Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
Ina almajiran Yesu 70 ɗin nan suke, a lokacin da ya kafa Jibin Maraice na Ubangiji? Sun daina bin sa ne?
Waɗannan almajiran Yesu guda 70 ba sa tare da shi a lokacin da ya kafa Jibin Maraice na Ubangiji kam, amma ba abin da ya nuna cewa Yesu ya ƙi su ne, ko sun daina bin sa. Yesu ya so ya yi taron da manzaninsa ne kawai a wannan lokacin.
Manzani 12 ɗin da waɗannan almajirai 70, duk mabiyan Yesu ne. Yesu ne ya zaɓi 12 daga cikin almajiransa kuma ya kira su manzanni. (Luk. 6:12-16) A Galili yake lokacin da ya “kira sha biyun” kuma ya “aike su su je su yi waꞌazin mulkin Allah, su kuma warkar da marasa lafiya.” (Luk. 9:1-6) Daga baya a yankin Yahudiya, Yesu “ya kuma zaɓi waɗansu mutum sabaꞌin . . . ya aike su biyu-biyu.” (Luk. 9:51; 10:1) Wannan ya nuna cewa Yesu yana da mabiya a wurare da dama da suke waꞌazi game da shi.
Yahudawa da suka zama mabiyan Yesu suna yin bikin Idin Ƙetarewa kowace shekara, kuma mai yiwuwa suna hakan ne tare da ꞌyan iyalinsu. (Fit. 12:6-11, 17-20) Da lokacin mutuwarsa ya kusa, Yesu ya kira manzanninsa suka tafi Urushalima. Amma bai kira sauran almajiransa da suke Yahudiya, da Galili, da yankin Perea ba. Hakan ya nuna cewa Yesu ya so ya kasance da manzanninsa ne kawai a wannan bikin Idin Ƙetarewa. Yesu ya gaya musu cewa: “Na yi marmari in ci wannan Bikin Ƙetarewa tare da ku kafin in sha wahala!”—Luk. 22:15.
Akwai dalilin da ya sa Yesu ya yi hakan. A lokacin, Yesu ya kusan mutuwa, kuma shi ne “Ɗan Rago na Allah, wanda zai ɗauke zunubin duniya.” (Yoh. 1:29, Mai Makamantu[n] Ayoyi) A Urushalima ne zai mutu, domin a nan ne ake yin hadayu ga Allah. Ragon da Israꞌilawa suke yankawa a ranar Bikin Ƙetarewa yakan tuna musu yadda Jehobah ya cece su daga ƙasar Masar. Amma hadayar Yesu za ta kawo ꞌyancin da ya fi wannan, domin za ta ꞌyantar da dukan ꞌyan Adam daga zunubi da mutuwa. (1 Kor. 5:7, 8) Ƙari ga haka, hadayar Yesu za ta ba wa manzanninsa sha biyu damar zama cikin waɗanda za su kafa ikilisiyar Kirista. (Afis. 2:20-22) Hakan ya dace, domin an “gina tushen” Urushalima birni mai tsarki ne “a kan duwatsu goma sha biyu,” da “aka rubuta sunayen almajirai goma sha biyu na Ɗan Ragon.” (R. Yar. 21:10-14) Hakika, manzannin Yesu masu amincin nan za su taka rawar gani wajen cika nufin Allah. Don haka, ya dace da Yesu ya so su kasance tare da shi a wannan Bikin Ƙetarewa na ƙarshe, da kuma Jibin Maraice na Ubangiji da suka yi bayan haka.
Ko da yake sauran almajiransa, har da 70 ɗin nan, ba sa wurin da suka yi bikin, dukan mabiyansa masu aminci za su amfana daga Jibin Maraice na Ubangiji da aka kafa. Kuma dukan waɗanda suka zama shafaffun Kiristoci daga baya za su sami damar yin mulki tare da Yesu, kamar yadda ya gaya wa manzanninsa a wannan daren.—Luk. 22:29, 30.