Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 36

Ku Dauki Abin da Ya Zama Dole Ku Dauka, Saꞌan nan Ku Yar da Sauran

Ku Dauki Abin da Ya Zama Dole Ku Dauka, Saꞌan nan Ku Yar da Sauran

“Bari mu tuɓe dukan abin da zai hana mu . . . , bari kuma mu yi tseren nan da aka sa a gabanmu cikin naciya.”​—IBRAN. 12:1.

WAƘA TA 33 Mu Miƙa Dukan Damuwarmu ga Jehobah

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1. Kamar yadda Ibraniyawa 12:1 ta ce, me muke bukatar mu yi don mu iya yin tseren nan har zuwa ƙarshe?

 LITTAFI MAI TSARKI ya kwatanta rayuwar Kiristoci da yin tsere. Waɗanda suka yi tseren har ƙarshe za su sami ladan rai na har abada. (2 Tim. 4:​7, 8) Ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu mu ci gaba da yin tseren nan, musamman yanzu da muka yi kusa da ƙarshe. Manzo Bulus ya yi tseren nan kuma ya yi nasara. Ya kuma gaya mana abin da zai taimaka mana mu yi nasara. Ya ce: “Mu tuɓe dukan abin da zai hana mu, . . . kuma mu yi tseren nan da aka sa a gabanmu cikin naciya.”​—Karanta Ibraniyawa 12:1.

2. Me ake nufi da cewa mu tuɓe duk “abin da zai hana mu”?

2 Bulus ya ce muna bukatar mu tuɓe duk wani ‘abin da zai hana mu.’ Amma hakan yana nufin cewa ba abin da Kirista zai ɗauka ke nan? Aꞌa. Bulus ya ce mu yar da duk wani abin da zai hana mu, wato, duk wani abin da zai zama mana nawaya kuma ya gajiyar da mu, ko ya hana mu yin gudun da kyau. Idan muna so mu yi nasara a wannan tseren, dole ne mu riƙa lura ko mun ɗauki irin kayan nan, kuma mu yar da su ba tare da ɓata lokaci ba. Amma bai kamata mu yar da kayan da muke bukata ba, domin idan ba mu ɗauki wannan kayan ba, za a cire mu daga tseren. (2 Tim. 2:5) Waɗanne abubuwa ne suka zama dole mu ɗauka?

3. (a) Bisa ga Galatiyawa 6:​5, mene ne ya zama dole mu ɗauka? (b) Me za mu tattauna a wannan talifin, kuma me ya sa?

3 Karanta Galatiyawa 6:5. Bulus ya gaya mana wani abin da ya zama dole mu ɗauka. Ya ce: “Kowa ya ɗauki kayan kansa.” Kayan da Bulus yake nufi shi ne, hakkin da kowannenmu yake da shi a gaban Allah. Wani ba zai iya ɗaukan hakkin wani ba. A talifin nan, za mu ga abin da “kayan” kowannenmu ya ƙunsa da kuma yadda za mu ɗauke shi. Bayan haka, za mu ga kaya marar amfani da wataƙila muke ɗauke da su, da yadda za mu yar da su. Idan muka ɗauki kayan kanmu, kuma muka yar da kaya marasa amfani, hakan zai taimaka mana mu gama tseren nan lafiya.

KAYAN DA YA ZAMA DOLE MU ƊAUKA

Kayan kanmu da ya zama dole mu ɗauka sun haɗa da cika alkawarin bauta wa Jehobah da muka yi, cika hakkinmu a iyali, da kuma amincewa da sakamakon zaɓin da muke yi (Ka duba sakin layi na 4-9

4. Me ya tabbatar mana da cewa cika alkawarin bauta wa Jehobah da muka yi bai fi ƙarfinmu ba? (Ka kuma duba hoton.)

4 Alkawarin bauta wa Jehobah da muka yi. A wannan alkawarin, mun ce za mu bauta wa Jehobah, kuma mu yi nufinsa. Dole mu cika wannan alkawarin. Cika shi bai da sauƙi, amma bai fi ƙarfinmu ba don tun dā ma, Jehobah ya halicce mu don mu yi nufinsa ne. (R. Yar. 4:11) Ya halicce mu yadda za mu so mu san shi kuma mu bauta masa. Ya kuma yi mu a kamanninsa, shi ya sa za mu iya kusantarsa, kuma yin nufinsa yana sa mu farin ciki. (Zab. 40:8) Ban da haka ma, idan muka yi nufin Allah kuma muka bi Ɗansa, ‘za mu sami hutu’ a zuciyarmu.​—Mat. 11:​28-30.

(Ka duba sakin layi na 4-5)

5. Me zai taimaka maka ka cika alkawarin da ka yi wa Jehobah? (1 Yohanna 5:3)

5 Me zai taimake ka ka ɗauki kayan? Akwai abubuwa biyu. Na ɗaya, ka ci gaba da yin abubuwa da za su sa ka ƙara ƙaunar Jehobah. Misali, ka dinga yin tunani mai zurfi a kan abubuwa masu kyau da Jehobah ya yi maka da waɗanda ya ce zai yi maka a nan gaba. Idan ka ƙara ƙaunar Jehobah, zai ƙara yi maka sauƙi ka yi abin da ya ce. (Karanta 1 Yohanna 5:3.) Na biyu, ka yi koyi da Yesu. Yesu ya dinga adduꞌa Jehobah ya taimake shi, kuma ya mai da hankali ga ladan da zai samu. Abubuwan da suka taimaka masa ya yi nufin Allah ke nan. (Ibran. 5:7; 12:2) Kai ma ka dinga adduꞌa ga Jehobah ya ba ka ƙarfin yin nufinsa kuma ka dinga tuna cewa za ka sami rai na har abada a ƙarshe. Ƙara ƙaunar Allah da kuma bin misalin Yesu za su sa ka iya cika alkawarinka.

6. Me ya sa ya zama dole mu cika hakkinmu a iyali? (Ka kuma duba hoton.)

6 Hakkinmu a iyali. Yayin da muke tsere don mu sami rai, dole mu ƙaunaci Jehobah da Yesu fiye da ꞌyan iyalinmu. (Mat. 10:37) Amma hakan ba ya nufin cewa za mu yi watsi da hakkin da muke da shi a iyalinmu. A maimakon haka, idan har muna so Jehobah da Yesu su amince da ibadarmu, dole mu cika hakkinmu a iyalinmu. (1 Tim. 5:​4, 8) Yin hakan zai ƙara sa mu farin ciki. Domin Jehobah ya san cewa idan mata da miji suna ƙaunar juna kuma suna daraja juna, suna ƙaunar yaransu da koyar da su da kyau, kuma yaran suna yi wa iyayensu biyayya, kowa a iyalin zai ji daɗi.​—Afis. 5:33; 6:​1, 4

(Ka duba sakin layi na 6-7)

7. Me zai taimake ka ka cika hakkinka a iyali?

7 Me zai taimake ka ka ɗauki kayan? Idan kai ne maigida, ko ke ce matar, ko ke ꞌya ce ko kai ɗa ne a gida, ka bi shawarar Littafi Mai Tsarki. Kar ka bi abin da kake ganin shi ne ya dace, ko abin da mutanen yankinku suka saba yi ko shawarar masana. (K. Mag. 24:​3, 4) Ka riƙa amfani da littattafanmu da suke bisa Littafi Mai Tsarki. Suna ɗauke da shawarwari masu kyau a kan yadda za mu bi abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. Misali, akwai talifofi a jw.org da suke ɗauke da bayanai game da matsalolin da maꞌaurata, da iyaye da kuma matasa suke fuskanta. b Ka dāge cewa za ka bi abin da Littafi Mai Tsarki ya ce ko da sauran ꞌyan iyalinka ba sa hakan. Idan ka yi hakan, iyalin za ta amfana kuma Jehobah zai albarkace ka a iyalin.​—1 Bit. 3:​1, 2.

8. Me zai iya faruwa da mu don zaɓin da muka yi?

8 Sakamakon zaɓin da muke yi. Jehobah ya ba mu damar zaɓan abin da za mu yi, kuma yana so mu tsai da shawarwari masu kyau, mu kuma amfana. Amma idan muka yi abin da bai dace ba, ba ya kāre mu daga sakamakon zaɓin da muka yi. (Gal. 6:​7, 8) Don haka, idan muka tsai da shawara marar kyau, mun faɗi ko kuma mun yi abin da bai dace ba, dole mu amince da sakamakon. Irin abin da muka yi zai iya sa zuciyarmu ta riƙa damun mu. Idan muka san cewa laifinmu ne, hakan zai sa mu tuba, mu gyara halinmu kuma mu guji maimaita abin da muka yi. Idan muka yi abubuwan nan, za mu ci gaba da yin tsere don mu sami rai na har abada.

(Ka duba sakin layi na 8-9)

9. Me zai taimaka maka idan ka riga ka yi abin da bai dace ba? (Ka kuma duba hoton.)

9 Me zai taimaka maka ka ɗauki wannan kayan? Idan ka riga ka yi abin da bai dace ba, me zai taimaka maka? Ka tuna cewa ba za ka iya mai da hanun agogo baya ba. Kar ka yi ta ƙoƙarin ba da hujja, ko kuma ka yi ta damuwa cewa laifinka ne, ko kuma ka ce laifin wasu ne. A maimakon haka, ka yarda cewa ka yi laifi kuma ka yi iya ƙoƙarinka ka yi gyara. Idan abin da ka yi yana damunka, ka yi adduꞌa ga Jehobah, ka gaya masa laifin da ka yi kuma ka roƙi gafara. (Zab. 25:11; 51:​3, 4) Ka ba waɗanda ka yi musu laifi haƙuri, kuma idan da bukata, ka nemi taimakon dattawa. (Yak. 5:​14, 15) Ka ɗauki darasi daga kuskuren da ka yi kuma ka guji maimaita shi. Idan ka yi hakan, ba shakka Jehobah zai yi maka jinƙai kuma zai taimake ka.​—Zab. 103:​8-13.

ABUBUWAN DA MUKE BUKATAR MU YAR

10. Me ya sa ƙoƙarin yin abin da ya fi ƙarfinmu kaya ne mai nauyi? (Galatiyawa 6:4)

10 Ƙoƙarin yin abin da ya fi ƙarfinmu. Idan muna gwada kanmu da mutane, hakan zai iya gajiyar da mu. (Karanta Galatiyawa 6:4.) Kuma idan muna ta gwada kanmu da mutane, za mu iya kishinsu kuma mu shiga yin gasa da su. (Gal. 5:26) Ƙari ga haka, idan muna so mu yi abin da ya fi ƙarfinmu don mun ga wasu suna yi, hakan zai iya zama mana da illa. Idan “sa rai wanda ba ta biya bukata ba, takan sa zuciya ta ɓace,” ai ranmu zai fi ɓacewa idan muka sa rai a kan abin da ba za mu taɓa iya yi ba. (K. Mag. 13:12) Idan muka yi hakan, za mu gajiyar da kanmu sosai kuma hakan zai iya hana mu yin tseren nan da kyau.​—K. Mag. 24:​10, New World Translation.

11. Me zai taimake ka ka guji yin abin da ya fi ƙarfinka?

11 Ta yaya za ka yar da wannan kayan? Jehobah ba ya bukatar mu ba shi abin da ba za mu iya ba. Don haka, kar ka yi ƙoƙarin yin abin da ya fi ƙarfinka. (2 Kor. 8:12) Jehobah fa, ba ya gwada abin da kake masa da abin da wasu suke yi. (Mat. 25:​20-23) Yana daraja hidimar da kake masa da dukan zuciyarka, da amincinka, da kuma jimrewarka. Ka yarda cewa akwai wasu abubuwa da ba za ka iya yi ba don shekarunka ko rashin lafiya ko kuma wasu yanayoyin rayuwa. Kamar Barzillai, idan ka san ba za ka iya yin wani aiki ba don shekarunka ko kuma rashin lafiya, ka ce aꞌa. (2 Sam. 19:​35, 36) Kamar Musa, ka yarda a taimaka maka kuma ka raba wasu ayyukanka ka ba ma wasu su yi. (Fit. 18:​21, 22) Hakan zai nuna cewa ka san kasawarka. A sakamako, ba za ka yi ƙoƙarin yin abin da ya fi ƙarfinka kuma ka gajiyar da kanka ba.

12. Laifinmu ne idan wani ko wata ta yi zaɓi marar kyau? Ka bayyana.

12 Ɗora wa kanmu laifin zaɓi marar kyau da wasu suka yi. Ba za mu iya tsai da wa mutane shawara ba kuma ba kullum ne za mu iya kāre su daga sakamakon zaɓi marar kyau da suka yi ba. Misali, ɗa ko ꞌya za ta iya daina bauta wa Jehobah kuma zaɓin da ta yi zai iya sa iyayen baƙin ciki sosai. Amma idan iyaye suka ɗora wa kansu laifi don zaɓin nan da ɗansu ko ꞌyarsu ta yi, hakan zai zama musu kaya mai nauyi. Jehobah ba ya so iyaye su ɗauki irin wannan kayan.​—Rom. 14:12.

13. Me zai taimaka ma iyaye idan ɗansu ko ꞌyarsu ta yi zaɓi marar kyau?

13 Me zai taimake ka ka yar da wannan kayan? Ka tuna cewa Jehobah ya ba kowa ꞌyancin zaɓan abin da zai yi, har da ꞌyancin zaɓan ko za mu bauta masa ko aꞌa. Kuma Jehobah ya san cewa iyaye ajizai ne. Abin da kawai yake so ku yi shi ne, iya ƙoƙarinku. Idan ɗanku ya yi zaɓi marar kyau, laifin nasa ne, ba naku ba. (K. Mag. 20:11) Duk da haka, mai yiwuwa ku yi ta damuwa a kan kurakuren da kuka yi yayin da kuke renon yaron. Idan kuka ji hakan, ku gaya wa Jehobah a cikin adduꞌa kuma ku roƙe shi ya yafe muku. Jehobah ya san cewa ba za ku iya gyara abin da ya wuce ba kuma bai ce sai kun kāre ꞌyaꞌyanku daga sakamakon abin da suka yi ba. Ku tuna cewa idan ꞌyarku ko ɗanku ya yi ƙoƙarin komowa ga Jehobah, Jehobah zai karɓe shi.​—Luk. 15:​18-20.

14. Me ya sa yawan damuwa a kan zunubin da muka yi kaya ne da ya kamata mu yar?

14 Idan zuciyarka tana damunka ko da yaushe. Idan muka yi zunubi, zuciyarmu takan dame mu. Amma Jehobah ba ya so mu bar zuciyarmu ta ci gaba da damun mu. Don haka, wannan abu ne da ya kamata mu yar. Yaya za mu san ko yadda zuciyarmu take damun mu ya yi yawa? Idan mun riga mun furta zunubin da muka yi, mun tuba, kuma muna yin iya ƙoƙarinmu kada mu sake yin zunubin, tabbas, Jehobah ya yafe mana. (A. M. 3:19) Bayan mun ɗauki matakan nan, Jehobah ba zai so zuciyarmu ta ci gaba da damun mu ba don ya san cewa hakan yana da illa sosai. (Zab. 31:10) Idan baƙin cikin ya yi mana yawa, hakan zai iya sa mu fid da rai kuma mu daina yin tseren.​—2 Kor. 2:7.

Bayan ka tuba da gaske, Jehobah ba ya sake tunani a kan zunubin da ka yi. Don haka, bai kamata ka ci gaba da damun kanka ba (Ka duba sakin layi na 15)

15. Me zai taimake ka idan zuciyarka ta ci gaba da damunka domin zunubin da ka yi? (1 Yohanna 3:​19, 20) (Ka kuma duba hoton.)

15 Me zai taimake ka ka yar da wannan kayan? Idan zuciyarka ta ci gaba da damun ka a kan zunubin da ka yi, ka tuna cewa Jehobah Allah mai yin “gafara” ne. (Zab. 130:4) Da yake zancen waɗanda suka tuba kuma ya yafe musu, Jehobah ya ce: “Ba kuwa zan sāke tunawa da zunubansu ba.” (Irm. 31:34) Wato, Jehobah ba zai sake tunanin zunubin da ka yi ba don ya riga ya yafe maka. Don haka, idan kana fuskantar sakamakon zunubin da ka yi, kar ka ɗauka cewa Jehobah bai gafarta maka ba shi ya sa. Kuma kada ka yi ta baƙin ciki idan ba ka yin wasu ayyuka a ikilisiya don zunubin da ka yi. Jehobah ba ya tunanin zunubin da ka yi, don haka, bai kamata ka yi ta damun kanka ba.​—Karanta 1 Yohanna 3:​19, 20.

KA YI TSEREN YADDA ZA KA YI NASARA

16. Yayin da muke yin tsere don samun rai, me ya kamata mu sani?

16 Yayin da muke tsere don mu sami rai, dole mu ‘yi ta gudu yadda za mu yi nasara.’ (1 Kor. 9:24) Za mu iya yin hakan idan muka san kayan da ya kamata mu ɗauka da kuma waɗanda ya kamata mu yar. ꞌYan ƙalila daga cikin abubuwa da ya zama dole mu ɗauka, da waɗanda ya kamata mu yar ne muka tattauna a wannan talifin. Akwai wasu da yawa. Yesu ya ce: “Ciye-ciye, da buguwa, da damuwar rayuwar duniya” za su iya ɗauke hankalinmu. (Luk. 21:34) Ayoyin nan da ma wasu da yawa, za su iya taimaka maka ka san abubuwan da ya kamata ka yar don ka iya yin tseren nan da kyau.

17. Me ya tabbatar mana cewa za mu iya yin nasara a tseren da muke yi don mu sami rai?

17 Muna da tabbaci cewa za mu iya yin nasara a tseren da muke yi don mu sami rai, domin Jehobah zai taimake mu. (Isha. 40:​29-31) Saboda haka, kada ka gaji! Ka yi koyi da manzo Bulus, wanda shi ma ya yi iya ƙoƙarinsa don ya sami ladan da ke gabansa. (Filib. 3:​13, 14) Ba wanda zai yi wannan tseren a madadinka, amma da taimakon Jehobah, za ka yi nasara. Jehobah zai taimake ka ka ɗauki kayan kanka, kuma ka yar da kayan da ba ka bukata. (Zab. 68:19) Da taimakonsa, za ka iya yin tseren nan da naciya kuma ka yi nasara.

WAƘA TA 65 Mu Riƙa Samun Ci Gaba!

a Wannan talifin zai taimaka mana a tseren da muke yi don mu sami rai. Yayin da muke tseren nan, dole mu ɗauki wasu abubuwa. A cikin abubuwan nan, akwai alkawarin bauta wa Jehobah da muka yi, da hakkin da muke da shi a iyalinmu, da kuma sakamakon zaɓin da muka yi. Amma, ya kamata mu yar da duk wani abin da zai hana mu yin tseren da kyau. Kamar me da me ke nan? Za mu ga amsar a wannan talifin.

b Za ka iya samun talifofin nan a ƙarƙashin sashen “Aure da Iyali” da kuma “Tambayoyin Matasa” a jw.org/ha. Wasu daga cikin talifofi don maꞌaurata su ne, “Idan Abokin Aurenka Yana da Halin da ba Ka So Fa?” da “Yadda Za Ka Zama Mai Haƙuri”; don iyaye kuma akwai, “Yadda Za Ku Koyar da ꞌYaꞌyanku” da “Shin Ya Kamata In Ba Ɗana Babban Waya?”; don matasa kuma, “Me Zai Taimaka Maka Ka Rage Kashe Kuɗi?” da “Me Zan Yi Idan Aka Matsa Mini In Yi Lalata?