Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 38

WAƘA TA 25 Mutane Masu Daraja

Kana Bin Gargadin Yesu?

Kana Bin Gargadin Yesu?

“Za a ɗauki ɗaya a bar ɗaya.”MAT. 24:40.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu bincika misalai uku da Yesu ya bayar don mu ga abin da suka koya mana game da shariꞌar da za a yi a ƙarshen zamanin nan.

1. Mene ne Yesu zai yi nan ba da daɗewa ba?

 MUNA rayuwa a lokaci mai muhimmanci! Nan ba da daɗewa ba, Yesu zai shariꞌanta dukan mutane. Yesu ya gaya mana abin da zai faru kafin ya yi shariꞌar. Ya gaya wa almajiransa abin da zai zama ‘alamar dawowarsa da kuma ta ƙarshen zamani?’ (Mat. 24:3) An bayyana alamar nan a Matiyu sura 24 da 25 da Markus sura 13 da kuma Luka sura 21.

2. Me za mu tattauna a wannan talifin, kuma ta yaya hakan zai taimaka mana?

2 Yesu ya ba da misalai uku, kuma a cikin kowannensu, akwai gargaɗin da ya yi mana. Misalan su ne na tumaki da awaki, da na ꞌyan mata masu hikima da wawaye, da kuma na talanti. Kowane misali ya nuna mana yadda ayyukan mutum za su shafi hukuncin da za a yi masa. Za mu bincika waɗannan misalan. Yayin da muke hakan, zai dace mu lura da darussan da ke cikinsu, da yadda za mu bi abin da muka koya. Bari mu fara da misalin tumaki da awaki.

TUMAKI DA AWAKI

3. Wane lokaci ne Yesu zai yi shariꞌa?

3 A misalin tumaki da awaki, Yesu ya ce za a yi wa mutane shariꞌa ne bisa ga yadda suka karɓi waꞌazin da aka yi musu da yadda suka goyi bayan ꞌyanꞌuwansa shafaffu. (Mat. 25:​31-46) Yesu zai yi shariꞌar nan a lokacin “azaba mai zafi,” wato ƙunci mai girma, kafin yaƙin Armageddon. (Mat. 24:21) Kamar yadda makiyayi yake ware tumaki daga awaki, haka Yesu zai ware waɗanda suka goyi bayan ꞌyanꞌuwansa shafaffu daga waɗanda ba su yi hakan ba.

4. Bisa ga Ishaya 11:​3, 4, me ya tabbatar mana da cewa Yesu zai yi shariꞌar gaskiya? (Ka kuma duba hoton.)

4 Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa Yesu zai yi shariꞌar gaskiya a matsayin alƙalin da Jehobah ya zaɓa. (Karanta Ishaya 11:​3, 4.) Yana lura da abubuwan da mutane suke yi, da tunaninsu, da abubuwan da suke faɗa, da kuma yadda suke shaꞌani da ꞌyanꞌuwansa shafaffu. (Mat. 12:​36, 37; 25:40) Yesu ya san waɗanda suka goyi bayan ꞌyanꞌuwansa shafaffu da kuma ayyukansu. a Wata muhimmiyar hanya da mutum zai goyi bayan shafaffu ita ce, ta wurin yin waꞌazi. Waɗanda suka taimaka wa shafaffu za a ce da su “masu adalci,” kuma za su sami “rai na har abada” a duniya. (Mat. 25:46; R. Yar. 7:​16, 17) Hakika, wannan ba ƙaramin lada ba ne! Idan kuma suka ci-gaba da riƙe aminci, za a bar sunayensu a “Littafin Rai.”—R. Yar. 20:15.

Nan ba da daɗewa ba, Yesu zai yi shariꞌa. Zai nuna ko su wane ne tumaki ko awaki (Ka duba sakin layi na 4)


5. Wane darasi ne za mu iya koya daga misalin tumaki da awaki, kuma su wa za su iya amfana?

5 Ka kasance da aminci. Da Yesu ya ba da misalin tumaki da awaki, yana magana ne game da waɗanda suke sa ran yin rayuwa a duniya. Za su nuna amincinsu ta wurin yin waꞌazi da kuma bin ja-gorancin bawan nan mai aminci mai hikima, da Yesu ya zaɓa. (Mat. 24:45) Amma masu begen yin rayuwa a sama su ma suna bukata su bi gargaɗin da Yesu ya yi a wannan misalin. Me ya sa? Domin Yesu yana lura da ayyukansu da tunaninsu da kuma abin da suke faɗa. Wajibi ne su ma su kasance da aminci. Yesu ya ba da wasu misalai biyu don ya gargaɗi shafaffun Kiristoci. Misalan nan suna Matiyu sura 25. Bari mu tattauna ɗaya daga cikinsu, wato misalin ꞌyan mata masu hikima da wawaye.

ꞌYAN MATA MASU HIKIMA DA WAWAYE

6. Ta yaya ꞌyan mata biyar suka nuna cewa su masu hikima ne? (Matiyu 25:​6-10)

6 A wannan misalin, Yesu ya yi magana game da ꞌyan mata guda goma da suke jiran zuwan wani ango. (Mat. 25:​1-4) Suna jiran angon ne don su raka shi zuwa wurin bikin aurensa. Yesu ya ce biyar daga cikin su “masu hikima ne,” biyar kuma “wawaye.” Masu hikimar sun zo a shirye. Sun yi shirin jiran angon ko da bai zo da wuri ba, har cikin dare. Shi ya sa suka riƙe fitilu da kuma isashen mai. Hakan ya nuna cewa sun yi shiri sosai. (Karanta Matiyu 25:​6-10.) Saꞌad da angon ya iso, sai ꞌyan mata masu hikiman suka bi shi zuwa wurin bikin. Yesu ne Angon. Kuma shafaffun Kiristoci da suka riƙe amincinsu har zuwan Yesu ne za su bi shi zuwa sama. b (R. Yar. 7:​1-3) Me ya faru da ꞌyan mata biyar wawayen?

7. Me ya faru da ꞌyan mata biyar wawayen, kuma me ya sa?

7 ꞌYan mata biyar wawayen ba su kasance a shirye kamar yadda masu hikiman suka yi ba. Fitilunsu sun kusan mutuwa kuma ba su zo da isashen mai ba. Da suka ji cewa angon ya kusan zuwa, sai suka je sayan mai. Kafin su dawo, angon ya riga ya iso. Sai “waɗanda suke a shirye kuma suka shiga wurin bikin da shi, aka kuma rufe ƙofa.” (Mat. 25:10) Da ꞌyan mata wawayen suka dawo kuma suka zo za su shiga, sai angon ya ce: “Ban san ku ba.” (Mat. 25:​11, 12) Waɗannan ꞌyan matan ba su kasance a shirye su jira angon har sai lokacin da zai zo ba. Wane darasi ne ake koya wa shafaffu a wannan misalin?

8-9. Wane darasi ne shafaffu za su koya daga misalin ꞌyan matan? (Ka kuma duba hoton.)

8 Ka kasance a shirye har ƙarshe. Yesu ba ya nufin cewa shafaffu za su rabu kashi biyu, wasu su riƙe aminci har ƙarshe, wasu kuma su kasa yin hakan. A maimakon haka, yana bayyana abin da zai faru da shafaffu ne, idan ba su kasance a shirye don su riƙe amincinsu har ƙarshe ba. Hakan zai sa su rasa ladansu. (Yoh. 14:​3, 4) Ko da muna sa ran yin rayuwa a sama ne ko a duniya, yana da muhimmanci mu bi gargaɗin Yesu da ke misalin nan. Me ya sa? Domin wajibi ne mu kasance a shirye kuma mu jimre har ƙarshe.—Mat. 24:13.

9 Bayan da Yesu ya gama ba da misalin ꞌyan matan don ya nuna muhimmancin kasancewa da shiri har zuwa ƙarshe, sai ya ba da misalin talanti. Wannan misalin ya nuna muhimmancin zama masu ƙwazo.

Yana da muhimmanci mu bi gargaɗin da Yesu ya yi mana a misalin ꞌyan mata goma, ta wajen kasancewa a shirye don mu jimre har ƙarshe (Ka duba sakin layi na 8-9)


TALANTI

10. Ta yaya bayi biyun suka nuna cewa su masu aminci ne? (Matiyu 25:​19-23)

10 A misalin talantin, Yesu ya ce wasu bayi biyu sun kasance da aminci ga maigidansu, amma ɗaya bai yi hakan ba. (Mat. 25:​14-18) Kafin maigidansu ya yi tafiya, ya ba su kuɗi mai yawa. Ta yaya bayi biyun suka nuna cewa su masu aminci ne? Ta wajen yin aiki tuƙuru don su yi riba. Sun yi aiki da ƙwazo kuma sun yi amfani da kuɗin a hanyar da ta dace. Shi ya sa da maigidansu ya dawo, sai ya ga cewa sun ninka kuɗin da ya ba su. Ya yaba musu kuma ya ce musu su zo su yi murna tare da shi. (Karanta Matiyu 25:​19-23.) Bawa na ukun kuma fa? Me ya yi da kuɗin da maigidansa ya ba shi?

11. Me ya faru da bawan nan mai “ƙyuya,” kuma me ya sa?

11 An ba wa bawa na ukun talanti ɗaya, amma shi mai “ƙyuya” ne. Maigidansa ya zata zai yi amfani da shi har ya sami riba. Amma maimakon haka, ya tona rami ya ɓoye kuɗin a ciki. Saꞌad da maigidan ya dawo, sai ya mayar masa da kuɗin. Bawan nan bai da kirki. Maimakon ya ba wa maigidansa haƙuri don bai nemi riɓa da kuɗin da aka ba shi ba, ya ce maigidansa yana da “wuyar shaꞌani.” Maigidansa bai ji daɗin abin da ya yi ba. Kuma ya kwace kuɗin, saꞌan nan ya kori bawan daga gidansa.—Mat. 25:​24, 26-30.

12. Su waye ne bayi biyu masu aminci suke wakilta?

12 Bayi biyu masu amincin suna wakiltar shafaffun Kiristoci masu aminci. Maigidan kuma, shi ne Yesu. Ya ce musu, ‘ku zo ku yi murna tare da ni.’ Hakan yana nufin cewa ya ba su ladansu na yin rayuwa a sama. Sun amfana daga tashin matattu na farko ke nan. (Mat. 25:​21, 23; R. Yar. 20:5b) Amma abin da ya faru da bawan nan mai ƙyuya, gargaɗi ne ga shafaffun Kiristoci. Me ya sa muka ce haka?

13-14. Wane darasi ne Yesu yake koya wa shafaffu a misalin talanti? (Ka kuma duba hoton.)

13 Ka kasance da ƙwazo. Da Yesu ya ba da misalin talanti da na ꞌyan mata goma, ba wai yana nufin cewa shafaffu za su zama masu ƙyuya ba ne. Amma yana bayyana abin da zai faru da su ne idan suka daina kasancewa da ƙwazo. Hakan zai sa ba za su ‘tabbatar da kiransu da zaɓansu’ da Allah ya yi ba. Ƙari ga haka, ba za su shiga Mulkin sama ba.—2 Bit. 1:10.

14 Misalin da Yesu ya bayar game da ꞌyan mata goma da na talanti sun nuna cewa yana da muhimmanci shafaffun Kiristoci su ci-gaba da kasancewa a shirye har ƙarshe kuma su zama masu ƙwazo. Ban da waɗannan, akwai wani gargaɗi da Yesu ya yi wa shafaffun Kiristoci kuwa? Ƙwarai kuwa! Abin da Yesu ya faɗa a Matiyu 24:​40, 41 shi ma gargaɗi ne ga shafaffu.

Yesu yana so shafaffun Kiristoci su yi hidimarsu da ƙwazo (Ka duba sakin layi na 13-14) d


WA ZA A ƊAUKA?

15-16. Ta yaya Matiyu 24:​40, 41 za su taimaka wa shafaffu su zauna da shiri?

15 Kafin Yesu ya ba da misalai uku da muka tattauna, ya yi magana a kan abin da zai faru a lokacin da zai shariꞌanta shafaffun Kiristoci. Ya yi amfani da maza biyu masu aiki a gona da mata biyu masu niƙa don ya kwatanta abin da zai faru. Aiki iri ɗaya mazan suke yi, matan ma aiki iri ɗaya suke, amma Yesu ya ce “za a ɗauki ɗaya a bar ɗaya.” (Karanta Matiyu 24:​40, 41.) Sai ya gargaɗi mabiyansa cewa: “Ku zauna da shiri, gama ba ku san ranar da Ubangijinku zai dawo ba.” (Mat. 24:42) Yesu ya yi irin gargaɗin nan bayan da ya ba da misalin ꞌyan mata goma. (Mat. 25:13) Da alama cewa darasi ɗaya ne Yesu yake so ya koya wa almajiransa a wurare biyun nan. Wato, shafaffu da suka kasance da aminci ne kaɗai zai ɗauka ya kai su sama.—Yoh. 14:3.

16 Ka zauna da shiri. Lokacin da Yesu zai zo ya tattara “waɗanda aka zaɓa,” ba zai ɗauki duk wani shafaffe da bai zauna da shiri ba. (Mat. 24:31) Ya kamata duka bayin Allah su ɗauki gargaɗin Yesu da muhimmanci, wato su zauna da shiri kuma su riƙe aminci. Ko da suna sa ran yin rayuwa a sama ne ko a duniya.

17. Me ya sa bai kamata mu damu da lokacin da Jehobah ya zaɓi mutum ya zama shafaffe ba?

17 Muna da tabbaci cewa duk abin da Jehobah ya yi daidai ne. Don haka, ko da Jehobah ya zaɓi wasu Kiristoci su zama shafaffu a zamaninmu, ba za mu damu ba. c Mun san abin da Yesu ya faɗa game da maꞌaikatan da aka kira su su yi aiki a gonar inabi wajen ƙarfe biyar na yamma. (Mat. 20:​1-16) Akwai wasu da suka soma aiki a gonar tun da safe, wasu kuma da rana, amma abin da aka biya su ɗaya ne da waɗanda suka zo da yamma. Don haka, ko da wane lokaci ne aka zaɓi mutum ya zama shafaffe, idan ya kasance da aminci har ƙarshe, zai sami ladan shiga Mulkin sama.

KA BI GARGAƊIN

18-19. Me muka koya daga misalan da muka tattauna?

18 Me muka tattauna a wannan talifin? Mun ga cewa misalin Yesu game da tumaki da awaki, musamman don waɗanda suke sa ran yin rayuwa a duniya ne. Ya nuna cewa suna bukatar su ci-gaba da riƙe amincinsu, har lokacin ƙunci mai girma. Kafin a soma yaƙin Armageddon, Yesu zai yi shariꞌa kuma zai ba ma waɗanda suka riƙe amincinsu “rai na har abada.”—Mat. 25:46.

19 Mun kuma bincika misalai biyu da suka zama gargaɗi ga shafaffun Kiristoci. A misalin ꞌyan mata goma da Yesu ya bayar, biyar sun nuna cewa su masu hikima ne. Ta yaya? Ta wurin kasancewa a shirye su jira angon har sai lokacin da zai zo. Amma ꞌyan mata wawayen ba su zo da shirin jiransa haka ba. Saboda haka, angon ya hana su shiga wurin bikin aurensa. Wajibi ne mu ma mu kasance a shirye don mu jira har lokacin da Yesu zai kawo ƙarshen zamanin nan. Kuma a misalin talanti, mun ga cewa bayi biyu sun kasance da ƙwazo sosai. Sun yi aiki tuƙuru da kuɗin maigidansu don su sami riba, kuma maigidan ya yaba musu. Amma ya kori bawa mai ƙyuyan. Mene ne darasin? Muna bukatar mu ci-gaba da yin hidimarmu da ƙwazo har ƙarshe. Bayan haka, mun ga cewa shafaffu suna bukata su zauna da shiri har ƙarshe. Abin da zai sa Yesu ya ɗauke su zuwa sama ke nan. Waɗannan shafaffun suna marmarin lokacin da za a “tattara” su zawa wurin Yesu a sama. Bayan yaƙin Armageddon, za su zama amarya a bikin auren Ɗan Ragon, wato, Yesu.—2 Tas. 2:1; R. Yar. 19:​7, 9.

20. Mene ne Jehobah zai yi wa waɗanda suka bi gargaɗin da Yesu ya yi mana?

20 Lokacin shariꞌar ya kusa, amma bai kamata mu ji tsoro ba. Idan muka riƙe amincinmu, Ubanmu mai ƙauna zai ba mu “cikakken ikon da ya fi duka” domin mu “sami ƙarfin” tsayawa “a gaban Ɗan Mutum,” wato Yesu. (2 Kor. 4:7; Luk. 21:36) Ko da muna sa ran yin rayuwa a duniya ne ko a sama, idan muka bi gargaɗin da Yesu ya yi mana a misalan nan, Jehobah zai amince da mu. Jehobah mai alheri ne sosai. Don haka, zai ‘rubuta sunanmu a cikin littafin’ rai.—Dan. 12:1; R. Yar. 3:5.

WAƘA TA 26 Kun Yi Domin Ni

a Ka duba talifin nan, “Me Muka Sani Game da Yadda Jehobah Zai Shariꞌanta Mutane a Nan Gaba?” a Hasumiyar Tsaro ta Mayu 2024.

b Don ƙarin bayani, ka duba talifin nan, “Ka Ci Gaba da ‘Yin Tsaro!’” a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Maris, 2015.

d BAYANI A KAN HOTUNA: Wata ꞌyarꞌuwa da take cikin shafaffu tana nazari da wata mata da ta same ta a lokacin da take waꞌazi.