TALIFIN NAZARI NA 32
WAƘA TA 44 Adduꞌar Wanda Ke Cikin Wahala
Jehobah Yana So Kowa Ya Tuba
“Ubangiji . . . ba ya so wani ya halaka, sai dai kowa ya zo ya tuba.”—2 BIT. 3:9.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga abin da ake nufi da tuba, da abin da ya sa dukanmu muke bukatar mu tuba, da kuma yadda Jehobah ya taimaka wa mutane su tuba.
1. Idan aka ce mutum ya tuba, me ake nufi?
IDAN muka yi zunubi, muna bukatar mu tuba. A Littafi Mai Tsarki, idan aka ce mutum ya tuba, ana nufin ya ƙi jinin zunubin da yake yi, ya daina yinsa, kuma ya yi niyya cewa ba zai sake yinsa ba.—Mat. 3:8; A. M. 3:19; 2 Bit. 3:9.
2. Me ya sa dukanmu muke bukatar mu san raꞌayin Allah game da yin tuba? (Nehemiya 8:9-11)
2 Dukan mutane suna bukatar su san raꞌayin Allah game da yin tuba. Me ya sa? Domin dukanmu muna yin zunubi kowace rana. Dukanmu mun gaji zunubi da mutuwa daga wurin Adamu da Hauwaꞌu, domin mu ꞌyaꞌyansu ne. (Rom. 3:23; 5:12) Babu waninmu da bai da zunubi. Mutane masu bangaskiya sosai ma, sun yi fama da zunubi. Abin da ya faru da manzo Bulus ke nan. (Rom. 7:21-24) Amma wannan yana nufin cewa kullum za mu yi ta baƙin ciki don zunubanmu ke nan? Aꞌa. Me ya sa? Domin Jehobah mai jinƙai ne, kuma yana so mu riƙa yin farin ciki. Ka lura da abin da ya faru da Yahudawa a kwanakin Nehemiya. (Karanta Nehemiya 8:9-11.) Jehobah bai so su ci-gaba da yin baƙin ciki a kan zunuban da suka yi ba, amma yana so su bauta masa da farin ciki. Jehobah ya san cewa tuba yakan kawo farin ciki. Shi ya sa ya koya mana abubuwa da dama game da yin tuba. Idan muka tuba, muna da tabbaci cewa Ubanmu mai jinƙai zai yafe mana zunubanmu.
3. Me za mu tattauna a wannan talifin?
3 A talifin nan, za mu bincika batun yin tuba. Don mu yi haka, za mu tattauna abubuwa uku. Na ɗaya, za mu tattauna abin da Jehobah ya koya wa Israꞌilawa game da yin tuba. Na biyu, za mu tattauna yadda Jehobah yake taimaka wa masu zunubi su tuba. A ƙarshe kuma, za mu tattauna abin da Yesu ya koya wa mabiyansa game da yin tuba.
ABIN DA JEHOBAH YA KOYA WA ISRAꞌILAWA GAME DA YIN TUBA
4. Mene ne Jehobah ya koya wa Israꞌilawa game da yin tuba?
4 A lokacin da Jehobah ya ba wa Israꞌilawa dokoki, sun yi masa alkawari cewa za su yi biyayya. Kuma Jehobah ya ce idan suka bi dokokinsa, zai yi musu albarka kuma zai kāre su. Ya kuma gaya musu cewa: “Hakika, wannan umarnin da nake umarce ku yau, bai fi ƙarfinku ba, ko ya gagare ku aikatawa ba.” (M. Sha. 30:11, 16) Amma ya ce idan suka ƙi bin dokokinsa ko suka koma bauta ma wasu alloli, zai daina ba su kāriya, kuma za su sha wuya. Duk da haka, Jehobah ba zai ƙyale su kwata-kwata ba. Idan suka ‘juyo ga Yahweh Allahnsu, su da ꞌyaꞌyansu suka yi masa biyayya,’ ya ce zai karɓe su. (M. Sha. 30:1-3, 17-20) Wato ke nan, Jehobah ya ba su damar yin tuba. Kuma da zarar sun tuba, Jehobah zai sake kusantar su kuma ya yi musu albarka.
5. Me ya nuna cewa Jehobah ya yi ta haƙuri da Israꞌilawa? (2 Sarakuna 17:13, 14)
5 Israꞌilawa sun yi ta yi wa Jehobah rashin biyayya. Sun bauta wa gumaka, kuma sun yi miyagun abubuwa iri-iri. A sakamakon haka, sun sha wuya. Amma Jehobah ya yi ta taimaka musu don su dawo gare shi. Ya yi ta tura annabawansa su roƙi Israꞌilawa su tuba kuma su bauta masa da dukan zuciyarsu.—Karanta 2 Sarakuna 17:13, 14.
6. Ta yaya Jehobah ya koya wa mutanensa muhimmancin yin tuba ta wurin annabawansa? (Ka kuma duba hoton.)
6 Idan mutanen Jehobah suka yi masa rashin biyayya, yakan aiki annabawansa su gargaɗe su. Alal misali, ya aiki Irmiya ya gaya musu cewa: “Ya ke Israꞌila marar aminci, ki dawo gare ni, . . . ba zan yi fushi da ke har abada ba . . . Ke dai ki yarda da laifinki cewa kin yi wa Yahweh Allahnki zunubin ganganci.” (Irm. 3:12, 13) Jehobah ya gaya wa annabi Yowel ya ce musu: “Ko yanzu, kuna iya juyo gare ni da dukan zuciyarku.” (Yow. 2:12, 13) Ya aiki Ishaya ya gaya musu cewa: “Ku tsabtace kanku sarai! Ku kawar da mugayen ayyukanku daga gabana. Ku daina aikata mugunta.” (Isha. 1:16-19) Kuma ta bakin Ezekiyel, Jehobah ya ce musu: “Ni ina jin daɗin mutuwar mugu ne? . . . Ai, na gwammanci ya juya daga yin mugunta ya rayu! Gama ni ba na jin daɗin mutuwar kowa, . . . saboda haka sai ku juyo gare ni ku rayu.” (Ezek. 18:23, 32) Jehobah yakan yi farin ciki sosai idan ya ga mutum ya tuba, domin yana so kowa ya rayu har abada! Don haka Jehobah ba ya jira sai mutane sun tuba kafin ya taimake su. Bari mu ga wasu misalan da suka nuna hakan.
7. Mene ne Jehobah ya koya wa mutanensa ta wurin Annabi Hosiya da matarsa?
7 Ka lura da darasin da Jehobah ya koya wa mutanensa ta wurin Annabi Hosiya da matarsa Gomer. Bayan da ta yi zina, ta bar annabi Hosiya ta shiga bin maza. Shin, zai yiwu irin wannan macen ta tuba kuwa? Jehobah, wanda ya san abin da ke zuciyar kowa, ya gaya wa Hosiya cewa: ‘Ka tafi, ka ci-gaba da nuna ƙaunarka ga matarkan nan wadda take bin maza tana zina da su. Ka ƙaunace ta kamar yadda ni Yahweh nake ƙaunar Israꞌila, ko da yake ta juya ga bin waɗansu alloli.’ (Hos. 3:1; K. Mag. 16:2) A lokacin matar Hosiya tana kan yin zina. Duk da haka Jehobah ya ce ma Hosiya ya je ya same ta, ya yafe mata, kuma ya dawo da ita ta wurinsa. a Jehobah ya yi amfani da wannan labarin ne don ya koya wa Israꞌilawa raꞌayinsa game da su. Wato, duk da yake suna kan yin zunubi mai tsanani, yana ƙaunarsu. Shi ya sa yake aikan annabawansa su taimaka musu su tuba. Wannan labarin ya koya mana cewa Jehobah ya san kome, kuma ko da mutum yana kan yin zunubi mai tsanani, Jehobah zai yi ƙoƙarin taimaka masa ya tuba. (K. Mag. 17:3) Bari mu ga yadda Jehobah ya yi hakan.
YADDA JEHOBAH YAKE TAIMAKA WA MASU ZUNUBI SU TUBA
8. Mene ne Jehobah ya yi don ya taimaki Kayinu ya tuba? (Farawa 4:3-7) (Ka kuma duba hoton.)
8 Kayinu ne ɗan farin Adamu da Hauwaꞌu. Shi ma ya gaji zunubi daga wurinsu. Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ayyukansa mugaye ne.” (1 Yoh. 3:12) Wataƙila abin da ya sa Jehobah “bai karɓi bayarwa ta Kayinu ba” ke nan. Maimakon Kayinu ya canja halinsa, “ya yi fushi sosai har ya ɗaure fuskarsa.” Mene ne Jehobah ya yi? Ya shawarci Kayinu. (Karanta Farawa 4:3-7.) Ka lura cewa Jehobah ya yi wa Kayinu magana da alheri. Ya gaya masa cewa zai albarkace shi idan ya canja halinsa, kuma ya ce idan bai daina fushin da yake yi ba, fushin zai kai shi ga yin zunubi. Amma abin baƙin cikin shi ne cewa, Kayinu ya ƙi ji. Bai karɓi taimakon da Jehobah ya yi masa don ya tuba ba. Amma hakan ya sa Jehobah ya daina taimakon masu zunubi su tuba ne? Aꞌa.
9. Mene ne Jehobah ya yi don ta taimaki Dauda ya tuba?
9 Jehobah ya ƙaunaci Sarki Dauda ba kaɗan ba. Ya ce: Dauda ‘mutum ne mai zuciya irin tasa.’ (A. M. 13:22) Amma Dauda ya yi zunubai masu tsanani. Ya yi zina kuma ya yi kisa. Bisa ga Dokar Musa, Dauda ya cancanci mutuwa. (L. Fir. 20:10; L. Ƙid. 35:31) Duk da haka, Jehobah ya yi ƙoƙarin taimaka masa ya tuba. b Ya aiki annabi Natan wurinsa, duk da cewa a lokacin, Dauda bai riga ya nuna ko alamar duba ba. Abin da annabin ya gaya masa ya ratsa zuciyarsa, kuma ya tuba. (2 Sam. 12:1-14) Ya rubuta wata waƙa da ta nuna baƙin cikinsa, wato Zabura ta 51. (Rubutu da ke saman Zab. 51) Wannan zaburar ta ƙarfafa masu zunubi da dama, kuma ta taimaka musu su tuba. Mun gode wa Jehobah sosai da ya nuna wa Dauda ƙauna kuma ya taimaka masa ya tuba.
10. Yaya kake ji game da yadda Jehobah yake haƙuri da mu da yadda yake so ya yafe mana zunubanmu?
10 Jehobah ya tsani zunubi, ko da wane iri ne. (Zab. 5:4, 5) Amma ya san cewa dukanmu masu zunubi ne, kuma yana ƙaunarmu. Shi ya sa idan muka yi zunubi yakan taimaka mana. A ko da yaushe, Jehobah yana ƙoƙari ya taimaka wa mai zunubi ya tuba, komen tsananin zunubinsa. Hakan ya nuna cewa Jehobah yana so ya yafe mana. Wannan ba abin ban ƙarfafa ba ne? Idan muka yi tunani a kan yawan haƙurin Jehobah da yadda yake so ya yafe mana, hakan zai sa mu yi iya ƙoƙarinmu mu riƙe amincinmu. Kuma idan muka yi zunubi, za mu yi saurin tuba. Yanzu bari mu tattauna abin da Yesu ya koya wa mabiyansa game da yin tuba.
ABIN DA YESU YA KOYA WA MABIYANSA GAME DA YIN TUBA
11-12. Wane labari ne Yesu ya bayar don ya nuna mana cewa Allah yana so ya yafe mana zunubanmu? (Ka duba hoton.)
11 A ƙarni na farko ne aka gano Almasihun da aka daɗe ana jira. Kuma kamar yadda muka gani a talifin da ya gabata, Jehobah ya yi amfani da Yohanna Mai Baftisma da Yesu ya koya wa mutanensa muhimmancin yin tuba.—Mat. 3:1, 2; 4:17.
12 Da Yesu yake duniya, ya koya wa mutane cewa Jehobah yana marmarin yafe mana zunubanmu. Wata hanyar da Yesu ya yi hakan, ita ce ta wurin ba da labarin wani Saurayi da Babansa. Labarin nan yana da ban-ƙarfafa. Saurayin ya bar gida, kuma ya je ya yi abubuwa da dama marasa kyau. A-kwana-a-tashi, “ya dawo ciki hankalinsa” kuma ya koma gida. Da babansa ya hango shi, me ya yi? Yesu ya ce: “Tun yana daga nesa, sai babansa ya gane shi. Tausayi ya kama baban, ya tashi da gudu ya je ya rungumi ɗansa, ya yi ta yi masa sumba.” Saurayin ya roƙi mahaifinsa ya mai da shi bawansa, amma sai mahaifinsa ya ce da shi “ɗan nan nawa,” kuma ya dawo da shi cikin iyalinsa. Mahaifin ya ce dā ɗan nasa “ya ɓace, amma yanzu an same shi.” (Luk. 15:11-32) Kafin Yesu ya zo duniya, ya saba ganin yadda Jehobah yake tausaya wa masu zunubi kuma yana gafarta musu da sauri idan suka tuba. Hakika, wannan labarin da Yesu ya bayar yana ƙarfafa mu. Ya nuna cewa Ubanmu Jehobah mai tausayi ne sosai!
13-14. Mene ne Bitrus ya fahimta game da tuba, kuma me ya koya wa mutane game da hakan? (Ka kuma duba hoton.)
13 Manzo Bitrus ya koyi darasi sosai daga wurin Yesu game da yadda Jehobah yake gafarta wa waɗanda suka tuba. Bitrus ya yi kurakure da dama, kuma Yesu ya yi ta yafe masa. Alal misali, a lokacin da Bitrus ya yi mūsun sanin Yesu, abin ya dame shi ba kaɗan ba. (Mat. 26:34, 35, 69-75) Amma da Yesu ya tashi daga mutuwa, ya bayyana ga Bitrus a lokacin da yake shi kaɗai. (Luk. 24:33, 34; 1 Kor. 15:3-5) Yesu ya san cewa Bitrus ya tuba, kuma ba mamaki ya tabbatar masa da cewa ya yafe masa.
14 Abubuwan da suka faru da Bitrus sun sa ya fahimci abin da ake nufi da yin tuba, da kuma yadda mutum yake ji idan aka yafe masa zunubinsa. Shi ya sa ya iya koyar da wasu. Alal misali, bayan bikin ranar Fentakos, Bitrus ya bayyana ma Yahudawa da suka taru cewa su ne suka kashe Almasihu. Amma ya ƙarfafa su da cewa: “Ku tuba, ku juyo ga Allah domin a wanke zunubanku, domin Ubangiji ya sabunta zuciyarku.” (A. M. 3:14, 15, 17, 19) Bitrus ya nuna cewa idan mutum ya tuba, yana bukatar ya juyo ga Allah. Wato zai canja tunaninsa, ya daina yin zunubin, kuma ya soma yin abin da zai gamshi Allah. Ya kuma ce Jehobah zai wanke zunubansu, wato zai gafarta musu gabaki-ɗaya. Shekaru da yawa bayan haka kuma, Bitrus ya gaya wa Kiristoci cewa Jehobah yana yin haƙuri da su, domin “ba ya so wani ya halaka, sai dai kowa ya zo ya tuba.” (2 Bit. 3:9) Hakan ya nuna cewa komen zunubin da muka yi, idan muka tuba, Jehobah zai yafe mana! Wannan ba abin ban ƙarfafa ba ne?
15-16. (a) Me ya taimaka wa manzo Bulus ya fahimci yadda Jehobah yake gafartawa? (1 Timoti 1:12-15) (b) Me za mu tattauna a talifi na gaba?
15 Bulus shi ma ya yi zunubi sosai a dā. Ya wulaƙanta mabiyan Yesu ba kaɗan ba. (A. M. 7:58–8:3) Wataƙila wasu Kiristoci sun ɗauka cewa ba zai taɓa iya canja halinsa ba. Amma Yesu ya san cewa Bulus zai iya canjawa kuma ya tuba. Shi da Jehobah sun ga cewa Bulus yana da halin kirki. Yesu ya ce: “Shi mutum ne da na zaɓa ya yi aikina.” (A. M. 9:15) Har Yesu ya yi abin ban mamaki don ya taimaki Bulus ya tuba. (A. M. 9:1-9, 17-20) Bulus ya tuba ya zama Kirista, kuma Yesu ya mai da shi manzonsa. Ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, Bulus ya yi ta faɗin irin godiyar da yake yi domin alheri da jinƙai da Jehobah da Yesu suka yi masa. (Karanta 1 Timoti 1:12-15.) Ya ce: ‘Nufin alherin Allah shi ne ya jawo ka ga tuba.’—Rom. 2:4.
16 Akwai lokacin da Bulus ya ji cewa wani mutum yana yin lalata a ikilisiyar da ke Korinti, kuma ba a yi masa kome ba. Mene ne Bulus ya ce musu su yi? Abin da ya gaya musu ya bayyana irin ƙaunar da Jehobah yake nuna wa bayinsa duk saꞌad da ya yi musu horo, da jinƙan da yake musu idan suka tuba. A talifi na gaba, za mu tattauna abin da ya faru a wannan ikilisiyar.
WAƘA TA 33 Mu Miƙa Dukan Damuwarmu ga Jehobah
a A yau, Jehobah bai ce idan miji ko matar mutum ta yi zina, dole su ci-gaba da zama tare ba. Saboda ƙaunar da Jehobah yake ma waɗanda aka ci amanarsu, Jehobah ya ba su dama su kashe auren idan suna so su yi hakan. Ya bayyana wannan ta bakin Ɗansa Yesu.—Mat. 5:32; 19:9.
b Ka duba talifin da ya ce, “Ka Amfana Daga Yadda Jehobah Yake Gafarta Mana?” da ke Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Nuwamba, 2012, shafi na 21-23, sakin layi na 3-10.