TARIHI
Rashin Ƙarfina Ya Sa Na Ga Ikon Jehobah
A LOKACIN da ni da matata muka je Kwalambiya a 1985, ana rikici da tashin hankali sosai a wurin. A biranen ƙasar, jamiꞌan tsaro suna fama da masu sayar da miyagun kwayoyi. A yankin da akwai tuddai kuma, suna fama da ꞌyan taꞌadda. Daga baya an tura mu yin hidima a birnin da ake kira Medellín, kuma a wurin, matasa da yawa suna yawo da bindiga. Suna da rukunonin ꞌyan daɓa da suke sayar da miyagun ƙwayoyi, suna tilasta wa mutane su ba su kuɗi in ba hakan ba su illata su, kuma ana hayar su su je su yi kisa. Irin mutanen nan suna mutuwa da wuri. Da muka je wurin, mun ji kamar an jefa mu wata duniya ne dabam.
Amma yaya aka yi mutane biyu daga ƙasar Finlan da ke can arewacin duniya, suka sami kansu a Amerika ta Kudu? Kuma waɗanne darussa ne na koya a cikin shekarun nan?
YADDA NA TASO A ƘASAR FINLAN
A shekara ta 1955 ne aka haife ni, kuma ni ne ƙarami cikin maza uku da iyayenmu suka haifa. Mun yi zama a birnin Vantaa da ke kusa da teku a kudancin Finlan.
ꞌYan shekaru kafin a haife ni ne mahaifiyata ta yi baftisma ta zama Mashaidiyar Jehobah. Mahaifinmu bai so hakan ba ko kaɗan, kuma ya ce kar mahaifiyarmu ta yi nazari da mu ko ta kai mu taro. Don haka, takan jira sai mahaifinmu ya fita kafin ta koya mana abubuwa daga Littafi Mai Tsarki.
Tun ina ƙarami na ce zan bauta ma Jehobah. Da nake shekara bakwai, akwai lokacin da malamarmu a makaranta ta yi fushi da ni don na ƙi cin wani irin gurasa da ake kira verilättyjä (gurasa ce da ake yi da jini a ƙasar Finlan). Malamar ta matse min kumatu da ƙarfi har sai da na buɗe baki, kuma ta yi ƙoƙarin sa min gurasar a baki. Amma sai na yi ƙoƙari na buge cokalin da yake hannunta.
Mahaifinmu ya rasu lokacin da nake shekara 12. Sai na soma zuwa taron ikilisiya. ꞌYanꞌuwa da ke ikilisiyar sun so ni, kuma ƙaunar da suka nuna min ya sa na samu ci-gaba sosai. Na fara karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana, ina kuma nazarin littattafanmu sosai. Ƙwazo da na saka wajen yin nazari ne ya taimaka min na yi baftisma da nake shekara 14, wato a ran 8 ga Agusta, 1969.
Ina gama makaranta, sai na soma hidimar majagaba. Bayan ꞌyan makonni, sai na je yin hidima a inda ake da bukatar masu shela, a wani gari da ake kira Pielavesi, da ke tsakiyar ƙasar Finlan.
A garin Pielavesi ne na haɗu da wadda na aura, sunanta Sirkka. Sauƙin kanta da yadda take ƙaunar Jehobah ne ya burge ni. Ita ba mai son yin suna ko abin duniya ba ce. Babban burinmu a lokacin shi ne mu yi iya ƙoƙarinmu a bautar Jehobah kuma mu yi duk wani aiki da aka ce mu yi. Mun yi aure a ran 23 ga Maris, 1974. Bayan auren, maimakon mu je mu shaƙata kamar yadda sabbin maꞌaurata suke yi, mun ƙaura zuwa wani gari mai suna Karttula, don ana bukatar masu yin waꞌazi sosai a wurin.
JEHOBAH YA KULA DA MU
Tun lokacin da muka yi aure, Jehobah ya yi ta nuna mana cewa zai biya bukatunmu idan muka sa alꞌamuran Mulkinsa farko a rayuwarmu. (Mat. 6:33) Alal misali, lokacin da muke garin Karttula ba mu da mota, da keke muke zuwa wurare. Idan lokacin sanyi ya zo, akan yi sanyi sosai har da ƙanƙara, kuma yankin da muke waꞌazi yana da girma sosai. Don haka sai da mota za mu iya zuwa yin waꞌazi, amma ba mu da kuɗin sayan mota.
Ana nan kawai sai yayana ya kawo mana ziyara. Da ya zo sai ya ba mu motarsa, kuma ya riga ya biya kuɗin inshora a kai. Abin da ya rage mana shi ne mu sa mai kawai. Yadda aka yi muka sami motar da muke bukata ke nan.
Jehobah ya nuna mana cewa hakkinsa ne ya biya bukatunmu. Abin da yake so mu yi kawai shi ne, mu sa yin aikinsa farko a rayuwarmu.
MAKARANTAR GILEAD
Da muke Makarantar Hidima ta Majagaba a shekara ta 1978, wani malaminmu mai suna Raimo Kuokkanen a ya shawarce mu mu cika fom na zuwa Makarantar Gilead. Ba mu iya Turanci ba, don haka mun soma koyo don mu cancanci zuwa makarantar. Amma kafin mu cika fom na makarantar, sai aka kira mu mu yi hidima a ofishinmu da ke Finlan, a shekara ta 1980 ke nan. Ga shi lokacin idan kana a Bethel, ba za ka iya zuwa Makarantar Gilead ba. Mu dai ba mu damu ba, mun bar Jehobah ya zaɓa mana inda ya ga ya fi dacewa mu yi hidima. Saboda haka, mun je yin hidima a Bethel. Amma ba mu daina koyan Turanci ba, don a tunaninmu, wataƙila wata rana mu samu damar zuwa Gilead.
Ana nan bayan ꞌyan shekaru, sai Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta ce waɗanda suke hidima a Bethel ma za su iya zuwa Makarantar Gilead. Don haka nan-da-nan muka cika fom na makarantar. Ba don ba ma jin daɗin hidimar da muke yi a Bethel ne muka cika fom na Makarantar Gilead ba. Mun yi hakan ne don idan an fi bukatarmu a wani wuri kuma an ga mun cancanta, a yi amfani da mu. An gayyace mu Makarantar Gilead, kuma muna cikin ꞌyan aji na 79. Da muka sauke karatu a watan Satumba 1985, sai aka tura mu yin hidima a Kwalambiya.
INDA MUKA SOMA YIN HIDIMAR MASU WAꞌAZI A ƘASAR WAJE
Da muka isa Kwalambiya, sai aka ce mu yi hidima a reshen ofishinmu da ke wurin. Na yi iya ƙoƙarina a aikin da aka ba ni, amma bayan shekara guda, sai na ga cewa ina bukatar a canja min wannan hidimar. A duk rayuwata, ban taɓa cewa a canja min hidimar da nake yi ba, amma a wannan karon na yi haka. Sai aka ce mu je yin waꞌazi a birnin Neiva, da ke wani yanki da ake kira Huila.
Tun dā ma ina son yin waꞌazi sosai. Da nake hidimar majagaba a Finlan, kafin in yi aure, wani lokaci nakan fita yin waꞌazi da sassafe kuma ni da dawowa sai dare. Bayan aurenmu ma, ni da Sirkka mukan wuni muna waꞌazi. Idan muka je yin waꞌazi a wuri mai nesa, wani lokaci a mota mukan kwana. Hakan yana rage mana yawan tafiye-tafiye, kuma yana sa mu yi saurin fita waꞌazi washegari.
Don haka, da muka bar ofishinmu kuma muka koma yin waꞌazi, sai ƙwazon da muke da shi a dā ya dawo. Ikilisiyar da muke ciki ta samu ƙaruwa sosai, kuma ꞌyanꞌuwanmu da ke Kwalambiya sun girmama mu, sun nuna mana ƙauna, kuma sun yi godiya don abubuwan da muke yi.
ADDUꞌA TANA DA IKO SOSAI
Na damu don akwai garuruwa da suke kusa da birnin Neiva da babu Mashaidi ko ɗaya. Na yi ta tunanin yadda za a yi mu je waꞌazi a wurin. Amma idan kai ba mutumin wurin ba ne, zuwa yin waꞌazi a wurin zai zama maka da haɗari sosai don ana yawan rikici da taꞌaddanci a wurin. Shi ya sa na roƙi Jehobah ya sa wani mutumin wurin ya zama Mashaidi. Kuma na yi tunani cewa kafin mutum ya koyi gaskiya, dole ya yi zama a birnin Neiva. Don haka, na sake roƙon Jehobah ya sa mutumin ya yi baftisma, ya samu ci-gaba sosai, kuma ya koma garinsu don ya yi waꞌazi. Ban san cewa Jehobah yana shirin magance wannan matsalar a wata hanya da ta fi wadda nake tunani ba.
Ba da jimawa ba sai na soma nazari da wani mai suna Fernando González. Mutumin yana zama ne a ɗaya daga cikin garuruwan nan da babu Mashaidi, sunan wurin Algeciras ne. Fernando yakan yi tafiyar da ta fi kilomita 50 daga wurin zuwa Neiva kowane mako don ya yi aiki. A nan ne muke samu mu yi nazari. Yakan yi shiri sosai kafin nazarin, kuma ba tare da ɓata lokaci ba, ya soma zuwa taro. Tun makon da na soma yin nazari da shi, idan Fernando ya koma gida, yakan tattara mutanen ƙauyensu ya koya musu abubuwan da ya koya a nazarinmu
Bayan wata shida, Fernando ya yi baftisma, a Janairu 1990 ke nan. Bayan haka, sai ya soma hidimar majagaba na kullum. Yanzu da an sami
mutumin Algeciras da ya zama mashaidi, sai ofishinmu ta ga cewa za su iya tura majagaba na musamman su je yin waꞌazi a yankin. A Fabrairu 1992, an kafa ikilisiya a garin.Shin a garinsu ne kawai Fernando ya yi waꞌazi? Aꞌa. Da ya yi aure, shi da matarsa sun ƙaura zuwa wani gari da babu Mashaidi, ana kiran garin San Vicente del Caguán. Har sun kafa ikilisiya a wurin. A 2002, Ɗanꞌuwa Fernando ya zama mai kula da daꞌira, kuma shi da matarsa mai suna Olga suna wannan hidimar har yau.
Abin da ya faru ya koya min muhimmancin yin adduꞌa a kan wasu abubuwa da suka danganci hidimar da muke yi. Jehobah yana yin abubuwan da ba za mu iya yi ba. Ballantana ma, girbin nasa ne ba namu ba.—Mat. 9:38.
JEHOBAH YAKAN SA ‘MU YI NIYYA MU KUMA YI AIKI’
A 1990, an ce mu yi hidimar masu kula masu ziyara. Daꞌira ta farko da aka tura mu yin hidima tana a birnin tarayyar ƙasar Kwalambiya, wato birnin Bogotá. Da muka ji hakan mun ji tsoro. Ni da matata mun ga kamar ba za mu iya ba, don ba wani takamammen baiwa ne da mu ba, kuma ba mu saba zama a cikin birni haka ba. Amma, Jehobah ya sa abin da yake Filibiyawa 2:13 ya cika a kanmu. Wurin ya ce: “Gama Allah shi ne yake aiki a zuciyarku, shi ne yake sa ku yi niyya ku kuma yi aiki bisa ga kyakkyawan nufinsa.”
Bayan haka ne aka tura mu yin hidima a birnin Medellín da na yi zancensa a farkon wannan labarin. Mutanen wurin sun saba ganin ana faɗa da tashin hankali, har abin ya daina damunsu. Alal misali, akwai lokacin da nake nazari da wani mutum a gidansa sai aka soma harbin bindiga a waje. Da na ji harbin, na so in kwanta a ƙasa, amma sai na ga cewa mutumin ya ci-gaba da karanta sakin layin kamar ba abin da yake faruwa. Da ya gama karatun sai ya ce min yana zuwa kuma ya fita. An jima, sai ga shi da ƙananan yara guda biyu kuma ya ce min, “Yi haƙuri na fita ne don in shigar da yarana cikin gida.”
Akwai kuma wasu lokutan da muka tsallake rijiya da baya. Wata rana da muke waꞌazi, sai na ga matata ta taho a guje, tsoro ya shiga jikinta. Ta ce min wani ne ya so ya harbe ta da bindiga. Na yi mamaki da na ji hakan. Daga baya, sai muka gano cewa wani mutum da yake kusa da ita ne ake so a harbe, ba ita ba.
A-kwana-a-tashi sai muka saba da yanayin. Abin da ya ƙarfafa mu shi ne, mun ga yadda ꞌyanꞌuwa a yankin suke fuskantar irin wannan yanayin da ƙarfin zuciya. Wasu yanayoyin ma sun fi hakan haɗari, amma ꞌyanꞌuwan ba su karaya ba. Saboda haka, mun ce Jehobah wanda yake taimakonsu, zai taimaka mana. Mun dinga yin hattara muna bin shawarwarin da dattawan yankin suke ba mu, kuma mun dogara ga Jehobah.
Akwai kuma lokuta da muka ji tsoro, ashe abin da muke tsoronsa bai kai hakan ba. Alal misali, akwai ran da nake waꞌazi sai na ji kamar wasu mata biyu suna zagin juna a waje. Ban so in ga rikicin da suke yi ba. Amma sai wadda nake mata waꞌazi ta yi ta matsa min in zo in ga abin da yake faruwa. Da na fito baranda, sai na ga cewa ashe aku (parrot) guda biyu ne suke kwaikwayon yadda maƙwabtanta suke gardama.
ƘARIN AYYUKA DA KUMA ƘALUBALE
A 1997, an mai da ni malamin Makarantar Koyar da Masu Hidima. b Nakan so zuwa makarantun ƙungiyarmu, amma ban san cewa wata rana ni ma za a ce in yi koyarwa a irin makarantun nan ba.
Daga baya, na zama mai kula da gunduma. Da aka daina irin wannan hidimar, sai na koma yin hidimar mai kula da daꞌira. Saboda haka na yi fiye da shekaru 30 ina yin hidimomi dabam-dabam kamar koyarwa a makarantunmu, da kuma hidimar mai kula mai ziyara. Na samu albarku da yawa da nake yin waɗannan ayyukan. Amma ba a kullum ne kome ya tafi sumul ba.
Alal misali, ni mutum ne mai ƙarfin zuciya da ƙwazo, kuma hakan ya taimaka min na fuskanci yanayoyi masu wuya. Amma akwai lokutan da garin gyara yadda ake yin abubuwa a ikilisiya, na wuce gona da iri. Akwai lokacin da na yi ta ƙarfafa ꞌyanꞌuwa su riƙa nuna ƙauna da sanin yakamata. Amma a gaskiya, yadda na yi hakan bai nuna cewa ina ƙaunarsu, kuma na san yakamata ba.—Rom. 7:21-23.
Akwai lokutan da na yi sanyin gwiwa sosai domin kasawata. (Rom. 7:24) Har akwai lokacin da na yi adduꞌa na gaya wa Jehobah cewa gwamma in bar aikin yin waꞌazi a ƙasar waje in koma ƙasarmu, wato Finlan. Amma da na je taron ikilisiya ranar da yamma, na ji abin da ya ƙarfafa ni. Abin da na ji ya nuna min cewa zai yi kyau in ci-gaba da yin hidimata da kuma ƙoƙarin gyara halina. Har yau, idan na tuna yadda Jehobah ya amsa wannan adduꞌar tawa, ina godiya sosai. Ƙari ga haka, ina godiya ga Jehobah don alherin da ya yi min, da yadda ya taimaka min in shawo kan kasawata.
YANZU NA SAN KO DA ME ZAI FARU, JEHOBAH ZAI TAIMAKE NI
Ni da matata Sirkka muna godiya sosai ga Jehobah don damar da ya ba mu mu yi yawancin rayuwarmu muna hidima ta cikakken lokaci. Na kuma gode masa da ya ba ni irin wannan mace mai aminci, da take ƙaunata sosai.
Nan ba da daɗewa ba zan cika shekaru 70, kuma zan daina hidimar mai kula da daꞌira da koyarwa a makarantunmu. Amma hakan bai dame ni ba. Me ya sa? Don na san cewa abin da ya fi sa Jehobah farin ciki shi ne, mu bauta masa da sauƙin kai don muna ƙaunarsa da kuma gode masa. (Mik. 6:8; Mar. 12:32-34) Za mu iya ɗaukaka Jehobah ko da ba ma yin wani aiki na musamman.
Idan na dubi ayyuka da dama da na yi a ƙungiyar Jehobah, nakan ga cewa ba don na fi cancanta ko na fi wasu ꞌyanꞌuwa ƙwarewa ba ne. Sam! Ba abin da ya sa Jehobah ya ba ni damar yin ayyukan nan ke nan ba. Alheri ne Jehobah ya yi min da ya ba ni wannan gatan duk da kasawata. Na san cewa taimakon Jehobah ne ya sa na yi nasara. Hakika, kasawata ta sa an ga ikon Jehobah.—2 Kor. 12:9.
a An wallafa labarin Ɗanꞌuwa Raimo Kuokkanen a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Afrilu 2006. Jigon labarin shi ne, “Determined to Serve Jehovah.”
b Wannan makarantar ce aka mai da ita Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki.