TALIFIN NAZARI NA 33
Ka Yi Koyi da Daniyel
“Kai mai daraja ne sosai.”—DAN. 9:23.
WAƘA TA 73 Ka Ba Mu Ƙarfin Zuciya
ABIN DA ZA A TATTAUNA a
1. Waɗanne abubuwa game da Daniyel ne suka burge Babiloniyawan?
ANNABI Daniyel matashi ne a lokacin da Babiloniyawa suka kama shi suka kai shi zaman bauta a Babila, inda yake da nisa da Urushalima. Babu shakka, Daniyel ya burge su domin sun ga abin da mutum yake gani “daga waje,” wato, Daniyel yana da kyan gani, marar taɓo kuma ya fito daga iyalin da ake darajawa sosai. (1 Sam. 16:7) Waɗannan dalilan ne suka sa Babiloniyawan suka koyar da Daniyel don ya yi hidima a fadar sarki.—Dan. 1:3, 4, 6.
2. Yaya Jehobah ya ji game da Daniyel? (Ezekiyel 14:14)
2 Jehobah ya ƙaunaci Daniyel, ba don kyansa ko matsayinsa ba, amma saboda halayensa masu kyau. Mai yiwuwa shekarun Daniyel wajen 20 ne a lokacin da Jehobah ya kwatanta shi da Nuhu da Ayuba. Ko da yake Daniyel matashi ne, a gun Jehobah, shi mai adalci ne kamar Nuhu da Ayuba, waɗanda suka daɗe suna bauta masa da aminci. (Far. 5:32; 6:9, 10; Ayu. 42:16, 17; karanta Ezekiyel 14:14.) Kuma Jehobah ya ci gaba da ƙaunar Daniyel har iyakar rayuwarsa.—Dan. 10:11, 19.
3. Mene ne za mu tattauna a talifin nan?
3 A wannan talifin, za mu tattauna halayen Daniyel guda biyu da suka sa Jehobah ya ƙaunace shi sosai. Da farko, za mu yi bayani a kan kowane hali, saꞌan nan mu tattauna yanayoyin da Daniyel ya nuna halayen nan. Na biyu, za mu ga abin da ya taimaka wa Daniyel ya kasance da halayen nan. Na uku, za mu tattauna yadda za mu yi koyi da shi. Ko da yake an shirya talifin nan musamman don matasa ne, dukanmu za mu iya koyan darasi daga Daniyel.
KA NUNA ƘARFIN ZUCIYA KAMAR DANIYEL
4. Ta yaya Daniyel ya nuna ƙarfin zuciya? Ka ba da misali.
4 Mutum mai ƙarfin zuciya zai iya jin tsoro, amma ba zai bar tsoron ya hana shi yin abin da ya dace ba. Daniyel matashi ne mai ƙarfin zuciya sosai. Ka ga yadda Daniyel ya nuna ƙarfin zuciya a yanayoyi guda biyu. Da alama na farkon ya faru ne wajen shekaru biyu bayan da Babiloniyawa suka hallaka Urushalima. Sarkin Babila, wato, Nebukadnezzar ya yi mafarki mai ban tsoro game da wani babban gunki. Ya ce zai kashe dukan masu hikima na Babila, har da Daniyel idan har ba su gaya masa mafarkin da ya yi, da maꞌanarsa ba. (Dan. 2:3-5) Daniyel yana bukatar ya yi wani abu nan da nan, in ba haka ba, mutane da yawa za su mutu. Sai “ya shiga wurin sarki, ya roƙe shi ya ba shi lokaci domin ya bayyana masa maꞌanar mafarkin.” (Dan. 2:16) Daniyel ya yi hakan ne domin yana da ƙarfin zuciya da kuma bangaskiya. Babu inda aka nuna a Littafi Mai Tsarki cewa Daniyel ya taɓa faɗan maꞌanar mafarki kafin wannan lokacin. Ya gaya wa abokansa Shadrach da Meshach da Abednego, cewa “su nemi jinƙai daga wurin Allah na sama game da wannan asirin.” (Dan. 2:18) b Jehobah ya amsa adduꞌoꞌinsu. Da taimakonsa, Daniyel ya bayyana maꞌanar mafarkin Nebukadnezzar kuma hakan ya sa ba a kashe Daniyel da abokanansa ba.
5. Wane abu ne kuma ya faru da ya bukaci Daniyel ya yi ƙarfin zuciya?
5 Bayan Daniyel ya bayyana maꞌanar mafarkin babban gunkin, wani abu ya faru da ya bukaci Daniyel ya sake nuna ƙarfin zuciya. Nebukadnezzar ya sake yin wani mafarki mai ban tsoro. Mafarkin game da wata babbar bishiya ce. Da ƙarfin zuciya, Daniyel ya gaya wa sarkin maꞌanar mafarkin, har ma ya gaya masa cewa zai haukace kuma ya rasa sarautarsa na ꞌyan shekaru. (Dan. 4:25) Abin da Daniyel ya faɗa zai iya sa sarkin ya ga kamar Daniyel maƙiyinsa ne, kuma ya ce a kashe shi. Duk da haka, Daniyel ya yi ƙarfin zuciya kuma ya bayyana maꞌanar mafarkin.
6. Mene ne ya taimaka wa Daniyel ya yi ƙarfin zuciya?
6 Mene ne ya taimaka wa Daniyel ya yi ƙarfin zuciya a dukan rayuwarsa? Babu shakka, saꞌad da Daniyel yake yaro, ya yi koyi da halaye masu kyau na iyayensa. Sun bi umurnin da Jehobah ya ba wa iyaye a Israꞌila kuma sun koya wa yaransu Dokar Allah. (M. Sha. 6:6-9) Daniyel ya san koyarwar Jehobah sosai. Ban da Dokoki Goma, ya san dabbobin da Jehobah ya amince Israꞌilawa su ci, da waɗanda ya haramta musu. c (L. Fir. 11:4-8; Dan. 1:8, 11-13) Ƙari ga haka, Daniyel ya san tarihin mutanen Allah, ya san abin da ya faru da su saꞌad da suka ƙi su bi dokokin Jehobah. (Dan. 9:10, 11) Abubuwan da Daniyel ya fuskanta a rayuwarsa sun sa ya kasance da tabbaci cewa Jehobah da malaꞌikunsa masu iko suna tare da shi.—Dan. 2:19-24; 10:12, 18, 19.
7. Waɗanne abubuwa ne kuma suka taimaka wa Daniyel ya yi ƙarfin zuciya? (Ka kuma duba hoton.)
7 Daniyel ya bincika abubuwan da annabawa suka rubuta, har da na annabi Irmiya. Ta haka ne Daniyel ya gano cewa zaman bauta da suke yi a Babila ya kusan ƙarewa. (Dan. 9:2) Daniyel ya ga yadda alkawarin Jehobah ya cika kuma hakan ya ƙara masa bangaskiya. Waɗanda suke da irin wannan bangaskiyar suna kasancewa da ƙarfin zuciya sosai. (Ga misali a Romawa 8:31, 32, 37-39.) Abu mafi muhimmanci da ya taimaka ma Daniyel shi ne, ya yi ta adduꞌa sosai ga Ubansa na sama. (Dan. 6:10) Ya gaya wa Jehobah laifuffukansa da yadda yake ji a zuciyarsa, kuma ya nemi taimakon Jehobah. (Dan. 9:4, 5, 19) Shi mutum ne kamar mu, don haka ba a haife shi da ƙarfin zuciya ba. A maimakon haka, ya kasance da halin nan ne domin ya yi nazari da adduꞌa sosai, kuma ya dogara ga Jehobah.
8. Me zai taimaka mana mu zama masu ƙarfin zuciya?
8 Me za mu yi idan muna so mu zama masu ƙarfin zuciya? Iyayenmu suna iya ƙarfafa mu mu yi ƙarfin zuciya. Amma ko da iyayenmu masu ƙarfin zuciya ne, hakan ba ya nufin cewa za mu zama da halin nan. Zama mai ƙarfin zuciya kamar koyan sabon abu ne. Idan kana koyan sabon abu, wani abin da zai taimaka maka shi ne, ka lura da yadda malaminka yake yin abin, saꞌan nan ka yi koyi da shi. Haka ma, za mu yi ƙarfin zuciya idan muna lura da yadda wasu suke nuna halin nan kuma muna yin koyi da su. Mene ne muka koya daga wurin Daniyel? Kamar Daniyel, muna bukatar mu san Kalmar Allah sosai. Muna bukatar mu riƙa tattaunawa da Jehobah a koyaushe, da gaya masa abin da ke zuciyarmu. Hakan zai sa mu kasance da dangantaka ta kud da kud da shi. Kuma muna bukatar mu dogara ga Jehobah, mu kasance da tabbacin cewa yana tare da mu. Idan mun yi hakan, za mu yi ƙarfin zuciya saꞌad da muka fuskanci yanayin da ya gwada bangaskiyarmu.
9. Ta yaya yin ƙarfin zuciya yake amfanar mu?
9 Idan muka nuna ƙarfin zuciya, za mu amfana sosai. Abin da ya faru da wani mai suna Ben ke nan. A lokacin da yake zuwa wata makaranta a Jamus, kowa a makarantar ya gaskata da juyin halitta, kuma cewa abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da halitta tatsuniya ne. Wata rana, Ben ya sami damar gaya wa kowa a ajin, dalilin da ya sa ya gaskata cewa Allah ne ya halicci abubuwa. Ben ya yi ƙarfin zuciya kuma ya gaya musu imaninsa. Wane sakamako ne hakan ya jawo? Ben ya ce: “Malamina ya saurare ni da kyau kuma ya kofe kayan binciken da na yi amfani da su don in bayyana imanina, saꞌan nan ya ba wa kowa a ajin.” Mene ne ꞌyan ajin Ben suka yi? Ben ya ce: “Da yawa daga cikinsu sun saurare ni kuma sun ce na burge su sosai.” Kamar yadda labarin Ben ya nuna, mutane sukan mutunta masu ƙarfin zuciya. Kuma nuna halin nan yakan sa masu zuciyar kirki su so su koya game da Jehobah. Hakika, muna da dalilai da yawa da suka sa ya kamata mu zama da ƙarfin zuciya.
KA ZAMA MAI AMINCI KAMAR DANIYEL
10. Me ake nufi da aminci?
10 A Ibrananci, kalmar nan “aminci” tana nufin mutum ya manne wa amininsa don yana ƙaunar sa. An yi amfani da kalmar sau da yawa a Littafi Mai Tsarki don a nuna irin ƙaunar da Allah yake yi wa bayinsa. Ban da wannan, an yi magana game da aminci da ƙauna marar canjawa da bayin Allah suke nuna ma juna. (2 Sam. 9:6, 7, NWT) Da shigewar lokaci, za mu iya ƙara kasancewa da aminci ga Jehobah. Bari mu ga yadda hakan ya faru da Daniyel.
11. Da Daniyel ya tsufa, wane abu ne ya faru da ya gwada amincinsa? (Ka duba hoton da ke shafin farko.)
11 A dukan rayuwar Daniyel, ya fuskanci abubuwan da suka gwada amincinsa ga Jehobah. Amma da ya ba shekaru 90 baya ne ya fuskanci wani abu da ya fi gwada amincinsa. A lokacin, mutanen Midiya da Fashiya sun ci Babiloniyawa da yaƙi, kuma Sarki Dariyus ne yake mulki. Waɗanda suke hidima a fadar sarki sun tsani Daniyel sosai kuma ba sa daraja Allahn da yake bauta wa. Sai suka ƙulla wani makirci don su kashe Daniyel. Sun sa an kafa doka da za ta sa ya zaɓi wanda zai yi wa aminci, ko Allah ko kuma sarki. Abin da Daniyel yake bukatar ya yi kawai shi ne ya ƙi yi wa Jehobah adduꞌa na kwanaki 30. Hakan zai nuna cewa yana yi wa sarkin aminci kamar kowa da kowa, amma Daniyel ya ƙi. Sai aka jefa shi a cikin ramin zakuna. Amma Jehobah ya sāka wa Daniyel don amincinsa ta wajen ceto shi daga bakin zakunan. (Dan. 6:12-15, 20-22) Me za mu yi don mu kasance da irin amincin Daniyel?
12. Me ya taimaka wa Daniyel ya kasance da aminci ga Jehobah?
12 Kamar yadda aka ambata ɗazu, sai muna ƙaunar Jehobah sosai ne za mu iya riƙe amincinmu gare shi. Da yake Daniyel yana ƙaunar Ubansa na sama, bai bar kome ya hana shi kasancewa da aminci ga Jehobah ba. Abin da ya taimaka wa Daniyel ya ƙaunaci Jehobah shi ne, ya yi tunani game da halayen Jehobah, da kuma yadda Jehobah ya nuna halayen. (Dan. 9:4) Ƙari ga haka, Daniyel ya yi tunani sosai game da abubuwa masu kyau da Jehobah ya yi masa da mutanensa, kuma ya yi godiya don hakan.—Dan. 2:20-23; 9:15, 16.
13. (a) Wane yanayi ne yake gwada amincin ꞌyanꞌwanmu matasa? Ka ba da misali. (Ka kuma duba hoton.) (b) Kamar yadda aka nuna a bidiyon, mene ne za ka ce idan wasu suka tambaye ka ko Shaidun Jehobah suna goyon bayan ꞌyan luwaɗi?
13 Kamar Daniyel, ꞌyanꞌuwanmu matasa suna rayuwa a tsakanin mutanen da ba sa daraja Jehobah da ƙaꞌidodinsa. Mutanen nan sukan ƙi jinin wanda imaninsa ya yi dabam da nasu. Wasu sukan yi ƙoƙarin tilasta wa matasanmu su yi abin da bai dace ba. Ga abin da ya faru da wani ɗanꞌuwa matashi mai suna Graeme a Ostareliya. Saꞌad da yake makarantar sakandare, ya fuskanci wani yanayi mai wuya. Wani malaminsu ya tambaye su a aji cewa me za su yi idan wani abokinsu ya gaya musu cewa shi ɗan luwaɗi ne? Malamin ya ce waɗanda za su goyi bayansa su tsaya a wani ɓangaren ajin; waɗanda ba za su goyi bayansa ba kuma su tsaya a wani ɓangare dabam. Graeme ya ce: “Ban da ni da wani Mashaidi a ajin, sauran sun yarda za su goyi bayansa.” Yanayin ya ƙara yin muni kuma Graeme ya bukaci ya nuna ko zai ci gaba da riƙe amincinsa. Ya ce: “Sauran ɗaliban, har da malamin sun yi ta zaginmu har muka ƙarasa aji na ranar kuma hakan ya ɗauki awa ɗaya. Na yi iya ƙoƙarina in bayyana imanina a hanyar da ta dace, amma ba su saurare ni ba ko kaɗan.” Yaya yanayin ya sa Graeme ya ji? Ya ce: “Ba na jin daɗi idan mutane suka zage ni, amma na yi farin ciki sosai domin na bayyana imanina kuma na riƙe aminci.” d
14. Me zai taimaka mana mu kasance da aminci ga Jehobah?
14 Kamar Daniyel, mu ma za mu iya kasance da aminci idan muna ƙaunar Jehobah sosai. Za mu ƙaunaci Jehobah idan muna koya game da halayensa. Alal misali, za mu iya yin nazari a kan abubuwan da ya halitta. (Rom. 1:20) Idan kana so ka ƙara ƙaunar Jehobah kuma ka daraja shi, ka karanta talifofin da ke jerin talifofin nan, “Halittarsa Aka Yi?” ko kuma ka kalli bidiyoyin. Ƙari ga haka, za ka iya karanta ƙasidun nan: Was Life Created? da kuma The Origin of Life—Five Questions Worth Asking. Ga abin da wata ꞌyarꞌuwa daga Denmark, mai suna Esther, ta ce game da littattafan nan: “Ƙasidun suna ɗauke da bayanai masu gamsarwa. Ba za su gaya maka abin da za ka gaskata ba amma za su ba ka bayanan gaskiya, saꞌan nan ka tsai da shawara da kanka.” Ben, da muka ambata ɗazu ya ce: “Ƙasidun sun ƙarfafa bangaskiyata sosai. Sun ba ni tabbacin cewa Allah ne ya yi abubuwa.” Bayan ka yi nazarin waɗannan ƙasidun, za ka yarda da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa cewa: “Ya Ubangiji Allahnmu, ka cancanci ka karɓi ɗaukaka, da girma, da iko. Gama ka halicci kome da kome.”—R. Yar. 4:11. e
15. Wane abu ne kuma zai taimaka mana mu ƙara kusantar Jehobah?
15 Wani abu kuma da zai taimaka maka ka ƙaunaci Jehobah sosai shi ne yin nazari game da Ɗansa Yesu. Abin da wata ꞌyarꞌuwa matashiya mai suna Samira, wadda take zama a Jamus, ta yi ke nan. Ta ce: “Nazari game da Yesu da na yi ya sa na san Jehobah sosai.” Saꞌad da take ƙarama, ya yi mata wuya ta yarda cewa Jehobah mai ƙauna ne. Amma ta yarda cewa Yesu yana ƙaunar mutane. Ta ce: “Ina son Yesu domin yana da kirki kuma yana ƙaunar yara.” Yayin da take ƙara koya game da Yesu, hakan ya sa ta ƙara sanin Jehobah, kuma ta soma ƙaunar sa. Me ya sa? Ta ce: “Daga baya, na fahimci cewa Yesu yana yin koyi da Ubansa ne. Halinsu ɗaya. Ashe wani abin da ya sa Jehobah ya aiko Yesu zuwa duniya ke nan, don ya sa ya yi wa ꞌyan Adam sauƙi su san shi Jehobah sosai.” (Yoh. 14:9) Idan kana so ka ƙara kusantar Jehobah, za ka iya ɗaukan lokaci don ka koyi abubuwa da yawa game da Yesu. Idan ka yi hakan, za ka ƙaunaci Jehobah sosai, kuma za ka ƙara riƙe amincinka a gare shi.
16. Wane amfani ne za mu samu idan muka riƙe amincinmu ga Jehobah? (Zabura 18:25; Mika 6:8)
16 Waɗanda suke da aminci suna iya ƙulla abokantaka da mutane na dogon lokaci. (Rut 1:14-17) Ƙari ga haka, waɗanda suke riƙe amincinsu ga Jehobah suna kasancewa da kwanciyar hankali da kuma gamsuwa. Me ya sa? Domin Jehobah ya yi alkawari cewa zai yi aminci ga waɗanda suka riƙe aminci a gare shi. (Karanta Zabura 18:25; Mika 6:8.) Duk da cewa shi ne Mahaliccinmu, Jehobah ya yi alkawari cewa zai ci gaba da nuna mana ƙauna. Wannan ba abin ban shaꞌawa ba ne? Kuma idan Jehobah yana ƙaunar mu, matsala, ko maƙiyi, kai ko mutuwa ma, ba za su iya raba mu da shi ba. (Dan. 12:13; Luk. 20:37, 38; Rom. 8:38, 39) Saboda haka, yana da muhimmanci mu yi koyi da Daniyel kuma mu riƙe amincinmu ga Jehobah!
KA CI GABA DA YIN KOYI DA DANIYEL
17-18. Mene ne kuma za mu iya koya daga wurin Daniyel?
17 A wannan talifin, halayen Daniyel guda biyu ne kawai muka tattauna. Amma akwai abubuwa da yawa da za mu iya koya daga wurin sa. Alal misali, Jehobah ya nuna wa Daniyel abubuwa da yawa a wahayoyi da mafarkai, kuma ya sa ya iya faɗan maꞌanar wasu annabce-annabce. Da yawa daga cikin annabce-annabcen sun riga sun cika. Wasu kuma sun yi bayani dalla-dalla game da abubuwa da za su faru a nan gaba, kuma abubuwan za su shafi kowa a nan duniya.
18 A talifi na gaba, za mu bincika annabci guda biyu da Daniyel ya rubuta. Idan dukanmu, manya da ƙanana, muka fahimci waɗannan annabce-annabcen, za mu iya yanke shawarwari masu kyau yanzu. Waɗannan annabce-annabcen za su taimaka mana mu zama a shirye don abubuwan da za su faru a nan gaba, domin za su sa mu kasance da ƙarfin zuciya da kuma aminci ga Jehobah.
WAƘA TA 119 Wajibi Ne Mu Kasance da Bangaskiya
a Matasa da suke bauta ma Jehobah a yau suna samun kansu a cikin yanayoyin da ke bukatar su nuna ƙarfin zuciya kuma su riƙe aminci. Wasu ꞌyan ajinsu suna musu dariya don sun gaskata cewa Allah ne ya halicci abubuwa. Wasu kuma tsaransu suna musu kallon wawaye don suna bauta wa Allah kuma suna bin abin da ya ce. Amma kamar yadda za mu gani a wannan talifin, waɗanda suke yin koyi da Daniyel ta wajen bauta wa Jehobah da ƙarfin zuciya da kuma aminci, su ne masu hikima ta gaske.
b Babiloniyawa ne suka ba su sunayen nan.
c Akwai dalilai guda uku da mai yiwuwa suka sa Daniyel ya ƙi cin abincin Babiloniyawan: (1) Ƙila naman dabbobin da Dokar Allah ta haramta ne. (M. Sha. 14:7, 8) (2) Ƙila ba a yanka naman yadda ya dace ba. (L. Fir. 17:10-12) (3) Mai yiwuwa cin abincin yana cikin ayyukan ibada da Babiloniyawan suke yi ma wani allahnsu.—Ka kuma duba Littafin Firistoci 7:15; 1 Korintiyawa 10:18, 21, 22.
d Ku kalli bidiyon nan a jw.org mai jigo: “Amfanin Yin Abin da Yake Daidai, Shi Ne Salama.”
e Don ka ƙara ƙaunar Jehobah, ka yi nazarin littafin nan, Ka Kusaci Jehovah. Littafin zai taimaka maka ka san Jehobah da halayensa sosai.