Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

2 Tasalonikawa 3:14 ta ce mu “lura” da wasu irin mutane. Shin dattawa ne za su yanke wannan shawarar, ko dai kowane Kirista ne?

A wasiƙar da manzo Bulus ya rubuta wa ꞌyanꞌuwa da ke Tasalonika, ya ce: “Idan wani ya ƙi biyayya da abin da muka faɗa a cikin wasiƙar nan, sai ku lura da shi.” (2 Tas. 3:14) A dā, mun ce dattawa ne aka ba wannan umurnin. Shi ya sa idan wani ya ƙi bin ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki duk da cewa an yi masa gargaɗi sau da yawa, dattawa za su sa ɗayansu ya yi jawabi da zai sa ꞌyanꞌuwa su lura da mutumin. Bayan haka, ꞌyanꞌuwa ba za su riƙa tarayya da shi ba.

Amma yanzu mun gane cewa umurnin nan da Bulus ya bayar, mataki ne da kowane Kirista zai ɗauka da kansa bisa ga abin da ya gani. Saboda haka, ba a bukatar a yi jawabi da zai nuna cewa dattawa suna so a lura da wani. Me ya sa muka yi gyara a yadda muka fahimci umurnin Bulus? Bari mu bincika abin da yake magana a kai a lokacin da ya ba da wannan umurnin.

Bulus ya ga cewa wasu a ikilisiyar suna “rayuwar ƙyuya.” Ba sa bin umurnan da yake basu daga Kalmar Allah. Kafin wannan lokacin, ya gaya musu cewa: “Duk wanda ya ƙi yin aiki, kada a ba shi abinci.” Duk da haka, wasu mutane sun ƙi yin aiki don biyan bukatunsu, duk da cewa suna da ƙarfin yin hakan. Ƙari ga haka, suna shishigi cikin alꞌamuran wasu. Yaya ꞌyanꞌuwa za su bi da irin waɗannan mutanen?—2 Tas. 3:​6, 10-12.

Bulus ya ce, “ku lura da” su. A Hellenanci hakan yana nufin cewa mu gane irin waɗannan mutanen, kuma mu yi hankali da su don kada halinsu ya shafe mu. Bulus ya yi wa ikilisiya gabaki ɗaya ne wannan gargaɗin, ba dattawa kaɗai ba. (2 Tas. 1:1; 3:6) Saboda haka kowane Kirista da ya ga wani ɗanꞌuwa ko ꞌyarꞌuwa da ta ƙi bin ƙaꞌidodin Kalmar Allah ne zai zaɓi ya “guje” wa iri wannan mutumin.

Wannan yana nufin cewa za a guje masa kamar wanda aka cire daga ikilisiya ne? Aꞌa. Bulus ya ce: “Ku gargaɗe shi kamar ɗanꞌuwa.” Saboda haka ꞌyanꞌuwa za su ci-gaba da yin waꞌazi da wanda ake lura da shi, kuma za su yi abubuwa tare da shi a taro. Amma ba za su riƙa yin nishaɗi ko shakatawa da shi ba. Me ya sa? Bulus ya ce: “Domin ya ji kunya.” Idan muka daina yin tarayya da mutumin, hakan zai iya sa ya ji kunya kuma ya canja halinsa.—2 Tas. 3:​14, 15.

Ta yaya Kirista zai san wanda ya kamata ya lura da shi? Kamar yadda Bulus ya ce, zai dace mu tabbata cewa halin mutumin ya saɓa wa abin da Kalmar Allah ta ce. Ba mutanen da raꞌayinsu ya bambanta da namu ko waɗanda suka ɓata mana rai ba ne Bulus yake nufi ba. Maimakon haka, Bulus yana magana ne musamman game da mutane da suka ƙi bin ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da gangan.

A yau, idan muka lura da wani ɗanꞌuwa da ba ya son bin ƙaꞌidodin Jehobah, a za mu iya yanke shawara cewa ba za mu riƙa yin tarayya da shi ba. Da yake wannan shawara ce da muka yanke da kanmu ko a iyalinmu, ba za mu gaya ma wasu mutane ba. Amma za mu ci-gaba da yin cuɗanya da ɗanꞌuwan a taro da kuma a waꞌazi. Kuma idan ya canja halinsa, sai mu soma yin tarayya da shi.

a Alal misali, idan Kirista ya ƙi yin aiki don biyan bukatunsa, duk da cewa yana da ƙarfin yin hakan, ko wataƙila ya nace da neman wadda ba ta bauta wa Jehobah, ko ƙila yana kushe umurnan da ƙungiyar Jehobah take bayarwa, ko kuma shi mai gulma ne. (1 Kor. 7:39; 2 Kor. 6:14; 2 Tas. 3:​11, 12; 1 Tim. 5:13) Zai dace mu lura da waɗanda suka ci-gaba da yin irin halayen nan.