Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Tuna?

Ka Tuna?

Ka karanta dukan fitowar Hasumiyar Tsaro na shekarar nan da kyau? Ka ga ko za ka iya amsa tambayoyi na gaba:

Ta yaya za mu amfana idan muka ɗauki lokaci muka yi addu’a ga Jehobah, muka saurare shi, kuma muka yi tunani a kansa?

Za mu iya yanke shawarwari masu kyau, za mu daɗa ƙwarewa a yadda muke wa’azi, bangaskiyarmu za ta daɗa ƙarfi, kuma za mu daɗa ƙaunar Jehobah.​—w22.01, shafuffuka na 30-31.

Ta yaya za mu amfana idan muka yarda da Jehobah da kuma waɗanda ya naɗa su yi mana ja-goranci?

Yanzu ne ya kamata mu soma yarda da yadda Jehobah yake yin abubuwa ta wajen bin umurnin dattawa ba tare da yin shakka ba. Idan aka soma ƙunci mai girma, za mu iya bin umurnai da aka ba mu ko da suna da wuya.​—w22.02, shafuffuka na 4-6.

Mene ne malaꞌikan yake nufi saꞌad da ya gaya wa Zakariya game da “igiyar awon kammalawar ginin a hannun Zerubbabel”? (Zak. 4:​8-10)

Wannan wahayin ya tabbatar wa bayin Allah cewa za a kammala gina haikalin kuma zai kasance daidai yadda Jehobah yake so.​—w22.03, shafuffuka 16-17.

Ta yaya za mu zama “abin koyi . . . cikin magana”? (1 Tim. 4:12)

Muna yi wa mutane magana da alheri sa’ad da muke waꞌazi, muna rera waƙa da dukan zuciyarmu kuma muna yin kalamai a taro. Ƙari ga haka, za mu riƙa faɗin gaskiya, mu ƙarfafa mutane kuma mu guji yin zage-zage.​—w22.04, shafuffuka na 6-9.

Me ya sa dabbar (gwamnatoci) da aka ambata a Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 13:​1, 2, take da kamannin dabbobi huɗu da aka ambata a Daniyel sura 7?

Domin dabbar ba ta wakiltar gwamnati ɗaya kawai, kamar gwamnatin Roma. Dabbar tana wakiltar dukan gwamnatocin da suke yin iko bisa ’yan Adam.​—w22.05, shafi na 9.

Ta yaya za mu nuna cewa mun amince da yadda Jehobah yake yin adalci?

Idan wani ya zage mu, ko ya yi mana laifi, za mu yi ƙoƙari kada mu yi fushi ko mu riƙe mutumin a zuciya. A maimakon haka, mu bar kome a hannun Jehobah. Zai kawar da duk wata matsala da zunubi ya jawo.​—w22.06, shafuffuka na 10-11.

Me ya kamata ɗan’uwa da aka ce ya yi adduꞌa a madadin ꞌyanꞌuwa a taro ya tuna?

Bai kamata ya yi amfani da addu’ar ya gargaɗi ’yan’uwa ko ya yi sanarwa ba, musamman idan za a soma taro. Bai kamata ya yi “dogon surutu” ba. (Mat. 6:7)​—w22.07, shafuffuka na 24-25.

Me ake nufi da cewa za a tā da “waɗanda suka yi rashin gaskiya” a kuwa yi musu hukunci ko shariꞌa? (Yoh. 5:29)

Ba za a yi musu shari’a bisa ga ayyukan da suka yi kafin su mutu ba. Shari’a ko hukuncin da za a yi musu zai dangana ne ga halayensu ko abubuwan da suka yi bayan tashinsu daga mutuwa.​—w22.09, shafi na 18.

Wane umurni mai ban sha’awa ne J. F. Rutherford ya bayar a wani babban taro a Satumba 1922?

A wani babban taro a Cedar Point, Ohio, a Amirka, ya ce: “Sarkin yana sarauta! Hakkinku ne ku gaya wa mutane game da hakan. Don haka, ku yi shela, ku yi shela, ku yi shelar Sarkin da kuma Mulkinsa!”​—w22.10, shafuffuka na 3-5.

A waɗanne hanyoyi uku ne Ishaya sura 30 ta nuna cewa Allah yana taimaka mana mu jimre?

Surar ta nuna mana cewa (1) yana saurara da kuma amsa addu’o’inmu, (2) yana yi mana ja-goranci, (3) yana yi mana albarka yanzu kuma zai yi hakan a nan gaba.​—w22.11, shafi na 9.

Me ya sa za mu iya cewa abin da aka rubuta a Zabura 37:​10, 11, 29 ya cika a dā kuma zai sake cika a nan gaba?

Kalmomin Dauda sun bayyana albarkun da Isra’ilawa suka mora, kamar yadda ya kasance a zamanin Sulemanu. Yesu ya yi magana game da Aljanna da za ta wanzu a nan gaba kuma ya yi ƙaulin aya ta 11. (Mat. 5:5; Luk. 23:43)​—w22.12, shafuffuka na 8-10, 14.