TALIFIN NAZARI 52
ꞌYan Mata, Ku Yi Kokari Ku Zama Kiristoci da Suka Manyanta
“Mata . . . su zama masu natsuwa, masu aminci cikin kome.”—1 TIM. 3:11.
WAƘA TA 133 Mu Bauta wa Jehobah da Kuruciyarmu
ABIN DA ZA A TATTAUNA a
1. Idan muna so mu zama Kiristoci da suka manyanta, mene ne za mu yi?
YADDA yaro yake girma ya zama babban mutum abin mamaki ne, kuma ba yaron ne yake sa kansa ya yi girma ba. Amma idan muna so mu zama Kiristoci da suka manyanta, dole ne mu ɗauki wasu matakai. b (1 Kor. 13:11; Ibran. 6:1) Wato muna bukatar mu kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah. Muna bukatar ruhunsa mai tsarki ya taimaka mana mu kasance da halaye da za su faranta masa rai. Muna kuma bukatar mu koyi yin wasu abubuwa da za su amfane mu, kuma mu yi shirin ɗaukan wasu hakkoki a nan gaba.—K. Mag. 1:5.
2. Mene ne muka koya daga Farawa 1:27, kuma me za mu tattauna a talifin nan?
2 Jehobah ya halicce mu maza da mata. (Karanta Farawa 1:27.) Yadda Jehobah ya tsara jikin namiji da tamace dabam ne, amma akwai wata hanya kuma da maza da mata suka bambanta. Alal misali, hakkin da Jehobah ya ba wa maza ya bambanta da wanda ya ba wa mata. Abubuwan da suke bukata don su iya cim ma hakkin da Jehobah ya ba su ba ɗaya ba ne. (Far. 2:18) A wannan talifin, za mu tattauna abin da ꞌyan mata suke bukatar su yi don su zama Kiristoci da suka manyanta. A talifi na gaba kuma, za mu tattauna abin da samari suke bukata su yi don su zama Kiristoci da suka manyanta.
KI KOYI HALAYEN DA ZA SU FARANTA RAN JEHOBAH
3-4. Su waye ne ꞌyan mata za su iya yin koyi da halayensu masu kyau? (Ka kuma duba hoton.)
3 Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da mata da yawa da suka ƙaunaci Jehobah sosai kuma suka bauta masa. (Ka duba talifin nan, “Women in the Bible—What Can We Learn From Them?” a jw.org) Matan sun nuna halaye da aka ambata a ayar da aka ɗauko jigon wannan talifin, wato “natsuwa” da “aminci cikin kome.” Ƙari ga haka, ꞌyan mata Kiristoci za su iya bin misalin mata a ikilisiyarsu da suke ƙaunar Jehobah.
4 ꞌYan mata, ku yi tunanin mata da kuka sani da ke da halaye masu kyau da za ku iya yin koyi da su. Ku lura da halayensu, saꞌan nan ku yi tunanin yadda ku ma za ku bi halinsu. Yanzu bari mu bincika halaye uku da ꞌyan mata suke bukatar su koya don su zama Kiristoci da suka manyanta. Halayen suna da muhimmanci sosai.
5. Me ya sa ꞌyan mata da suke so su manyanta suke bukatar sauƙin kai?
5 Idan muna so mu zama Kiristoci da suka manyanta, muna bukatar sauƙin kai. Idan mace tana da sauƙin kai, za ta kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah da kuma mutane. (Yak. 4:6) Alal misali, macen da take ƙaunar Jehobah za ta bi abin da ke 1 Korintiyawa 11:3. A wurin, Jehobah ya nuna waɗanda yake so su yi ja-goranci a ikilisiya da kuma wanda zai yi hakan a iyali. Akwai hanyoyi da Jehobah yake so dukanmu mu bi abin da ya faɗa a ayar nan a ikilisiya da kuma a iyali. c
6. Mene ne ꞌyan mata za su iya koya daga Rifkatu game da sauƙin kai?
6 Bari mu yi laꞌakari da misalin Rifkatu, wato Rebeka. Tana da basira sosai. Ta san lokacin da ya kamata ta ɗau mataki da kuma yadda za ta yi hakan. Kuma a dukan rayuwarta, ta yanke shawarwarin da suka bukaci ƙarfin zuciya sosai. (Far. 24:58; 27:5-17) Duk da haka, ita mace ce da ke daraja mutane kuma a shirye take ta bi umurnin da aka ba ta. (Far. 24:17, 18, 65) Idan kina da sauƙin kai kamar Rifkatu kuma kika yi biyayya ga waɗanda Jehobah ya naɗa su yi ja-goranci a ikilisiya da kuma a iyali, za ki kafa misali mai kyau a iyalinki da kuma a ikilisiya.
7. Ta yaya ꞌyan mata za su iya nuna cewa sun san kasawarsu kamar Esta?
7 Dukan Kiristoci da suke so su manyanta suna bukatar su san kasawarsu. Littafi Mai Tsarki ya ce “hikima ta masu sanin kasawarsu ce.” (K. Mag. 11:2, New World Translation) Esta mace ce da ta san kasawarta kuma tana ƙaunar Jehobah sosai. Da yake Esta ta san kasawarta, ba ta nuna girman kai saꞌad da ta zama sarauniya ba. Ta saurari shawarar da ɗan kawunta mai suna Mordekai ya ba ta. (Esta 2:10, 20, 22) Za mu nuna cewa mun san kasawarmu idan muna neman shawarar mutanen kirki kuma muna bin abin da suka gaya mana.—Tit. 2:3-5.
8. Bisa ga 1 Timoti 2:9, 10, idan mace ta san kasawarta, ta yaya hakan zai taimaka mata ta san irin kayan da za ta sa da iri adon da za ta yi?
8 Esta ta kuma nuna wannan halin ta wajen daraja raꞌayin mutane. Ko da yake ita “kyakkyawa . . . mai kyan gani” ce, ba ta yi ƙoƙarin sa mutane su mai da hankali ga kyan ta ba. (Esta 2:7, 15) Ta yaya Kiristoci mata za su bi halinta? An bayyana hanya ɗaya da za su iya yin hakan a littafin 1 Timoti 2:9, 10. (Karanta. d) Manzo Bulus ya umurci mata su yi adon da zai nuna cewa suna da kunya da kamun kai, wato suna daraja mutane. Don Kiristoci mata su daraja mutane, zai dace yadda suke ado ya nuna cewa suna yin laꞌakari da yadda mutane suke ji. Muna alfahari da ꞌyanꞌuwanmu mata da suke bin wannan shawarar.
9. Wane darasi ne za mu iya koya daga wurin Abigail?
9 Wani hali kuma da dukan ꞌyanꞌuwanmu mata suke bukata don su zama Kiristoci da suka manyanta shi ne sanin yakamata. Me ake nufi da sanin yakamata? Sanin yakamata yana nufi mutum ya san abu mai kyau da marar kyau, kuma ya yanke shawarar da ta dace. Ki yi laꞌakari da misalin Abigiyel, wato Abigail. Da maigidanta ya yanke wata mummunar shawara da za ta iya shafan rayukan dukan mambobin iyalinta, Abigail ta ɗauki mataki nan-da-nan kuma hakan ya ceci rayuka. (1 Sam. 25:14-23, 32-35) Sanin yakamata zai kuma taimaka mana mu san lokacin da za mu yi magana da lokacin da za mu yi shiru. Kuma yana taimaka mana mu nuna cewa mun damu da mutane ba tare da mun takura musu ko mun tambaye su abubuwan da ba za su so su faɗa ba.—1 Tas. 4:11.
KI KOYI WASU ABUBUWA DA ZA SU AMFANE KI
10-11. Ta yaya iya yin karatu da kuma rubutu zai taimaka miki da ma wasu? (Ka kuma duba hoton.)
10 Mace Kirista tana bukatar ta koyi wasu abubuwa da za su taimake ta a rayuwa. Idan ta koyi abubuwan nan tun tana ƙarama, za su amfane ta har iya rayuwarta. Ga wasu daga cikin abubuwan da take bukatar ta koya.
11 Ki koyi yin karatu da kuma rubutu da kyau. A alꞌadar wasu mutane, ana ganin bai da muhimmanci mace ta koyi karatu da kuma rubutu. Amma yin hakan yana da muhimmanci ga kowane Kirista. e (1 Tim. 4:13) Don haka, kada ki bar wani abu ya hana ki koyan yin karatu da kuma rubutu. Ta yaya hakan zai amfane ki? Yin karatu da kuma rubutu zai iya taimaka miki ki sami aikin yi. Zai sa ki iya yin nazarin Kalmar Allah kuma ki iya koyar da shi. Mafi muhimmanci ma za ki yi kusa da Jehobah idan kina karanta Kalmarsa kuma kina yin tunani mai zurfi a kai.—Yosh. 1:8; 1 Tim. 4:15.
12. Ta yaya Karin Magana 31:26 za ta taimaka miki ki iya yin magana da kyau?
12 Ki koyi yin magana da alheri da kuma sauraran mutane da kyau. Yana da muhimmanci Kiristoci su iya yin hakan. Mabiyin Yesu mai suna Yakub ya ba mu shawara mai kyau game da hakan, ya ce: “Kowa ya kasance mai saurin ji, amma ba mai saurin magana . . . ba.” (Yak. 1:19) Idan kina sauraran mutane da kyau saꞌad da suke magana, hakan zai nuna cewa kin damu da su, wato kina ƙaunar su. (1 Bit. 3:8) Idan ba ki fahimci abin da mutumin yake faɗa ba ko kuma ba ki fahimci yadda yake ji ba, za ki iya tambayar sa a hanyar da ta dace. Bayan haka, sai ki ɗan dakata ki yi tunani, don ki san amsar da za ki ba shi. (K. Mag. 15:28) Ki yi wa kanki tambayoyin nan: ‘Shin abin da nake so in faɗa gaskiya ne kuma zai ƙarfafa shi ko ita? Alheri ne kuma zai nuna cewa na daraja shi ko ita?’ Ki koyi darasi daga mata da suka manyanta da suke saurarar mutane da kyau, kuma suke faɗin alheri. (Karanta Karin Magana 31:26.) Ki lura da yadda suke yin magana. Idan kin koyi yin hakan, zai taimaka miki ki ƙulla dangantaka mai kyau da mutane kuma ki zauna lafiya da su.
13. Ta yaya za ki koyi yadda za ki kula da gidanki? (Ka kuma duba hoton.)
13 Ki koyi yadda za ki kula da gidanki. Mata ne suke yin yawancin ayyukan gida. Mahaifiyarki ko kuma wata ꞌyarꞌuwa za ta iya koya miki yadda za ki yi ayyukan nan. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Cindy ta ce: “Wani abu mai muhimmanci da na koya daga wurin mahaifiyata shi ne cewa yin aiki da ƙwazo yakan sa mutane farin ciki. Da yake ta koya min abubuwa kamar dafa abinci, da shara, da ɗinki, da kuma yadda zan yi sayayya da kyau, ina iya kula da kaina kuma in yi wasu ayyuka a ikilisiya. Ta kuma koya min yadda zan riƙa karɓan baƙi, kuma hakan ya sa na haɗu da mutane maza da mata masu halayen kirki da zan iya koya.” (K. Mag. 31:15, 21, 22) Mace mai ƙwazo da ke iya kula da gidanta da kyau albarka ce ga iyalinta da kuma ikilisiya.—K. Mag. 31:13, 17, 27; A. M. 16:15.
14. Mene ne kika koya daga misalin Crystal, kuma wane abu ne ya kamata ki mai da hankali a kai?
14 Ki koyi yin abubuwa da kanki. Hakan yana da muhimmanci ga Kiristoci da suka manyanta. (2 Tas. 3:7, 8) Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Crystal ta ce: “Saꞌad da nake makarantar sakandare, iyayena sun shawarce ni in koyi abubuwan da za su taimake ni a rayuwa. Babana ya shawarce ni in koyi yadda ake kula da harkokin kuɗi a kamfani, kuma hakan ya taimaka min sosai.” Ban da koyan abubuwan da za su sa ki sami aiki, ki yi ƙoƙari ki koyi yadda za ki iya yin amfani da kuɗin da kike da shi. (K. Mag. 31:16, 18) Idan kin gamsu da abubuwan da kike da su, kuma ba kya sayan abubuwa da suka fi ƙarfinki, hakan zai ba ki zarafin yi wa Jehobah hidima a hanyoyi dabam-dabam.—1 Tim. 6:8.
KI YI SHIRI DON NAN GABA
15-16. Ta yaya muke amfana daga Kiristoci mata da ba su yi aure ba? (Markus 10:29, 30)
15 Idan kin koyi halayen da suke faranta wa Allah rai kuma kika koyi abubuwan da za su taimaka miki a rayuwa, za su amfane ki a nan gaba. Ga misalin wasu abubuwa da za ki iya yi.
16 Za ki iya jira na wasu lokuta kafin ki yi aure. Kamar yadda Yesu ya faɗa, wasu mata sun zaɓa su ƙi yin aure ko da ba a son hakan a alꞌadarsu. (Mat. 19:10-12) Wasu kuma ba su yi aure ba saboda wasu dalilai. Ki san cewa Jehobah ba ya ɗaukan ki a matsayin marar amfani domin ba ki yi aure ba. A duk faɗin duniya, ꞌyanꞌuwa mata da ba su yi aure ba suna taimaka wa ikilisiyarsu sosai. Da yake suna ƙaunar mutane kuma suna kula da su, sun zama kamar ꞌyanꞌuwa da kuma iyaye ga mutane da yawa.—Karanta Markus 10:29, 30; 1 Tim. 5:2.
17. Ta yaya ꞌyan mata za su iya yin shiri yanzu don su iya yin hidima ta cikakken lokaci?
17 Za ki iya yin hidima ta cikakken lokaci. A dukan faɗin duniya, mata ne suka fi yin waꞌazi. (Zab. 68:11) Za ki iya yin shiri yanzu don ki yi hidima ta cikakken lokaci? Za ki iya yin hidima a matsayin majagaba, ko ki yi hidima a sashen gine-gine, ko kuma a Bethel. Ki roƙi Jehobah ya taimaka miki ki cim ma burinki. Ki tattauna da ꞌyanꞌuwa da suka taɓa yin irin hidimar da kike so, kuma ki tambaye su abin da kike bukatar ki yi don ke ma ki iya yinsa. Sai ki shirya yadda za ki iya cim ma wannan burin. Idan kika cika burinki, hakan zai ba ki zarafin yin ayyuka da yawa a ƙungiyar Jehobah.
18. Me ya sa ya dace mace ta yi tunani sosai a kan mijin da za ta aura? (Ka kuma duba hoton.)
18 Za ki iya yanke shawarar yin aure. Halaye masu kyau da abubuwa da za ki iya koya da muka tattauna, za su taimaka miki ki zama macen kirki. Idan kina so ki yi aure, ki yi tunani sosai a kan wanda za ki aura. Aure yana ɗaya daga cikin shawarwari mafi muhimmanci da za ki yanke. Ki tuna cewa, bayan kin yi aure, za ki riƙa bin ja-gorancin maigidanki. (Rom. 7:2; Afis. 5:23, 33) Don haka, ki yi wa kanki tambayoyin nan: ‘Shi Kirista ne da ya manyanta? Bautar Jehobah ce abu mafi muhimmanci a rayuwarsa? Yana yanke shawarwari masu kyau? Yana yarda da kurakuransa? Yana daraja mata? Shin zai iya taimaka min in kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah, ya yi min tanadi, kuma ya zama abokina? Yana cika hakkokinsa da kyau? Alal misali, wane aiki ne aka ba shi a ikilisiya kuma yaya yake yin sa?’ (Luk. 16:10; 1 Tim. 5:8) Gaskiyar ita ce, idan kina so ki auri mijin kirki dole ne ke ma ki yi shirin zama macen kirki.
19. Me ya sa aikin da aka ba wa mace a matsayin “mai taimako” babban gata ne?
19 Littafi Mai Tsarki ya ce macen kirki za ta zama “mai taimako” ga maigidanta. (Far. 2:18) Shin hakan yana nufin cewa macen ba ta da daraja kamar maigidanta ne? Aꞌa! Aikin da aka ba wa mace a matsayin mai taimako babban gata ne. Jehobah da kansa ma, Littafi Mai Tsarki ya ce shi ‘mai taimako’ ne. (Zab. 54:4; Ibran. 13:6) Idan miji ya yanke shawara da ta shafi iyali kuma matarsa ta taimaka masa don shawarar ta yi nasara, hakan zai nuna cewa ita mai taimakonsa ce. Kuma da yake tana ƙaunar Jehobah, za ta yi iya ƙoƙarinta don ta sa mutane su ga halaye masu kyau na maigidanta. (K. Mag. 31:11, 12; 1 Tim. 3:11) Za ki iya shirya yin hakan ta wurin ƙara ƙaunar Jehobah, da kuma taimaka wa mutane a iyalinki da kuma a ikilisiya.
20. Ta yaya halin mace zai iya amfanar kowa a iyali?
20 Za ki iya haifan yara. Bayan kin yi aure, ke da maigidanki za ku iya haifan yara. (Zab. 127:3) Don haka yana da muhimmanci ki yi shiri tun da wuri. Halaye da kuma abubuwan da za ki iya koya da muka tattauna a talifin nan, za su taimaka miki ki zama macen kirki da kuma mahaifiyar kirki. Idan kina da ƙauna da alheri da kuma haƙuri, hakan zai sa kowa a iyalinki ya yi farin ciki, kuma yaranki ma za su yi rayuwa hankali a kwance.—K. Mag. 24:3.
21. Yaya muke ɗaukan ꞌyanꞌuwanmu mata, kuma me ya sa? (Ka duba hoton da ke shafin farko.)
21 ꞌYan mata, muna ƙaunar ku sosai domin ayyukan da kuke yi wa Jehobah da kuma ƙungiyarsa. (Ibran. 6:10) Kuna yin iya ƙoƙarinku don ku kasance da halaye da za su faranta wa Jehobah rai, kuma kuna koyan abubuwan da za su taimaka muku, da waɗanda suke tare da ku. Ƙari ga haka, kuna yin shiri don nan gaba. Kuna da muhimmanci sosai a ƙungiyar Jehobah!
WAƘA TA 137 Mata Masu Aminci
a ꞌYan mata, kuna da daraja sosai a ikilisiya. Za ku iya zama Kiristocin da suka manyanta ta wajen koyan halayen da za su faranta ran Jehobah, da koyan abubuwa da za su taimaka muku a rayuwa, da kuma yin shiri don nan gaba. Yin hakan zai sa ku mori albarku da dama yayin da kuke bauta ma Jehobah.
b MAꞌANAR WASU KALMOMI: Kirista da ya manyanta yana bin ja-gorancin ruhu mai tsarki, ba raꞌayoyin mutanen duniya ba. Yana yin iya ƙoƙarinsa ya yi koyi da Yesu don ya ci-gaba da kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah, kuma yana nuna wa mutane ƙauna ta gaskiya.
d 1 Timoti 2:9, 10 (Mai Makamantun] Ayoyi): “Mata kuma su riƙa sa tufafin da ya dace da su saboda kunya da kamunkai, ba adon kitso, ko kayan zinariya, ko lu’ulu’u, ko tufafi masu tsada ba, sai dai su yi aiki nagari, yadda ya dace da mata masu bayyana shaidar ibadarsu.”
e Don ƙarin bayani a kan muhimmancin karatu, ka duba talifin nan, “Why Reading Is Important for Children—Part 1: Read or Watch?” a jw.org.