Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Kana a Shirye Ka “Gāji Duniya”?

Kana a Shirye Ka “Gāji Duniya”?

DUKANMU muna sa ran ganin cikar alkawarin da Yesu ya yi cewa: “Masu albarka ne masu tawaliꞌu, gama za su gāji duniya.” (Mat. 5:5) Shafaffun Kiristoci za su gāji duniya a lokacin da suka zama sarakuna kuma suna mulki tare da Yesu a sama. (R. Yar. 5:10; 20:6) Yawancin Kiristoci na gaskiya a yau suna sa ran gādan duniya da kuma zama a cikinta har abada a cikin salama da farin ciki kuma za su zama kamiltattu. Akwai ayyuka masu muhimmanci da za a bukace su su yi kafin hakan ya faru. Alal misali, za su taimaka wajen mai da duniya ta zama aljanna, kuma za su tabbata cewa sun tanada wa matattu da aka tā da su kuma sun koyar da su. Ka yi tunanin abin da muke bukatar mu yi yanzu don mu nuna cewa muna so mu yi abubuwan nan a sabuwar duniya.

KANA A SHIRYE KA MAI DA DUNIYA TA ZAMA ALJANNA?

A lokacin da Allah ya ba ꞌyan Adam umurni cewa ‘su ciccika duniya su kuma sha ƙarfinta,’ hakan ya nuna cewa a kwana a tashi duniya gabaki ɗaya za ta zama aljanna. (Far. 1:28) Waɗanda za su gāji duniya har abada ma suna bukatar su bi wannan doka. Duniya ba za ta zama aljanna nan take bayan an hallaka tsarin Shaiɗan ba, domin lambun Adnin ya riga ya daina wanzuwa. Nan da nan bayan Armageddon, za mu yi aiki sosai wajen tsabtace wuraren da aka gurɓatar da su a duniya. Hakan ba zai zama ƙaramin aiki ba!

Wannan ya tuna mana da irin aikin da Israꞌilawa suka yi bayan da suka dawo daga bauta a Babila. Ƙasar ta yi shekaru 70 ba wanda yake zama a ciki. Amma Ishaya ya annabta cewa da taimakon Jehobah za su iya kyautata ƙasar kuma. Annabcin ya ce: “Yahweh zai sa ta zama kamar Gonar Eden, dajinta kuma kamar gonar Yahweh.” (Isha. 51:3) Jehobah ya taimaka wa Israꞌilawan su yi nasara. Haka ma, da taimakon Jehobah, waɗanda suka gāji duniya za su iya mai da ita ta zama aljanna. Akwai abubuwa da za ka iya yi yanzu don ka nuna cewa kana so ka yi wannan aikin da za a yi a nan gaba.

Ɗaya daga cikin abubuwan da ya kamata ka yi shi ne tsabtace muhallinka da kuma adana kayanka da kyau. Za ka iya yin hakan ko da maƙwabtanka ba sa tsabtace gidajensu. Ƙari ga haka, za ka iya taimakawa wajen tsabtace da kuma adana Majamiꞌar Mulkin da kuke amfani da shi da kuma Majamiꞌar Babban Taro. Idan da hali, za ka iya ba da kanka don ka taimaka a lokacin ba da agaji. Ta hakan, za ka nuna cewa kana a shirye ka taimaka ma ꞌyanꞌuwa idan da bukata. Ka tambayi kanka, ‘Shin zan iya koyan sanaꞌar hannu da zan yi amfani da ita a Sabuwar Duniya idan Allah ya bar ni in shiga?’

KA SHIRYA DON KA TAIMAKI WAƊANDA ZA A TĀ DA SU DAGA MUTUWA

Nan da nan bayan da Yesu ya tayar da ꞌyar Yayirus daga mutuwa, ya ce a ba ta abinci. (Mar. 5:​42, 43) Hakika ciyar da ꞌyar shekara 12 ba wani aiki ba ne. Amma ka yi tunanin irin babban aikin da za a bukace mu mu yi bayan da Yesu ya cika alkawarinsa cewa: “Duk waɗanda suke cikin kaburbura za su ji muryarsa, su fito.” (Yoh. 5:​28, 29) Ko da yake Littafi Mai Tsarki bai gaya mana kome da kome game da abin da zai faru a lokacin ba, za mu iya cewa waɗanda aka tā da su daga mutuwa za su bukaci a taimaka musu su sami abinci da sutura da kuma wurin kwana. Shin za ka iya nuna tun yanzu cewa kana a shirye ka taimaka? Ga wasu abubuwa da za ka iya yi don ka nuna cewa kana a shirye.

Me za ka yi a yau don ka nuna cewa kana a shirye ka gāji duniya?

Idan aka yi sanarwa cewa mai kula da daꞌira zai ziyarci ikilisiyarku, ka ƙoƙarta ka gayyace shi ya zo ya ci abinci tare da ku. Idan aka ce waɗanda suke hidima a Bethel su daina yin hakan kuma su koma gida ko kuma mai kula da daꞌira ya daina hidimar da yake yi, za ka iya taimaka wajen samar musu gida. Idan za a yi taron yanki ko babban taro na musamman a yankinku, za ka iya ba da kai ka taimaka da aikin da za a yi kafin taron ko bayan taron ko kuma ka kasance a wurin don ka marabci waɗanda za su halarci taron.

KA KASANCE A SHIRYE KA KOYAR DA WAƊANDA ZA A TA DA SU DAGA MUTUWA

Bisa ga abin da Ayyukan Manzanni 24:15 ta faɗa, muna sa rai cewa za a ta da biliyoyin mutane daga mutuwa. Da yawa daga cikinsu za su zama waɗanda ba su taɓa jin maganar Allah ba. Za a ba su damar koya game da Jehobah bayan an tā da su. a Kwararrun amintattun bayin Allah za su koyar da su. (Isha. 11:9) Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Charlotte da ta yi waꞌazi a Turai da kuma Kudancin Amirka tana sa ran yin hakan. Da farin ciki ta ce: “Ina ɗokin koyar da mutanen da za a tā da su daga mutuwa. A duk lokacin da na karanta labarin wani da ya yi rayuwa a dā, nakan yi tunani cewa: ‘Da a ce wannan mutum ya san Jehobah da ba haka rayuwarsa ta kasance ba.’ Ina ɗokin koyar da waɗanda za a tā da su daga mutuwa, da kuma nuna musu yadda za su ji daɗin rayuwa idan suka bauta ma Jehobah.”

Ko bayin Jehobah masu aminci da suka rayu kafin a haifi Yesu a duniya ma za su bukaci a koyar da su. Ka yi tunanin yadda za mu yi farin cikin bayyana ma Daniyel maꞌanar annabcin da ya rubuta domin bai fahimci abin da ya rubuta ba. (Dan. 12:8) Ko kuma ka yi tunanin yadda za ka ji daɗin taimaka ma Rut da Naꞌomi su san yadda aka yi Almasihu ya fito daga zuriyarsu. Za mu ji daɗin koyar da mutane a faɗin duniya kuma za mu yi hakan ba tare da matsi da kuma abubuwa masu ɗaga hankali irin na muguwar duniya da muke ciki a yau ba!

Me za ka iya yi yanzu don ka kasance a shirye ka koyar da waɗanda za a tā da su daga mutuwa? Wani abu da za ka iya yi shi ne ka kyautata yadda kake koyarwa da kuma yin wa’azi a kai a kai a yau. (Mat. 24:14) Ko da yake ba ka iya yin wa’azi yanzu kamar yadda ka saba yi domin tsufa ko wasu dalilai dabam, za ka iya yin iyakacin ƙoƙarinka a yin wa’azi yanzu. Ta hakan za ka nuna cewa kana a shirye ka koyar da waɗanda za a ta da su daga mutuwa.

Yana da kyau ka yi tunanin muhimman tambayoyin da ke gaba. Tambayoyin su ne: Kana marmarin ka zama ɗaya daga cikin waɗanda za su gāji duniya? Kana ɗokin taimakawa wajen mai da duniya ta zama aljanna da kula da kuma koyar da waɗanda aka tā da su daga mutuwa? Za ka iya nuna cewa kana a shirye ka yi hakan ta wajen yin irin ayyukan da za ka yi idan ka gāji duniya!

a Ka duba talifin nan ‘Sa Mutane Su Juya Zuwa Rayuwar Adalci’ a Hasumiyar Tsaro ta Satumba, 2022.