TALIFIN NAZARI NA 17
WAƘA TA 111 Dalilan da Suke Sa Mu Murna
Kada Ka Daina Bauta wa Jehobah Tare da Mutanensa
“Ku yi murna da farin ciki har abada a kan abin da nake halittarsa.”—ISHA. 65:18.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga yadda muke amfana don yanayin salama da haɗin kai da muke morewa a bautar mu ga Jehobah, da yadda za mu taimaki mutane su ma su zo su amfana.
1. Wane irin aljanna ne muke ciki a yau, kuma me ya kamata ya zama ƙudurinmu?
AKWAI wani irin aljanna a yau inda mutane da yawa suna yin ayyukan kirki. Kuma a wannan aljannar, miliyoyin mutane suna moran salama ta ƙwarai. Waɗanda suke cikinta sun ƙudiri niyyar ci-gaba da kasancewa a cikinta, kuma suna so kowa ya bi su don ya mori wannan yanayi mai kyan gaske. Wannan aljanna da muke magana a kai ita ce yanayin salama da haɗin kai da muke morewa a bautarmu ga Jehobah! a
2. Me ya sa yanayin salama da haɗin kai da muke morewa a yau abin ban mamaki ne?
2 Duk da cewa muna rayuwa a duniyar Shaiɗan da ke cike da mugunta da ƙiyayya, Jehobah ya sa mutanensa cikin yanayin salama da haɗin kai, hakan abin ban mamaki ne. (1 Yoh. 5:19; R. Yar. 12:12) Allahnmu mai ƙauna ya ga yadda mutane suke shan wahala a duniyar nan, shi ya sa yake kiyaye bayinsa don su ci-gaba da bauta masa da farin ciki. Ya kwatanta yanayin da muke ciki da “wurin ɓuya” da kuma “gonar da ake yi mata ban ruwa kullum.” (Isha. 4:6; 58:11) Waɗanda suke cikin wannan aljannar suna farin ciki kuma suna samun kwanciyar hankali don Jehobah yana musu albarka.—Isha. 54:14; 2 Tim. 3:1.
3. Ta yaya littafin Ishaya sura 65 ta cika a zamanin dā?
3 Annabi Ishaya ne Jehobah ya yi amfani da shi don ya kwatanta irin yanayin da bayin Allah za su kasance a ciki. Wannan kwatancin yana littafin Ishaya sura 65, kuma ya fara cika ne a shekara ta 537 kafin haihuwar Yesu. A lokacin ne aka saki Yahudawa daga zaman bauta a Babila kuma suka koma ƙasarsu. Jehobah ya yi wa mutanensa albarka sosai. Ya taimaka musu su sake gina Urushalima ta zama birni mai kyau, kuma su sa haikalinsa ta sake zama cibiyar bauta ta gaskiya a Israꞌila.—Isha. 51:11; Zak. 8:3.
4. Ta yaya littafin Ishaya sura 65 take cika a yau?
4 Wannan annabci da Ishaya ya yi, ya sake cika a zamaninmu. Bayin Allah sun soma ganin cikarsa tun daga shekara ta 1919 bayan haihuwar Yesu. A lokacin ne bayin Jehobah suka sami ꞌyanci daga Babila Babba, kuma bayan hakan ne wannan yanayi na salama da haɗin kai da muke morewa ya soma yaɗuwa a dukan duniya. ꞌYanꞌuwa sun yi waꞌazi da ƙwazo kuma sun kafa ikilisiyoyi da yawa. Hakan ya sa mutane da yawa, maza da mata, da a dā su mugaye ne da masu yin lalata, sun “ɗauki sabon halin nan da Allah ya halitta bisa ga kamannin kansa.” (Afis. 4:24) Hakika, a sabuwar duniya ne za mu ga cikar abubuwa da yawa da Ishaya ya yi magana a kai. Amma ko a yanzu ma muna samun albarku da yawa. Bari mu ga yadda wannan yanayi mai kyau da muke bauta ma Jehobah a ciki yake amfanar mu, da abin da ya sa babban kuskure ne mutum ya daina bauta ma Jehobah tare da mutanensa.
ABUBUWAN DA BAYIN ALLAH SUKE MOREWA A YAU
5. Kamar yadda Ishaya 65:13 ta ce, mene ne muke morewa don muna bauta ma Jehobah?
5 Isasshen abinci da wartsakewa. Annabcin da Ishaya ya yi ya nuna yanayin da bayin Jehobah suke ciki, da yanayin da waɗanda ba sa bauta masa suke ciki. (Karanta Ishaya 65:13.) Jehobah yana ba wa bayinsa dukan abubuwan da suke bukata don su ci-gaba da kusantar sa. Ya ba mu ruhunsa mai tsarki, da Littafi Mai Tsarki, da kuma littattafan da suke bayyana Littafi Mai Tsarki, don mu samu “ci” da “sha” kuma mu “yi farin ciki.” (Ka kuma duba Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 22:17.) Amma waɗanda ba sa tare da mu ba su san Allah ba, suna fama “da yunwa . . . da ƙishi,” kuma suna shan “kunya.”—Amos 8:11.
6. Yaya aka kwatanta tanadodi da Jehobah yake mana a Yowel 2:21-24, kuma yaya suke amfanar mu?
6 A annabcin da Yowel ya yi, ya yi amfani da muhimman abubuwa irin su hatsi, da ruwan inabi, da man zaitun, don ya nuna yadda Jehobah yake ba mu abubuwan da muke bukata don mu ƙarfafa bangaskiyarmu. Hakan ya haɗa da koyarwa da muke samu daga Kalmarsa. (Yow. 2:21-24) Jehobah yana ciyar da mu ta wurin Littafi Mai Tsarki, da littattafanmu, da dandalinmu da kuma taro iri-iri da muke zuwa. Za mu iya yin amfani da abubuwan nan kowace rana, saboda haka, za mu iya cewa muna samun isasshen abinci da wartsakewa.
7. Me yake sa mu ji ‘farin ciki a zuciyarmu’? (Ishaya 65:14)
7 Farin ciki da gamsuwa. Bayin Allah suna godiya don alherinsa, hakan yana sa su farin ciki sosai. (Karanta Ishaya 65:14.) Gaskiyar da muke koya da alkawura masu ban ƙarfafa da suke Kalmar Allah da begen da muke da shi don hadayar Yesu suna sa mu yi ‘farin ciki a zuciyarmu.’ Kuma idan muna hira game da abubuwan nan da ꞌyanꞌuwanmu, hakan yana ƙara sa mu farin ciki!—Zab. 34:8; 133:1-3.
8. Waɗanne abubuwa biyu ne suke sa mu ji daɗin bauta ma Jehobah tare da mutanensa?
8 Wasu abubuwa biyu da suke sa mu ji daɗin bauta ma Jehobah a yau su ne ƙauna da haɗin kai da ke tsakanin bayinsa. Wannan “ɗayantaka” da muke da shi yana sa mu ga yadda rayuwa za ta kasance a aljanna. A lokacin, ƙauna da haɗin kai da ke tsakanin bayin Jehobah za su ma fi yadda muke gani a yau. (Kol. 3:14) Wata ꞌyarꞌuwa ta faɗi abin da ya fi jan hankalinta lokacin da ta fara haɗuwa da Shaidun Jehobah, ta ce: “A dā ba na farin ciki, ꞌyan iyalinmu ma ba sa sa ni farin ciki. Sai da na haɗu da Shaidun Jehobah ne na ga yadda ake nuna ƙauna ta gaskiya.” Hakika, duk wanda yake so ya yi farin ciki da gaske kuma ya yi rayuwa mai gamsarwa, yana bukatar ya bauta ma Jehobah tare da mutanensa. Ko da me mutane za su ce game da Shaidun Jehobah, gaskiyar ita ce, suna yin suna mai kyau a gaban Allah da kuma dukan bayinsa.—Isha. 65:15.
9. Mene ne Ishaya 65:16, 17 suka ce game da abubuwan da suke sa mu wahala a yau?
9 Kwanciyar hankali da natsuwa. Ishaya 65:14 ta ce waɗanda ba sa cikin yanayin da bayin Allah suke ciki, ‘za su yi kuka domin baƙin cikin zuciyarsu da kuma ɓacin ransu.’ Amma me zai faru da abubuwan da suke sa bayin Allah baƙin ciki da wahala? A-kwana-a-tashi, za a manta da su kuma za a ɓoye su daga idanun Allah. (Karanta Ishaya 65:16, 17.) Jehobah zai cire dukan abubuwa da suke sa mu damuwa, kuma ba za mu sake tuna da wahalar da muka sha ba.
10. Me ya sa kake ganin yadda kake bauta ma Jehobah tare da ꞌyanꞌuwanka Kiristoci albarka ne sosai? (Ka kuma duba hoton.)
10 Ko a yanzu ma, muna samun kwanciyar hankali a duk lokacin da muka je taronmu, domin mukan natsu kuma mu manta da abubuwan da suke damunmu a duniyar nan. Za mu ƙara sa ꞌyanꞌuwanmu su samu kwanciyar hankali idan muna da halin ƙauna, da farin ciki, da salama, da haƙuri, da kirki. Duk waɗannan sassa ne na halin da ruhun Allah yake haifar. (Gal. 5:22, 23) Ba shakka, kasancewa a cikin ƙungiyar Jehobah ba ƙaramar albarka ba ce! Kuma waɗanda suka ci-gaba da bauta ma Jehobah tare da mutanensa za su ga lokacin da zai kawo “sabon sama da sabuwar ƙasa” kamar yadda ya yi alkawari.
11. Bisa ga Ishaya 65:18, 19, me ya kamata yanayi mai kyau da muke a ciki ya sa mu yi?
11 Muna godiya da kuma murna. Annabi Ishaya ya kuma gaya mana abin da ya sa muke “murna da farin ciki” a wannan aljannar. Ya ce halittar Jehobah ce, wato Jehobah ne ya shirya aljannar. (Karanta Ishaya 65:18, 19.) Shi ya sa Jehobah yake amfani da mu wajen taimaka wa mutane su bar ƙungiyoyin da ba sa koya musu gaskiya game da shi, kuma su zo su ji daɗin da muke ji! Abubuwan da muke morewa don muna a ƙungiyar Jehobah suna sa mu murna sosai, kuma muna marmarin ba wa mutane labarinsu.—Irm. 31:12.
12. Yaya kake ji idan ka tuna alkawuran da suke Ishaya 65:20-24, kuma me ya sa?
12 Muna kuma farin ciki da godiya don begen da muke yi sakamakon danganta mai kyau da muke da ita da Jehobah. Ka yi tunanin abubuwan da za su faru a sabuwar duniya! Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba za a sāke samun jariri wanda zai rayu na ꞌyan kwanaki kawai ba, ko a sami tsohon da bai cika shekarunsa ba.” Za mu ‘gina gidaje, mu zauna a cikinsu, za mu shuka gonakin inabi, mu ci amfaninsu.’ Ba za mu ‘yi aiki a banza ba,’ domin za mu zama waɗanda Jehobah ya “sa musu albarka.” Ya yi mana alkawarin rayuwa mai gamsarwa da kuma kwanciyar hankali, bisa ga nufinsa. ‘Kafin mu yi kira’ zai san abin da muke bukata, kuma zai “ƙosar da kowane mai rai bisa ga bukatarsa.”—Isha. 65:20-24; Zab. 145:16.
13. Yaya Ishaya 65:25 ta kwatanta canjin da mutane suke yi idan sun soma bauta ma Jehobah?
13 Salama. Ruhun Allah ya taimaka wa mutane da yawa masu mugun hali su yi canje-canje sosai a rayuwarsu. (Karanta Ishaya 65:25.) Sun yi ƙoƙari har sai da suka daina halaye marasa kyau. (Rom. 12:2; Afis. 4:22-24) A wasu lokuta mukan yi kuskure domin mu ajizai ne. Amma, Jehobah ya haɗa kan “dukan mutane” da suke ƙaunarsa kuma suke ƙaunar juna, shi ya sa muna zaman lafiya da juna. (Tit. 2:11) Allah mai iko duka ne kaɗai zai iya yin wannan abin ban alꞌajabi!
14. Ta yaya Ishaya 65:25 ta cika a rayuwar wani ɗanꞌuwa?
14 Zai yiwu mutum ya canja halinsa gabaki-ɗaya kuwa? Ƙwarai kuwa! Ga wani misali. Akwai wani matashi da an kulle shi a fursun sau da yawa tun bai wuce shekara 20 ba. Yana faɗa sosai, kuma yana yin lalata. Shi ɗan fashi ne da ke sata motoci, kuma yana yin sata a gidajen mutane. Ya kuma aikata wasu manyan laifuka. A shirye yake ya yi faɗa da kowa. Amma da ya koyi gaskiyar da ke Kalmar Allah kuma ya soma zuwa taron Shaidun Jehobah, ya ga cewa bauta wa Jehobah tare da mutanensa ita ce rayuwa mafi kyau. Bayan da ya yi baftisma, yakan yi tunani a kan yadda Ishaya 65:25 ta cika a kansa. Dā kamar zaki yake don mugun halinsa, amma yanzu ya zama kamar ɗan rago don ya zama mai son zaman lafiya.
15. Me ya sa muke so mu jawo mutane su zo su zama ꞌyan iyalin Jehobah, kuma ta yaya za mu yi hakan?
15 Ishaya 65:13 ta fara da cewa: “In ji Ubangiji Yahweh.” Aya ta 25 kuma ta kammala da cewa “Ni Yahweh na faɗa.” A koyaushe, Jehobah yana cika alkawarinsa. (Isha. 55:10, 11) A yau, muna bauta masa cikin yanayi mai kama da aljanna, kamar yadda ya yi alkawari. Jehobah ya sa muna bauta masa a matsayin iyali da babu irinta. Da yake muna a cikin iyalinsa, muna more salama da kwanciyar hankali a wannan duniyar da ke cike da mugunta. (Zab. 72:7) Shi ya sa muke so mu taimaka wa dukan mutane su zo su bauta ma Allah tare da mu. Ta yaya za mu taimaka musu? Ta wurin sa ƙwazo a aikin almajirtarwa.—Mat. 28:19, 20.
YADDA ZA MU SA MUTANE SU YI MARMARIN BAUTA MA JEHOBAH TARE DA MU
16. Me yake sa mutane su yi marmarin bauta ma Jehobah tare da mutanensa?
16 Akwai abin da kowannenmu zai iya yi don ya sa mutane su yi marmarin bauta wa Jehobah tare da mu. Don mu yi hakan, dole mu yi koyi da Jehobah. Jehobah ba ya sa mutane dole su shigo cikin ƙungiyarsa. A maimako, a hankali ne Jehobah yakan “jawo” mutum, idan ya ga cewa mutumin yana so ya kusace shi. (Yoh. 6:44; Irm. 31:3) Idan masu zuciyar kirki suka fahimci yawan ƙaunar Jehobah da halayensa masu ban shaꞌawa, hakan yana sa su yi kusa da shi. Ta yaya halayenmu masu kyau za su sa mutane su yi marmarin bauta ma Jehobah tare da mu?
17. Me za mu yi don mu sa mutane su yi marmarin bauta ma Jehobah tare da mu?
17 Idan mutane suka ga cewa muna nuna wa ꞌyanꞌuwanmu ƙauna da alheri, za su yi marmarin bauta ma Jehobah tare da mu. Muna so waɗanda suka zo taronmu a ƙaro na farko su ga cewa ‘lallai Allah yana cikinmu.’ Da alama wasu da suka je taron Kiristoci a Korinti a dā sun yi wannan furucin. (1 Kor. 14:24, 25; Zak. 8:23) Shi ya sa muke bukatar mu bi gargaɗin da aka yi mana cewa mu “yi zaman lafiya da juna.”—1 Tas. 5:13.
18. Me zai sa mutane su yi marmarin bauta ma Jehobah tare da mu?
18 A kullum, zai dace mu yi iya ƙoƙarinmu don mu kasance da raꞌayin Jehobah game da ꞌyanꞌuwanmu. Za mu yi hakan idan muna lura da halayensu masu kyau ba kurakurensu ba, don a ƙarshe, za su zama kamilai. Idan matsala ta taso a tsakaninmu, za mu iya sasantawa cikin ƙauna. Ta yaya? Ta wurin “yi wa juna kirki,” da jin “tausayin juna,” da kuma “yafe wa juna.” (Afis. 4:32) Hakan zai sa waɗanda suke so a nuna musu irin wannan ƙaunar su yi marmarin bauta ma Jehobah tare da mu. b
KA CI-GABA DA BAUTA MA JEHOBAH TARE DA MUTANENSA
19. (a) Bisa ga akwatin nan “ Sun Bar Ƙungiyar Jehobah Amma Sun Dawo,” mene ne waɗanda suka bar ƙungiyar Jehobah suka ce bayan sun dawo? (b) Me ya kamata mu ƙuduri niyyar yi? (Ka kuma duba hoton.)
19 Muna godiya sosai don yanayin salama da haɗin kai da muke morewa a bautarmu ga Jehobah! Ba a taɓa jin daɗin bauta ma Jehobah a ƙungiyarsa kamar yanzu ba, kuma mutanen da suke masa sujada sai ƙaruwa suke yi. Bari mu ci-gaba da gode ma Jehobah don wannan yanayi mai kama da aljanna da ya sa mu a ciki. Duk wanda yake so ya samu wartsakewa, da gamsuwa, da kwanciyar hankali da kuma kāriya, dole ya zo ya bauta ma Jehobah tare da mutanensa kuma ya ci-gaba da yin hakan har abada! Amma ka tuna cewa ƙoƙarin Shaiɗan shi ne ya ruɗe mu don mu daina bauta ma Jehobah tare da mutanensa. (1 Bit. 5:8; R. Yar. 12:9) Kada mu yarda masa. Bari mu sa ƙwazo sosai wajen kiyaye wannan yanayi mai kyau, mai tsabta da kuma salama, da muke morewa a bautarmu ga Jehobah.
MECE CE AMSARKA?
-
Wane irin aljanna ne bayin Jehobah suke ciki a yau?
-
Waɗanne abubuwa ne muke morewa don muna bauta ma Jehobah tare da mutanensa a yau?
-
Ta yaya za mu sa mutane su yi marmarin zuwa su bauta ma Jehobah tare da mu?
WAƘA TA 144 Mu Riƙa Ɗokin Samun Ladan!
a MAꞌANAR WASU KALMOMI: Za mu iya kwatanta yanayi mai kyau da muke bauta ma Jehobah a ciki a yau da aljanna. Muna kuma jin daɗin kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah da kuma ꞌyanꞌuwanmu.
b Don ka ga yadda bauta ma Jehobah tare da mutanensa ya amfani wata ꞌyarꞌuwa, ka je jw.org/ha kuma ka kalli bidiyon nan: Ina Suke Yanzu? Alena Žitníková: Yadda Burina Ya Cika.
c BAYANI A KAN HOTO: Yayin da sauran ꞌyanꞌuwa suna jin daɗin yin hira da juna kafin a soma taro, wani ɗanꞌuwa ya zauna shi kaɗai.