Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 50

“Za Ka Kasance Tare da Ni a Aljanna”

“Za Ka Kasance Tare da Ni a Aljanna”

“Ina gaya maka yau, za ka kasance tare da ni a Aljanna.”​—LUK. 23:​43, New World Translation.

WAƘA TA 145 Allah Ya Yi Mana Alkawarin Aljanna

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1. Jim kaɗan kafin Yesu ya mutu, me ya gaya wa ɓarawon da aka rataye a gefen shi? (Luka 23:​39-43)

 YESU KRISTI tare da ɓarayi guda biyu da aka rataye a gefensa suna shan wahala yayin da suke mutuwa a hankali. (Luk. 23:​32, 33) Da yake ɓarayin suna yi wa Yesu ba’a, hakan ya nuna cewa su ba almajiransa ba ne. (Mat. 27:44; Mar. 15:32) Amma ɗaya daga cikin su ya canja ra’ayinsa. Ya ce: “Ya Yesu, ka tuna da ni sa’ad da ka shiga mulkinka!” Yesu ya ce masa: ‘Hakika ina gaya maka yau, za ka kasance tare da ni a Aljanna.’ (Luka 23:​43, NWT) (Karanta Luka 23:​39-42.) Wataƙila ɓarawon ya taɓa jin saƙon nan cewa “Mulkin sama ya yi kusa”, amma bai riga ya zama almajirin Yesu ba. Kuma Yesu bai ce mutumin zai shiga Mulkin sama ba. (Mat. 4:17) Yesu yana magana ne game da Aljanna da za ta kasance a duniya a nan gaba. Me ya sa muka faɗi hakan?

Me za mu iya faɗa game da ɓarawon da ya yi magana da Yesu da kuma abin da ɓarawon ya sani? (Ka duba sakin layi na 2-3)

2. Me ya nuna cewa ɓarawon da ya tuba Bayahude ne?

2 Mai yiwuwa wannan ɓarawon da ya tuba Bayahude ne. Ɓarawon ya gaya wa ɗayan cewa: ‘Ba ka ma tsoron Allah? Kai da ka sami hukunci daidai da shi?’ (Luk. 23:40) Yahudawa sun bauta wa Allah ɗaya ne amma sauran mutanen al’ummai sun gaskata cewa akwai alloli da yawa. (Fit. 20:​2, 3; 1 Kor. 8:​5, 6) Da a ce ɓarayin ba Yahudawa ba ne da tambayar ta zama, “Ba ka jin tsoron alloli ne?” Ƙari ga haka, an aiki Yesu zuwa ga “tumakin Isra’ila waɗanda suka ɓata” ne, ba zuwa wurin mutanen al’ummai ba. (Mat. 15:24) Allah ya riga ya gaya wa Isra’ilawa cewa zai tā da mutane daga mutuwa. Mai yiwuwa ɓarawon ya san da hakan shi ya sa daga abin da ya faɗa, za mu iya cewa ya ɗauka cewa Jehobah zai tā da Yesu don ya yi mulki a sama. Da alama, mutumin ya sa rai cewa Allah zai tā da shi ma.

3. Mene ne wataƙila ɓarawon da ya tuba ya yi tunani a kai a lokacin da Yesu ya yi maganar Aljanna? Ka bayyana. (Farawa 2:15)

3 Idan ɓarawon Bayahude ne, wataƙila ya san game da Adamu da Hauwa’u da kuma Aljanna da Jehobah ya sa su a ciki. Saboda haka, mai yiwuwa ɓarawon ya gano cewa Aljanna da Yesu yake maganarsa za ta zama kyakkyawar lambu ne a nan duniya.​—Karanta Farawa 2:15.

4. Me ya kamata mu yi tunani a kai don abin da Yesu ya faɗa wa ɗaya daga cikin ɓarayin nan?

4 Ya kamata abin da Yesu ya faɗa wa ɓarawon ya sa mu yi tunanin yadda rayuwa za ta kasance a duniya. Hakika za mu iya koyan wasu abubuwa game da Aljanna daga lokacin sarautar Sulemanu da aka sami zaman lafiya sosai. Littafi Mai Tsarki ya ce Yesu ya fi Sulemanu girma. Saboda haka, mun san cewa Yesu zai yi aiki tare da abokan aikinsa don su mai da duniya ta zama Aljanna. (Mat. 12:42) A bayyane yake cewa ya kamata “waɗansu tumaki” su yi tunanin abin da za su yi don su sami damar zama a wannan Aljannar har abada.​—Yoh. 10:16.

YAYA RAYUWA ZA TA KASANCE A CIKIN ALJANNA?

5. Yaya kake ganin rayuwa za ta kasance a cikin Aljanna?

5 Me ke zuwa zuciyarka a duk lokacin da ka yi tunanin yadda rayuwa za ta kasance a duniya? Mai yiwuwa kakan yi tunanin wani lambu mai kyau kamar lambun Adnin. (Far. 2:​7-9) Mai yiwuwa za ka kuma tuna annabcin da annabi Mika ya rubuta cewa mutanen Allah za su zauna ‘a ƙarƙashin itacen inabinsu da na ɓaurensu.’ (Mik. 4:​3, 4) Ƙari ga hakan, za ka iya yin tunanin wasu ayoyi a cikin Littafi Mai Tsarki da suka ce abinci zai zama a yalwace. (Zab. 72:16; Isha. 65:​21, 22) Don haka, za ka iya tunani cewa kana zama a kan teburi cike da abinci mai daɗi. Za ka iya tunanin yadda iska za ta cika da ƙanshi mai daɗi na furanni da shuke-shuke. Kuma wataƙila kana tunanin yadda iyalinka da abokanka da waɗanda aka tā da su daga mutuwa suna tare da juna a cikin annashuwa suna dariya. Ba mafarki kake yi ba. Tabbas mun san cewa abubuwan nan za su faru a duniya. Ƙari ga haka, za mu yi aikin da za mu ji daɗinsa a Aljanna.

Za a ba mu aiki mai muhimmanci na koyar da waɗanda aka tā da su daga mutuwa (Ka duba sakin layi na 6)

6. Me za mu riƙa yi a cikin Aljanna? (Ka duba hoton da ya shafi sakin layi na 6)

6 Jehobah ya halicce mu a hanyar da za mu ji daɗin aiki. (M. Wa. 2:24) Za mu yi aiki tuƙuru a lokacin Sarautar Kristi na Shekara Dubu. Waɗanda za su tsira wa ƙunci mai girma da kuma miliyoyin mutane da za a tā da su daga mutuwa za su bukaci riguna da abinci da kuma wurin kwana. Kafin mu iya tanadar musu da abubuwan nan, wajibi ne mu yi aiki tuƙuru, kuma za mu ji daɗin aikin! Kamar yadda Jehobah ya gaya wa Adamu da Hauwa’u su kula da duniya, haka mu ma za mu ji daɗin kula da duniya. Ka yi tunanin yadda za mu ji daɗin koyar da miliyoyin mutane da aka tā da su daga mutuwa, waɗanda ba su san kome game da Jehobah da kuma nufinsa ba, ko mu taimaka wa masu aminci da suka yi rayuwa kafin Yesu ya zo duniya don su san abubuwan da suka faru bayan mutuwarsu.

7. Wane tabbaci ne za mu iya kasancewa da shi kuma me ya sa?

7 Za mu iya kasancewa da tabbaci cewa idan mun shiga Aljanna, za mu zauna lafiya, mu sami kome da muke bukata, kuma abubuwa za su kasance da tsari. Me ya sa? Domin Jehobah ya riga ya ba mu misalin yadda rayuwa za ta kasance idan Ɗansa ya soma mulki. Misalin shi ne abin da ya faru a lokacin sarautar Sarki Sulemanu.

SARAUTAR SULEMANU SOMA TAƁIN ALJANNA CE

8. A wace hanya ce kalmomin da ke Zabura 37:​10, 11, 29 suka cika bayan da Sarki Dauda ya rubuta su? (Ka duba “Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” a wannan fitowar.)

8 An hure Sarki Dauda ya rubuta yadda rayuwa za ta kasance a lokacin da wani sarki mai hikima mai aminci zai yi sarauta. (Karanta Zabura 37:​10, 11, 29.) Sau da yawa mukan karanta wa mutane Zabura 37:11 yayin da muke magana game da abin da zai faru a nan gaba. Muna da dalili mai kyau na yin hakan domin Yesu ya yi ƙaulin wannan ayar a cikin Huɗubarsa a kan Dutse kuma hakan ya nuna cewa wannan annabcin zai cika a nan gaba. (Mat. 5:5) Amma kalmomin Dauda sun nuna yadda rayuwa za ta kasance a zamanin Sarki Sulemanu. A lokacin da Sulemanu ya yi sarauta a Isra’ila, mutanen Allah sun ji daɗin salama a yalwace a cikin ƙasa “mai zubar da madara da zuma.” Allah ya ce: “Idan kuka yi tafiya bisa ga ƙa’idodina . . .  zan ba ku salama a ƙasar, za ku kwanta babu tsoron kowa.” (L. Fir. 20:24; 26:​3, 6) Waɗannan alkawuran sun cika a lokacin da Sulemanu yake sarauta. (1 Tar. 22:9; 29:​26-28) Kuma Jehobah ya yi alkawari cewa mugayen mutane “za su ɓace.” (Zab. 37:10) Saboda haka, abin da aka rubuta a Zabura 37:​10, 11, 29 ya cika a dā kuma za su sake cika a nan gaba.

9. Mene ne Sarauniya Sheba ta faɗa game da sarautar Sulemanu?

9 Sarauniya Sheba ta ji labarin yadda al’ummar Isra’ila ta samu zaman lafiya da kuma yalwa a ƙarƙashin sarautar Sulemanu. Ta yi tafiya daga ƙasa mai nisa zuwa Urushalima don ta tabbatar da gaskiyar labarin. (1 Sar. 10:1) Bayan da ta gan daular Sulemanu sai ta ce: “Ko rabi ma ba a faɗa mini ba. . . . Lallai mutanenka da masu yi maka hidima sun yi sa’a, saboda ta dalilin aikinsu a nan kullum suna jin hikimarka.” (1 Sar. 10:​6-8) Amma abubuwan da Isra’ilawa suka mora a ƙarƙashin sarautar Sulemanu misali ne kawai na abubuwan da Jehobah zai yi ma ’yan Adam a ƙarƙashin sarautar Yesu.

10. A waɗanne hanyoyi ne Yesu ya fi Sulemanu?

10 Yesu ya fi Sulemanu ta kowace fanni. Sulemanu mutum ne ajizi da ya yi kurakurai masu tsanani kuma hakan ya jawo wa mutanen Allah da ke ƙarƙashin sarautarsa matsaloli. Amma Yesu kamiltaccen sarki ne da ba ya kuskure. (Luk. 1:32; Ibran. 4:​14, 15) Yesu ya riƙe amincinsa ga Jehobah duk da cewa Shaiɗan ya jarraba shi a hanyoyi da dama. Yesu ya riga ya nuna cewa ba zai taɓa yin zunubi ba ko kuma ya yi wani abin da zai jawo lahani ga talakawansa masu aminci. Yesu shi ne sarki mafi kyau da za mu iya samuwa.

11. Su waye ne za su taimake Yesu wajen yin mulki?

11 Yesu zai samu abokan sarauta guda 144,000 waɗanda za su yi aiki tare da shi su kula da ’yan Adam kuma su cika nufin da Jehobah yake da shi wa ’yan Adam. (R. Yar. 14:​1-3) Sun fuskanci jarrabobi da kuma matsaloli da yawa yayin da suke nan duniya, don haka za su fahimci yanayin talakawansu. Amma mene ne waɗannan abokan sarauta za su yi?

MENE NE SHAFAFFU ZA SU YI?

12. Wane aiki ne Jehobah zai ba shafaffu 144,000?

12 Aikin da Jehobah ya ba Yesu da abokan aikinsa ya fi aikin da Jehobah ya ba Sulemanu girma. An ba Sulemanu hakkin kula da miliyoyin mutane a ƙasa guda ɗaya kawai. Amma waɗanda za su yi sarauta a cikin Mulkin Allah za su kula da biliyoyin mutane a duniya gaba ɗaya. Ba ƙaramin gata ba ne Jehobah ya ba wa shafaffu 144,000!

13. Wane hakki na musamman ne abokan sarautar Yesu za su samu?

13 Kamar Yesu, shafaffu ma za su yi sarauta kuma su zama firistoci. (R. Yar. 5:10) A lokacin da Isra’ilawa suke ƙarƙashin Dokar da Allah Ya Bayar ta Hannun Musa, aikin firistoci ne su taimaka musu su samu lafiyar jikinsu kuma su kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah. Koyarwar Musa kuwa “kwatanci ce kawai na abubuwa masu kyau waɗanda suke a gaba.” Don haka, za mu iya cewa abokan sarautar Yesu za su taimaka wajen sa mutanen Allah su zama da lafiyar jiki kuma su ci gaba da samun dangantaka mai kyau da Allah. (Ibran. 10:1) Ba mu san hanyar da sarakuna da firistocin nan za su ja-goranci talakawan Mulkin Allah da suke duniya ba. Ko da wane tsari ne Jehobah ya yi, mun tabbata cewa a cikin Aljanna waɗanda suke duniya za su samu ja-gorancin da suke bukata.​—R. Yar. 21:​3, 4

MENE NE YA ZAMA DOLE “WAƊANSU TUMAKI” SU YI DON SU CANCANCI ZAMA A ALJANNA?

14. Wace dangantaka ce ke tsakanin “waɗansu tumaki” da ‘ƙaramin garken’?

14 Yesu ya kira waɗanda za su yi sarauta tare da shi ‘ƙaramin garke.’ (Luk. 12:32) Ya kuma yi magana game da wani rukuni dabam wanda ya kira su “waɗansu tumaki.” Rukunoni biyun nan sun haɗu sun zama garke ɗaya. (Yoh. 10:16) Waɗanda suke rukunoni biyun nan suna aiki tare, kuma za su ci gaba da yin aiki tare a lokacin da duniya ta zama Aljanna. Hakika a lokacin, ƙaramin garken za su kasance a sama, amma “waɗansu tumaki” za su samu begen jin daɗin rayuwa a nan duniya har abada. Amma akwai abubuwan da “waɗansu tumaki” suke bukatar su yi yanzu don su cancanci yin rayuwa a Aljanna.

Ko yanzu ma, za mu iya nuna cewa muna shirya kanmu don mu yi rayuwa a cikin Aljanna (Ka duba sakin layi na 15) b

15. (a) A wace hanya ce “waɗansu tumaki” suke haɗa kai da ꞌyanꞌuwan Kristi? (b) Ta yaya za ka iya bin misalin ɗanꞌuwa da ke cikin shagon nan? (Ka duba hoton da ya shafi sakin layi na 15.)

15 Ɓarawon da ya tuba bai sami damar nuna cewa yana godiya ga Yesu Kristi domin abin da ya yi masa ba. Amma mu da muke cikin “waɗansu tumaki” muna da damar nuna yadda muke ji game da Yesu yanzu. Alal misali, za mu iya nuna cewa muna ƙaunar sa ta yadda muke bi da ꞌyanꞌuwansa shafaffu. Yesu ya ce zai yi wa tumakin shariꞌa bisa ga yadda suka bi da ꞌyanꞌuwansa. (Mat. 25:​31-40) Za mu iya goyon bayan ꞌyanꞌuwan Kristi ta wajen taimaka musu a yin waꞌazi da kuma koyar da mutane da himma. (Mat. 28:​18-20) Shi ya sa ya kamata mu yi amfani da littattafan nazari da suka tanadar mana yayin da muke yin nazari da mutane. Alal misali, littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! Idan ba ka soma yin nazari da wani ba tukun, za ka iya kafa maƙasudin gabatar da nazarin Littafi Mai Tsarki ga mutane da yawa a duk lokacin da ka sami damar yin hakan.

16. Mene ne za mu iya yi yanzu don mu nuna cewa muna shirin zama a cikin Aljanna?

16 Ba sai mun jira har sai mun shiga Aljanna kafin mu kasance da halin da Jehobah yake so ba. Tun daga yanzu ya kamata mu yi ƙoƙari sosai don mu zama masu gaskiya a abin da muke faɗa da halinmu kuma mu yi rayuwar da ba za ta wuce kima ba. Kuma ya kamata mu riƙe aminci ga Jehobah da abokan aurenmu da kuma ꞌyanꞌuwanmu Kiristoci. Idan mun iya yin biyayya ga Jehobah yanzu a wannan duniyar, zai yi mana sauƙi mu yi masa biyayya a Aljanna. Za mu kuma iya koyan ayyuka da halaye masu kyau za su nuna cewa muna so mu yi rayuwa a Aljanna. Ka duba talifin nan “Kana a Shirye Ka ‘Gaji Duniya’?” a wannan fitowar.

17. Shin ya kamata mu riƙa yin baƙin ciki don zunuban da muka yi a dā? Ka bayyana.

17 Zai dace mu yi ƙoƙari mu daina baƙin ciki don zunubai da muka yi a dā. Hakika, bai kamata mu ɗauka cewa hadayar Yesu ta ba mu damar yin “zunubi da gangan” ba. (Ibran. 10:​26-31) Amma za mu iya kasancewa da tabbaci cewa idan mun riga mun tuba don zunubin mai tsanani da muka yi, mun roƙi Jehobah ya taimaka mana, mun je wurin dattawa kuma mun canja halinmu, Jehobah ya riga ya gafarta mana gabaki ɗaya. (Isha. 55:7; A. M. 3:19) Ka tuna abin da Yesu ya faɗa wa Farisiyawa, ya ce: “Ban zo domin in kira masu adalci ba, sai dai domin masu zunubi.” (Mat. 9:13) Hadayar Yesu ya isa ya sa Allah ya gafarta dukan zunubanmu.

ZA KA IYA YIN RAYUWA HAR ABADA A CIKIN ALJANNA

18. Me za ka so ka tattauna da ɓarawon da ya mutu kusa da Yesu?

18 Ka yi tunanin kanka a Aljanna kana tattaunawa da ɓarawon da ya yi magana da Yesu. Babu shakka za ku faɗi yadda kuke godiya ga Yesu don fansarsa. Za ka iya tambayar sa ya gaya maka abubuwan da suka faru da Yesu jim kaɗan kafin ya mutu, da yadda ya ji saꞌad da Yesu ya amsa roƙonsa. Shi kuma zai iya tambayarka yadda rayuwa ta kasancewa a kwanakin ƙarshe jim kaɗan kafin a hallaka duniyar Shaiɗan. Babu shakka yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane kamar haka zai sa mu farin ciki sosai.​—Afis. 4:​22-24.

A lokacin Sarautar Yesu na Shekara Dubu, wani ɗan’uwa yana farin ciki yayin da yake koyan yin zane, kuma ya daɗe yana marmarin yin hakan (Ka duba sakin layi na 19)

19. Me ya sa ba za mu gaji da rayuwa a Aljanna ba? (Ka duba hoton da ke shafin farko.)

19 Ba za mu gaji da rayuwa a cikin Aljanna ba. A kowane lokaci za mu ji daɗin haɗuwa da mutane da kuma yin aiki mai gamsarwa. Amma abu mafi muhimmanci shi ne, kowace rana za mu daɗa koya game da Ubanmu na sama, kuma za mu ji daɗin abin da ya tanadar mana. Ba za mu taɓa gaji da koyan abubuwa game da shi ba, kuma za mu san abubuwa da yawa game da halittunsa. Yayin da muke daɗa yin rayuwa, za mu daɗa ƙaunar Allah. Muna godiya ga Jehobah da kuma Yesu don alkawarin da suka yi mana cewa za mu yi rayuwa har abada!

WAƘA TA 22 Ya Allah, Ka Kawo Mulkinka!

a Kakan yi tunanin yadda rayuwa za ta kasance a Aljanna? Yana da kyau ka riƙa yin hakan. Idan muna yawan tunani a kan abin da Jehobah zai yi mana a nan gaba, za mu kasance da farin ciki yayin da muke gaya ma wasu game da Aljanna. Wannan talifin zai ƙarfafa begen da muke da shi a kan alkawarin da Yesu ya yi cewa aljanna za ta zo a nan gaba.

b BAYANI A KAN HOTUNA: Wani ɗanꞌuwa da yake sa rai cewa zai koyar da waɗanda aka tā da su daga mutuwa, ya soma koyar da mutane tun yanzu.