TALIFIN NAZARI NA 34
Ka Koyi Darussa Daga Annabcin Littafi Mai Tsarki
“Waɗanda suke da hikima za su gane.”—DAN. 12:10.
WAƘA TA 98 Nassosi Hurarre Ne Daga Allah
ABIN DA ZA A TATTAUNA a
1. Me zai taimaka mana mu soma jin daɗin yin nazarin annabcin Littafi Mai Tsarki?
WANI ɗanꞌuwa matashi mai suna Ben ya ce: “Ina jin daɗin yin nazarin annabcin Littafi Mai Tsarki.” Kai ma kana jin daɗin nazarin annabcin Littafi Mai Tsarki? Ko dai kana jin tsoro don yana da wuyar fahimta? Wataƙila ma ba ka jin daɗinsa. Amma idan ka fahimci dalilin da ya sa Allah ya sa aka rubuta annabce-annabce a cikin Kalmarsa, mai yiwuwa hakan zai canja raꞌayinka game da su.
2. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
2 A talifin nan, za mu tattauna dalilin da ya sa ya kamata mu yi nazarin annabcin Littafi Mai Tsarki da kuma abin da zai taimaka mana mu yi hakan. Ƙari ga haka, za mu tattauna annabci guda biyu daga littafin Daniyel, kuma za mu ga yadda za mu amfana yanzu idan muka fahimci maꞌanarsu.
ME YA SA YA KAMATA MU YI NAZARIN ANNABCIN LITTAFI MAI TSARKI?
3. Me muke bukatar mu yi idan muna so mu fahimci annabcin Littafi Mai Tsarki?
3 Don mu iya fahimtar annabcin Littafi Mai Tsarki, muna bukatar taimakon Jehobah. Ka yi laꞌakari da misalin nan. A ce za ka je wani wuri da ba ka taɓa zuwa ba, amma abokin tafiyarka ya san wurin sosai. Ya san inda kake, kuma ya san inda kowace hanya ta nufa. Hankalinka zai kwanta ko ba haka ba? Jehobah yana kama da abokin tafiyar nan. Ya san abubuwan da za su faru da mu dalla-dalla. Don haka, idan muna so mu fahimci maꞌanar annabcin Littafi Mai Tsarki, dole ne mu nemi taimakon Jehobah.—Dan. 2:28; 2 Bit. 1:19, 20.
4. Me ya sa Jehobah ya sa aka rubuta annabce-annbace a Kalmarsa? (Irmiya 29:11) (Ka kuma duba hoton.)
4 Iyayen kirki sukan so yaransu su ji daɗin rayuwa a nan gaba. Abin da Jehobah yake so mu ma mu samu ke nan. (Karanta Irmiya 29:11.) Sai dai iyaye ba za su iya gaya wa yaransu abin da zai faru da su a nan gaba ba. Amma Jehobah zai iya yin hakan babu kuskure. Ya sa an rubuta annabce-annbace a Kalmarsa don ya sanar da mu muhimman abubuwan da za su faru a nan gaba. (Isha. 46:10) Don haka, annabce-annabcen kyaututtuka ne daga Ubanmu na sama. Amma me zai tabbatar maka da cewa abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa zai faru da gaske?
5. Mene ne Shaidu matasa za su iya koya daga labarin Max?
5 ꞌYanꞌuwanmu matasa da suke makaranta suna gamuwa da mutanen da ba sa daraja abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. Maganganunsu da ayyukansu za su iya sa Mashaidi ya soma shakkar imaninsa. Ga abin da ya faru da wani ɗanꞌuwa mai suna Max. Ya ce: “Da nake makaranta, na soma shakkar addinin da iyayena suke koya min da kuma Littafi Mai Tsarki.” Me iyayensa suka yi? Max ya ce: “Sun yi min magana a hankali duk da cewa abin ya dame su.” Iyayen Max sun yi amfani da Littafi Mai Tsarki sun amsa tambayoyi da ya yi musu. Shi ma Max bai naɗe hannunsa ba. Ya ce: “Na yi nazarin annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki da kaina kuma na gaya wa abokaina a ikilisiya abin da na koya.” Ta yaya hakan ya amfane shi? Max ya ce: “Hakan ya ba ni tabbacin cewa Littafi Mai Tsarki daga wurin Allah ne.”
6. Me kake bukatar ka yi idan kana shakka, kuma me ya sa?
6 Idan kai ma ka soma shakkar abin da Littafi Mai Tsarki ya ce, ba ka yi laifi ba. Sai dai kana bukatar ka ɗauki mataki, domin shakka kamar tsatsa take. Idan ba a kawar da ita ba, za ta iya ɓata abu mai daraja. Don ka kawar da shakkar da za ta iya ɓata bangaskiyarka, ka tambayi kanka cewa, ‘Na gaskata abubuwan da Littafi Mai Tsarki ya ce za su faru kuwa?’ Idan kana shakka, to ya kamata ka bincika annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki da suka riga suka cika. Bari mu tattauna yadda za ka yi hakan.
YADDA ZA KA YI NAZARIN ANNABCIN LITTAFI MAI TSARKI
7. Me ya taimaka wa Daniyel ya iya yin nazarin annabace-annabce? (Daniyel 12:10) (Ka kuma duba hoton.)
7 Idan ana zancen nazarin annabci, Daniyel abin koyi ne. Ya yi bincikensa da dalili mai kyau, burinsa ya san gaskiya. Kuma Daniyel mutum mai sauƙin kai ne, ya san cewa idan ya kusaci Jehobah kuma ya yi masa biyayya, Jehobah zai taimake shi ya fahimci annabce-annabcen. (Dan. 2:27, 28; karanta Daniyel 12:10.) Ya nuna sauƙin kansa ta yadda ya dogara ga Jehobah ya taimake shi. (Dan. 2:18) Ya kuma natsu ya yi bincike sosai. Ya yi nazarin Nassosin da ake da su a lokacin. (Irm. 25:11, 12; Dan. 9:2) Ta yaya kai ma za ka yi koyi da Daniyel?
8. Me ya sa wasu suke nazarin annabcin Littafi Mai Tsarki, amma me ya kamata mu yi?
8 Ka yi binciken da dalili mai kyau. Me ya sa kake so ka bincika annabcin Littafi Mai Tsarki? Kana yin hakan ne domin kana so ka san gaskiya? Idan haka ne, Jehobah zai taimake ka. (Yoh. 4:23, 24; 14:16, 17) Amma wasu suna bincika annabcin Littafi Mai Tsarki da wani dalili dabam. Wasu suna hakan don su nemi hujjar da za ta nuna cewa Littafi Mai Tsarki ba Kalmar Allah ba ce. Amma mu, muna bukatar mu yi binciken da dalili mai kyau. Ban da haka, akwai wani hali mai muhimmanci da muke bukata idan muna so mu fahimci annabcin Littafi Mai Tsarki.
9. Idan muna so mu fahimci annabcin Littafi Mai Tsarki, wane hali muke bukata? Ka bayyana.
9 Ka zama mai sauƙin kai. Jehobah ya ce zai taimaki masu sauƙin kai. (Yak. 4:6) Don haka, muna bukatar mu nemi taimakon sa idan muna so mu fahimci annabcin Littafi Mai Tsarki. Kuma idan muna da sauƙin kai, za mu amince da taimakon da bawa mai aminci mai hikima yake mana. Me ya sa? Don Jehobah yana amfani da bawan ne ya koyar da mu abubuwan da muke bukatar mu sani game da shi a daidai lokaci. (Luk. 12:42) Da yake Allahnmu ba na rikicewa ba ne, ba abin mamaki ba ne cewa hanya ɗaya tak yake amfani da ita ya taimaka mana mu fahimci gaskiyar da ke cikin Kalmarsa.—1 Kor. 14:33; Afis. 4:4-6.
10. Me ka koya daga labarin Esther?
10 Ka natsu ka yi bincike. Ka zaɓi annabcin da ka fi so ka fahimta. Saꞌan nan ka yi bincike a kansa. Abin da wata ꞌyarꞌuwa mai suna Esther ta yi ke nan. Ta so ta tabbatar da annabce-annabce da aka yi game da zuwan Almasihu. Ta ce: “Da nake shekara 15, na soma bincike sosai don in ga ko da gaske tun kafin Yesu ya zo duniya ne aka yi annabce-annabcen nan.” Abin da ta karanta game da littattafan da aka samo daga Tekun Gishiri ne ya tabbatar mata cewa haka ne. Ta ce, “Wasu rubuce-rubucen tun kafin zamanin Yesu aka yi su. Don haka, annabcin daga wurin Allah ne.” Amma binciken bai yi mata sauƙi ba. Ta ce, “Sai da na karanta wasu abubuwa sau da sau kafin na fahimce su. Amma ta ji daɗi don kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Bayan ta yi bincike a kan wasu annabce-annabce, ga abin da ta ce, “Yanzu ni da kaina na ga cewa abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa gaskiya ne!”
11. Me ya sa yake da kyau mu tabbatar wa kanmu cewa abin da Littafi Mai Tsarki ya ce gaskiya ne?
11 Idan muka ga yadda annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki suka cika, hakan zai sa mu dogara ga Jehobah kuma mu yarda da duk wani umurnin da ya ba mu. Ban da haka ma, abubuwan da Littafi Mai Tsarki ya ce za su faru a nan gaba suna ba mu bege. Kuma begen nan yana ƙarfafa mu mu jimre kowace irin matsala. Yanzu bari mu ɗan bincika wasu annabce-annabce guda biyu da Daniyel ya rubuta kuma suke cika a yau. Idan muka fahimce su, hakan zai taimaka mana mu tsai da shawarwari masu kyau a rayuwa.
YADDA TAFIN ƘAFAFU NA ƘARFE GAURAYE DA LAKA YA SHAFE KA
12. Me tafin ƙafafun gunkin da aka yi da “baƙin ƙarfe gauraye da laka” yake nufi? (Daniyel 2:41-43)
12 Karanta Daniyel 2:41-43. A mafarkin da Daniyel ya bayyana wa Sarki Nebukadnezzar, “da baƙin ƙarfe gauraye da laka” aka yi tafin ƙafafun gunkin. Da muka gwada abin da ke annabcin nan da wasu annabce-annabce da ke littafin Daniyel da kuma Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna, mun ga cewa Mulkin Burtaniya da Amurka ne ake nufi da tafin ƙafafun gunkin, kuma mulkin ne ya fi iko a duniya a yau. Da yake zancen wannan mulkin, Daniyel ya ce “zai kasance gauraye da ƙarfi da rashin ƙarfi.” Me zai jawo rashin ƙarfin? Mutanen mulkin da aka kwatanta da laƙa, za su hana mulkin amfani da ikon da yake da shi. b
13. Waɗanne abubuwa masu muhimmanci ne wannan annabcin ya koya mana?
13 Abin da Daniyel ya faɗa game da gunkin nan ya koya mana abubuwa da yawa, musamman tafin ƙafafun gunkin. Mulkin Burtaniya da Amurka ya nuna cewa yana da iko sosai a wasu hanyoyi. Misali, Burtaniya da Amurka suna cikin ƙasashe da suka ci Yaƙin Duniya na 1 da na 2. Sai dai wani abin da ke rage ƙarfin wannan mulkin shi ne yadda talakawansa suke gwagwarmaya da juna kuma suke adawa da gwamnatin. Na biyu, wannan mulkin shi ne zai zama mulki na ƙarshe da zai yi mulkin duniya kafin Mulkin Allah ya halaka dukan mulkokin ꞌyan Adam. Duk da cewa wasu ƙasashe suna hamayya da Burtaniya da Amurka, ba za su iya kwace mulkin ba. Muna da wannan tabbacin domin “dutse” da ke wakiltar Mulkin Allah ne zai farfashe tafin ƙafafun gunkin wanda shi yake wakiltar Mulkin Burtaniya da Amurka.—Dan. 2:34, 35, 44, 45.
14. Me ya sa fahimtar annabcin tafin ƙafafun baƙin ƙarfe gauraye da laka, zai taimaka mana mu yi zaɓi mai kyau?
14 Ka gaskata abin da annabcin Daniyel ya ce game da tafin ƙafafun gunkin da aka yi da baƙin ƙarfe gauraye da laka? Idan ka gaskata, hakan zai shafi yadda kake yin rayuwarka. Ba za ka duƙufa neman kuɗi sosai ko ka tara abin duniya ba don ka san cewa an kusan halaka wannan duniya. (Luk. 12:16-21; 1 Yoh. 2:15-17) Kuma idan ka fahimci annabcin nan, za ka ga cewa yin waꞌazi da kuma koyarwa suna da muhimmanci sosai. (Mat. 6:33; 28:18-20) Yanzu da muka ɗan bincika wannan annabcin, ka tambayi kanka cewa, ‘Shin irin zaɓin da nake yi a rayuwa, yana nuna cewa na gaskata Mulkin Allah ya kusan halaka dukan mulkokin duniya?’
YADDA ANNABCIN “SARKIN AREWA” DA “SARKIN KUDU” YA SHAFE KA
15. Su wane ne suke wakiltar “sarkin arewa,” da kuma “sarkin kudu” a yau? (Daniyel 11:40)
15 Karanta Daniyel 11:40. Littafin Daniyel sura 11 ta yi zancen sarakuna ko kuma masu mulki guda biyu da suka yi ta kokuwa da juna a kan mulkin duniya. Da muka gwada abin da ke annabcin nan da sauran annabce-annabcen da ke Littafi Mai Tsarki, mun ga cewa a yau Rasha da ƙasashen da ke goyon bayanta su ne “sarkin arewa,” saꞌan nan Mulkin Burtaniya da Amurka shi ne “sarkin kudu.” c
16. Mene ne waɗanda suke zama a inda “sarkin arewa” yake mulkin suke fuskanta?
16 “Sarkin arewa” yana tsananta wa mutanen Allah da suke a ƙarƙashinsa sosai. An yi ma wasu Shaidun Jehobah dūka kuma an kai su kurkuku saboda imaninsu. Amma maimakon tsanantawa da sarkin yake musu ta sa ꞌyanꞌuwanmu su ja da baya, ta ma ƙara musu bangaskiya ne. Me ya sa? Domin ꞌyanꞌuwanmu sun san cewa wannan tsanantawa da ake yi wa mutanen Allah yana cika annabcin da Daniyel ya yi ne. d (Dan. 11:41) Mu ma idan muka san hakan, zai ƙara ba mu bege kuma zai sa mu ƙudiri niyyar riƙe amincinmu.
17. Me da me suka jarraba bangaskiyar mutanen Allah a ƙasashen da “sarkin kudu” yake mulki?
17 A dā, “sarkin kudu” shi ma ya tsananta wa mutanen Allah. Misali, a lokacin Yaƙin Duniya na 1 da na 2, ya sa an kulle ꞌyanꞌuwanmu da yawa a kurkuku don sun ƙi yin aikin soja. Ban da haka, an kori yaran Shaidun Jehobah da yawa daga makaranta don sun ƙi su sara wa tutar ƙasarsu. A shekarun baya-bayan nan, ta wasu hanyoyi dabam ne ake jarraba bangaskiyar waɗanda suke zama a ƙasashen da wannan sarkin yake mulki. Misali, idan aka zo lokacin zaɓe, mai yiwuwa Kirista ya so ya goyi bayan wani ɗan takara ko wata jamꞌiya. Ko da bai je ya yi zaɓe ba, ƙila can cikin zuciyarsa yana fatan cewa wannan jamꞌiyar ko waccan ta ci zaɓen. Yana da muhimmanci sosai mu nuna cewa ba ruwanmu da siyasar duniyar nan a furucinmu da ayyukanmu, har ma da tunanin zuciyarmu!—Yoh. 15:18, 19; 18:36.
18. Ya muke ji in muka ga “sarkin arewa” da “sarkin kudu” suna jayayya da juna? (Ka kuma duba hoton.)
18 Ƙila hankalin waɗanda ba su gaskata da Littafi Mai Tsarki ba ya tashi sosai idan suka ga “sarkin kudu” ya kai wa “sarkin arewa” hari. (Dan. 11:40) Domin su biyun suna da boma-bomai na nukiliya da za su iya halaka duniyar nan gabaki ɗaya. Amma mun san Jehobah ba zai bar hakan ya faru ba. (Isha. 45:18) Don haka, maimakon jani-in-jaka da “sarkin kudu” da “sarkin arewa” suke yi da juna ya sa mu ji tsoro, yana ma ƙara mana bangaskiya ne. Ya nuna cewa ƙarshen duniyar nan ya kusa.
KA CI GABA DA NAZARIN ANNABCI
19. Wane tabbaci ne ya kamata mu kasance da shi game da annabcin Littafi Mai Tsarki?
19 Ba mu san yadda wasu annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki za su cika ba. Annabi Daniyel da kansa ma bai gama gane abubuwan da ya rubuta ba. (Dan. 12:8, 9) Amma ko da ba mu gama gane yadda wani annabci zai cika ba, tabbas zai cika. Muna da tabbaci cewa idan lokaci ya yi, Jehobah zai fahimtar da mu kamar yadda ya yi a dā.—Amos 3:7.
20. Waɗanne muhimman annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki ne sun yi kusan cika, kuma me ya kamata mu yi?
20 Za a yi sanarwar “zaman lafiya da salama.” (1 Tas. 5:3) Saꞌan nan gwamnatocin duniyar nan za su fuskanci addinan ƙarya kuma su halaka su. (R. Yar. 17:16, 17) Bayan haka, za su kai wa mutanen Allah hari. (Ezek. 38:18, 19) Wannan hari ne zai kai ga yaƙi na ƙarshe, wato yaƙin Armageddon. (R. Yar. 16:14, 16) Babu shakka, dukan abubuwan nan za su faru nan ba da daɗewa ba. Yayin da muke jira, bari mu ci gaba da yin godiya ga Ubanmu na sama mai ƙauna ta wurin yin nazarin annabcin Littafi Mai Tsarki, kuma mu taimaki mutane su ma su yi hakan.
WAƘA TA 95 Muna Samun Ƙarin Haske
a Ko da yanayin duniya ya ci gaba da lalacewa, za mu iya kasance da tabbaci cewa abubuwa za su yi kyau a nan gaba. Yin nazarin annabcin Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana mu kasance da wannan tabbacin. Talifin nan zai bayyana dalilan da suka sa zai dace mu yi nazarin annabcin Littafi Mai Tsarki. Ban da haka, za mu tattauna annabce-annabce guda biyu da Daniyel ya rubuta. Kuma za mu ga yadda kowannenmu zai iya amfana idan ya fahimci maꞌanarsu.
b Ka duba sakin layi na 7-9 a talifin nan “Jehobah Ya Bayyana Alꞌamura da Lallai ‘Za Su Faru Ba da Daɗewa Ba’” da ke Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuni 2012.