Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 17

Abin da Iyaye Mata Za Su Iya Koya Daga Misalin Afiniki

Abin da Iyaye Mata Za Su Iya Koya Daga Misalin Afiniki

“Kada . . . ka ƙi koyarwar mamarka. . . . Tana ƙara maka kyau kamar hular daraja, kyakkyawan kayan ado [ne] a wuyanka.”​—K. MAG. 1:​8, 9.

WAƘA TA 137 Mata Masu Aminci

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

Mamar Timoti Afiniki, da kakarsa Loyis suna farin ciki yayin da suke kallon yadda ake masa baftisma a matsayin Kirista (Ka duba sakin layi na 1)

1-2. (a) Wace ce Afiniki kuma wane ƙalubale ne ta fuskanta? (b) Ka yi kalami a kan hoton da ke shafin farko.

 KO DA yake Littafi Mai Tsarki bai gaya mana yadda Timoti ya yi baftisma ba, za mu iya tunanin irin farin cikin da mamarsa Afiniki ta yi ranar da aka yi masa baftisma. (K. Mag. 23:25) Ka yi tunanin yadda take alfahari da Timoti yayin da yake tsaye a cikin ruwa. Tana murmushi yayin da kakar Timoti, wato Loyis take riƙe ta. Afiniki ta ɗan riƙe numfashinta yayin da aka nitsar da Timoti a cikin ruwan. Sa’an nan ya fito yana murmushi sosai. Da ta ga hakan, sai ta fara zub da hawaye don farin ciki. Ko da yake bai kasance mata da sauƙi ba, Afiniki ta yi nasarar koya wa ɗanta ya ƙaunaci Jehobah da Yesu Kristi. Waɗanne ƙalubale ne ta shawo kansu yayin da take ƙoƙarin koyar da ɗanta?

2 Addinin baban Timoti ya bambanta da na mamarsa. Babansa Baheleni ne, amma mamarsa da kakarsa Yahudawa ne. (A. M. 16:1) Da alama Timoti matashi ne sa’ad da Afiniki da Loyis suka zama Kiristoci. Amma babansa bai zama Kirista ba. Shin wane addini ne Timoti zai zaɓa? Da yake shi ba yaro ba, ya isa ya yanke shawara da kansa. Zai bi addinin babansa? Zai ci gaba da bin al’adun Yahudawa da aka koya masa tun yana yaro? Ko kuma zai zama almajirin Yesu?

3. Bisa ga Karin Magana 1:​8, 9, yaya Jehobah yake ɗaukan aikin da iyaye mata suke yi don su taimaka ma yaransu su kusace shi?

3 Iyaye mata Kiristoci suna ƙaunar iyalansu sosai. Abin da ya fi musu muhimmanci shi ne su taimaki yaransu su kusaci Jehobah. Kuma Allahnmu yana farin ciki sosai don ƙoƙarin da suke yi. (Karanta Karin Magana 1:​8, 9.) Jehobah ya taimaki iyaye mata da yawa su koya wa yaransu su ƙaunace shi.

4. Waɗanne ƙalubale ne iyaye mata suke fuskanta a yau?

4 A wasu lokuta, iyaye mata za su iya tunanin ko yaransu za su zaɓa su bauta ma Jehobah kamar yadda Timoti ya yi. Iyaye sun san cewa ba shi da sauƙi yara su bauta wa Jehobah a duniyar nan. (1 Bit. 5:8) Ƙari ga haka, iyaye mata da yawa suna renon yaransu ba tare da mazansu ba ko kuma mazansu ba sa bauta ma Jehobah, kuma hakan yakan musu wuya sosai. Alal misali, wata ’yar’uwa mai suna Christine * ta ce: “Maigidana yana kula da yaranmu da kyau kuma yana ƙaunar iyalinmu, amma ba ya so in koya ma yaranmu ƙa’idodin Jehobah. Sau da yawa nakan yi kuka domin ina tunanin yaya yaranmu za su san Jehobah kuma su bauta masa.”

5. Me za mu tattauna a wannan talifin?

5 Idan kina ƙoƙarin koya ma yaranki ƙa’idodin Jehobah, za ki iya yin nasara kamar yadda Afiniki ta yi. A talifin nan, za mu tattauna yadda za ki iya bin misalinta yayin da kike koyar da yaranki ta furucinki da ayyukanki. Kuma za mu ga yadda Jehobah zai taimake ki.

KI KOYAR DA YARANKI TA FURUCINKI

6. Kamar yadda aka nuna a 2 Timoti 3:​14, 15, me ya taimaka wa Timoti ya zama Kirista?

6 Sa’ad da Timoti yake yaro, mamarsa ta yi iya ƙoƙarinta ta koya masa “Rubutattun Kalmomin Allah masu tsarki” kamar yadda Yahudawa suka fahimta a lokacin. Hakika a lokacin ba ta san kome game da Yesu ba. Duk da haka, abubuwan da Timoti ya koya daga Nassosi sun taimaka masa ya zama Kirista. Amma zai yarda ya yi hakan? A matsayin matashi, Timoti zai iya zaɓan ko zai zama Kirista. Babu shakka, ɗaya daga cikin abubuwan da suka taimaki Timoti ya zama Kirista, shi ne tabbacin da mamarsa ta ba shi. (Karanta 2 Timoti 3:​14, 15.) Afiniki ta yi farin ciki sosai cewa ta iya koya wa ɗanta game da Jehobah duk da cewa hakan bai yi mata sauƙi ba! Afiniki ta yi abin da ya jitu da ma’anar sunanta, wanda yake nufin “nasara.”

7. Ta yaya Afiniki za ta iya taimaka wa ɗanta ya ci gaba da ƙaunar Allah bayan ya yi baftisma?

7 Sa’ad da Timoti ya yi baftisma, ya cika maƙasudi mai muhimmanci a rayuwarsa. Duk da haka, Afiniki ba ta daina damuwa game da ɗanta bayan ya yi baftisma ba. Mai yiwuwa ta yi tunanin: Me ɗanta zai yi da rayuwarsa? Zai yi tarayya da abokan banza ne? Zai je makaranta a Atina ne kuma ya soma bin koyarwar ’yan falsafa? Zai duƙufa neman dukiya ne da lokacinsa da ƙarfinsa da duk rayuwarsa? Afiniki ba za ta iya yi masa zaɓi ba, amma za ta iya taimaka masa. Ta yaya? Za ta iya ci gaba da yin ƙoƙari ta koyar da ɗanta ya ƙaunaci Jehobah sosai kuma ya nuna godiya don abin da Jehobah da Yesu suka yi musu a matsayin iyali. Ba iyalan da iyayen suke bin addini dabam-dabam ne kaɗai suke fama da yadda za su taimaka wa yaransu su ƙaunaci Jehobah ba. Ko da iyayen Shaidun Jehobah ne, zai iya yi musu wuya su taimaka wa yaransu su bauta ma Jehobah da dukan zuciyarsu. Mene ne iyaye za su iya koya daga misalin Afiniki?

8. Ta yaya iyaye mata za su iya taimaka wa mazansu da Shaidun Jehobah ne su koyar da yaransu game da Jehobah?

8 Ki yi nazarin Littafi Mai Tsarki da yaranki. ’Yan’uwa mata, idan mazanku Shaidun Jehobah ne, Jehobah yana so ku taimaka musu don su koya wa yaranku ƙa’idodinsa. Hanya ɗaya da za ku iya yin hakan ita ce ta goyon bayan tsarin ibada ta iyalinku. Ku faɗi abubuwa masu kyau game da ibada ta iyalin kuma ku yi tunanin abin da za ku iya yi don ku sa kowa ya ji daɗin ibada ta iyalin. Za ku iya taimaka wa mazanku su shirya wani abu na musamman don ibadarku ta iyali. Ƙari ga haka, idan kuka ga cewa wasu daga cikin yaranku sun isa a yi nazarin littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! da su, za ku iya taimaka wa mazanku don ku yi nazarin.

9. Me zai taimaka wa mahaifiya da maigidanta ba ya bauta wa Jehobah?

9 A wasu lokuta, mace ce za ta bukaci ta yi nazari da yaranta, mai yiwuwa domin mijinta ya mutu ko ba ya bauta wa Jehobah. Idan haka yanayin yake a iyalinki, kada ki damu ainun. Jehobah zai taimake ki. Ki yi amfani da abubuwan da ƙungiyarmu ta tanadar don ki yi nazari da yaranki. Za ki iya tambayar iyayen da suka ƙware a gudanar da ibada ta iyali don su nuna miki yadda suke amfani da waɗannan abubuwan a ibada ta iyalinsu. * (K. Mag. 11:14) Jehobah ma zai taimaka miki ki tattauna da yaranki. Ki gaya masa ya taimake ki ki san irin tambayoyin da za ki yi wa yaranki don ki san abin da ke zuciyarsu da kuma yadda suke ji. (K. Mag. 20:5) Wata tambaya da za ki iya yi musu ita ce, ‘Wane ƙalubale ne kuke fuskanta a makaranta?’ Hakan zai iya taimaka miki ki san abin da ke zuciyarsu da kuma yadda suke ji.

10. A waɗanne hanyoyi ne kuma za ki iya taimaka ma yaranki su san Jehobah?

10 Ki nemi damar koya wa yaranki game da Jehobah. Ki riƙa magana game da Jehobah da alherin da ya yi miki. (M. Sha. 6:​6, 7; Isha. 63:7) Hakan yana da muhimmanci sosai idan ba za ki iya yin nazari da su a kai a kai a gida ba. Christine, wadda aka ambata a baya ta ce: “Ba na cika samun damar gaya wa yarana game da Jehobah. Don haka, ina amfani da duk wata dama da na samu. Nakan fita yawo tare da su ko kuma in kai su cikin kwalekwale inda za mu iya tattauna game da halittun Jehobah da kuma abubuwa da za su taimaka musu su kusaci Jehobah. Da zarar yarana sun yi girma, sai in ƙarfafa su su yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kansu.” Ƙari ga haka, ki riƙa faɗin alheri game da ƙungiyar Jehobah da kuma ’yan’uwanki masu bi. Kada ki yi gunaguni a kan dattawa. Abubuwa da kike faɗa game da su za su iya sa yaranki su nemi taimakonsu idan da bukata.

11. Bisa ga abin da ke Yakub 3:​18, me ya sa yake da muhimmanci mu nemi zaman lafiya a iyalinmu?

11 Ki sa zaman lafiya ya kasance a iyalinki. Ki riƙa gaya wa maigidanki da yaranki cewa kina ƙaunar su. Ki yi magana game da mijinki a hanyar da za ta daraja shi kuma ki koya wa yaranki su ma su yi hakan. Idan kika yi hakan, zai yi ma yaranki sauƙi su koya game da Jehobah. (Karanta Yakub 3:18.) Ki yi la’akari da misalin Jozsef, wani majagaba na musamman a Romania. Da yake girma, mahaifinsa ya yi ƙoƙarin hana shi da ’yan’uwansa da kuma mamarsu bauta wa Jehobah. Jozsef ya ce: “Mamata ta yi iya ƙoƙarinta don a sami zaman lafiya a gida. Yayin da babanmu yake daɗa mata mugunta, tana daɗa yi masa alheri. A duk lokacin da ta ga cewa yana mana wuya mu daraja babanmu, sai ta tattauna Afisawa 6:​1-3 tare da mu, sa’an nan ta fara gaya mana halaye masu kyau da babanmu yake da su, kuma ta gaya mana dalilan da suka sa ya kamata mu daraja shi. Ta hakan ta sa zaman lafiya ya kasance a iyalinmu.”

KI KOYAR DA YARANKI TA AYYUKANKI

12. Bisa ga 2 Timoti 1:​5, ta yaya misalin Afiniki ya shafi Timoti?

12 Karanta 2 Timoti 1:5. Afiniki ta kafa wa Timoti misali mai kyau. Babu shakka, ta koya masa cewa idan mutum yana da bangaskiya, dole ya nuna hakan ta halinsa. (Yak. 2:26) Hakika, Timoti ya lura cewa yadda mamarsa take ƙaunar Jehobah ne yake sa ta yin abubuwan da take yi. Ya ga cewa bauta wa Jehobah yana sa mamarsa farin ciki. A wace hanya ce misalin Afiniki ya shafi Timoti? Manzo Bulus ya ce bangaskiyar mamar Timoti ce ta taimaka wa Timoti ya kasance da bangaskiya. Ba haka kawai ya kasance da bangaskiya ba. Timoti ya ga misalin mamarsa kuma ya zaɓi ya bi misalin. A yau ma, iyaye mata da yawa sun taimaka wa iyalansu su soma bauta wa Jehobah ba tare da “magana ba.” (1 Bit. 3:​1, 2) Ke ma za ki iya yin hakan. Ta yaya?

13. Me ya sa ya kamata mahaifiya ta sa dangantakarta da Jehobah farko a rayuwarta?

13 Ki sa dangantakarki da Jehobah farko a rayuwarki. (M. Sha. 6:​5, 6) Kamar yadda yawancin iyaye mata suke yi, ke ma kina sadaukar da kuɗi, da lokacinki da barci da wasu abubuwa don ki kula da yaranki. Amma bai kamata ki sa kai a yin hakan har ki rasa lokacin kyautata dangantakarki da Jehobah ba. Ki riƙa keɓe lokaci don yin addu’a da nazarin Littafi Mai Tsarki, da kuma halartan taro. Yin hakan zai sa ki daɗa kusantar Jehobah kuma iyalinki da ma wasu za su iya bin misalinki.

14-15. Me ka koya daga labarin Leanne, da Maria, da João?

14 Ga labarin wasu matasa da misalin iyayensu mata ne ya taimake su su ƙaunaci Jehobah kuma su dogara gare shi. ’Yar Christine mai suna Leanne ta ce: “Ba mu iya yin nazari a gaban babanmu ba, amma mamarmu ba ta fasa halartan taro ba. Ko da yake ba mu san abubuwa da yawa game da Littafi Mai Tsarki ba, ayyukanta sun taimaka mana mu kasance da bangaskiya mai ƙarfi. Mun san cewa Shaidun Jehobah ne suke koyar da gaskiya tun kafin mu soma halartan taro.”

15 Wata ’yar’uwa mai suna Maria wadda a wasu lokuta babansu yakan yi wa ita, da ’yan’uwanta, da mamarsu dūka, ko ya zazzage su don sun halarci taro ta ce: “Mamata tana da ƙarfin zuciya sosai. A lokacin da nake yarinya, tsoron mutane yakan hana ni yin wasu abubuwa. Amma ganin yadda take da ƙarfin zuciya da yadda take sa Jehobah farko a rayuwarta ya taimaka min in shawo kan tsoron mutum.” Wani ɗan’uwa mai suna João, wanda babansa ya hana su tattaunawa game da Jehobah a gida ya ce: “Abin da ya fi ratsa zuciyata shi ne yadda mamata ta kasance a shirye ta sadaukar da kome, ban da dangantakarta da Jehobah, don ta faranta wa babana rai.”

16. A wace hanya ce misalin iyaye mata zai iya taimaka ma wasu?

16 Iyaye mata, ku tuna cewa misalinku zai iya shafan wasu. Me ya sa muka faɗi hakan? Ku yi tunanin yadda misalin Afiniki ya shafi manzo Bulus. Ya gano cewa sahihiyar bangaskiyar da Timoti yake da ita ‘da farko [ta kasance] tare da . . . mahaifiyarsa Afiniki’ ne. (2 Tim. 1:​5, Mai Makamantu Ayoyi) A wane lokaci ne Bulus ya fara lura cewa Afiniki tana da bangaskiya? Da alama lokacin da ya fara zuwa wa’azi a ƙasashen waje ne ya haɗu da Loyis da kuma Afiniki a Listira, kuma mai yiwuwa shi ya taimaka musu su zama Kiristoci. (A. M. 14:​4-18) Wajen shekaru 15 bayan haka, sa’ad da Bulus ya rubuta wasiƙa ga Timoti, har ila ya tuna da ayyukan Afiniki da suka nuna cewa tana da bangaskiya kuma ya ce ta kafa misali mai kyau! Babu shakka, misalinta ya ƙarfafa Bulus sosai da Kiristoci da yawa a lokacin. Idan kuna renon yaranku ba tare da mijinku ba, ko kuma mijinku ba ya bauta wa Jehobah, ku tabbata cewa misalinku mai kyau zai iya ƙarfafa waɗanda suke ganin ku.

Koya ma yara su ƙaunaci Jehobah yana ɗaukan lokaci amma kar ki fid da rai (Ka duba sakin layi na 17)

17. Me za ki yi idan kina ganin ɗanki ba ya so ya bi koyarwarki?

17 Amma idan kina ganin kamar ɗanki ba ya bin koyarwar da kike masa fa? Ki tuna cewa tarbiyyartar da yara yana ɗaukan lokaci. Kamar yadda aka nuna a cikin hoton, idan mutum ya shuka iri, zai iya tunanin ko irin zai yi girma har ya ba da ’ya’ya. Ko da yake ba shi da tabbaci cewa irin zai yi girma, zai ci gaba da yin ban ruwa don ya taimaka ma irin ya yi girma idan da hali. (Mar. 4:​26-29) Haka ma, a wasu lokuta, mahaifiya za ta iya tunanin ko tana yin nasara a taimaka ma ɗanta ya ƙaunaci Jehobah. Ba za ki iya tilasta wa yaranki su ƙaunace shi ba. Amma idan kika ci gaba da yin iya ƙoƙarinki don ki tarbiyyartar da su, za ki ba su damar zama abokan Allah.​—K. Mag. 22:6.

KI DOGARA GA JEHOBAH YA TAIMAKE KI

18. A wace hanya ce Jehobah zai iya taimakon yaranki su kusace shi?

18 Tun zamanin dā, Jehobah ya taimaki matasa da yawa su zama abokansa. (Zab. 22:​9, 10) Zai iya taimakon yaranki ma su kusace shi, idan abin da suke so ke nan. (1 Kor. 3:​6, 7) Ko da yaranki ba sa yin ƙwazo a bauta wa Jehobah, Jehobah zai ci gaba da ƙaunar su. (Zab. 11:4) Idan sun ɗan nuna cewa suna da “zuciya ta samun rai na har abada,” Jehobah zai taimaka musu nan da nan. (A. M. 13:​48, New World Translation; 2 Tar. 16:9) Zai taimake ki ki faɗi abin da zai ratsa zuciyarsu a daidai lokacin da ya kamata. (K. Mag. 15:23) Ko ya sa wani ɗan’uwa ko wata ’yar’uwa a ikilisiya ta taimaka musu. Ko bayan yaranki sun yi girma ma, Jehobah zai iya taimaka musu su tuna abin da kika koya musu sa’ad da suke ƙanana. (Yoh. 14:26) Idan kin ci gaba da koyar da yaranki ta furucinki ko ayyukanki, Jehobah zai yi miki albarka.

19. Me ya sa za ki iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah ya amince da ke?

19 Matakan da yaranki suke ɗaukawa ba sa shafan yadda Jehobah yake ƙaunarki. Yana ƙaunarki domin kina ƙaunar shi. Idan kina renon yaranki ke kaɗai, Jehobah ya yi miki alkawari cewa zai zama Uba ga yaranki kuma zai kāre ki. (Zab. 68:5) Ba za ki iya tilasta wa yaranki su bauta wa Jehobah ba. Amma idan kika ci gaba da dogara gare shi kuma kin yi iya ƙoƙarinki, za ki sami amincewarsa.

WAƘA TA 134 Yara Amana Ne Daga Allah

^ Wannan talifin ya tattauna yadda iyaye mata Kiristoci za su iya bin misalin mamar Timoti, wato, Afiniki ta wajen taimaka ma yaransu su san Jehobah kuma su ƙaunace shi.

^ An canja wasu sunayen.

^ Alal misali, ki duba darasi na 50 a cikin littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! da kuma talifin nan, “Ideas for Family Worship and Personal Study,” a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Agusta, 2011, shafuffuka na 6-7 a Turanci.