TALIFIN NAZARI NA 52
Ka Taimaka ma Wasu Su Iya Jimre Matsalolinsu
“Kada ka janye alheri daga waɗanda sun cancanta a yi musu, sa’ad da ikon yin haka yana hannunka.”—K. MAG. 3:27.
WAƘA TA 103 Jehobah Ya Yi Tanadin Makiyaya
ABIN DA ZA A TATTAUNA a
1. Ta yaya Jehobah yake amsa adduꞌoꞌin bayinsa masu aminci?
SHIN ka san cewa Jehobah zai iya yin amfani da kai ya amsa adduꞌar da wani ya yi? Zai iya yin hakan ko da kai dattijo ne ko bawa mai hidima ko majagaba ko kuma mai shela da ya yi baftisma. Zai iya amfani da kai ko da kai matashi ne ko ɗanꞌuwa ko kuma ꞌyarꞌuwa ce. Saꞌad da wani bawan Jehobah ya yi adduꞌa gare shi, Jehobah yakan yi amfani da dattawa ko wasu bayinsa masu aminci domin ya ƙarfafa mutumin. (Kol. 4:11) Hakika, muna farin cikin bauta ma Jehobah da kuma taimaka ma ꞌyanꞌuwanmu ta wannan hanyar! Za mu iya taimaka da kuma ƙarfafa ꞌyanꞌuwanmu saꞌad da annoba ta ɓarke ko a lokacin balaꞌi ko kuma a lokacin da ake tsananta ma ꞌyanꞌuwanmu.
KA TAIMAKA MA WASU A LOKACIN ANNOBA
2. Me ya sa zai iya yi mana wuya mu taimaka ma junanmu a lokacin annoba?
2 Zai iya yi mana wuya mu taimaka ma junanmu a lokacin annoba. Alal misali, za mu so mu ziyarci abokanmu, amma yin hakan zai kasance da haɗari. Za mu kuma so mu gayyaci ꞌyanꞌuwanmu da suke fama da matsalar kuɗi don mu ci abinci tare, amma hakan ma ba zai iya yiwuwa ba. Muna so mu taimaki ꞌyanꞌuwanmu, amma hakan zai iya yi mana wuya idan wasu a iyalinmu suna fama da matsaloli. Duk da haka, muna so mu taimaka ma ꞌyanꞌuwanmu kuma Jehobah zai yi farin ciki idan muka yi iya ƙoƙarinmu don mu taimaka musu. (K. Mag. 3:27; 19:17) Mene ne za mu iya yi?
3. Mene ne muka koya daga misalin dattawa da ke ikilisiyar Desi? (Irmiya 23:4)
3 Abin da dattawa za su iya yi. Idan kai dattijo ne, ka yi ƙoƙari ka san ꞌyanꞌuwa da kyau. (Karanta Irmiya 23:4.) ꞌYarꞌuwa Desi da aka ambata a talifin baya ta ce: “Dattawa da ke rukunin waꞌazinmu sukan yi waꞌazi tare da ni da wasu ꞌyanꞌuwa a rukunin, kuma mukan yi liyafa tare.” b Ƙoƙarin da dattawan suka yi ya sa ya yi musu sauƙi su iya taimaka ma Desi a lokacin annobar korona, saꞌad da wasu a iyalinta suka mutu sanadiyyar cutar.
4. Me ya sa dattawa sun iya taimaka ma Desi kuma wane darasi ne muka koya daga hakan?
4 Desi ta ce: “Da yake na riga na san dattawan da kyau, ya yi mini sauƙi in gaya musu damuwata da yadda nake ji.” Wane darasi ne dattawa za su iya koya daga hakan? Ku yi ƙoƙari ku san ꞌyanꞌuwa a ikilisiyarku da kyau tun kafin su fuskanci matsaloli. Ku zama abokansu. Idan annoba ta ɓarke kuma ba za ku iya ziyarce su ba, ku nemi wata hanya da za ku iya ji daga gare su. Desi ta ce: “A wasu lokuta, a rana ɗaya, dattawa dabam-dabam sukan kira ni ko kuma su aika mini saƙonni. Nassosi da suka tattauna da ni sun ƙarfafa ni ko da yake na riga na san Nassosin da kyau.”
5. Ta yaya dattawa za su iya sanin abubuwa da ꞌyanꞌuwa suke bukata, kuma su iya taimaka musu?
5 Hanya ɗaya da za ka iya sanin abubuwan da ꞌyanꞌuwanka suke bukata, ita ce ta wajen yi musu tambayoyin da ba za su kunyatar da su ba. (K. Mag. 20:5) Za ka iya yin tambayoyi don ka san ko suna da isasshen abinci da magunguna da kuma wasu abubuwan biyan bukata. Shin akwai abin da ya nuna cewa za a iya korar su daga aiki, ko kuma ba su da kuɗin biyan gidan haya? Ko za su bukaci mu taimaka wajen nema musu tallafi daga gwamnati idan zai yiwu? ꞌYanꞌuwa sun taimaka ma Desi da abubuwan biyan bukata. Amma ƙauna da dattawa suka nuna mata da kuma yadda suka ƙarfafa ta da Littafi Mai Tsarki ne ya fi taimaka mata. Ta ce: “Dattawan sun yi adduꞌa tare da ni. Ko da yake ba zan iya tuna abubuwan da suka faɗa ba, amma na tuna yadda na ji. Kamar dai Jehobah yana gaya min cewa, ‘Ina tare da ke.’ ”—Isha. 41:10, 13.
6. Mene ne ꞌyanꞌuwa za su iya yi don su taimaka ma wasu? (Ka duba hoton da ya shafi sakin layi na 6.)
6 Abin da wasu za su iya yi. Muna sa rai cewa dattawa za su taimaka ma ꞌyanꞌuwa da ke da bukata. Amma Jehobah yana gaya wa dukanmu cewa mu ƙarfafa da kuma taimaka ma juna. (Gal. 6:10) Ko da mun yi ƙaramin abu ne don mu nuna wa ꞌyanꞌuwanmu cewa muna ƙaunar su, hakan zai iya ƙarfafa su. Yara za su iya bin iyayensu idan iyayen suka je su gai da wani ɗanꞌuwa. Matasa kuma za su iya zuwa aika ko su yi cefane ma wata ꞌyarꞌuwa. Wasu a ikilisiya za su iya dafa abinci su kai ma wani da ke rashin lafiya. Hakika, a lokacin annoba, kowa a ikilisiya yana bukatar ƙarfafa. Za mu iya ɗan dakatawa bayan an gama taro don mu iya tattauna da ꞌyanꞌuwanmu ido da ido ko kuma ta bidiyo. Dattawa ma suna bukatar ƙarfafa. Wasu ꞌyanꞌuwa sun aika saƙon godiya ga dattawa domin aikin da suke yi tuƙuru a lokacin annoba. Hakika, yana da muhimmanci mu ci gaba da ƙarfafa juna da kuma gina juna!—1 Tas. 5:11.
KA TAIMAKA MA WAƊANDA BALAꞌI YA AUKO MUSU
7. Wane ƙalubale ne za mu iya fuskanta bayan balaꞌi ya auko mana?
7 Balaꞌi zai iya canja rayuwar mutum farat ɗaya. Waɗanda balaꞌi ya auko musu za su iya rasa gidajensu da dukiyarsu ko ƙaunatattunsu. Irin balaꞌin nan yakan auko ma ꞌyanꞌuwanmu Kiristoci. Ta yaya za mu iya taimaka musu?
8. Mene ne dattawa ko waɗanda suke ja-goranci a iyali za su iya yi kafin balaꞌi ya auko?
8 Abin da dattawa za su iya yi. Dattawa, ku taimaka ma ꞌyanꞌuwanku su shirya kafin balaꞌi ya auko. Ku tabbata cewa kowa da kowa a ikilisiya ya san matakan da zai ɗauka don ya kāre kansa kuma yana da hanyoyin da zai iya kiran dattawa. ꞌYarꞌuwa Margaret da aka ambata a talifin baya ta ce: “Dattawanmu sun gargaɗe mu saꞌad da suke tattauna bukatun ikilisiya cewa gobarar dajin ba ta ƙare ba. Sun ce idan hukumomi sun umurce mu mu fita daga yankin, ko kuma yanayin ya daɗa tsanani, zai dace mu fita ba tare da ɓata lokaci ba.” ꞌYanꞌuwan sun ba da umurnin a lokacin da ya dace domin gobarar daji ta soma makonni biyar bayan hakan. Zai dace kowane iyali su tattauna abin da kowannensu zai yi saꞌad da suke ibada ta iyali. Idan iyalinku sun shirya da kyau kafin balaꞌi ya auko, za ku iya kasancewa da kwanciyar hankali a lokacin balaꞌi.
9. Ta yaya dattawa za su iya yin aiki tare kafin balaꞌi ya auku ko kuma bayan hakan?
9 Idan kai ne mai kula da rukunin waꞌazinku, ka tabbata cewa ka karɓi lambobin waya da kuma adireshin ꞌyanꞌuwa da ke rukuninku idan sun yarda su ba ka. Ka adana lambobin kuma ka riƙa tuntuɓar ꞌyanꞌuwan don ka tabbata cewa ba abin da ya canja. Da hakan, a lokacin balaꞌi za ka iya kiran kowane mai shela kuma ka san abubuwan da yake bukata. Bayan haka, sai ka gaya wa mai tsara ayyukan rukunin dattawa ba tare da ɓata lokaci ba, shi kuma zai gaya wa mai kula da daꞌira. Idan ꞌyanꞌuwan nan sun yi aiki tare, za su iya taimakawa. Bayan gobarar dajin, mai kula da daꞌirar su Margaret bai yi barci ba na saꞌoꞌi 36, yana aiki tuƙuru wajen yi wa dattawa ja-goranci yayin da suke ƙoƙarin kiran ꞌyanꞌuwa 450 da suka gudu daga gidajensu don su kula da su. (2 Kor. 11:27) Don haka, an tanadar da masauƙi ga dukan ꞌyanꞌuwa da suke bukatarsa.
10. Me ya sa dattawa suke ɗaukan ziyarar ƙarfafa da muhimmanci sosai? (Yohanna 21:15)
10 An ba dattawa aikin ƙarfafa da kuma taimaka ma waɗanda suke cikin damuwa. (1 Bit. 5:2) Idan balaꞌi ya auku, abu na farko da dattawa za su yi shi ne su tabbata cewa kowane ɗanꞌuwa ko ꞌyarꞌuwa tana da isasshen abinci, da kayan sakawa, da wurin kwana. Amma watanni bayan bala’in ma za su bukaci su ci gaba da ƙarfafa ꞌyanꞌuwan daga Littafi Mai Tsarki. (Karanta Yohanna 21:15.) Wani memban Kwamitin da Ke Kula da Reshen Ofishinmu mai suna Harold yakan je wurin ꞌyanꞌuwa da yawa da balaꞌi ya auko musu. Ɗan’uwan ya ce: “Yakan ɗauki lokaci kafin mutum ya sami sauƙi. Za su iya soma mantawa da hasarar da suka yi, amma tunanin ꞌyanꞌuwansu da suka rasu ko kuma wani kayan tarihi mai daraja da suka rasa ko yadda suka tsallake rijiya da baya, zai iya daɗe yana damun su. Tunanin zai iya sa su riƙa yin baƙin ciki. Hakan ba ya nufin cewa ba su da bangaskiya, amma yana nuna cewa su ma ꞌyan Adam ne.”
11. Waɗanne abubuwa ne wataƙila iyalai za su ci gaba da bukata?
11 Dattawa suna bin shawarar nan cewa: “Ku yi kuka tare da masu kuka.” (Rom. 12:15) Dattawa suna bukatar su tabbatar ma waɗanda suka fuskanci balaꞌi cewa Jehobah da kuma ꞌyanꞌuwansu suna ƙaunar su. Zai dace dattawa su taimaka wa iyalai su ci gaba da yin ayyukan ibada, kamar adduꞌa da nazarin Littafi Mai Tsarki da halartan taro da kuma yin waꞌazi. Ƙari ga haka, dattawa za su iya ƙarfafa iyaye su taimaka ma yaransu su mai da hankali ga abubuwan da za su dawwama. Iyaye, ku tuna wa yaranku cewa Jehobah zai ci gaba da zama Abokinsu kuma zai kasance tare da su a kullum don ya taimaka musu. Kuma ku bayyana musu cewa a kullum ꞌyanꞌuwansu da ke duk faɗin duniya suna tare da su, kuma za su taimaka musu a lokacin da suke bukata.—1 Bit. 2:17.
12. Mene ne wasu za su iya yi don su taimaka da aikin agaji? (Ka duba hoton da ya shafi sakin layi na 12.)
12 Abin da wasu za su iya yi. Idan balaꞌi ya auku kusa da kai, ka tambayi dattawa abin da za ka iya yi don ka taimaka. Mai yiwuwa za ka iya taimaka wajen ba da masauƙi ga ꞌyanꞌuwa da suka gudu daga gidajensu, ko ꞌyanꞌuwa da ke aikin gine-gine. Za ka kuma iya kai abinci da wasu kayayyaki ga ꞌyanꞌuwa da ke bukatarsu. Ƙari ga haka, za ka iya taimakawa idan balaꞌi ya auku a wurin da ke da nisa da kai. Ta yaya? Ta wajen yin adduꞌa a madadin waɗanda hakan ya shafa. (2 Kor. 1:8-11) Za ka kuma iya tallafa ma aikin agajin da ake yi ta wajen ba da gudummawa ga ayyukan da ake yi a dukan faɗin duniya. (2 Kor. 8:2-5) Idan kuma za ka iya zuwa inda balaꞌin ya auku, ka gaya ma dattawa cewa za ka so ka taimaka. Idan aka gayyace ka ka taimaka, ba mamaki za a koya maka yadda za ka taimaka a lokaci da kuma wurin da ake bukatar ka.
KA TAIMAKA MA ꞌYANꞌUWA SU JIMRE TSANANTAWA
13. Waɗanne ƙalubale ne ꞌyanꞌuwanmu suke fuskanta a ƙasashe da aka saka mana takunkumi?
13 A ƙasashe da aka hana aikinmu, tsanantawa yakan sa rayuwa ya yi ma ꞌyanꞌuwanmu wuya. Ƙari ga haka, ꞌyanꞌuwa a ƙasashen nan sukan fuskanci matsalar kuɗi, sukan yi rashin lafiya kuma sukan rasa ƙaunatattunsu. Amma saboda takunkumin, dattawa ba za su iya ziyarci ꞌyanꞌuwan a gidajensu ko kuma su tattauna da ꞌyanꞌuwan da ke bukatar ƙarfafa da kyau ba. Abin da ya faru da Andrei da muka ambata a talifin baya ke nan. Wata ꞌyarꞌuwa a rukunin waꞌazinsu ta yi fama da rashin kuɗi. Sai ta yi hatsari a mota. Ta bukaci a yi mata tiyata a wurare da dama, kuma ta kasa yin aiki. Duk da takunkumi da aka saka musu a ƙasar da kuma annobar korona, ꞌyanꞌuwan sun yi iya ƙoƙarinsu su taimaka mata, kuma Jehobah ya lura da hakan.
14. Ta yaya dattawa za su nuna cewa suna dogara ga Jehobah don ꞌyanꞌuwa su bi misalinsu?
14 Abin da dattawa za su iya yi. Andrei ya yi adduꞌa kuma ya yi iya ƙoƙarinsa. Mene ne Jehobah ya yi? Ya yi tanadin ꞌyanꞌuwa a ikilisiya da za su iya taimakawa sosai. Wasu sun kai ꞌyarꞌuwar asibiti da motarsu. Wasu kuma sun ba ta gudummawar kuɗi. Jehobah ya sa sun taimaka mata, kuma ya tabbata cewa ƙoƙarin da ꞌyanꞌuwa maza da mata a ikilisiya suka yi ya biya ma ꞌyarꞌuwar bukata. (Ibran. 13:16) Dattawa, idan aka hana wasu ɓangare na ayyukanmu, ku ba wasu dama su yi aikin tare da ku. (Irm. 36:5, 6) Abu mafi muhimmanci shi ne, ku dogara ga Jehobah. Zai iya taimaka muku ku tanada ma ꞌyanꞌuwanmu abubuwan da suke bukata.
15. Ta yaya za mu ci gaba da kasancewa da haɗin kai da ꞌyanꞌuwanmu saꞌad da ake tsananta mana?
15 Abin da wasu za su iya yi. Saꞌad da aka saka ma ayyukanmu takunkumi, za mu bukaci mu soma yin taro a ƙananan rukuni. Don haka, a wannan lokaci ne ya fi dacewa mu riƙa zaman lafiya da juna. Mu yi faɗa da Shaiɗan, ba da junanmu ba. Idan wani ya yi muku laifi, ku gafarta masa, kuma ku yi ƙoƙari ku sasanta da shi da wuri. (K. Mag. 19:11; Afis. 4:26) Ku kasance a shirye ku taimaka ma junanku. (Tit. 3:14) Taimakon da ꞌyanꞌuwa suka yi ma ꞌyarꞌuwar da ke da bukata ya sa rukunin waꞌazinsu ya amfana. Sun kasance da haɗin kai sosai kamar iyali ɗaya.—Zab. 133:1.
16. Bisa ga Kolosiyawa 4:3, 18, ta yaya za mu iya taimaka ma ꞌyanꞌuwanmu da ake tsananta musu?
16 Dubban ꞌyanꞌuwanmu suna bauta ma Jehobah duk da cewa gwamnati ta hana wasu sassan ayyukanmu. An saka wasunsu a kurkuku domin imaninsu. Za mu iya yin adduꞌa domin su da kuma iyalinsu, mu kuma yi adduꞌa a madadin waɗanda suke nuna ƙarfin zuciya ta wajen taimaka ma ꞌyanꞌuwa maza da mata da ke kurkuku duk da cewa su ma za a iya kama su. ’Yan’uwan nan suna ƙarfafa ꞌyanꞌuwansu su ci gaba da bauta ma Jehobah, suna tanada musu abubuwan da suke bukata kuma suna kāre su a kotuna. c (Karanta Kolosiyawa 4:3, 18.) Kada ku manta cewa adduꞌoꞌinku za su iya taimaka ma ꞌyanꞌuwa maza da matan nan!—2 Tas. 3:1, 2; 1 Tim. 2:1, 2.
17. Ta yaya za ku yi shiri tun yanzu domin tsanantawa?
17 Kai da iyalinka za ku iya yin shiri tun yanzu don tsanantawa da za ku iya fuskanta. (A. M. 14:22) Kada ka zauna kana tunanin abubuwa marasa kyau da za su iya faruwa da ku. A maimakon haka, ka kyautata dangantakarka da Jehobah kuma ka taimaka ma yaranka su ma su yi hakan. Idan a wasu lokuta kakan damu, ka gaya ma Jehobah yadda kake ji. (Zab. 62:7, 8) Ku tattauna a iyalinku dalilai da suka sa ya kamata ku dogara ga Jehobah. d Kamar yadda yin shiri kafin balaꞌi ya auku zai taimake yaranku, haka ma idan kuka yi shiri domin tsanantawa zai taimake yaranku su kasance da ƙarfin zuciya da kuma kwanciyar hankali domin kun koyar da su su dogara ga Jehobah.
18. Wane abu ne za mu mora a nan gaba?
18 Salamar Allah tana kāre mu. (Filib. 4:6, 7) Ta wurin salamar, Jehobah yana ba mu kwanciyar hankali duk da annoba da balaꞌoꞌi da kuma tsanantawa da za su iya shafanmu a yau. Yana amfani da dattawa da suke aiki tuƙuru domin ya ƙarfafa mu. Kuma yana ba ma dukanmu gatan taimaka ma juna. Salamar da muke da ita a yanzu za ta iya taimaka mana mu iya jimre matsaloli masu wuya da za mu iya fuskanta a gaba, har ma da ƙunci mai girma ko “azaba mai zafi.” (Mat. 24:21) A lokacin ƙunci mai girma, za mu bukaci mu ci gaba da kasancewa da kwanciyar hankali kuma mu taimaka ma wasu ma su yi hakan. Amma bayan ƙunci mai girma, ba za mu fuskanci yanayi da zai sa mu damu kuma ba. Za mu mori abin da Jehobah yake so mu mora, wato cikakkiyar salama da za ta kasance har abada.—Isha. 26:3, 4.
WAƘA TA 109 Mu Kasance da Ƙauna ta Gaske
a Jehobah yakan yi amfani da bayinsa masu aminci ya taimaka ma waɗanda suke fama da matsaloli. Zai iya amfani da kai wajen ƙarfafa ꞌyanꞌuwa maza da mata. Bari mu ga yadda za mu iya taimaka wa ꞌyanꞌuwanmu saꞌad da suke fuskantar matsaloli.
b An canja wasu sunayen.
c Ba zai yiwu reshen ofishinmu ko hedkwatarmu ya aika wasiƙun da ꞌyanꞌuwa suka rubuta zuwa ga ꞌyanꞌuwa da ke kurkuku ba.
d Ka duba talifin nan “Ku Yi Shiri Yanzu Don Tsanantawa” a Hasumiyar Tsaro ta Yuli, 2019.
e BAYANI A KAN HOTUNA: Wasu maꞌaurata sun kawo ma wata iyali da balaꞌi ya auko musu kuma suke zama a tanti abinci.