Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 51

Za Ka Iya Samun Kwanciyar Hankali a Kwanakin Masifa

Za Ka Iya Samun Kwanciyar Hankali a Kwanakin Masifa

“Kada ku damu, kada kuma ku ji tsoro.”​—YOH. 14:27.

WAƘA TA 112 Jehobah Allah Ne Na Salama

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1. Me ake nufi da salamar Allah, kuma ta yaya take amfanar mu? (Filibiyawa 4:​6, 7)

 AKWAI irin salama da mutanen duniya ba su san da ita ba. Hakan yana nufin irin kwanciyar hankali da mutum yake samu domin yana da dangantaka mai kyau da Ubanmu na sama. Idan muna da salamar Allah ba za mu ji tsoro ba. (Karanta Filibiyawa 4:​6, 7.) Muna da dangantaka mai kyau da Allah na salama, da kuma waɗanda suke ƙaunar sa. (1 Tas. 5:23) Idan mun san Allah, muna masa biyayya kuma mun dogara gare shi, salamar Allah za ta iya kwantar mana da hankali a lokacin da muke cikin matsala.

2. Me ya sa muka tabbata cewa zai yiwu mu samu salamar Allah?

2 Shin zai yiwu mu kasance da salamar Allah idan muna fuskantar matsaloli kamar annoba, da balaꞌi da tashe-tashen hankula ko kuma tsanantawa? Kowanne daga cikin matsalolin nan zai iya tsoratar da mu. Duk da haka, Yesu ya umurci mabiyansa cewa: “Kada ku damu, kada kuma ku ji tsoro.” (Yoh. 14:27) Abin farin ciki shi ne ꞌyanꞌuwa maza da mata suna bin wannan shawarar da Yesu ya bayar. Da taimakon Jehobah, sun sami kwanciyar hankali duk da cewa suna fuskantar matsaloli.

YADDA ZA KA SAMI KWANCIYAR HANKALI A LOKACIN ANNOBA

3. A wace hanya ce annoba za ta iya tayar mana da hankali?

3 Annoba za ta iya canja yanayin rayuwa gabaki ɗaya. Ka yi tunanin yadda annobar korona ta shafi mutane da yawa. A wani binciken da aka yi, fiye da rabin mutanen da aka tambaya sun ce ya yi musu wuya su yi barci a lokacin annobar. Annobar ta sa an sami ƙarin adadin mutanen da suka yi fama da matsananciyar damuwa, da tsananin baƙin ciki, da shan giya fiye da kima, da shan ƙwayoyi da zaluntar iyalinsu ko kuma yunƙurin kashe kansu. Idan wata annoba ta ɓarke a inda kake zama, me za ka iya yi don ka rage yawan damuwar da kake yi kuma ka sami salamar Allah?

4. Me ya sa sanin annabcin da Yesu ya yi game da kwanakin ƙarshe yana ba mu kwanciyar hankali?

4 Yesu ya yi annabci cewa a kwanakin ƙarshe za a yi cututtuka dabam-dabam da annoba a “wurare dabam-dabam.” (Luk. 21:11) Ta yaya sanin hakan yana ba mu kwanciyar hankali? Hakan yana sa ba ma mamaki idan annoba ta ɓarke. Mun gane cewa abin da Yesu Kristi ya faɗa ne yake cika. Saboda haka, yana da kyau mu bi shawarar da Yesu ya ba waɗanda za su yi rayuwa a kwanakin ƙarshe, cewa: “Kada ku ji tsoro.”​—Mat. 24:6.

Sauraron karatun Littafi Mai Tsarki da aka ɗauka a sauti zai iya taimaka maka ka sami kwanciyar hankali a lokacin annoba (Ka duba sakin layi na 5)

5. (a) Bisa ga abin da ke Filibiyawa 4:​8, 9, me ya kamata mu yi adduꞌa a kai a lokacin annoba? (b) Ta yaya sauraron sautin karatun Littafi Mai Tsarki ya amfani wata ꞌyarꞌuwa kuma me za ka iya koya daga misalinta?

5 Annoba za ta iya sa mu damu sosai har ma mu ji tsoro. Abin da ya faru da wata ꞌyarꞌuwa mai suna Desi ke nan. b Bayan da kawunta da ɗan kawunta da kuma likitanta duk sun mutu sanadiyyar cutar korona, ta soma jin tsoro cewa ita ma za ta kamu da annobar kuma ta haye wa mamarta da ta tsufa. Ƙari ga haka, ta ji tsoro cewa za ta rasa aikinta, kuma ta soma damuwa a kan yadda za ta ciyar da kanta, kuma ta biya kuɗin haya. Tunanin batutuwan nan yakan hana ta barci da dare. Amma a hankali Desi ta sake samun kwanciyar hankali. Me ya taimaka mata? Ta yi adduꞌa ga Jehobah kuma ta gaya masa musamman cewa ya taimaka mata ta samu kwanciyar hankali kuma ta yi tunani da kyau. (Karanta Filibiyawa 4:​8, 9.) Takan saurari Jehobah ta wajen saurarar sauti na karatun Littafi Mai Tsarki. Ta ce: “Irin muryar da masu karatun suka yi amfani da ita tana ba ni kwanciyar hankali kuma ta tuna min cewa Jehobah ya damu da ni.”​—Zab. 94:19.

6. Ta yaya nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma zuwa taro za su taimake ka?

6 Ɓarkewar annoba zai iya sa ya yi mana wuya mu yi dukan abubuwan da muka saba yi, amma kada mu bar hakan ya hana mu yin nazarin Littafi Mai Tsarki ko kuma zuwa taro. Labaran ꞌyanꞌuwanmu da ke littattafanmu da kuma bidiyoyi za su tuna mana cewa ꞌyanꞌuwanmu suna riƙe amincinsu ga Jehobah duk da cewa suna fuskantar matsaloli kamar namu. (1 Bit. 5:9) Zuwa taro zai taimaka maka ka riƙa tunanin abubuwa daga Littafi Mai Tsarki da za su ƙarfafa ka. Ƙari ga haka, za su ba ka damar ƙarfafa wasu da kuma samun ƙarfafa. (Rom. 1:​11, 12) Idan kana tunanin yadda Jehobah ya taimaka ma bayinsa a lokacin da suke rashin lafiya, ko suka ji tsoro ko suka kaɗaita, za ka ƙarfafa bangaskiyarka kuma za ka kasance da tabbaci cewa kai ma zai taimake ka.

7. Wane darasi ne za ka iya koya daga manzo Yohanna?

7 Ka yi ƙoƙari ka riƙa sadawa da ꞌyanꞌuwanka. Ɓarkewar annoba za ta iya bukace mu mu ba mutane tazara, ko da ꞌyanꞌuwanmu ne. Idan kana yanayin, za ka iya ji kamar yadda manzo Yohanna ya ji. Ya so ya gan abokinsa Gayus ido da ido. (3 Yoh. 13, 14) Amma Yohanna ya gane cewa hakan ba zai iya faruwa nan da nan ba. Don haka, Yohanna ya yi abin da zai iya yi, wato ya rubuta wa Gayus wasiƙa. Idan ba za ka iya zuwa wurin ꞌyanꞌuwanka ba, ka yi ƙoƙari ka yi magana da su ta wayar tarho, ko ka kira su ta bidiyo ko kuma ta wasu hanyoyin sadarwa. Idan kana sadawa da ꞌyanꞌuwanka masu bi a kai a kai, hakan zai iya sa ba za ka kaɗaita ba kuma za ka samu kwanciyar hankali. Ka yi magana da dattawa idan kana jin tsoro, kuma ka bi shawarar da suka ba ka yayin da suke ƙarfafa ka.​—Isha. 32:​1, 2.

YADDA ZA KA SAMI KWANCIYAR HANKALI A LOKACIN BALAꞌI

8. A wace hanya ce balaꞌi zai iya tayar maka da hankali?

8 Idan ambaliyar ruwa ko girgizar ƙasa ko gobara ta taɓa aukuwa a inda kake, hakan zai iya sa ka damuwa na dogon lokaci. Idan wani da kake ƙauna ya mutu sanadiyyar balaꞌi, ko kuma ka yi asarar kayanka, za ka iya baƙin ciki, ka ji kamar naka ya ƙare, ko kuma ka yi fushi. Hakan ba ya nufin cewa kana son abin duniya ne ko kuma ka rasa bangaskiyar ka. Ka fuskanci yanayi mai wuya ne, kuma mun san cewa yanayin zai iya sa ka baƙin ciki. (Ayu. 1:11) Amma duk da irin matsalolin nan, za ka iya samun kwanciyar hankali. Me zai taimaka maka?

9. Mene ne Yesu ya faɗa don ya shirya zukatanmu don balaꞌoꞌi da za su iya aukuwa?

9 Ka tuna annabcin da Yesu ya yi. Wasu mutane suna ganin cewa balaꞌi ba zai taɓa shafan su ba, amma mun san cewa a kwana a tashi balaꞌoꞌi za su ƙaru kuma wasunsu za su iya shafan mu. Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa “mummunar rawar ƙasa” ko girgizar ƙasa da kuma wasu balaꞌoꞌi za su auku kafin ƙarshe ya zo. (Luk. 21:11) Ƙari ga haka, ya yi annabci cewa mugunta za ta yi yawa kuma muna ganin hakan ta yadda mutane suke aikata laifi, suke aikata taꞌaddanci kuma suke cin zalin mutane. (Mat. 24:12) Matsaloli da balaꞌoꞌi sun riga sun faɗo wa bayin Allah masu aminci da yawa. Yesu bai ce idan muka fuskanci yanayoyin nan hakan yana nufin cewa Jehobah bai damu da mu ba. (Isha. 57:1; 2 Kor. 11:25) Ba kowane lokaci ba ne Jehobah zai kāre mu ta hanyar muꞌujiza idan balaꞌi ya auku, amma zai ba mu abubuwan da muke bukata don mu sami kwanciyar hankali.

10. Me ya sa kasancewa a shirye don aukuwar balaꞌi zai nuna cewa mu masu bangaskiya ne? (Karin Magana 22:3)

10 Idan muna a shirye, ba za mu rasa na yi idan balaꞌi ya auku ba. Amma yin shiri yana nuna cewa ba mu da bangaskiya ne? Ba haka ba ne sam. Akasin haka, yin shiri domin aukuwar balaꞌi zai nuna cewa mun ba da gaskiya cewa Jehobah zai iya kula da mu. Kalmar Allah ta umurce mu mu shirya kanmu domin balaꞌoꞌi da za su iya aukuwa. (Karanta Karin Magana 22:3.) Kuma ta mujallunmu da taron ikilisiya da kuma sanarwa, ƙungiyar Jehobah ta daɗe tana ƙarfafa mu mu shirya kanmu don balaꞌi da zai iya aukuwa. c Shin mun yarda da abin da Jehobah ya faɗa? Idan haka ne, za mu bi wannan shawarar yanzu tun kafin balaꞌi ya auku.

Yin shiri tun kafin balaꞌi ya auku zai iya cece ka a lokacin balaꞌi (Ka duba sakin layi na 11) d

11. Me ka koya daga labarin Margaret?

11 Ka yi laꞌakari da misalin wata ꞌyarꞌuwa mai suna Margaret. Hukumomin gwamnati sun umurce ta ta bar gidanta bayan da gobarar daji ta ɓarke a inda suke. Da yake mutane da yawa suna ƙoƙarin ficewa daga yankin a lokaci ɗaya, motoci sun yi cunkoso a hanya kuma babu wanda ya iya tafiya. Hayaƙi ya sa koꞌina ya yi baƙi ƙirin, kuma Margaret ta kasa fita daga cikin mota na dan lokaci. Amma ta tsira domin ta yi shiri. A cikin jakarta, tana ɗauke da taswira da ya taimaka mata ta san wata hanya dabam da za ta iya bi don ta fice daga yankin. Ta ma taɓa bin hanyar don ta san yadda yake tun kafin balaꞌin ya auku. Shirin da Margaret ta yi ya ceci ranta.

12. Me ya sa ya kamata mu bi umurnan da aka bayar don a kāre mu?

12 A wasu lokuta, hukumomi za su iya ba da dokar hana fita, ko su ce mu bar gidajenmu ko kuma mu bi wasu umurnai da suka bayar don su kāre mu kuma su mayar da doka. Wasu mutane za su iya jinkirin bin waɗannan dokoki ko kuma su ƙi bi, domin ba sa so su rasa abubuwan da suka mallaka. Me ya kamata Kiristoci su yi a wannan yanayin? Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa: “Domin a girmama Ubangiji, ku yi biyayya ga kowace hukuma wadda take da iko a kan mutane. Ku yi wa babban sarki biyayya, gama yana mulki bisa kowa. Ku kuma yi wa gwamnoni biyayya, da yake sarki ne ya zaɓe su.” (1 Bit. 2:​13, 14) Ƙungiyar Jehobah ma takan ba da umurni don ta kāre mu. Ana yawan tuna mana cewa mu ba dattawa adireshinmu da kuma lambobin wayarmu domin su iya su kira mu a lokacin balaꞌi. Ka riga ka yi hakan? Ƙungiyarmu za ta kuma iya ba da umurni cewa mu zauna a gida ko mu bar gidajenmu, ko su ba mu umurni a kan yadda za mu iya samun kayan agaji, ko yadda za mu taimaka ma wasu da kuma lokacin da ya kamata mu yi hakan. Idan mun ƙi bin waɗannan umurnan, za mu iya sa rayukanmu da kuma na dattawa a cikin haɗari. Ka tuna cewa waɗannan amintattun mutanen suna lura da mu ne. (Ibran. 13:17) Margaret ta ce: “Na yarda da dukan zuciyata cewa bin umurnan da dattawa suka bayar ne ya ceci raina.”

13. Me ya taimaka wa Kiristoci da yawa da suka yi gudun hijira su ci gaba da samun farin ciki da kuma kwanciyar hankali?

13 ꞌYanꞌuwa da yawa da suka zama ꞌyan gudun hijira saboda balaꞌi, ko yaƙi, ko tashe-tashen hankula sun yi iya ƙoƙarinsu don su saba da yanayinsu kuma su ƙara ƙwazo a hidimarsu ga Jehobah. Kamar yadda Kiristocin ƙarni na farko suka yi saꞌad da tsanantawa ya sa suka warwatse, su ma “suna yin shelar labarin nan mai daɗi.” (A. M. 8:4) Yin waꞌazi yana taimaka masu su mai da hankali a kan Mulkin Allah maimakon a kan yanayinsu mai wuya. Hakan ya sa sun ci gaba da kasancewa da farin ciki da kuma kwanciyar hankali.

YADDA ZA KA SAMU KWANCIYAR HANKALI A LOKACIN TSANANTAWA

14. A wace hanya ce tsanantawa za ta iya hana mu samun kwanciyar hankali?

14 Idan aka soma tsananta mana, za mu iya rasa abubuwa da yawa da suke taimaka mana mu samu kwanciyar hankali. Muna farin ciki saꞌad da muka halarci taro da kuma yi waꞌazi tare da ꞌyanꞌuwanmu a sake. Muna yin abubuwan da muka saba yi ba tare da jin tsoro cewa za a kama mu ba. Idan aka hana mu yin abubuwan nan za mu iya soma damuwa kuma mu ji tsoron abin da zai faru a nan gaba. Jin hakan ba laifi ba ne. Duk da haka, ya kamata mu yi hattara. Yesu ya ce tsanantawa za su iya sa wasu mabiyansa su ja da baya daga bin sa. (Yoh. 16:​1, 2) Don haka, mai zai taimaka mana mu ci gaba da samun kwanciyar hankali idan ana tsananta mana?

15. Me ya sa bai kamata mu ji tsoron tsanantawa ba? (Yohanna 15:20; 16:33)

15 Kalmar Allah ta gaya mana cewa: “Duk wanda yake so ya yi rayuwa irin hali na Allah a cikin Almasihu Yesu zai sha tsanani.” (2 Tim. 3:12) Ya yi ma wani ɗanꞌuwa mai suna Andrei wuya ya amince cewa dukan bayin Allah za su sha tsanantawa bayan da aka hana aikin shaidun Jehobah a ƙasarsu. A zuciyarsa ya yi tunani cewa: ‘Ai akwai shaidu da yawa a nan. Yaya hukumomi za su kama dukanmu?’ Amma maimakon irin wannan tunanin ya kawo wa Andrei kwanciyar hankali, hakan ya sa shi damuwa. Wasu ꞌyanꞌuwa sun dogara ga Jehobah kuma ba su yi tunani cewa ba za a iya kama su ba. Sun san cewa za a iya kama su, amma ba su damu kamar yadda Andrei ya damu ba. Don haka Andrei ya yanke shawarar bin raꞌayinsu kuma ya dogara ga Jehobah da dukan zuciyarsa. Ba da daɗewa ba bayan hakan, ya soma farin ciki duk da cewa matsalar ba ta kare ba. Mu ma hakan zai iya faruwa da mu. Gaskiya ne cewa Yesu ya ce za a tsananta mana. Amma ya tabbatar mana cewa zai yiwu mu riƙe amincinmu.​—Karanta Yohanna 15:20; 16:33.

16. Wane umurni ne ya kamata mu bi idan ana tsananta mana?

16 Idan aka hana aikinmu ko kuma an dakatar da wasu sassan aikin, reshen ofishinmu da kuma dattawa za su iya ba mu umurni game da hakan. Suna ba mu umurnan don su kāre mu ne, su tabbata cewa za mu ci gaba da samun abubuwan da za su ƙarfafa dangantakarmu da Allah, kuma za mu ci gaba da yin waꞌazi iyakacin ƙoƙarinmu. Ka yi ƙoƙari ka bi umurnin da aka bayar ko da ba ka fahimci dalilin da ya sa aka ba da umurnin ba. (Yak. 3:17) Ƙari ga haka, kada ka ba da bayanai game da ꞌyanꞌuwanmu ko ayyukan ikilisiya ga waɗanda ba su cancanci su sami bayanan ba.​—M. Wa. 3:7.

Me zai taimake ka ka samu kwanciyar hankali, ko da kana fuskantar yanayi mai wuya? (Ka duba sakin layi na 17) e

17. Kamar yadda manzanni suka yi a ƙarni na farko, mene ne mu ma mun ƙudiri niyyar yi?

17 Ɗaya daga cikin muhimman dalilan da suka sa Shaiɗan yana yaƙi da bayin Allah shi ne domin “suna . . . riƙe da shaidar Yesu.” (R. Yar. 12:17) Kada ka bar Shaiɗan da duniyarsa su sa ka ji tsoro. Yin waꞌazi da kuma koyar da mutane duk da cewa ana hamayya da mu zai sa mu farin ciki kuma ya ba mu kwanciyar hankali. A ƙarni na farko, saꞌad da hukumomin Yahudawa suka umurci manzannin Yesu su daina yin waꞌazi, amintattun mutanen nan sun zaɓi su yi biyayya ga Allah. Sun ci gaba da yin waꞌazi kuma hakan ya sa su farin ciki. (A. M. 5:​27-29, 41, 42) Hakika, idan aka hana mu yin aikinmu a sake, dole ne mu nuna basira idan muna yin waꞌazi. (Mat. 10:16) Amma idan muka yi iyakacin ƙoƙarinmu mu ci gaba da yin waꞌazi, za mu sami kwanciyar hankali domin mun san cewa muna faranta ran Jehobah kuma muna yaɗa saƙon da zai ceci rayukan mutane.

“ALLAH MAI SALAMA . . . ZAI KASANCE TARE DA KU”

18. Me ya kamata mu tuna game da wanda zai iya ba mu salama ta ƙwarai?

18 Ka tabbata cewa ko da kana cikin yanayi mai wuya, za ka iya samun kwanciyar hankali ko kuma salama. A lokuta kamar haka, dole ne mu tuna cewa irin salamar da muke bukata ita ce wadda take fitowa daga wurin Allah, wato salama da Jehobah ne kaɗai zai iya bayarwa. Ka dogara gare shi a lokacin annoba, ko balaꞌi ko kuma tsanantawa. Kada ka wāre kanka daga ƙungiyar Jehobah. Ka yi ɗokin lokacin da alkawuran Allah za su cika. Idan ka yi hakan, ‘Allah mai salama kuwa zai kasance tare da kai.’ (Filib. 4:9) A talifi na gaba, za mu tattauna yadda za mu iya taimaka wa ꞌyanꞌuwanmu Kiristoci da suke fuskantar matsaloli su sami salamar Allah.

WAƘA TA 38 Zai Ƙarfafa Ka

a Jehobah ya yi alkawari cewa zai ba da kwanciyar hankali ko kuma salama ga waɗanda suke ƙaunar sa. Wace irin salama ce Allah yake bayarwa kuma ta yaya za mu iya samun ta? Ta yaya ne salamar Allah za ta taimaka mana idan muna fuskantar annoba, ko balaꞌoꞌi ko kuma tsanantawa? Wannan talifin zai ba da amsar tambayoyin nan.

b An canja wasu sunayen.

c Ka duba talifin nan “When Disaster Strikes​—Steps That Can Save Lives” a Awake! Na 5 2017 a Turanci.

d BAYANI A KAN HOTUNA: Wata ꞌyarꞌuwa ta yi shiri tun da daɗewa kafin balaꞌi ya auku, don ta fice daga gidanta.

e BAYANI A KAN HOTUNA: Wani ɗanꞌuwa da yake zama a inda aka saka wa aikinmu takunkumi ya ci gaba da yin waꞌazi da basira.