Ga Mai Karatu
Ga Mai Karatu
A wannan Hasumiyar Tsaro, akwai talifofi guda biyar da suke da alaƙa da juna:
Talifi na farko zai bayyana irin ƙaunar da Jehobah yake mana, da abin da ya yi don ya taimaka mana mu yi nasara a kan zunubi.
Talifi na biyu zai bayyana abin da tuban gaske yake nufi, da kuma yadda Jehobah ya taimaki mutane su tuba.
Talifi na uku zai bayyana yadda Jehobah ya ce ikilisiyar da ke Korinti su bi da wani da ya yi zunubi da gangan kuma ya ƙi ya tuba.
Talifi na huɗu zai bayyana yadda dattawa za su taimaka wa waɗanda suka yi zunubi mai tsanani.
A talifi na biyar kuma, za mu ga abin da dattawa da dukan ꞌyanꞌuwa za su yi idan aka cire wani daga ikilisiya, don su ci-gaba da nuna masa ƙauna da jinƙai.