Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 51

Abin da Kake Sa Zuciya a Kai Zai Tabbata

Abin da Kake Sa Zuciya a Kai Zai Tabbata

“Sa zuciyar nan ba za ta zama abin banza ba ko kaɗan.” —ROM. 5:5.

WAƘA TA 142 Mu Jimre, Aljanna Ta Kusa

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1. Me ya sa ya dace da Ibrahim ya sa rai cewa zai haifi ɗa?

 JEHOBAH ya yi wa Ibrahim alkawari cewa ta wurin sa, dukan ƙabilun duniya za su samu albarka. (Far. 15:5; 22:18) Da yake Ibrahim mutum ne mai bangaskiya sosai, ya gaskata cewa alkawarin Jehobah zai cika. Amma, har lokacin da Ibrahim ya kai shekaru ɗari kuma shekarun matarsa sun kai casaꞌin, Ibrahim bai samu ɗa ba. (Far. 21:​1-7) Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya ce: “[Ibrahim] ya ci gaba da sa zuciya, yana ba da gaskiya har ya zama ‘uban kabilu masu yawa.’ Wannan kuwa bisa ga alkawarin da aka yi masa ne.” (Rom. 4:18) Hakika, ka san cewa abin da Ibrahim ya sa zuciyarsa a kai ya faru. A-kwana-a-tashi Ibrahim ya samu ɗa mai suna Ishaku. Amma, me ya tabbatar wa Ibrahim cewa Jehobah zai cika alkawarin nan?

2. Me ya tabbatar wa Ibrahim cewa Jehobah zai cika alkawarin da ya yi masa?

2 Da yake Ibrahim aminin Jehobah ne, ‘ya kasance da cikakken tabbaci’ cewa Allah zai cika alkawarinsa. (Rom. 4:21) Saboda bangaskiyar Ibrahim, Jehobah ya amince da shi kuma ya ce shi mai adalci ne. (Yak. 2:23) Kamar yadda Romawa 4:18 ta ce, Ibrahim ya sa zuciya kuma yana da bangaskiya. Yanzu, bari mu bincika abin da manzo Bulus ya faɗa game da sa zuciya ko kuma bege a littafin Romawa sura 5.

3. Wane bayani ne Bulus ya yi game da sa zuciya?

3 Manzo Bulus ya bayyana abin da ya sa za mu iya kasance da tabbaci cewa “sa zuciyar nan [tamu] ba za ta zama abin banza ba ko kaɗan.” (Rom. 5:5) Ya kuma nuna mana abin da za mu yi don sa zuciyarmu ta ƙaru. Za mu bincika wasu matakan da Bulus ya bayyana a Romawa 5:​1-5. Yayin da muke hakan, ka yi tunanin yadda sa zuciyarka ta ƙaru da shigewar lokaci. Za mu kuma tattauna abin da za ka yi don ka ƙara sa zuciya a kan alkawuran Jehobah. Bari mu fara da wata sa zuciya mai ban shaꞌawa da manzo Bulus ya ce ba za ta zama banza ba.

SA ZUCIYARMU MAI BAN SHAꞌAWA

4. Wane bayani ne Bulus ya yi a Romawa 5:​1, 2?

4 Karanta Romawa 5:​1, 2. Manzo Bulus yana magana ne da Kiristocin da ke ikilisiyar Roma. ꞌYanꞌuwan sun riga sun koya game da Jehobah da Yesu, sun ba da gaskiya kuma sun zama Kiristoci. Sun samu alherin Allah, wato Allah ya amince da su domin bangaskiyarsu kuma ya yi amfani da ruhunsa mai tsarki ya zaɓe su. Don haka, suna da babban dalilin sa zuciya cewa za su samu lada na musamman.

5. Wane lada ne Jehobah zai ba shafaffun Kiristoci?

5 Daga baya, sai Bulus ya yi magana game da sa zuciya ko kuma begen da Jehobah ya ba shafaffun Kiristoci da ke Afisa. Begen ya ƙunshi samun “gādon nan wanda yake domin tsarkaka.” (Afis. 1:18) Kuma Bulus ya gaya wa Kolosiyawa inda za su samu ladan da suke sa zuciya a kai. Ya ce, suna ‘sa zuciya ne a kan abin da aka yi musu ajiyarsa a sama.’ (Kol. 1:​4, 5) Don haka, abin da Kiristoci shafaffu suke sa zuciya a kai shi ne, za a ta da su kuma a ba su rai na har abada a sama, inda za su yi mulki tare da Yesu.—1 Tas. 4:​13-17; R. Yar. 20:6.

Ɗanꞌuwa F. W. Franz ya bayyana irin tabbacin da shafaffun Kiristoci suke da shi a kan begensu (Ka duba sakin layi na 6)

6. Mene ne wani ɗanꞌuwa da shafaffe ne ya ce game da ladan da yake begen samuwa?

6 Shafaffun Kiristoci suna son wannan ladan sosai. A 1991, Ɗanꞌuwa Frederick Franz wanda yake ɗaya daga cikinsu ya bayyana yadda yake ji a ransa, ya ce: “Tabbas Allah zai ba mu wannan ladan, kuma kowanne cikin mu 144,000, zai samu abin da Allah ya yi mana alkwarinsa. Ladan nan zai fi duk wani abin da muke tsammani.” Ɗanꞌuwa Franz ya yi shekaru da yawa yana bauta wa Jehobah da aminci. Ya ci-gaba da cewa: “Har wa yau, wannan ladan yana da muhimmanci sosai a gare mu. . . . Yayin da muke jiran wannan landan, godiyar da muke yi sai ƙaruwa take. Abu ne da ya cancanci mu jira shi, ko da miliyoyin shekaru za mu yi muna jira. Yanzu, ina daraja begen samun wannan ladan fiye da dā.”

7-8. Wane lada ne yawancin bayin Jehobah suke sa zuciya a kai? (Romawa 8:​20, 21)

7 Amma, wannan ba shi ne ladan da yawancin bayin Jehobah a yau suke sa zuciya a kai ba. Kamar Ibrahim, yawancinsu suna sa ran yin rayuwa har abada a duniya a ƙarƙashin Mulkin Allah. (Ibran. 11:​8-10, 13) Manzo Bulus ya yi magana a kan wannan lada mai ban shaꞌawa. (Karanta Romawa 8:​20, 21.) Da ka fara sanin abubuwan da Jehobah ya yi alkawari zai yi mana a nan gaba, wanne ne a cikinsu ya fi burge ka? Shin wanda ya ce wata rana za ka zama marar zunubi ne? Ko dai wanda ya ce waɗanda kake ƙauna za su sake rayuwa a aljanna ne? Hakika, wannan bege ko kuma sa zuciya da Allah ya ba mu ya sa kana marmarin moran abubuwa da yawa.

8 Ko da muna begen yi rayuwa har abada a sama ne ko a duniya, kowannenmu yana da lada mai ban shaꞌawa da yake sa ran samu. Kuma wannan sa zuciyar da ke faranta mana rai za ta iya ƙaruwa. Bulus ya bayyana yadda hakan zai iya faruwa. Bari mu ga abin da ya rubuta game da sa zuciyar da muke yi. Hakan zai ƙara tabbatar mana da cewa, sa zuciyar nan tamu za ta ci-gaba da ƙaruwa kuma ba za ta zama banza ba ko kaɗan.

YADDA SA ZUCIYARMU TAKE ƘARUWA

Dukan Kiristoci sun san za su yi fama da wata matsala (Ka duba sakin layi na 9-10)

9-10. Kamar yadda ya faru da Bulus, me zai iya faruwa da yawancin Kiristoci a yau? (Romawa 5:3) (Ka kuma duba hotunan.)

9 Karanta Romawa 5:3. Wurin ya ce wahala za ta iya sa mutum ya ƙara sa zuciya. Hakan zai iya ba mu mamaki. Gaskiyar ita ce, dukan mabiyan Yesu za su sha wahala. Abin da ya faru da manzo Bulus ke nan. Ya gaya wa Kiristocin da ke Tasalonika cewa: “Saꞌad da muke tare da ku, mun gaya muku tun da wuri, cewa za mu sha azaba. Haka kuwa ya kasance.” (1 Tas. 3:4) Ya kuma gaya wa Korintiyawa cewa: “ꞌYanꞌuwa, ba ma so ku kasance da rashin sani game da irin wahalar da muka sha . . . har ba mu san za mu rayu ba.”—2 Kor. 1:8; 11:​23-27.

10 Kiristoci a yau su ma sun san za su iya fuskantar matsaloli iri-iri. (2 Tim. 3:12) Kai kuma fa? An taɓa tsananta maka don ka ba da gaskiya ga Yesu kuma kana bin sa? Wataƙila abokanka ko danginka sun taɓa zolayarka. Ƙila ma sun taɓa zaluntarka. Ko kuma ƙila shugabanka ko abokan aikinka sun taɓa tsananta maka don kana faɗin gaskiya. (Ibran. 13:18) Hukuma ta taɓa tsananta maka don kana gaya wa mutane game da abubuwan da kake begen su? Ko da wane irin wahala ne za mu sha, Bulus ya ce mu yi farin ciki. Me ya sa ya ce hakan?

11. Me ya sa muke bukatar mu yi shirin jimre kowane irin wahala?

11 Za mu iya yin farin ciki saꞌad da muke shan wahala idan muka tuna abin da take jawowa. Romawa 5:3 ta ce, ‘wahala takan jawo jimrewa.’ Dukan Kiristoci za su sha wahala. Don haka, dole ne dukan Kiristoci su zama masu jimiri. Muna bukatar mu yi shirin jimre duk wata matsalar da za ta same mu. Ta hakan ne za mu samu ladan da muke sa zuciya a kai. Kada mu zama kamar waɗanda Yesu ya kwatanta su da irin da ya faɗi a wuri mai duwatsu. Da farko sun karɓi maganar Allah da farin ciki. Amma da “azaba ko tsanani” suka taso musu, sai suka ja baya. (Mat. 13:​5, 6, 20, 21) Fuskantar tsanantawa ko wahala bai da sauƙi kam. Amma idan muka jimre kuma muka ci-gaba da bauta wa Jehobah, za mu amfana. Ta yaya?

12. Ta yaya jimre wahala take amfanar mu?

12 Yakub ya bayyana amfanin jimre wahala, ya ce: “Sai jimrewarku kuma ya cika aikinsa, ya kai ku ga zaman natsatsu da cikakku har kada ku rasa kome.” (Yak. 1:​2-4) Yakub yana nufin cewa jimrewa tana da aikin da take cikawa. Wane aiki ke nan? Za ta iya taimaka maka ka ƙara zama mai halaye masu kyau kamar, haƙuri da bangaskiya da kuma mai dogara da Allah. Amma, akwai wani babban amfani kuma da za mu iya samu.

13-14. Mene ne jimrewa take jawowa kuma mece ce alaƙar da ke tsakanin jimrewa da sa zuciya? (Romawa 5:4)

13 Karanta Romawa 5:4. Manzo Bulus ya ce, ‘jimrewa takan jawo halin kirki.’ Jehobah yana son masu halin kirki. Don haka idan kana jimrewa, Jehobah zai yarda da kai. Amma hakan ba ya nufin cewa Jehobah yana jin daɗin ganin ka kana shan wahala. Yadda kake jimrewa da aminci ne yake sa Jehobah farin ciki. Jimrewarka za ta sa Jehobah ya yarda da kai. Hakan abin ban ƙarfafa ne sosai, ko ba haka ba?—Zab. 5:12.

14 Ka tuna cewa Ibrahim shi ma ya jimre matsalolin da ya fuskanta kuma hakan ya sa Jehobah ya yarda da shi. Jehobah ya ce shi abokinsa ne kuma ya ɗauke shi a matsayin mai adalci. (Far. 15:6; Rom. 4:​13, 22) Mu ma hakan zai iya faruwa da mu. Ba yawan ayyukan da muke yi ko inda muke hidima ne yake sa Jehobah ya yarda da mu ba. Yadda muke jimre matsaloli da aminci ne zai sa Jehobah ya yarda da mu. Kuma ko da a wane yanayi muke, komen shekarunmu ko baiwarmu, kowannenmu zai iya jimrewa. Akwai matsalar da kake jimrewa a yanzu da aminci? Idan haka ne, ka san cewa kana faranta ran Jehobah kuma ya yarda da kai. Idan muka san cewa Jehobah ya yarda da mu, hakan zai sa mu ƙara sa zuciya a kan ladan da ya ce zai ba mu.

SA ZUCIYAR DA BA ZA TA ZAMA ABIN BANZA BA

15. Mene ne Bulus ya faɗa daga baya kuma me ya sa hakan zai ba wasu mamaki?

15 Za mu sami amincewar Jehobah idan muka jimre matsalolinmu kuma muka riƙe aminci. Bulus ya ci-gaba da cewa: “Halin kirki kuma [‘idan Allah ya yarda da mutum,’ NWT] yakan jawo sa zuciya. Sa zuciyar nan ba za ta zama abin banza ba ko kaɗan.” (Rom. 5:​4, 5) Hakan zai iya sa wasu su yi mamaki. Domin a Romawa 5:​2, Bulus ya riga ya ce ꞌyanꞌuwan nan da suke Roma suna ‘sa zuciya cewa za su zama masu tarayya cikin ɗaukakar Allah.’ Don haka, mutum zai iya cewa, ‘Da yake tun dā ma Kiristocin nan suna da abin da suka sa zuciya a kai, me ya sa manzo Bulus ya sake kawo zancen sa zuciya?’

Da shigewar lokaci, ka ƙara tabbata cewa za ka samu abin da ka sa zuciya a kai, kana marmarinsa kuma kana godiya don begen nan fiye da dā (Ka duba sakin layi na 16-17)

16. Me yake sa mutum ya fara sa zuciya a kan alkawuran Allah? (Ka kuma duba hotunan.)

16 Don mu fahimci abin da manzo Bulus yake nufi, muna bukatar mu san cewa sa zuciya ko kuma bege, abu ne da take iya ƙaruwa. Ga misali, ka tuna lokacin da ka fara jin alkawura masu ban mamaki da suke cikin Kalmar Allah? Ƙila ka yi tunanin cewa, “Begen yin rayuwa har abada a aljanna a duniya abu ne mai kyau sosai. Amma zai faru kuwa?” Amma da ka ƙara sanin Jehobah da kuma alkawuransa da ke Littafi Mai Tsarki, sai ka ƙara ganin tabbacin cewa zai faru da gaske.

17. Ta yaya sa zuciyar da kake yi za ta ci-gaba da ƙaruwa bayan ka yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ka yi baftisma?

17 Har bayan da ka yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ka yi baftisma, ka ƙara samun tabbacin cewa ladan da kake begen samuwa zai tabbata, don ka ci-gaba da koyan abubuwa game da Jehobah kuma ka ƙara ƙaunarsa. (Ibran. 5:13–6:1) Ba mamaki abin da ke Romawa 5:​2-4 ya faru da kai. Ka fuskanci matsaloli da yawa amma ka jimre dukansu kuma ka ga cewa Allah ya yarda da kai. Yanzu da ka san cewa Allah yana ƙaunar ka, kana da babban dalilin sa zuciya cewa zai cika alkawarin da ya yi maka. Sa zuciya da kake yi yanzu ta fi ta dā. Ka ƙara sanin cewa abin da ka sa zuciya a kai lallai zai faru. Yanzu wannan sa zuciyar tana shafan rayuwarka sosai fiye da dā. Tana shafan kome da kake yi, ta canja yadda kake kula da ꞌyan iyalinka da shawarwarin da kake yankewa, har ma da yadda kake amfani da lokacinka.

18. Wane tabbaci ne Jehobah ya ba mu?

18 Manzo Bulus ya kuma faɗi wani abu mai muhimmanci game da sa zuciyar da kake yi saꞌad da Allah ya yarda da kai. Ya ba ka tabbaci cewa, za ka sami ladan da kake sa zuciya a kai. Me zai ba ka wannan cikakken tabbacin? Ga tabbacin da Allah ya sa manzo Bulus ya rubuta wa Kiristoci, ya ce: “Sa zuciyar nan ba za ta zama abin banza ba ko kaɗan, gama Allah ya zuba ƙaunarsa cikin zukatanmu ta wurin Ruhu Mai Tsarki da Allah ya ba mu.” (Rom. 5:5) Hakika, kana da cikakken tabbaci cewa Jehobah zai ba ka wannan ladan da kake sa rai a kai.

19. Wane tabbaci ne kake da shi game da ladan da kake sa zuciya a kai?

19 Ka yi tunani a kan alkawarin da Jehobah ya yi wa Ibrahim da yadda Ya yarda da shi kuma Ya ɗauke shi a matsayin abokinsa. Sa zuciyar da Ibrahim ya yi bai zama banza ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Bayan da Ibrahim ya jimre da haƙuri sosai, sai ya karɓi abin da aka yi masa alkawari.” (Ibran. 6:15; 11:​9, 18; Rom. 4:​20-22) Hakika, sa zuciyar da Ibrahim ya yi ba ta bi ruwa ba. Kai ma za ka iya kasance da tabbacin cewa idan ka riƙe aminci, Jehobah zai ba ka ladan da kake begen samuwa. Ya kamata ka yi farin ciki sosai, don ka san cewa sa zuciyar da kake yi ba a banza ba ne. Tabbas za ta cika. (Rom. 12:12) Manzo Bulus ya rubuta cewa: “Bari Allah mai kawo sa zuciya ya ba ku cikakken farin ciki da salama a saꞌad da kuke ba da gaskiya gare shi, domin ku yalwata da sa zuciya ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.”—Rom. 15:13.

WAƘA TA 139 Rayuwa a Cikin Aljanna

a A wannan talifin, za mu tattauna abin da sa zuciya ko kuma begenmu ya ƙunsa, da kuma abin da ya tabbatar mana da cewa abin da muka sa zuciya a kai zai faru da gaske. Littafin Romawa sura 5 za ta taimaka mana mu ga yadda sa zuciyarmu a yanzu ta yi dabam da wadda muka yi saꞌad da muka soma koyan gaskiya.