Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 37

WAƘA TA 118 Ka “Ƙara Mana Bangaskiya”

Wasiƙa da Za Ta Taimake Mu Mu Jimre har Karshe

Wasiƙa da Za Ta Taimake Mu Mu Jimre har Karshe

“Mun tsaya da ƙarfi a kan amincewarmu ta fari har zuwa ƙarshe.”—IBRAN. 3:14.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu bincika wasiƙar da aka rubuta wa Ibraniyawa don mu ga abubuwan da za su taimaka mana mu riƙe aminci kuma mu jimre har ƙarshe.

1-2. (a) Wane hali ne Kiristoci da ke Yahudiya suke ciki lokacin da Bulus ya rubuta musu wasiƙa? (b) Me ya sa za mu ce wasiƙar ta zo daidai lokaci?

 BAYAN da Yesu ya mutu, Kiristoci da suke zama a Urushalima da Yahudiya sun sha wuya. A lokacin ne aka kafa ikilisiyar Kirista. Kuma ba da jimawa ba sai aka soma tsananta musu sosai. (A. M. 8:1) Wajen shekaru 20 bayan haka, mabiyan Yesu sun yi fama da yunwa da talauci. (A. M. 11:​27-30) Amma a wajen shekara ta 61 bayan haihuwar Yesu, abubuwa sun ɗan yi sauƙi, ko da yake ba da daɗewa ba za su fuskanci tsanantawa da ba su taɓa gani ba. A wannan lokacin ne Allah ya sa manzo Bulus ya rubuta musu wasiƙa. Wasiƙar ta taimaka musu su yi shiri don abin da ke zuwa.

2 Wasiƙar da manzo Bulus ya rubuta wa Ibraniyawa ta zo daidai lokaci, domin ba da daɗewa ba za su shiga cikin hali mai wuya sosai. Za a hallaka Urushalima da haikalinta kamar yadda Yesu ya annabta. (Luk. 21:20) Kuma wasiƙar tana ɗauke da shawarwarin da za su taimaka musu su jimre wahalar da za su sha. Bulus bai san daidai lokacin da halakar za ta zo ba, Ibraniyawan ma ba su sani ba. Amma kafin ta zo, Kiristocin nan za su iya yin shiri ta wurin yin abubuwan da za su sa su ƙara zama da bangaskiya da kuma jimiri.—Ibran. 10:25; 12:​1, 2.

3. Me ya sa muke bukatar mu bincika shawarwari da ke littafin Ibraniyawa?

3 Mu ma nan ba daɗewa ba za mu fuskanci wahalar da ta fi wanda Ibraniyawa Kiristocin suka fuskanta. (Mat. 24:21; R. Yar. 16:​14, 16) Don haka, bari mu bincika wasu shawarwarin da Jehobah ya ba su. Shawarwarin nan za su taimaka mana.

“MU ZAMA MASU CIKAKKEN GANEWA”

4. Me ya sa abubuwa ba su yi wa Yahudawa da suka zama Kiristoci sauƙi ba? (Ka kuma duba hoton.)

4 Abubuwa ba su yi wa Yahudawan da suka zama Kiristoci sauƙi ba. Me ya sa? Domin a dā Yahudawa ne mutanen da Jehobah ya zaɓa wa kansa. Urushalima kuma wuri ne mai muhimmanci sosai domin sarkinta ne yake wakiltar Jehobah. Ƙari ga haka, duk wanda yake so ya bauta wa Jehobah dole ya zo yin ibada a haikalin da ke Urushalima. Yahudawa masu aminci suna bin Dokar Musa da koyarwar malaman addininsu. Suna da dokoki a kan cin abinci, da yin kaciya, da kuma yadda za su yi shaꞌani da waɗanda ba Yahudawa ba. Amma bayan Yesu ya mutu, sai Jehobah ya daina amincewa da hadayu da ake yi a haikalin. Yanzu dole Yahudawa da suka zama Kiristoci su canja yadda suke yin ibada. Wannan canjin ba ƙaramin abu ba ne. (Ibran. 10:​1, 4, 10) Ko Kiristoci masu bangaskiya sosai kamar Bitrus ma, bai yi musu sauƙi su yi wannan canjin ba. (A. M. 10:​9-14; Gal. 2:​11-14) Da yake imanin Kiristoci ya bambanta da na Yahudawa, shugabannin addinin Yahudawa sun tsananta musu.

Kiristocin suna bukatar su ci-gaba da riƙe gaskiya da ke Kalmar Allah, kuma su ƙi koyarwar ƙarya da magoya bayan addinin Yahudawa suke yi (Ka duba sakin layi na 4-5)


5. Su waye ne suka takura wa Ibraniyawa Kiristocin?

5 Mutane kashi biyu ne suka takura wa Ibraniyawa Kiristocin. Na farko su ne shugabannin addinin Yahudawa da suke musu kallon ꞌyan ridda. Na biyu kuma sune wasu da suke daꞌawa cewa su Kiristoci ne, amma sun nace cewa dole Kiristoci su ci-gaba da bin Dokar Musa. Mai yiwuwa sun yi hakan ne don kada a tsananta musu. (Gal. 6:12) Me zai taimaka wa Kiristocin su ci-gaba da riƙe amincinsu?

6. Mene ne Bulus ya ƙarfafa ꞌyanꞌuwansa Ibraniyawan su yi? (Ibraniyawa 5:14–6:1)

6 A wasiƙar da Bulus ya rubuta wa ꞌyanꞌuwansa Ibraniyawa, ya ƙarfafa su su yi bincike mai zurfi a Kalmar Allah. (Karanta Ibraniyawa 5:14–6:1.) Ya kuma yi amfani da wurare da dama a Nassosin Ibrananci don ya nuna musu cewa, yadda Kiristoci suke ibada ya fi yadda Yahudawa suke yi. a Bulus ya san cewa idan sun san nassosi sosai kuma sun fahimci gaskiyar da ke cikinsu, za su iya gane koyarwa da ba daidai ba kuma su guje mata.

7. Mene ne muke fama da shi a yau?

7 A yau ma, muna fama da mutanen da suke baza raꞌayoyinsu kuma suke faɗin abubuwa da suka saɓa wa ƙaꞌidodin Jehobah. Wasu sun ce yadda muke bin abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da yin jimaꞌi bai dace ba. Mutane suna ƙara ɓullowa da raꞌayoyin da suka saɓa wa koyarwar Jehobah. (K. Mag. 17:15) Shi ya sa yake da muhimmanci mu iya gane raꞌayin da bai dace ba, kuma mu ƙi shi. Kada mu yarda maƙiyanmu su sa mu yi sanyin gwiwa kuma mu daina bauta wa Jehobah.—Ibran. 13:9.

8. Me za mu yi don mu zama masu cikakken ganewa?

8 Kamar yadda manzo Bulus ya shawarci Ibraniyawa Kiristocin, mu ma muna bukatar mu ƙoƙarta don mu zama masu cikakken ganewa. Hakan yana nufin cewa mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kyau don mu san Jehobah sosai, kuma mu san raꞌayinsa game da abubuwa. Muna bukatar mu ci-gaba da yin irin wannan nazarin ko da mun yi baftisma. Komen daɗewarmu a ƙungiyar Jehobah, muna bukatar mu ci-gaba da karanta Littafi Mai Tsarki da nazarinsa babu fashi. (Zab. 1:2) Idan muna nazarin Littafi Mai Tsarki babu fashi, bangaskiyarmu za ta ƙaru. A wasiƙar da manzo Bulus ya rubuta wa Ibraniyawa, ya nuna cewa bangaskiya tana da muhimmanci sosai.—Ibran. 11:​1, 6.

BANGASKIYA ZA TA SA MU SAMI CETO

9. Me ya sa Ibraniyawa Kiristocin suke bukatar bangaskiya sosai?

9 Ibraniyawa Kiristocin suna bukatar bangaskiya sosai don ita ce za ta sa su tsira. (Ibran. 10:​37-39) Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa idan suka ga sojoji sun kewaye Urushalima, su gudu zuwa kan tuddai. Duka Kiristoci ne Yesu ya ce su gudu, ko suna cikin birnin ko suna ƙauyukan da ke kewaye. (Luk. 21:​20-24) Amma a lokacin, idan aka kawo hari, waɗanda suke ƙauyuka sukan gudu su shiga cikin birni ne, domin birane suna da katanga da suke kāre su. Hakika, Ibraniyawan suna bukatar bangaskiya, domin in ba da bangaskiya ba, ba wanda zai so ya bi abin da Yesu ya ce.

10. Mene ne ꞌyanꞌuwa za su yi idan suna da bangaskiya? (Ibraniyawa 13:17)

10 Ibraniyawa Kiristocin suna kuma bukatar su yarda da waɗanda Yesu ya naɗa su yi ja-goranci a ikilisiya. Ba mamaki ꞌyanꞌuwa da suke ja-goranci sun ba su umurnai a kan lokacin da za su gudu da kuma yadda za su yi hakan. (Karanta Ibraniyawa 13:17.) A Helenanci, kalmar da aka fassara zuwa “ku yi musu biyayya” a Ibraniyawa 13:​17, tana nufin mutum ya bi abin da aka gaya masa domin ya yarda da wanda ya ba shi umurnin, ba don kawai abin da ya kamata ya yi ke nan ba. Don haka, idan ma a dā wasunsu suna shakkar ꞌyanꞌuwa da suke ja-goranci, suna bukatar su daina shakkar kafin lokacin wahalar nan ta zo. Gaskiyar ita ce, idan ꞌyanꞌuwan suna yi wa dattawa biyayya a lokacin da ake zaman lafiya, zai yi musu sauƙi su yi hakan a lokacin masifa.

11. Me ya sa muke bukatar bangaskiya sosai a yau?

11 Kamar Ibraniyawa Kiristocin, mu ma muna bukatar bangaskiya sosai. Me ya sa? Domin yawancin mutane a yau ba su yarda cewa duniyar nan za ta zo ga ƙarshe ba. Har ma suna mana dariya don muna cewa ƙarshen ya yi kusa. (2 Bit. 3:​3, 4) Ƙari ga haka, ko da yake Littafi Mai Tsarki ya gaya mana wasu abubuwan da za su faru a lokacin ƙunci mai girma, akwai abubuwa da yawa da ba mu sani ba. Don haka muna bukatar bangaskiya sosai. Bangaskiya ce za ta sa mu yarda cewa idan lokacin Jehobah ya kai, zai kawo ƙarshen duniyar nan kuma zai taimaka mana mu tsira.—Hab. 2:3.

12. Me zai taimaka mana mu tsira a lokacin ƙunci mai girma?

12 Muna kuma bukatar mu ƙara gaskata cewa, Jehobah ne yake mana ja-goranci ta wurin “bawan nan mai aminci, mai hikima.” (Mat. 24:45) A lokacin da za a soma ƙunci mai girma, za a iya ba mu umurnai kamar yadda mai yiwuwa aka ba wa Ibraniyawa Kiristocin a lokacin da sojojin Roma suka kewaye Urushalima. Yin biyayya ne zai taimaka mana mu tsira. Don haka, yana da muhimmanci mu yarda da ꞌyanꞌuwa da suke ja-goranci a ƙungiyar Jehobah a yau. Idan muna shakkarsu ko yana mana wuya mu bi abin suke gaya mana a yanzu, zai yi mana wuya sosai mu bi abin da za su gaya mana a lokacin ƙunci mai girma.

13. Me ya sa Ibraniyawa Kiristocin suke bukatar gargaɗin da ke Ibraniyawa 13:5?

13 Yayin da Ibraniyawa Kiristocin suke jiran lokacin da za su gudu kamar yadda Yesu ya ce, suna bukatar su guji “halin son kuɗi” kuma su fi mai da hankali ga ibadarsu. (Karanta Ibraniyawa 13:5.) Wasunsu sun yi fama da yunwa da talauci a dā. (Ibran. 10:​32-34) Sun yi haƙuri kuma sun jimre don suna ƙaunar Jehobah. Duk da haka, mai yiwuwa sun soma neman kuɗi sosai don su sami kāriya kuma kada su sake shiga cikin talauci. Amma idan aka zo halaka Urushalima, kuɗi ba zai cece su ba. (Yak. 5:3) A maimakon haka, kuɗin zai iya zama musu tarko. Domin zai yi ma waɗanda suke son kuɗi wuya su bar gidajensu da dukiyoyinsu su gudu.

14. Idan mun gaskata cewa Jehobah zai halaka duniyar nan, mene ne ba za mu yi ba?

14 Idan mun gaskata cewa nan ba da daɗewa ba Jehobah zai halaka duniyar nan, ba za mu sa neman kuɗi kan gaba a rayuwarmu ba. Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa a lokacin ƙunci mai girma, mutane “za su jefar da azurfarsu a kan tituna,” don za su ga cewa “azurfarsu da zinariyarsu ba za su iya kuɓutar da su ba, a ranar fushin Yahweh.” (Ezek. 7:19) Don haka maimakon mu yi ta ƙoƙarin tara kuɗi kawai, zai dace mu nemi abin biyan bukatunmu da na ꞌyan iyalinmu, kuma mu ci-gaba da bauta wa Jehobah. Ba zai dace mu ci bashi da yawa, ko mu tara abin duniya kuma mu yi ta faman kula da su ba. Ƙari ga haka, mu yi hankali don kada mu so abubuwan da muke da su fiye da kima. (Mat. 6:​19, 24) Me ya sa? Domin abubuwan nan za su iya zama mana jaraba a nan gaba, yayin da ƙarshen yake gabatowa.

MUNA BUKATAR JIMIRI

15. Me ya sa Ibraniyawa Kiristocin suke bukatar jimiri sosai?

15 Ibraniyawa Kiristocin suna bukatar jimiri yayin da suke bauta wa Jehobah, domin nan ba daɗewa ba za su shiga cikin wahala. (Ibran. 10:36) Ko da yake an tsananta ma wasu cikinsu sosai a dā, da yawa daga cikinsu ba su taɓa shiga irin wannan halin ba. Shi ya sa manzo Bulus ya ce musu su yi shirin fuskantar tsanantawa mai yawa, kuma su yi niyyar riƙe amincinsu har mutuwa kamar yadda Yesu ya yi. (Ibran. 12:4) A lokacin, Yahudawa sun soma fushi da Kiristocin sosai don yadda mutane da yawa suke zama Kiristoci. Bai daɗe sosai ba da mutane suka so su kashe Bulus saꞌad da yake waꞌazi a Urushalima. Yahudawa fiye da 40 sun “yi rantsuwa cewa ba za su ci ba, ba za su sha ba, sai sun kashe Bulus.” (A. M. 22:22; 23:​12-14) Ba a son ganin Kiristocin, kuma sun san cewa za a tsananta musu. Duk da haka, dole su ci-gaba da yin taro da waꞌazi, kuma su riƙe bangaskiyarsu.

16. Idan muka sa abin da Bulus ya gaya wa Ibraniyawa Kiristocin a zuciyarmu, yaya za mu ɗauki tsanantawa? (Ibraniyawa 12:7)

16 Me zai taimaka wa Ibraniyawa Kiristocin su jimre tsanantawa? Suna bukatar su san cewa tsanantawa za ta iya amfanar mutum. Manzo Bulus ya san da hakan, shi ya sa ya bayyana cewa idan mutum yana shan wuya, Allah zai iya amfani da wannan damar ya koyar da shi. (Karanta Ibraniyawa 12:7.) Wahalar za ta iya sa mutum ya koyi wasu halaye masu kyau. Idan Ibraniyawa Kiristocin suka mai da hankali a kan yadda wahalar za ta amfane su, jimrewa zai ɗan zo musu da sauƙi.—Ibran. 12:11.

17. Wace shawara ce Bulus ya bayar game da jimre tsanantawa?

17 Bulus ya ƙarfafa Ibraniyawa Kiristocin su yi ƙarfin zuciya kuma kada su fid da rai komen tsanantawa. Ya san abin da yake gaya musu, domin a dā shi da kansa ya tsananta wa Kiristoci, kuma ya san yadda ake wulaƙanta su. Ban da haka, shi ma an tsananta masa sosai bayan da ya zama Kirista kuma ya jimre. (2 Kor. 11:​23-25) Don haka, ya san abin da zai taimaka wa mutum ya jimre idan ana tsananta masa. Ya gaya wa Ibraniyawan cewa idan ana tsananta musu, su dogara ga Jehobah kada su dogara ga kansu. Za su yi ƙarfin zuciya idan suka tuna abin da ke Ibraniyawa 13:​6, da ta ce: “Ubangiji mai taimakona ne, ba zan ji tsoro ba.”

18. Me zai taimaka mana mu jimre tsanantawa a nan gaba?

18 A yanzu haka, ana tsananta ma wasu ꞌyanꞌuwanmu kuma suna jimrewa. Zai yi kyau mu taimaka musu ta wurin sa su cikin adduꞌa, kuma mu ba su abin da suke bukata idan zai yiwu. (Ibran. 10:33) Amma fa, Littafi Mai Tsarki ya ce “duk wanda yake so ya yi rayuwa irin hali na Allah a cikin Almasihu Yesu zai sha tsanani.” (2 Tim. 3:12) Don haka, dukanmu ne muke bukatar mu yi shirin fuskantar tsanantawa. Abin da zai taimaka mana mu jimre ke nan. Ta yaya za mu yi shiri? Mu ci-gaba da dogara ga Jehobah da dukan zuciyarmu, da tabbaci cewa zai taimaka mana mu jimre duk wata tsanantawa da za mu fuskanta. A-kwana-a-tashi, Jehobah zai ceci dukan bayinsa masu aminci daga hannun maƙiyansu.—2 Tas. 1:​7, 8.

19. Me zai taimaka mana mu jimre abin da za mu fuskanta a lokacin ƙunci mai girma? (Ka kuma duba hoton.)

19 Ba shakka, wasiƙar Bulus ta taimaka wa Ibraniyawan su yi shiri don wahalar da za su sha a lokacin. Bulus ya ƙarfafa su su yi nazarin Kalmar Allah da kyau don su fahimce ta sosai. Hakan zai sa su gane koyarwa da ba daidai ba kuma su guje mata, don irin koyarwar nan za ta iya sa su yi sanyin gwiwa. Ya kuma ƙarfafa su su yi ƙoƙari su ƙara zama masu bangaskiya don su yi saurin bin ja-gorancin Yesu da na dattawa a ikilisiya. Ƙari ga haka, Bulus ya taimaka wa Kiristocin su zama da raꞌayin da ya dace game da tsanantawa. Ya ce su ɗauke shi a matsayin horarwa. Wato Ubanmu mai ƙauna zai iya amfani da wannan damar ya koya musu wasu halaye masu kyau. Bari mu ma mu bi waɗannan shawarwarin da Allah ya sa a rubuta. Abin da zai taimaka mana mu jimre har zuwa ƙarshe ke nan.—Ibran. 3:14.

Kiristoci masu aminci sun jimre kuma sun sami albarka. Bayan da suka gudu daga yankin Yahudiya, sun ci-gaba da yin taron ibada. Me wannan ya koya mana? (Ka duba sakin layi na 19)

WAƘA TA 126 Mu Yi Tsaro, Mu Riƙe Aminci, Mu Yi Ƙarfi

a A Ibraniyawa sura ɗaya, manzo Bulus ya yi amfani da aƙalla Nassosin Ibrananci guda bakwai don ya nuna cewa yadda Kiristoci suke yin ibada ya fi na Yahudawa.—Ibran. 1:​5-13.