Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 35

Ku Daraja ’Yan’uwanmu Tsofaffi

Ku Daraja ’Yan’uwanmu Tsofaffi

“Furfurar tsufa rawanin daraja ce.”​—K. MAG. 16:31.

WAƘA TA 138 Tsofaffi Masu Aminci Suna da Daraja

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. (a) Kamar yadda Karin Magana 16:31 ta nuna, yaya ya kamata mu ɗauki tsofaffi? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu amsa a wannan talifin?

AKWAI wani irin lu’u-lu’u da idan ba a sarrafa shi ba, ba zai yi ƙyalli ko kyaun gani ba. Don haka, idan mutum ya ga lu’u-lu’un nan, ba zai san cewa yana da daraja ba.

2 Kamar lu’u-lu’u da muka ambata, ’yan’uwanmu maza da mata tsofaffi suna da daraja sosai. Kalmar Allah ta kwatanta furfurarsu da rawani. (Karanta Karin Magana 16:31; 20:29) Amma idan ba mu mai da hankali ba, za mu iya manta da ’yan’uwan nan masu daraja. Idan matasa suka fahimci cewa tsofaffi suna da daraja, za su iya samun abin da ya fi kuɗi daraja daga wurin tsofaffin. A wannan talifin, za mu amsa tambayoyin nan: Me ya sa Jehobah yake ɗaukan tsofaffi da daraja? Me ya sa tsofaffi suke da amfani a ƙungiyar Jehobah? Mene ne za mu yi don mu amfana daga misalinsu?

ME YA SA JEHOBAH YAKE ƊAUKAN TSOFAFFI MASU AMINCI DA DARAJA?

Tsofaffi masu aminci suna da daraja a gaban Jehobah da kuma bayinsa (Ka duba sakin layi na 3)

3. Bisa ga abin da ke Zabura 92:12-15, me ya sa tsofaffi masu aminci suke da daraja a gaban Jehobah?

3 Tsofaffi masu aminci suna da daraja a wurin Jehobah. Ya san da su sosai, kuma yana farin ciki domin halayensu masu kyau. Yana so tsofaffi su gaya wa matasa darussan da suka koya a rayuwa. (Ayu. 12:12; K. Mag. 1:1-4) Jehobah yana daraja su don yadda suka jimre. (Mal. 3:16) Sun fuskanci matsaloli da yawa, amma bangaskiyarsu ba ta yi sanyi ba. Yanzu suna daɗa sa rai ga alkawuran Allah fiye da yadda suka yi a lokacin da suka koyi gaskiya. Jehobah yana ƙaunar su domin suna kan yabon sunansa har yanzu da suka ‘tsufa.’​—Karanta Zabura 92:12-15.

4. Mene ne zai iya ƙarfafa ’yan’uwanmu da suka tsufa?

4 Idan ka riga ka soma tsufa, ka kasance da tabbaci cewa Jehobah yana tunawa da ayyuka masu kyau da ka yi a dā. (Ibran. 6:10) Alal misali, ka yi wa’azi da ƙwazo, kuma hakan ya sa Ubanmu na sama farin ciki. Ka jimre matsaloli, har da masu tsanani. Ka bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma ka koyar da su. Ƙari ga haka, ka yi ayyuka da yawa a ƙungiyar Jehobah kuma ka horar da ’yan’uwa. Ka yi iya ƙoƙarinka domin ka bi canje-canje da ƙungiyar Jehobah ta yi. Ka ƙarfafa da kuma taimaka ma ’yan’uwa da ke hidima ta cikakken lokaci. Jehobah yana ƙaunar ka sosai domin amincinka. Ya yi alkawari cewa “ba zai ƙyale masu ƙaunarsa ba”! (Zab. 37:28) Ga alkawarin da ya yi maka, cewa: ‘Har zuwa lokacin furfurarka, ni ne zan ɗauki nauyinka.’ (Isha. 46:4) Kar ka ɗauka cewa domin ka tsufa, ba ka da amfani a ƙungiyar Jehobah. Kana da daraja sosai!

TSOFAFFI SUNA DA MUHIMMANCI A ƘUNGIYAR JEHOBAH

5. Mene ne ya dace waɗanda suka tsufa su tuna?

5 Akwai abubuwa da yawa da tsofaffi za su iya yi a ƙungiyar Jehobah. Ko da yake a yanzu mai yiwuwa ba su da ƙarfi kamar a dā, akwai abubuwa da yawa da suka sani. Jehobah zai iya ci gaba da amfani da su kamar yadda za mu gani a misalan mutanen dā da na yanzu.

6-7. Ka ba da misalin tsofaffi a Littafi Mai Tsarki da aka yi musu albarka domin amincinsu.

6 A Littafi Mai Tsarki, akwai misalan mutane da suka ci gaba da yi wa Jehobah hidima har suka tsufa. Alal misali, Musa ya kai wajen shekara 80 sa’ad da ya soma hidima a matsayin annabin Jehobah, da kuma shugaban da Jehobah ya zaɓa ma Isra’ilawa. Jehobah ya ci gaba da amfani da Daniyel a matsayin kakakinsa, har a lokacin da annabin ya fi shekara 90. Kuma da alama manzo Yohanna ya fi shekara 90 sa’ad da Jehobah ya hure shi ya rubuta littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna.

7 Akwai tsofaffi masu aminci da yawa a zamanin dā da mai yiwuwa mutane ba su san da su sosai ba. Duk da haka, Jehobah ya lura da su kuma ya ba su lada domin amincinsu. Alal misali, abubuwan da aka rubuta a cikin Littafi Mai Tsarki game da Simeyon, wani “mutum mai adalci . . . , mai bautar Allah” ba su da yawa. Amma Jehobah ya lura da shi, ya ba shi gatan ganin Yesu a lokacin da yake jariri da kuma yin annabci game da Yesu da mahaifiyarsa. (Luk. 2:22, 25-35) Ban da haka, ka yi tunanin gwauruwar nan, annabiya Hannatu. Duk da cewa shekarunta 84, “ba ta barin Haikali.” Jehobah ya albarkace ta domin tana zuwa haikali a kai a kai. Ya bar ta ita ma ta ga Yesu a lokacin da yake jariri. Jehobah ya ɗauki Simeyon da Hannatu da daraja sosai.​—Luk. 2:36-38.

’Yar’uwa Didur wadda ta fi shekara 80 yanzu, tana kan bauta wa Jehobah da aminci (Ka duba sakin layi na 8)

8-9. Mene ne wata ’yar’uwa ta yi a ƙungiyar Jehobah sa’ad da ta zama gwauruwa?

8 A zamaninmu, tsofaffi masu aminci suna kafa misali mai kyau wa matasa. Ga misalin wata ’yar’uwa mai suna Lois Didur. Tana ’yar shekara 21 a lokacin da ta soma yin hidimar majagaba na musamman a Kanada. Bayan haka, ita da mijinta mai suna John sun yi shekaru da yawa suna hidimar mai kula mai ziyara. Daga baya sun yi fiye da shekara 20 suna yin hidima a Bethel na Kanada. A lokacin da Lois take shekara 58, an ce ita da mijinta su je hidima a ƙasar Yukiren. Me za su yi? Za su ce sun tsufa sosai kuma ba za su iya ƙaura zuwa wata ƙasa ba ne? Sun yarda su yi hidimar, kuma aka naɗa John memban Kwamitin da Ke Kula da Ofishinmu a ƙasar. Bayan shekaru bakwai, John ya rasu, amma Lois ta ci gaba da hidimarta. Yanzu shekarun Lois 81, kuma tana kan bauta wa Jehobah da aminci a Bethel na Yukiren. Tana aiki da ƙwazo kuma ’yan’uwa suna ƙaunar ta sosai.

9 An fi lura da ayyukan da gwauraye kamar Lois suke yi a lokacin da mazajensu suke da rai. Duk da haka, rasuwar mazajensu ba ta rage darajarsu. Jehobah yana daraja ’yan’uwa mata da suka yi shekaru da yawa suna taimaka wa mazansu, kuma suna kan bauta wa Jehobah da aminci har yanzu. (1 Tim. 5:3) Ƙari ga haka, ’yan’uwan nan suna ƙarfafa matasa.

10. Wane misali mai kyau ne Tony ya kafa?

10 Akwai tsofaffi da yawa da ba sa iya barin gidajensu. Su ma suna da daraja sosai. Alal misali, wani ɗan’uwa mai suna Tony yana zama a gidan da ake kula da tsofaffi. Ya yi baftisma a Pennsylvania a Amirka a watan Agusta na 1942. A lokacin yana ɗan shekara 20. Ba da daɗewa ba bayan ya yi baftisma, sai aka tilasta masa ya shiga soja. Da ya ƙi, sai aka saka shi a kurkuku na tsawon shekaru biyu da rabi. Shi da matarsa mai suna Hilda sun yi renon yara biyu da suke bauta wa Jehobah yanzu. Tony ya yi hidima a matsayin dattijo mai shugabanci (yanzu, dattijo da ke wannan hidimar ana kiransa mai tsara ayyukan rukunin dattawa) a ikilisiyoyi uku, da kuma hidimar mai kula da taron da’ira. Yakan je kurkuku ya gudanar da taron ikilisiya kuma ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da fursunoni. Duk da cewa Tony ya kai shekara 98 yanzu, yana kan yi wa Jehobah hidima. Yana yin iya ƙoƙarinsa ya bauta wa Jehobah tare da ’yan’uwa maza da mata a ikilisiyarsu!

11. Ta yaya za mu nuna cewa muna daraja tsofaffin da ba sa iya barin gidajensu?

11 Ta yaya za mu daraja tsofaffi da ba sa iya barin gidajensu? A duk lokacin da zai yiwu, zai dace dattawa su taimaka musu su halarci taro ko su saurari taro kuma su yi wa’azi. Za mu iya nuna cewa mun damu da su ta wajen ziyartarsu ko kuma kiransu ta bidiyo. Zai dace mu mai da hankali sosai ga tsofaffi da suke zama nesa da ikilisiyarsu. Idan ba mu mai da hankali ba, za mu iya mance da waɗannan tsofaffin. Yakan yi wuya ma wasu daga cikinsu su yi magana game da kansu. Amma za mu amfana sosai idan muka yi musu tambaya kuma muka saurare su yayin da suke gaya mana abubuwan da suka cim ma a ƙungiyar Jehobah.

12. Waɗanne irin ’yan’uwa ne za mu iya samu a ikilisiyarmu?

12 Zai iya ba mu mamaki mu ga cewa akwai tsofaffi a ikilisiyarmu da suke da labarai masu ban ƙarfafa sosai. Wata ’yar’uwa mai suna Harriette ta yi shekaru da yawa tana bauta wa Jehobah a ikilisiyarsu da ke jihar New Jersey a Amirka. Sai ta ƙaura don ta zauna da ’yarta. ’Yan’uwa a sabuwar ikilisiyar sun ƙoƙarta su kusace ta kuma suka gano cewa ita mai bangaskiya ce sosai. Ta ƙarfafa su da labaran yadda ake wa’azi a lokacin da ta koyi gaskiya, a wajen shekara ta 1925. A lokacin, takan ɗauki buroshi a jakarta domin ta sami abin goge haƙora idan ’yan sanda suka kama ta. An kama ta sau biyu a shekara ta 1933, kuma sau biyun, ta yi mako ɗaɗɗaya a kurkuku. A duk lokacin da aka kama ta, mijinta da ba Mashaidi ba yakan kula da yaransu uku. Hakika, tsofaffi masu aminci kamar Harriette sun cancanci mu daraja su!

13. Me muka koya game da yadda tsofaffi suke da daraja a ƙungiyar Jehobah?

13 ’Yan’uwa tsofaffi suna da daraja sosai a ƙungiyar Jehobah. Sun ga hanyoyi da yawa da Jehobah ya nuna cewa ya amince da su da kuma ƙungiyarsa. Sun koyi darussa da yawa daga kurakuransu. Ka ɗauki tsofaffin nan a matsayin “maɓuɓɓugar hikima,” kuma ka koyi abubuwa daga wurinsu. (K. Mag. 18:4) Idan ka ɗauki lokaci don ka koya game da su, za ka iya ƙarfafa bangaskiyarka kuma za ka koyi abubuwa da yawa!

KA AMFANA DAGA MISALIN TSOFAFFI

Kamar yadda Elisha ya amfana daga yin tarayya da Iliya, haka ma ’yan’uwa za su iya amfana daga labaran waɗanda suka daɗe suna bauta wa Jehobah (Ka duba sakin layi na 14-15)

14. Mene ne littafin Maimaitawar Shari’a 32:7 ya ƙarfafa matasa su yi?

14 Ka yi ƙoƙari ka riƙa tattaunawa da tsofaffi. (Karanta Maimaitawar Shari’a 32:7.) Mai yiwuwa ba sa iya gani da kyau, ko sun soma tafiya a hankali, ko kuma muryarsu ba ta da ƙarfi kamar a dā. Amma har ila suna so su yi ayyuka da yawa a ƙungiyar Jehobah, kuma suna da “suna mai kyau” a gaban shi. (M. Wa. 7:1) Ka tuna abin da ya sa Jehobah yake ɗaukansu da daraja kuma ka ci gaba da girmama su. Ka yi koyi da Elisha. A rana ta ƙarshe da Iliya ya yi tare da shi, Elisha ya nace cewa ba zai bar Iliya ba. Sau uku Elisha ya ce: “Ba zan bar ka ba.”​—2 Sar. 2:2, 4, 6

15. Waɗanne tambayoyi ne za mu iya yi wa tsofaffi?

15 Ka nuna ka damu da tsofaffi ta wajen yi musu tambayoyi don ka san abin da ke zuciyarsu. (K. Mag. 1:5; 20:5; 1 Tim. 5:1, 2) Ka yi musu tambayoyi kamar: “Me ya tabbatar maka cewa wannan ƙungiyar ce Jehobah yake amfani da ita?” “Ta yaya abubuwan da ka fuskanta sun sa ka kusaci Jehobah?” “Mene ne ya taimaka maka ka ci gaba da farin ciki yayin da kake bauta wa Jehobah?” (1 Tim. 6:6-8) Sai ka saurara yayin da suke ba ka labarinsu.

16. Ta yaya tsofaffi da matasa za su amfana idan suna tattaunawa da juna?

16 Idan tsofaffi da matasa suna tattaunawa, dukansu za su amfana. (Rom. 1:12) Hakan zai sa matasa su daɗa godiya domin yadda Jehobah yake kula da bayinsa masu aminci, kuma tsofaffi za su ga cewa ana ƙaunar su. Zai ji daɗin gaya maka yadda Jehobah ya yi masa albarka.

17. Me ya sa za mu iya ce ’yan’uwa tsofaffi suna daɗa kyau da shigewar shekaru?

17 Kyaun fuska takan ragu yayin da mutum yake tsufa, amma waɗanda suka riƙe aminci suna daɗa kyau a idon Jehobah yayin da suke tsufa. (1 Tas. 1:2, 3) Me ya sa hakan gaskiya ne? Domin da shigewar lokaci, sun bar ruhu mai tsarki ya horar da su kuma ya taimaka musu su kasance da halaye masu kyau. Yayin da muke daɗa sanin ’yan’uwanmu tsofaffi maza da mata kuma muke koyan abubuwa daga wurinsu, za mu daɗa girmama su kuma mu ɗauke su da daraja!

18. Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

18 ’Yan’uwa a ikilisiya za su daɗa kusantar juna idan matasa da tsofaffi suna daraja juna. A talifi na gaba, za mu tattauna yadda tsofaffi za su nuna cewa suna daraja matasa a ikilisiya.

WAƘA TA 144 Mu Riƙa Ɗokin Samun Ladan!

^ sakin layi na 5 ’Yan’uwanmu tsofaffi suna da daraja sosai. A wannan talifin, za mu tattauna yadda za mu daɗa daraja su, mu ƙauna ce su da kuma yadda za mu amfana daga hikimarsu. Ƙari ga haka, talifin zai tabbatar wa ’yan’uwanmu tsofaffi cewa suna da muhimmanci a ƙungiyar Jehobah.