Ka Sani?
Me ya sa waɗanda ba Yahudawa ba suna cikin sojojin Sarki Dauda?
A CIKIN sojojin Dauda, akwai mutanen da ba Israꞌilawa ba ne. Alal misali, Zelek mutumin Ammon da Uriya mutumin Hitti da kuma Itma mutumin Mowab. a (1 Tar. 11:39, 41, 46) Ban da haka ma, akwai “Cherethawa,” da “Pelethawa” da kuma “Gittiyawa” a cikinsu. (2 Sam. 15:18, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Da alama cewa Cherethawa da Pelethawa suna da alaƙa sosai da Filistiyawa. (Ezek. 25:16) Kuma Gittiyawa Filistiyawa ne da suke zama a birnin Gat.—Yosh. 13:2, 3; 1 Sam. 6:17, 18.
Me ya sa Dauda ya yarda irin mutanen nan su zama sojojinsa? Domin yana da tabbaci cewa za su riƙe aminci a gare shi da kuma Jehobah. Alal misali, ga abin da wani ƙamus da ke bayyana Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da Cherethawa da Pelethawa, ya ce: “Da Dauda yake sarauta, ya fuskanci matsaloli sosai, amma mutanen nan ba su bar shi ba.” Me ya nuna hakan? A lokacin da “dukan mutanen Israꞌila” suka bar Sarki Dauda kuma suka bi wani mai rikici da sunansa Sheba, Cherethawa da Pelethawa ba su bar shi ba, kuma sun taimaka masa ya yi maganin Sheba. (2 Sam. 20:1, 2, 7) Ban da haka ma, akwai lokacin da ɗan Dauda mai suna Adoniya ya yi ƙoƙari ya kwace sarauta. Amma Cherethawa da Pelethawa ba su bi Adoniya ba, sun taimaka wa Dauda ya naɗa Sulemanu sarki domin shi ne wanda Jehobah ya zaɓa.—1 Sar. 1:24-27, 38, 39.
Wani mutum kuma da ya riƙe amincinsa ga Dauda sosai shi ne Ittai mutumin Gat. A lokacin da ɗan Dauda mai suna Absalom ya yi masa tawaye, kuma ya yi ƙoƙari ya saci zukatan mutanen Israꞌila su mai da shi sarki maimakon Dauda, Ittai da sojojinsa guda 600 sun goyi bayan Dauda. Dauda ya gaya wa Ittai kar ya bi shi don shi baƙo ne. Amma Ittai ya ce: “Na rantse da Sunan Yahweh mai rai da kuma ran sarki, duk inda za ka tafi, ko a mutu ko a yi rai, ni bawanka zan bi ka.”—2 Sam. 15:6, 18-21.
Duk da cewa Cherethawa da Pelethawa da Gittiyawa ba Israꞌilawa ba ne, sun yi imani cewa Jehobah ne Allah na gaskiya kuma Dauda ne wanda Jehobah ya zaɓa. Ba shakka Dauda ya yi farin ciki sosai da ya samu irin waɗannan maza masu riƙon amana.
a A littafin Maimaitawar Shariꞌa 23:3-6, Allah ya ba da doka cewa kada Ammonawa da Mowabawa su shiga cikin jamaꞌar Israꞌila. Amma da alama cewa abin da dokar nan take nufi shi ne, ba za su iya zama cikakkun ꞌyan ƙasa kamar sauran Israꞌilawan ba. Amma za su iya yin tarayya da su kuma su zauna a ƙasar Israꞌila idan suna bauta ma Jehobah. Ka duba Insight on the Scriptures, Littafi na 1, shafi na 95.