Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 50

Bangaskiya da Ayyukanmu Za Su Sa Mu Zama Masu Adalci

Bangaskiya da Ayyukanmu Za Su Sa Mu Zama Masu Adalci

‘Mu bi misalin irin bangaskiyar da Ibrahim yake da ita.’ —ROM. 4:12.

WAƘA TA 119 Wajibi Ne Mu Kasance da Bangaskiya

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1. Idan muka yi tunani game da Ibrahim, wace tambaya ce za mu yi wa kanmu?

 KO DA yake mutane da yawa sun ji labarin Ibrahim, yawancinsu ba su san shi sosai ba. Amma kai ka san Ibrahim sosai. Alal misali, ka san cewa an kira Ibrahim “uban masu ba da gaskiya ga Allah.” (Rom. 4:11) Kana iya tunanin cewa, ‘Zan iya zama kamar Ibrahim kuma in kasance da irin bangaskiyarsa kuwa?’ Ƙwarai, za ka iya.

2. Me ya sa yin nazari a kan rayuwar Ibrahim yake da muhimmanci? (Yakub 2:​22, 23)

2 Wani abin da zai taimaka mana mu kasance da bangaskiya kamar Ibrahim shi ne yin nazarin rayuwarsa. Ibrahim ya yi ta bin umurnin Jehobah a kowane lokaci. Ya ƙaura zuwa wata ƙasa mai nisa, ya yi shekaru da yawa yana zama a tenti, kuma ya kasance a shirye ya yi hadaya da ɗansa Ishaku. Ya yi dukan abubuwan nan ne don yana da bangaskiya sosai. Bangaskiyar Ibrahim da ayyukansa masu kyau sun sa Allah ya amince da shi kuma ya zama abokin Jehobah. (Karanta Yakub 2:​22, 23.) Jehobah yana son dukanmu mu zama abokansa, har da kai ma. Saboda hakan ne ya sa Bulus da Yakub su rubuta labarin Ibrahim. Yanzu bari mu tattauna abin da Romawa sura 4 da Yakub sura 2 suka ce. Surori biyun nan sun ambaci wani abu mai muhimmanci game da Ibrahim.

3. Wane nassi ne Bulus da Yakub suka yi ƙaulin sa?

3 Bulus da Yakub sun maimaita abin da ke Farawa 15:​6, wadda ta ce: “Ibram ya ba da gaskiya ga Yahweh, sai Yahweh ya lissafta wannan adalci ne ga Ibram.” Idan mutum yana yin abin da yake faranta wa Allah rai, Allah yakan ɗauke shi a matsayin mai adalci ko marar laifi. Abin ban ƙarfafa ne mu san cewa Jehobah yana iya ɗaukan mutum ajizi a matsayin marar laifi! Hakika, za ka so Allah ya ce kai mai adalci ne, kuma hakan zai yiwu. Yanzu bari mu ga dalilin da ya sa Jehobah ya kira Ibrahim mai adalci, da abubuwan da ya kamata mu yi don mu ma mu zama masu adalci.

SAI DA BANGASKIYA NE ZA MU ZAMA MASU ADALCI

4. Mene ne yake hana ꞌyan Adam zama masu adalci?

4 A wasiƙar da Bulus ya rubuta wa Romawa, ya ce dukan ꞌyan Adam masu zunubi ne. (Rom. 3:23) To, ta yaya za mu zama masu adalci ko marar laifi a gaban Allah har ma mu samu amincewarsa? Bulus ya yi amfani da misalin Ibrahim don ya taimaka wa Kiristoci su san amsar tambayar nan.

5. Me ya sa Jehobah ya kira Ibrahim mai adalci? (Romawa 4:​2-4)

5 Saꞌad da Ibrahim yake zama a ƙasar Kanꞌana ne Jehobah ya ce da shi mai adalci. Me ya sa Jehobah ya ce da Ibrahim mai adalci? Shin don Ibrahim ya bi Dokar Musa babu kuskure ne? Aꞌa. (Rom. 4:13) Domin, a lokacin da Jehobah ya ce da Ibrahim mai adalci, ba a kafa Dokar Musa ba. Shekaru fiye da 400 sun wuce kafin aka ba da wannan dokar. To me ya sa Jehobah ya ce Ibrahim mai adalci ne? Alheri ne Jehobah ya yi wa Ibrahim, saboda bangaskiyarsa ya ce da shi mai adalci.—Karanta Romawa 4:​2-4.

6. Me zai sa Jehobah ya ce da wanda ya yi zunubi mai adalci?

6 Bulus ya ce idan mutum ya ba da gaskiya ga Allah, “Za a ɗauki bangaskiyar mutumin nan kamar adalcinsa ke nan. Wannan shi ne abin da Dawuda yake nufi da ya yi magana game da albarkar da aka yi wa mutumin da Allah ya ce da shi mai adalci, ba ta dalilin ayyukan da mutumin ya yi ba cewa, ‘Mai albarka ne mutumin da aka gafarta masa zunuban gangancinsa, wanda aka yafe masa zunubansa. Mai albarka ne mutumin da Ubangiji bai lissafta laifofinsa ba.’” (Rom. 4:​5-8; Zab. 32:​1, 2) Allah yakan yafe zunuban waɗanda suka ba da gaskiya gare shi. Idan ya yafe zunubansu, ba ya tunawa da zunuban. Yana ɗaukansu a matsayin masu adalci, marasa laifi saboda bangaskiyarsu.

7. Me ya sa muka ce bayin Allah a dā masu adalci ne?

7 Ko da yake Allah ya ce Ibrahim da Dauda da wasu bayinsa masu adalci ne, hakan ba ya nufin cewa sun zama kamiltattu. Bangaskiyarsu ce ta sa Allah ya ce da su marasa laifi, musamman ma idan yana gwada su da waɗanda ba sa bauta masa. (Afis. 2:12) A wasiƙarsa ga Romawa, Bulus ya bayyana cewa sai da bangaskiya ne za mu iya zama aminan Allah. Mu ma idan muna so mu zama aminan Allah, dole ne mu kasance da bangaskiya.

TA YAYA AYYUKANMU ZA SU NUNA CEWA MUNA DA BANGASKIYA?

8-9. Wane raꞌayi marar kyau ne wasu suke da shi game da abin da Bulus da Yakub suka rubuta, kuma me ya sa?

8 Shugabannin addinai sun yi shekaru da yawa suna gardama a kan muhimmancin bangaskiya da nuna hakan ta ayyukanmu. Wasu malaman addinai suna cewa idan mutum ya gaskata da Yesu Kristi kawai, zai samu ceto. Sukan ce: “Ka karɓi Yesu don ka samu ceto.” Wasunsu suna iya yin ƙaulin abin da Bulus ya faɗa cewa Allah zai iya ce da mutum “mai adalci, ba ta dalilin ayyukan da mutumin ya yi ba.” (Rom. 4:6) Wasu kuma suna cewa mutum zai samu ceto idan yana yin ayyukan kirki kuma yana zuwa wuraren da aka ce suna da tsarki. Za su iya yin ƙaulin Yakub 2:​24, da ta ce: “Mutum yana samun zaman marar laifi a gaban Allah saboda ayyukansa ne, ba saboda bangaskiya ita kaɗai ba.”

9 Saboda wannan bambancin raꞌayi, wasu masanan Littafi Mai Tsarki suna ganin cewa Bulus da Yakub ba su da raꞌayi ɗaya game da abin da ya kamata mutum ya yi don Allah ya amince da shi. Wasu malaman addinai suna ganin cewa a gun Bulus, bangaskiya ce kawai mutum yake bukata don ya samu amincewar Allah, a gun Yakub kuma, sai ta ayyuka ne mutum zai samu amincewar Allah. Wani farfesan ilimin addini ya ce Yakub bai fahimci dalilin da ya sa Bulus ya ce bangaskiya kawai ta isa ta sa mutum ya sami amincewar Allah ba, kuma Yakub bai yarda da bayanin Bulus ba. Amma Jehobah ne ya sa Bulus da Yakub su rubuta kalaman nan. (2 Tim. 3:16) Saboda haka, akwai hanya mai sauƙi da za mu iya sanin abin da suke nufi. Muna bukatar mu bincika wasu abubuwa da suka tattauna a wasiƙunsu don mu iya fahimtar abin da suka faɗa da kyau.

Bulus ya gaya wa Kiristoci Yahudawa da ke Roma cewa bangaskiya tana da muhimmanci ba yin ayyukan Koyarwar Musa kawai ba (Ka duba sakin layi na 10) b

10. Waɗanne “ayyuka” ne manzo Bulus yake magana a kai? (Romawa 3:​21, 28) (Ka kuma duba hoton.)

10 Waɗanne “ayyuka” ne Bulus yake zancen su a Romawa sura 3 da 4? Yana magana ne game da “ayyukan Koyarwar Musa,” wato dokar da aka ba wa Musa a Dutsen Sinai. (Karanta Romawa 3:​21, 28.) A zamanin Bulus, wasu Kiristoci Yahudawa suna ganin cewa suna bukatar su ci-gaba da bin Dokar Musa. Saboda haka, Bulus ya yi amfani da misalin Ibrahim don ya nuna cewa ba dole ne mutum ya bi “ayyukan Koyarwar Musa” kafin Allah ya yarda da shi ba. A maimako, bangaskiya ce muke bukata. Sanin wannan yana da ban ƙarfafa, don ya nuna cewa za mu iya samun dangantaka mai kyau da Allah. Idan muka ba da gaskiya ga Allah da kuma Yesu, za mu sami amincewar Allah.

Yakub ya ƙarfafa Kiristoci cewa su nuna bangaskiyarsu ta “ayyuka” kamar yi wa mutane alheri ba tare da nuna bambanci ba (Ka duba sakin layi na 11-12) c

11. Waɗanne “ayyuka” ne Yakub yake magana a kai?

11 Amma “ayyukan” da aka ambata a Yakub sura 2, ba “ayyukan Koyarwar Musa” da Bulus ya yi magana a kai ba ne. Yakub yana magana ne game da ayyukan da Kiristoci suke yi a rayuwarsu na yau da kullum. Ayyukan nan suna nuna ko Kirista ya gaskata da Allah da gaske ko aꞌa. Ga wasu misalai biyu da Yakub ya yi amfani da su.

12. Ta yaya Yakub ya nuna cewa muna bukatar bangaskiya kuma mu nuna ta ta ayyukanmu? (Ka kuma duba hoton.)

12 A misali na farko, Yakub ya bayyana cewa bai kamata Kiristoci su nuna bambanci ba. Ya yi misali da wani mutum da ya yi wa wani mai arziki alheri, amma ya rena wani don shi talaka ne. Yakub ya bayyana cewa irin mutumin nan zai iya ce shi mai bangaskiya ne, amma ayyukansa ba sa nuna hakan. (Yak. 2:​1-5, 9) A na biyun, Yakub ya yi misali da wani mutum da ya ga “wani ɗanꞌuwa ko wata ꞌyarꞌuwa” ba ta da ‘rigar sawa, da kuma abinci,’ amma ya ƙi ya taimaka mata. Ko da wannan ɗanꞌuwan yana ganin yana da bangaskiya, ayyukansa ba su nuna hakan ba. Don haka, bangaskiyarsa ba ta da amfani. Kamar yadda Yakub ya rubuta, “bangaskiya wadda ba ta da ayyukan da suke tabbatar da ita banza ce.”—Yak. 2:​14-17.

13. Wane misali ne Yakub ya bayar don ya nuna cewa muna bukatar mu nuna bangaskiya ta ayyukanmu? (Yakub 2:​17, 25)

13 Yakub ya ce Rahab ta nuna bangaskiya ta ayyukanta. (Karanta Yakub 2:​17, 25.) Ta ji labarin Jehobah kuma ta ga cewa yana taimaka wa Israꞌilawa. (Yosh. 2:​9-11) Sai ta nuna bangaskiyarta ta ayyukanta. Ta ɓoye ꞌyan leƙen asiri guda biyu da ake nema a kashe. Abin da ta yi ya sa Jehobah ya ɗauke ta a matsayin mai adalci kamar yadda ya yi da Ibrahim. Kuma ya nuna mana cewa yana da muhimmanci mu nuna bangaskiyarmu ta ayyukanmu.

14. Me ya sa za mu ce abin da Bulus ya faɗa, da abin da Yakub ya faɗa sun jitu da juna?

14 Saboda haka, Bulus da Yakub suna magana ne game da bangaskiya da kuma ayyuka a hanyoyi dabam-dabam. Abin da Bulus yake cewa shi ne, idan ayyukan Koyarwar Musa ne kawai Kiristoci Yahudawa suka ce za su yi, ba za su taɓa samun amincewar Allah ba. Yakub kuma yana nufin cewa dukan Kiristoci suna bukatar su nuna bangaskiyarsu ta yi wa mutane alheri.

Bangaskiyarka tana sa ka ka yi abubuwan da Jehobah ya amince da su? (Ka duba sakin layi na 15)

15. A waɗanne hanyoyi ne za mu nuna cewa muna da bangaskiya? (Ka kuma duba hotunan.)

15 Jehobah bai ce kafin mu zama masu adalci, dole ne mu yi daidai abin da Ibrahim ya yi ba. Akwai hanyoyi da yawa da za mu iya nuna cewa muna da bangaskiya. Za mu iya marabtar mutane saꞌad da suka zo ikilisiyarmu, ko mu taimaka wa ꞌyanꞌuwanmu da suke cikin bukata kuma mu yi wa ꞌyan iyalinmu alheri. Yin abubuwan nan zai sa Allah ya amince da mu kuma ya albarkace mu. (Rom. 15:7; 1 Tim. 5:​4, 8; 1 Yoh. 3:18) Wata hanya mai muhimmanci da za mu nuna cewa muna da bangaskiya ita ce ta yin waꞌazi da ƙwazo. (1 Tim. 4:16) Dukanmu za mu iya nuna ta ayyukanmu cewa, mun gaskata alkawuran Jehobah za su faru da gaske kuma yadda yake yin abu ne ya fi dacewa. Idan muka yi hakan, babu shakka Jehobah zai ce da mu masu adalci kuma za mu zama aminansa.

BEGENMU YANA ƘARA SA MU KASANCE DA BANGASKIYA

16. Wane abu ne Ibrahim ya sa rai cewa zai faru kuma ta yaya ya nuna bangaskiya?

16 Romawa sura 4 ta ƙara ambata wani darasi mai muhimmanci da za mu iya koya daga Ibrahim. Surar ta koya mana cewa yana da muhimmanci mu ci-gaba da yin marmarin abin da muke begen sa. Jehobah ya yi alkawari cewa Ibrahim zai “zama baban dubun dubban kabilu” kuma ta wurinsa “dubban kabilu” za su sami albarka. Wannan alkawari ne mai ban ƙarfafa da Ibrahim ya yi marmarin ganin cikawar sa. (Far. 12:3; 15:5; 17:4; Rom. 4:17) Amma Ibrahim ba shi da ɗa har saꞌad da ya kai shekaru 100, Saratu kuma shekara 90. A gun ꞌyan Adam, Ibrahim da Saratu ba za su taɓa iya samun ɗa ba. Bai kasance wa Ibrahim da sauƙi ba. Duk da haka, “ya ci gaba da sa zuciya, yana ba da gaskiya har ya zama uban kabilu masu yawa.” (Rom. 4:​18, 19) Kuma daga baya, wannan alkawarin ya cika. Ibrahim ya haifi Ishaku wato ɗan da ya daɗe yana jira.—Rom. 4:​20-22.

17. Ta yaya muka san cewa Allah zai iya ce da mu masu adalci?

17 Mu ma Allah zai iya amincewa da mu kuma mu zama aminansa kamar Ibrahim. Abin da Bulus ya yi magana a kai ke nan saꞌad da ya ce: “Wannan magana mai cewa, ‘aka lissafta bangaskiya adalci ne a gare shi,’ ba saboda [Ibrahim] kaɗai ne aka rubuta ba. Amma an rubuta wannan magana saboda mu, mu ma, mu da Allah zai lissafta mu masu adalci, wato mu da muka ba da gaskiya ga wanda ya tā da Yesu.” (Rom. 4:​23, 24) Kamar Ibrahim, muna bukatar mu kasance da bangaskiya, mu nuna ta ta ayyukanmu kuma mu gaskata cewa alkawuran Jehobah za su cika. Bulus ya ci-gaba da tattauna game da begen da muke da shi a Romawa sura 5, kuma abin da za mu tattauna ke nan a talifi na gaba.

WAƘA TA 28 Yadda Za Mu Zama Abokan Jehobah

a Muna so Allah ya yarda da mu kuma muna so ya ce mu masu adalci ne. A talifin nan, za mu yi amfani da abin da Bulus da Yakub suka rubuta don mu tattauna yadda za mu zama masu adalci da kuma yadda bangaskiyarmu da ayyukanmu za su sa Jehobah ya amince da mu.

b BAYANI A KAN HOTUNA: Manzo Bulus ya ƙarfafa Yahudawan su mai da hankali a kan kasancewa da bangaskiya maimakon yin ayyukan “Koyarwar Musa,” kamar ɗaura igiya mai kalar ruwan bula a rigarsu, da yin Bikin Ƙetarewa da wanke hannu da dai sauransu.

c BAYANI A KAN HOTO: Yakub ya ƙarfafa ꞌyanꞌuwan su nuna bangaskiyarsu ta wajen yin ayyuka masu kyau kamar taimaka wa talakawa.