadda Jehobah yake yi. Yana sa rana ta haskaka a kullum ba tare da mun roƙe shi ya yi hakan ba! Kuma kowa da kowa yana amfana daga ranar ba waɗanda suke gode masa kawai ba. Jehobah yana nuna mana cewa yana ƙaunar mu ta wajen biyan bukatunmu. Muna ƙaunar Jehobah domin alherinsa da kuma yadda yake bayarwa hannu sake!

14 ’Yan’uwanmu da yawa ma suna bayarwa hannu sake kamar yadda Jehobah yake yi. Alal misali, a 2013, Mahaukaciyar Guguwa mai suna Haiyan ta yi ɓarna sosai a ƙasar Filifin. ’Yan’uwa da yawa sun yi hasarar gidajensu da dukiyoyinsu. Amma ’yan’uwansu a faɗin duniya sun hanzarta sun taimaka musu. Wasu sun ba da gudummawar kuɗi, wasu kuma sun taimaka da gyara ko kuma sake gina gidaje kusan 750 a cikin ƙasa da shekara ɗaya! A lokacin annobar korona, Shaidun Jehobah sun yi aiki sosai don su taimaka ma ’yan’uwansu. Idan muna hanzarin taimaka wa ’yan’uwanmu, za mu nuna musu cewa muna ƙaunar su.

15-16. Mene ne Kolosiyawa 3:13 ta ce mu yi don mu nuna cewa muna koyi da Ubanmu na sama?

15 Jehobah yana gafartawa sosai. (Karanta Kolosiyawa 3:13.) A kullum Jehobah yana gafarta mana zunubanmu. (Zab. 103:10-14) Yesu ya gafarta wa mabiyansa duk da cewa su ajizai ne. Ya ma ba da ransa hadaya don a gafarta zunubanmu. (1 Yoh. 2:1, 2) Yadda Jehobah da Yesu suke gafarta mana, yana sa mu yi kusa da su, ko ba haka ba?

16 Idan muna “yafe wa juna” za mu daɗa ƙaunar juna. (Afis. 4:32) A wasu lokuta, ba zai yi mana sauƙi mu gafarta ma ’yan’uwanmu ba. Don haka, muna bukatar mu koyi yadda za mu riƙa yin hakan. Wata ’yar’uwa ta ce talifin Hasumiyar Tsaro mai jigo “Ka Riƙa Gafarta Wa Mutane” ya taimaka mata sosai. * Ta rubuto cewa: “Wannan talifin ya taimaka mini in ga cewa ni ma zan amfana idan na gafarta wa mutane. A talifin, an bayyana cewa gafarta wa mutane ba ta nufin ka amince da laifin da aka yi maka, ko kuma ka ce laifin bai ɓata maka rai ba. Amma gafartawa tana nufin ka daina fushi da wanda ya yi maka laifi, kuma ka kwantar da hankalinka.” Idan muna gafarta wa ’yan’uwanmu, za mu nuna cewa muna ƙaunar su, kuma muna koyi da Jehobah, Ubanmu na sama.

KA YI GODIYA DON KANA CIKIN IYALIN JEHOBAH

’Yan’uwa yara da manya suna nuna wa juna ƙauna (Ka duba sakin layi na 17) *

17. Kamar yadda Matiyu 5:16 ta nuna, ta yaya za mu nuna cewa muna ɗaukaka Ubanmu na sama?

17 Abin farin ciki ne cewa muna da ’yan’uwa a duk faɗin duniya kuma muna ƙaunar juna. Muna so mutane da yawa su zo su bauta ma Jehobah tare da mu. Don haka, kada mu yi wani abin da zai ɓata sunan Jehobah ko kuma na bayinsa. Ya kamata mu riƙa yin abin da ya dace a kullum domin hakan zai iya sa mutane su soma bauta wa Jehobah.​—Karanta Matiyu 5:16.

18. Mene ne zai taimaka mana mu yi wa’azi ba tare da jin tsoro ba?

18 A wasu lokuta, wasu za su iya tsananta mana ko kuma su rena mu don muna yin biyayya ga Ubanmu na sama. Me za mu yi idan muna jin tsoron gaya wa mutane abubuwan da muka yi imani da su? Mu tabbata cewa Jehobah da Ɗansa Yesu za su taimaka mana. Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa kada su damu a kan abin da za su faɗa. Me ya sa? Ya gaya musu cewa: “Za a ba ku abin da za ku ce a lokacin. Domin ba ku ne kuke magana ba, ruhun Ubanku ne yake magana ta wurinku.”​—Mat. 10:19, 20.

19. Ka ba da misalin wani ɗan’uwa da ya yi wa’azi ba tare da jin tsoro ba.

19 Ka yi la’akari da misalin Robert. Akwai lokacin da aka kai shi gaban kotu a Afirka ta Kudu don ya bayyana dalilin da ya sa ya ƙi shiga aikin soja. A lokacin, ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki ke nan kuma bai san abubuwa sosai a Littafi Mai Tsarki ba. Ya bayyana wa kotun ba tare da jin tsoro ba cewa ya ƙi shiga aikin soja ne domin yana ƙaunar ’yan’uwansa. Yana godiya don ’yan’uwa masu bi da yake da su! Ɗaya daga cikin alƙalan ya tambaye shi cewa, “Su waye ne ’yan’uwanka?” Robert bai yi zaton za a yi masa tambayar ba, amma nan da nan sai ya tuna da nassin yini na ranar. Nassin shi ne Matiyu 12:50, wanda ya ce: “Duk wanda ya yi abin da Ubana da yake cikin sama yake so, shi ne ɗan’uwana, da ’yar’uwata da kuma mamata.” Ko da yake Robert bai daɗe da soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki ba, ruhu mai tsarki ya taimaka masa ya amsa tambayar, da kuma wasu tambayoyi da bai yi zaton za a yi masa ba. Hakika, Jehobah ya yi alfahari da Robert! Haka ma, Jehobah yana alfahari da mu a duk lokacin da muka yi wa’azi ba tare da jin tsoro ba a yanayi mai wuya.

20. Me ya kamata mu ƙuduri niyyar yi? (Yohanna 17:11, 15)

20 Muna farin ciki cewa muna da Uba da kuma ’yan’uwa masu bi da suke ƙaunar mu. Mu riƙa nuna godiya don wannan iyalin da Allah ya ba mu. Shaiɗan da mugayen mabiyansa suna so su sa mu soma shakka cewa Ubanmu na sama yana ƙaunar mu, kuma su raba kanmu. Amma Yesu ya yi addu’a a madadinmu, kuma ya roƙi Jehobah ya taimaka mana mu kasance da haɗin kai. (Karanta Yohanna 17:11, 15.) Jehobah yana amsa addu’ar. Mu bi misalin Yesu, kuma kada mu yi shakka cewa Ubanmu na sama yana ƙaunar mu kuma zai taimaka mana. Mu yi iya ƙoƙarinmu don mu daɗa kusantar Jehobah da kuma ’yan’uwanmu.

WAƘA TA 99 Miliyoyin ’Yan’uwa

^ sakin layi na 5 Muna farin ciki cewa muna da ’yan’uwa maza da mata masu bi da suke ƙaunar mu sosai. Zai dace dukanmu mu daɗa ƙaunar juna. Ta yaya za mu yi hakan? Za mu iya yin hakan ta wajen yin koyi da yadda Ubanmu na sama yake nuna mana ƙauna, da kuma bin misalin Yesu da ’yan’uwanmu maza da mata.

^ sakin layi na 16 Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Nuwamba, 2012, shafuffuka na 26-30.

^ sakin layi na 57 BAYANI A KAN HOTO: Jehobah ya aika mala’ika ya ƙarfafa Yesu a lambun Gatsemani.

^ sakin layi na 59 BAYANI A KAN HOTO: A lokacin annobar korona, ’yan’uwa sun yi aiki da ƙwazo wajen shirya da kuma rarraba abinci.

^ sakin layi na 61 BAYANI A KAN HOTO: Wata mahaifiya tana taimaka ma ’yarta da take rubuta wasiƙa don ta ƙarfafa wani ɗan’uwa da ke kurkuku.