TALIFIN NAZARI NA 36
WAƘA TA 89 Mu Ji, Mu Yi Biyayya Don Mu Sami Albarka
“Ku Zama Masu Aikata Kalmar Allah”
“Ku zama masu aikata kalmar Allah, ba masu ji kawai ba.”—YAK. 1:22.
ABIN DA ZA MU KOYA
Talifin nan zai sa mu ƙara yin marmarin karanta Kalmar Allah kowace rana, mu yi tunani a kan abin da muka karanta, kuma mu bi shi a rayuwarmu.
1-2. Me ya sa bayin Allah suke farin ciki? (Yakub 1:22-25)
JEHOBAH da Ɗansa Yesu suna so mu yi farin ciki. Marubucin Zabura ta 119:2 ya ce: “Masu albarka [farin ciki] ne masu kiyaye ƙaꞌidodinsa, masu nemansa da dukan zuciyarsu.” Yesu ma ya ƙara tabbatar mana cewa farin ciki ya “fi tabbata ga waɗanda suke jin kalmar Allah, suke kuma kiyaye ta!”—Luk. 11:28.
2 An san Shaidun Jehobah da yin farin ciki. Me ya sa? Akwai dalilai da dama. Amma wani dalili mai muhimmanci shi ne, don muna karanta Kalmar Allah a-kai-a-kai kuma muna ƙoƙarin bin abin da muke koya.—Karanta Yakub 1:22-25.
3. Wane amfani za mu samu idan muna bin abin da muke koya daga Kalmar Allah?
3 Idan muka zama masu “aikata kalmar Allah,” za mu amfana a hanyoyi da dama. Alal misali, Jehobah yana jin daɗi idan ya ga muna bin abin da yake koya mana, don haka mu ma muna farin ciki. (M. Wa. 12:13) Bin abin da muke koya daga Kalmar Allah zai sa mu zauna lafiya a iyalinmu, kuma zumuncin da ke tsakaninmu da ꞌyanꞌuwa a ikilisiya zai ƙaru. Ƙari ga haka, zai taimake mu kada mu shiga irin matsalolin da mutanen da ba sa bin dokokin Jehobah suke fama da su. Ba mamaki kai ma ka shaida hakan a rayuwarka. Shi ya sa da Sarki Dauda yake magana a kan koyarwar Jehobah da ƙaꞌidodinsa da kuma umurnansa, ya kammala da cewa: “Ta wurin kiyaye su akwai lada mai yawa.”—Zab. 19:7-11.
4. Me ya sa wani lokaci yana da wuya mu karanta Kalmar Allah kuma mu bi abin da muka koya?
4 A gaskiya, ba koyaushe ba ne yake da sauƙi mutum ya karanta Kalmar Allah kuma ya bi abin da ya koya. Muna da ayyuka da yawa, saboda haka wajibi ne mu nemi lokacin karanta Littafi Mai Tsarki don mu san abin da Jehobah yake so mu yi. Bari mu tattauna wasu abubuwan da za su taimaka mana mu riƙa karanta Kalmar Allah babu fashi. Za mu kuma ga abin da zai taimaka mana mu yi tunani a kan abin da muka karanta kuma mu san yadda za mu bi shi.
KA KEƁE LOKACI DON KARATUN LITTAFI MAI TSARKI
5. Waɗanne abubuwa ne suke cin lokacinmu sosai?
5 Yawancin bayin Jehobah suna da ayyukan yi da dama. Muna amfani da lokaci sosai wajen yin abubuwa masu muhimmanci. Alal misali, yawancinmu muna yin aiki don mu biya bukatunmu da na ꞌyan iyalinmu. (1 Tim. 5:8) Da yawa daga cikinmu kuma suna kula da danginsu da ba su da lafiya ko sun tsufa. Muna kuma bukatar mu kula da lafiyarmu, kuma hakan yana ɗaukan lokaci. Ban da waɗannan, muna da ayyukan yi a ikilisiya. Wani aiki mai muhimmanci kuma shi ne yin waꞌazi, kuma ya kamata mu yi shi da ƙwazo. Duk da cewa muna da ayyuka da yawa, ta yaya za ka sami lokacin karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana, da yin tunani a kai, da kuma bin abin da ka koya?
6. Me zai taimaka maka ka riƙa karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana? (Ka kuma duba hoton.)
6 Karanta Littafi Mai Tsarki yana cikin abubuwan da suka fi muhimmanci a rayuwar Kirista. Don haka muna bukatar mu tabbata cewa muna yin sa. (Filib. 1:10) Zabura ta ɗaya ta ce mutum zai yi farin ciki idan “yana jin daɗin dokar Jehobah, yana karanta da kuma tunani a kai dare da rana.” (Zab. 1:1, 2, NWT) Wannan ya nuna cewa muna bukatar mu keɓe lokaci don karatun Littafi Mai Tsarki. Amma wane lokaci ne zai fi kyau ka karanta Littafi Mai Tsarki? Kowa yana da lokacin da zai fi dacewa da shi. Abin da ya fi muhimmanci shi ne ka zaɓi lokacin da za ka iya yin karatun babu fashi. Wani ɗanꞌuwa mai suna Victor ya ce: “Na fi so in yi karatun Littafi Mai Tsarki da safe. Ko da yake tashiwa da sassafe ba ya min sauƙi, na fi son shi, don ba abubuwan raɓa hankali sosai a lokacin. Yana min sauƙi in mai da hankali a kan abin da nake karantawa.” Wataƙila kai ma abin da ka fi so ke nan? Ka tambayi kanka, ‘Wane lokaci ne zai fi min sauƙi in karanta Littafi Mai Tsarki?’
KA YI TUNANI A KAN ABIN DA KA KARANTA
7-8. Me zai iya hana mu amfana daga karatun Littafi Mai Tsarki? Ka ba da misali.
7 A wasu lokuta, mukan karanta abubuwa da yawa kuma mu kasa tuna da abin da muka karanta. Ka taɓa yin karatu amma jim kaɗan bayan haka ka kasa tuna abin da ka karanta? Abu ne da ke faruwa da dukanmu. Abin baƙin cikin shi ne, hakan zai iya faruwa saꞌad da muka karanta Littafi Mai Tsarki. Alal misali, wataƙila mu ce za mu riƙa karanta wasu surori kowace rana. Hakan yana da kyau. Ya kamata mutum ya zama da burin yin abu kuma ya yi ƙoƙarin yin sa. (1 Kor. 9:26) Amma fa, idan muna so mu amfana sosai daga karatun Littafi Mai Tsarki, ba karatu kawai za mu yi ba, akwai wani abu kuma da muke bukatar mu yi.
8 Ga wani misali: Duk wani abin da aka shuka yana bukatar ruwa. Amma idan aka yi ruwan sama da yawa cikin ƙanƙanin lokaci, ba wuya ruwan ya yi yawa a ƙasa. Idan aka ci-gaba da yin ruwan, ba zai shiga ƙasa ba, kuma ba zai amfani abin da aka shuka ba. Abin da zai fi shi ne ruwan ya riƙa zubowa a hankali, don ƙasa ta samu ta shanye kuma abin da aka shuka ya amfana. Haka yake da karatun Littafi Mai Tsarki. Kada mu karanta shi sama-sama kuma da wuri yadda ba za mu iya yin tunani a kai ba. Idan ba mu yi hakan ba, zai yi mana sauƙi mu tuna abin da muka karanta kuma mu yi amfani da shi.—Yak. 1:24.
9. Me ya kamata mu yi idan mun lura cewa muna karanta Littafi Mai Tsarki sama-sama kuma da wuri?
9 Kana ganin a wasu lokuta kai ma kana karanta Littafi Mai Tsarki sama-sama kuma da wuri? Idan haka ne, me ya kamata ka yi? Ka yi karatun a hankali, don ka iya yin tunani a kan abin da kake karantawa, ko ka yi tunani a kansa bayan ka gama karatun. Hakan abu ne da za ka iya yi. Wataƙila idan ka ƙara tsawon lokacin da ka keɓe na yin nazari don ka sami lokacin yin tunani, hakan zai taimaka. Ko kuma ka rage yawan ayoyin da kake karantawa, sai ka yi amfani da sauran lokacin ka yi tunani a kan abin da ka karanta. Victor da muka ambata a baya ya ce: “Ayoyi kaɗan nake karantawa, wani lokaci, sura ɗaya kawai. Kuma da yake da sassafe nake yin karatun, ina iya yin tunani a kan abin da na karanta yayin da nake sauran ayyukana a ranar.” Kai ne za ka zaɓi yawan ayoyin da za ka karanta. Abin da ya fi muhimmanci shi ne ka yi karatun a hankali yadda za ka iya yin tunani a kan abin da ka karanta.—Zab. 119:97; Ka duba akwatin da ya ce, “ Tambayoyin da Za Su Taimaka.”
10. Ka ba da misalin da ya nuna yadda za mu yi tunani don mu san yadda za mu bi abin da muka koya. (1 Tasalonikawa 5:17, 18)
10 Bayan ka karanta wasu ayoyi, yana da muhimmanci ka yi tunani a kan yadda za ka bi abin da ka koya. Idan ka karanta wani wuri a Littafi Mai Tsarki, ka tambayi kanka, ‘Ta yaya zan yi amfani da abin da na koya yanzu da kuma a nan gaba?’ Alal misali, a ce ka karanta 1 Tasalonikawa 5:17, 18. (Karanta.) Bayan ka karanta ayoyi biyun nan, zai dace ka dakata kuma ka yi tunani a kan yadda kake yin adduꞌa. Ka tambayi kanka, ‘Ina yawan yin adduꞌa kuwa? Ina yinsa da dukan zuciyata?’ Ƙari ga haka, zai yi kyau ka yi tunani a kan abubuwan da Allah ya yi maka. Ƙila kuma ka zaɓi abubuwa uku da za ka gode wa Jehobah dominsu. Ko da ꞌyan mintoci ne kawai ka ɗauka kana irin wannan tunanin, zai taimake ka ka fahimci Kalmar Allah kuma ka bi abin da ya ce. Idan kana karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana, kuma kana bin abin da ka koya, ba shakka, a-kwana-a-tashi za ka kyautata yadda kake bauta ma Jehobah. Amma me za ka yi idan ka ga cewa kana bukatar ka yi gyara a fannoni da dama a rayuwarka?
KA ZAƁI ABUBUWAN DA ZA KA IYA YI
11. Me zai iya sa ka yi sanyin gwiwa idan kana karanta Littafi Mai Tsarki? Ka ba da misali.
11 Idan kana karanta Littafi Mai Tsarki, wataƙila ka ga cewa kana bukatar ka yi gyara a fannoni da dama a rayuwarka, kuma hakan zai iya sa ka yi sanyin gwiwa. Alal misali: A ce inda ka karanta ran Litinin ya ce kada mu riƙa nuna bambanci. (Yak. 2:1-8) Sai ka ga cewa kana bukatar ka yi gyara a yadda kake shaꞌani da mutane, kuma ka ce za ka yi hakan. Ran Talata, ka karanta inda ya nuna cewa ya kamata mu lura da abin da muke faɗa. (Yak. 3:1-12) Kuma ka ga cewa akwai lokutan da ka yi maganganun da ba su dace ba. Don haka, ka ce za ka yi ƙoƙari ka riƙa yin maganganu da za su ƙarfafa mutane. Ran Laraba kuma sai ka karanta inda ya ce kada mu yi abota da mutanen duniyar nan. (Yak. 4:4-12) Kuma da ka yi tunani, sai ka ga cewa kana bukatar ka sake duba abubuwan da kake karantawa, da saurarawa, da kallo, kuma ka yi gyara. Wataƙila a ran Alhamis, za ka ji kamar ba za ka iya yin dukan gyare-gyaren nan a rayuwarka ba.
12. Idan kana karanta Littafi Mai Tsarki kuma ka ga cewa kana bukatar ka yi gyara sosai, me ya sa bai kamata ka yi sanyin gwiwa ba? (Ka kuma duba ƙarin bayani.)
12 Idan ka ga cewa kana bukatar yin gyare-gyare da yawa, kada ka fid da rai. Da yake ka ga cewa kana bukatar ka yi gyara, hakan ya nuna cewa kai mai sauƙin kai ne kuma kana so ka yi abin da ya dace. Idan mai sauƙin kai yana karatun Littafi Mai Tsarki, zai so ya ga inda zai yi gyara. a Kuma ka tuna cewa zama da “sabon halin nan” na Kirista, ba abu ne da ake yi a rana ɗaya ba. (Kol. 3:10) Me zai taimaka maka ka ci-gaba da aikata abin da kake koya daga Kalmar Allah?
13. Me zai taimaka maka ka iya yin gyare-gyaren da kake bukatar yi? (Ka kuma duba hoton.)
13 Maimakon ka yi ƙoƙarin yin duka gyare-gyaren a lokaci guda, ka zaɓi ɗaya ko biyu. (K. Mag. 11:2) Ka gwada rubuta duka gyare-gyaren da kake bukatar yi. Saꞌan nan ka zaɓi ɗaya ko biyu ka fara da su. Sauran kuma ka yi su daga baya. Da wanne za ka fara?
14. Wane gyara ne za ka iya fara yi?
14 Za ka iya farawa da gyaran da zai fi maka sauƙin yi. Ko kuma ka fuskanci wanda kake ganin ka fi bukata. Idan ka zaɓi gyaran da za ka yi, ka yi bincike game da shi a littattafanmu. Za ka iya yin amfani da Littafin Bincike don Shaidun Jehobah, ko Watch Tower Publications Index. Ka roƙi Jehobah ya ba ka niyya kuma ya sa ka iya aikata abin da ke zuciyarka. (Filib. 2:13) Bayan haka, ka yi ƙoƙarin yin gyaran. Idan ka ga cewa ka yi nasara wajen yin wannan gyaran, za ka sami ƙarfin yin wani kuma. Kuma wataƙila wannan gyara da ka yi zai sa yin sauran gyare-gyaren ya zo da sauƙi.
BARI KALMAR ALLAH TA YI ‘AIKI A ZUCIYARKA’
15. Mene ne bambancin bayin Jehobah da sauran mutanen da suke karanta Littafi Mai Tsarki? (1 Tasalonikawa 2:13)
15 Wasu mutane suna takama cewa sun karanta Littafi Mai Tsarki sau da yawa. Amma yawancinsu ba su gaskata abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa ba, ko kuma ba sa bin abin da ya faɗa a rayuwarsu. Ba haka bayin Jehobah suke ba! Kamar Kiristoci na farko, muna ɗaukan Littafi Mai Tsarki ‘ainihin yadda yake, wato Kalmar Allah.’ Ƙari ga haka, muna yin iya ƙoƙarinmu mu bi abin da ya ce.—Karanta 1 Tasalonikawa 2:13.
16. Me zai taimaka mana mu zama masu aikata abin da muke koya daga Kalmar Allah?
16 Wani lokaci bai da sauƙi mu karanta Kalmar Allah kuma mu bi abin da ta ce. Samun lokacin karatun zai iya mana wuya. Ƙila mu yi karatun sama-sama ko da wuri yadda ba za mu iya yin tunani a kan abin da muka karanta ba. Ƙila kuma mu ga cewa muna da gyara da yawa da ya kamata mu yi, kuma hakan ya sa mu yi sanyin gwiwa. Ko da wace matsala ce kake fuskanta dangane da karatun Littafi Mai Tsarki, za ka iya shawo kanta da taimakon Jehobah. Bari mu amince da taimakonsa don kada mu zama masu ji kawai mu manta, amma masu aikatawa. Ba shakka, idan muka ci-gaba da karanta Littafi Mai Tsarki muna bin abin da ya faɗa a rayuwarmu, za mu ƙara yin farin ciki.—Yak. 1:25.
WAƘA TA 94 Muna Godiya Jehobah Don Kalmarka
a Ka kalli bidiyon nan, Karatun Littafi Mai Tsarki, a jw.org/ha.