Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 31

WAƘA TA 12 Jehobah, Allah Mafi Iko

Abin da Jehobah Ya Yi don Ya Cece Mu Daga Zunubi

Abin da Jehobah Ya Yi don Ya Cece Mu Daga Zunubi

“Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da makaɗaicin Ɗansa.”YOH. 3:16.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga abin da Jehobah ya yi don ya taimaka mana mu yi nasara a kan zunubi kuma mu yi nufinsa. Za mu kuma ga yadda ya buɗe mana hanyar yin rayuwa har abada ba tare da zunubi ba.

1-2. (a) Mene ne zunubi, kuma me zai taimaka mana mu yi nasara a kansa? (Ka kuma duba “Maꞌanar Wasu Kalmomi.”) (b) Me za mu tattauna a wannan talifin da sauran talifofin da ke wannan Hasumiyar Tsaro? (Ka kuma duba bayani da aka yi mai jigo: “Ga Mai Karatu” a wannan Hasumiyar Tsaro.)

 JEHOBAH yana ƙaunarka sosai kuwa? Bincika abin da ya yi don ya cece ka daga zunubi da mutuwa zai taimaka maka ka san amsar tambayar nan. Zunubi a babban maƙiyinmu ne, kuma ya fi ƙarfinmu. Dukanmu muna yin zunubi kowane rana, kuma shi ne ya sa muke mutuwa. (Rom. 5:12) Amma abin farin cikin shi ne, za mu iya yin nasara a kan zunubi da taimakon Jehobah!

2 Jehobah ya yi wajen shekaru 6,000 yana taimaka wa mutane su yi nasara a kan zunubi. Me ya sa yake hakan? Domin yana ƙaunar mu. Jehobah ya ƙaunaci mutane sosai tun lokacin da ya halicce su. Shi ya sa ya yi abubuwa da dama don ya taimaka mana idan muka yi zunubi. Ya san cewa zunubi yakan kai ga mutuwa, kuma ba ya so mu mutu. Yana so mu rayu har abada. (Rom. 6:23) Irin rayuwar da Jehobah yake so ka more ke nan. A talifin nan, za mu sami amsar tambayoyin nan guda uku: (1) Wane bege ne Jehobah ya ba wa ꞌyan Adam? (2) Mene ne masu zunubi a zamanin dā suka yi don su kusaci Jehobah? (3) Mene ne Yesu ya yi don ya ceci ꞌyan Adam daga zunubi da mutuwa?

WANE BEGE NE JEHOBAH YA BA WA ꞌYAN ADAM?

3. Yaya aka yi Adamu da Hauwaꞌu suka zama masu zunubi?

3 Da Jehobah ya halicci Adamu da Hauwaꞌu, ya so su ji daɗin rayuwa sosai. Ya ba su wurin zama mai kyau, ya so su ji daɗin aurensu, kuma ya ba su aiki mai ƙayatarwa. Ya so su haifi ꞌyaꞌya su cika duniya, kuma su mayar da koꞌina ya zama aljanna kamar gonar Adnin. Doka ɗaya ne kawai Allah ya ba su, kuma binsa ba wuya. Ya gaya musu cewa idan sun karya dokar, sun yi zunubi, kuma za su mutu. Kamar yadda muka sani, wani mugun malaꞌika wanda ba ya ƙaunar Allah kuma ba ya ƙaunar su, ya zo ya ruɗe su suka yi zunubi. Maimakon su yarda da Mahaliccinsu mai ƙauna, sun bi raꞌayin mugun malaꞌikan. Kuma abin da Jehobah ya ce zai faru da su, ya faru. Sun yi ta shan wahala sakamakon zunubinsu. Sun tsufa, kuma a ƙarshe sun mutu.—Far. 1:​28, 29; 2:​8, 9, 16-18; 3:​1-6, 17-19, 24; 5:5.

4. Me ya sa Jehobah ya tsani zunubi kuma yana taimaka mana mu yin nasara a kansa? (Romawa 8:​20, 21)

4 Jehobah ya sa an rubuta abin da ya faru don ya koya mana wani abu mai muhimmanci. Labarinsu ya nuna mana abin da ya sa Jehobah ya tsani zunubi. Zunubi yana ɓata dangantakarmu da Jehobah, kuma yana jawo mutuwa. (Isha. 59:2) Shaiɗan maƙiyinmu ne kuma ba ya ƙaunar Jehobah, shi ya sa ya jarrabci Adamu da Hauwaꞌu har suka yi zunubi, kuma mu ma bai ƙyale mu ba. Bayan da suka yi zunubi, ƙila Shaiɗan ya ɗauka cewa ya gama ɓata tsakaninmu da Jehobah ke nan. Amma bai san irin ƙaunar da Jehobah yake mana ba. Allah ya ce sai nufinsa ya cika a kan ꞌyaꞌyan Adamu. Don haka, nan tāke ya ba mu bege. (Karanta Romawa 8:​20, 21.) Jehobah ya san cewa wasu ꞌyaꞌyan Adamu za su ƙaunace shi kuma za su so ya taimake su su yi nasara a kan zunubi. Don haka, ya buɗe musu hanyar kusantarsa da kuma samun ceto daga zunubi da mutuwa. Ta yaya Jehobah ya yi hakan?

5. A wane lokaci ne Jehobah ya ba wa ꞌyan Adam bege, kuma mene ne maꞌanar annabcin da ke Farawa 3:15?

5 Karanta Farawa 3:15. A lokacin da Jehobah ya faɗi hukuncin da zai yi wa Shaiɗan ne ya ba wa ꞌyan Adam bege. Allah ya ce za a yi wani ɗa da zai cece mu. Shi zai halaka Shaiɗan kuma zai gyara kome. (1 Yoh. 3:8) Amma, ɗan zai sha wahala kafin ya cece mu. Allah ya ce Shaiɗan zai sare shi, wato zai yi sanadiyyar mutuwarsa. Mutuwarsa za ta yi wa Jehobah zafi sosai. Amma Jehobah ya yarda ya jimre wannan zafin don ya ceci ꞌyan Adam daga zunubi.

MENE NE MUTANE A DĀ SUKA YI DON SU KUSACI JEHOBAH?

6. Mene ne Habila da Nuhu da wasu bayin Allah suka yi don su kusaci Jehobah?

6 A-sannu-a-hankali, Jehobah ya yi ta bayyana yadda ꞌyan Adam za su sami gafara kuma su kusace shi. Bayan da Adamu da Hauwaꞌu suka yi zunubi, Habila ne mutum na farko da ya ba da gaskiya ga Jehobah. Habila yana ƙaunar Jehobah shi ya sa ya miƙa masa hadaya. Ya so ya faranta masa rai kuma ya kusace shi. Da yake Habila makiyayi ne, ya yi amfani da wasu tumakinsa ya yi wa Jehobah hadaya. Me Jehobah ya yi da ya ga haka? Ya ji daɗi kuma ya karɓi hadayar Habila. (Far. 4:4) Da Nuhu da wasu bayin Jehobah da suke ƙaunarsa suka yi hadaya, Jehobah ya ji daɗi kuma ya karɓa. (Far. 8:​20, 21) Yadda Jehobah ya karɓi hadayunsu ya nuna cewa masu zunubi za su iya samun gafara kuma su kusace shi. b

7. Me muka koya daga abin da Ibrahim ya yi?

7 Jehobah ya gaya wa Ibrahim ya yi wani abu mai wuya sosai. Ya ce ya yi hadaya da ɗansa Ishaku. Babu shakka da Ibrahim ya ji hakan, ya damu sosai. Amma ya yarda zai yi hadaya da Ishaku. Sai dai kafin ya yi hakan, Jehobah ya dakatar da shi. Abin da ya faru ya nuna wa bayin Jehobah abin da zai yi. Wato, Jehobah zai ba da Ɗansa hadaya dominmu. Hakan ya nuna irin ƙaunar da Jehobah yake mana.—Far. 22:​1-18.

8. Mene ne hadayun da aka ce Israꞌilawa su yi suka nuna? (Littafin Firistoci 4:​27-29; 17:11)

8 A lokacin da Jehobah ya ba Israꞌilawa dokoki, ya ce su riƙa yin hadayu don neman gafara. (Karanta Littafin Firistoci 4:​27-29; 17:11.) Hadayun sun nuna cewa a-kwana-a-tashi, Jehobah zai yi wani hadaya da zai ceci ꞌyan Adam daga zunubi. Jehobah ya sa annabawansa su yi rubutu game da ɗan da aka yi alkawarinsa. Sun bayyana cewa zai sha wahala kuma ya mutu. Za a kashe shi kamar yadda ake kashe ɗan rago a yi hadaya da shi. (Isha. 53:​1-12) Jehobah ya ce zai yi hadaya da Ɗansa don ya ceci ꞌyan Adam daga zunubi. Ba ƙaramin abu ba ne Jehobah ya yi mana, har da kai!

MENE NE YESU YA YI DON YA CECI ꞌYAN ADAM?

9. Mene ne Yohanna Mai Baftisma ya ce game da Yesu? (Ibraniyawa 9:22; 10:​1-4, 12)

9 A shekara ta 29 bayan haihuwar Yesu, Yohanna Mai Baftisma ya ga Yesu kuma ya ce: “Duba, ga Ɗan Rago na Allah wanda yana ɗauke da zunubin duniya.” (Yoh. 1:29) Wannan ya nuna cewa Yesu ne ɗan nan da aka yi alkawarinsa. Shi ne zai ba da ransa hadaya. Kuma a lokacin ne ɗan da Jehobah ya yi alkawarinsa ya bayyana don ya ceci ꞌyan Adam daga zunubi.—Karanta Ibraniyawa 9:22; 10:​1-4, 12.

10. Ta yaya Yesu ya nuna cewa ya zo ne “domin masu zunubi”?

10 Yesu ya mai da hankali ga waɗanda suke damuwa don zunubin da suka yi, kuma ya ce musu su zama mabiyansa. Ya san cewa zunubi ne ainihin abin da ya sa muke shan wahala. Don haka, ya taimaki masu zunubi sosai. Har ma ya ba da misali cewa: “Masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya.” Ya daɗa da cewa: “Gama ban zo domin in kira masu adalci ba, sai dai domin masu zunubi.” (Mat. 9:​12, 13) Abin da Yesu ya yi ke nan. Alal misali, da wata mata mai zunubi ta wanke ƙafafunsa da hawayenta, ya yi mata magana da alheri kuma ya gafarta mata zunubanta. (Luk. 7:​37-50) Ko da yake ya san cewa ꞌyar Samariya da suka haɗu a bakin rijiya tana yin lalata, ya koya mata wasu abubuwa masu muhimmanci. (Yoh. 4:​7, 17-19, 25, 26) Zunubi ne ya sa mutane suke mutuwa, amma Allah ya ba wa Yesu iko a kan mutuwa. Kuma Yesu ya ta da maza da mata, da yara da manya daga mutuwa.—Mat. 11:5.

11. Me ya sa bai yi wa masu zunubi wuya su je wurin Yesu ba?

11 Bai yi wa masu zunubi wuya su je wurin Yesu ba. Me ya sa? Domin ya fahimce su kuma ya tausaya musu. Hakan ya sa sun saki jiki da shi. (Luk. 15:​1, 2) Yesu ya yaba wa irinsu don bangaskiyarsu, kuma ya yi musu alheri. (Luk. 19:​1-10) Ya tausaya wa mutane, kamar Ubansa. (Yoh. 14:9) Yadda Yesu ya bi da mutane, ya nuna cewa Ubansa mai tausayi da kuma jinƙai ne. Yana ƙaunar masu zunubi kuma yana so ya taimaka musu. Yesu ya taimaka wa masu zunubi su canja halinsu kuma su bi shi.—Luk. 5:​27, 28.

12. Me Yesu ya faɗa game da mutuwarsa?

12 Yesu ya san cewa zai yi hadaya da ransa. Sau da yawa ya gaya wa almajiransa cewa za a bashe shi, kuma a rataye shi a kan gungume. (Mat. 17:22; 20:​18, 19) Kuma ya san cewa hadayar da zai yi, za ta ɗauke zunubin duniya, kamar yadda Yohanna Mai Baftisma da sauran annabawa suka annabta. Yesu ya kuma ce bayan ya mutu, zai “jawo dukan [ire-iren] mutane zuwa” wurinsa. (Yoh. 12:32) Duk wanda ya ba da gaskiya ga Yesu kuma ya yi masa biyayya, Allah zai amince da shi. Kuma a nan gaba, zai sami ꞌyanci “daga zunubi.” (Rom. 6:​14, 18, 22; Yoh. 8:32) Shi ya sa Yesu ya yi ƙarfin zuciya kuma ya yarda ya mutu.—Yoh. 10:​17, 18.

13. Yaya aka kashe Yesu, kuma me mutuwarsa ta koya mana game da Jehobah? (Ka kuma duba hoton.)

13 Wani aminin Yesu ya bashe shi. Sai aka kama shi, aka zazzage shi, aka yi ƙarya a kansa. An ce ya cancanci ya mutu, kuma an azabtar da shi. Bayan haka, sai sojoji suka rataya shi a kan gungume ta wurin buga masa ƙusa. Yesu ya sha wahala sosai kuma ya jimre. Amma akwai wanda ya fi jin zafin abin da ya faru, shi ne Jehobah. Yana da ikon da zai hana abubuwan nan faruwa amma bai yi hakan ba. Da yake Jehobah yana ƙaunar Ɗansa sosai, me ya sa ya bar shi ya sha wahala kuma ya mutu? Domin yana ƙaunar mu. Yesu ya ce: “Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin dukan wanda ya ba da gaskiya gare shi kada ya halaka, amma ya sami rai na har abada.”—Yoh. 3:16.

Ba za mu iya kwatanta irin zafin da Jehobah ya ji a ransa a lokacin da ya ƙyale mutane su kashe Ɗansa domin ya cece mu daga zunubi da mutuwa ba (Ka duba sakin layi na 13)


14. Mene ne yadda Jehobah ya ba da hadayar Ɗansa ya nuna maka?

14 Yadda Jehobah ya ba da hadayar Ɗansa ya nuna irin ƙaunar da yake yi wa ꞌyan Adam. Ya nuna cewa Jehobah yana ƙaunar ka sosai. Ya ba da makaɗaicin Ɗansa kuma ya jimre zafin da hakan ya jawo masa domin ya cece ka daga zunubi da mutuwa. (1 Yoh. 4:​9, 10) Ba shakka, Jehobah yana so ya taimaki kowannenmu ya yi nasara a kan zunubi!

15. Me ya kamata mu yi idan muna so Allah ya gafarta mana?

15 Yanzu za a iya gafarta mana zunubanmu domin Allah ya ba da Ɗansa makaɗaici. Amma kafin Allah ya gafarta mana, akwai abin da muke bukata mu yi. Me ke nan? Yohanna Mai Baftisma da kuma Yesu Kristi sun ba da amsar. Sun ce: “Ku tuba, gama mulkin sama ya kusa!” (Mat. 3:​1, 2; 4:17) Da yake mu masu zunubi ne, muna bukatar mu tuba. Abin da zai taimaka mana mu yi nasara a kan zunubi, kuma mu ci-gaba da kusantar Jehobah ke nan. Amma me ake nufi da tuba, kuma ta yaya zai taimake mu mu yi nasara a kan zunubanmu? Abin da za mu tattauna a talifi nazari na gaba ke nan.

WAƘA TA 18 Muna Godiya Domin Mutuwar Yesu

a MAꞌANAR WASU KALMOMI: A Littafi Mai Tsarki, idan aka ce mutum ya yi “zunubi,” wani lokaci ana nufin ya aikata abin da bai dace ba a gaban Jehobah, ko kuma bai yi abin da Jehobah ya ce a yi ba. Wani lokaci kuma, ana nufin ajizanci ko zunubin da muka gada daga wurin Adamu. Zunubin da muka gada ne ya sa muke mutuwa.

b Jehobah ya amince da hadayun waɗannan bayinsa ne domin ya san cewa daga baya, Yesu zai ba da hadayar da za ta goge zunuban ꞌyan Adam gaba-ɗaya.—Rom. 3:25.