Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

SHAWARA A KAN YIN NAZARI

Ka Yi Shirin Koyan Sabon Abu

Ka Yi Shirin Koyan Sabon Abu

Idan muna shirin yin nazari, zai yi kyau mu kasance da manufa. Amma, mu tuna cewa ban da abin da muke da niyyar koya, Jehobah zai iya koya mana wasu abubuwa da ba mu zata ba. Don haka, ka yi shirin koyan sabon abu. Ta yaya za ka yi hakan?

Ka roƙi Jehobah ya ba ka hikima. Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka gane abin da yake so ya koya maka a lokacin. (Yak. 1:5) Kada ka dogara a kan abin da ka riga ka sani.—K. Mag. 3:​5, 6.

Ka bar Kalmar Allah ta ja-gorance ka. “Kalmar Allah tana da rai.” (Ibran. 4:12) Don haka, a duk lokacin da muka karanta Kalmar Allah za ta iya koya mana sabon abu, ko ta taimaka mana a wata hanya dabam. Amma hakan zai faru ne idan muna da niyyar koyan abin da Allah yake so ya koya mana.

Kada ka yi wasa da duk wani abin da Jehobah yake amfani da shi ya koyar da mu. Abubuwan da Jehobah yake koya mana dukansu kamar “abinci mafi kyau” ne. (Isha. 25:6) Saboda haka, kada ka guje ma wasu batutuwa da kana ganin ba za ka ji daɗin yin nazarinsu ba. Za su amfane ka, kuma za ka ji daɗinsu sosai!