Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Kasance da Irin Raꞌayin Jehobah Game da Giya

Ka Kasance da Irin Raꞌayin Jehobah Game da Giya

BA SHAKKA, kana farin ciki don kyaututtuka da yawa da Jehobah ya ba ka, kuma kana godiya don ya ba ka ꞌyancin zaɓan yadda za ka yi amfani da kyaututtukan. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa giya ko kuma ruwan inabi kyauta ce daga wurin Allah. Ya ma ce: “Akan shirya biki domin jin daɗi, ruwan inabi kuwa domin faranta rai.” (M. Wa. 10:19; Zab. 104:15) Amma mai yiwuwa ka lura cewa wasu mutane suna shan giya yadda bai kamata ba. Ƙari ga haka, mutane da yawa suna da raꞌayoyi dabam-dabam game da shan giya. To, mene ne zai taimaka wa Kiristoci su kasance da raꞌayin da ya dace game da giya?

Ko da a ina ne muke zama, ko mece ce alꞌadarmu, zai dace mu bi raꞌayin Allah game da giya, ba raꞌayin mutane ba. Yin hakan zai sa mu yi farin ciki a rayuwa.

Mai yiwuwa ka lura cewa mutane da yawa a faɗin duniya suna shan giya fiye da kima kuma suna yin hakan kusan kullum. Wasu suna shan giya domin yana kwantar musu da hankali. Wasu kuma suna sha don su manta da damuwoyinsu. A wasu wurare, mutumin da ke shan giya sosai, ana masa ganin namiji ko kuma jarumi.

Amma, Kiristoci suna bin shawara mai kyau da Allah ya ba su game da giya. Alal misali, ya gargaɗe mu game da munanan sakamakon da yawan shan giya yake jawowa. Mai yiwuwa mun taɓa karanta Karin Magana 23:​29-35, game da abubuwan da mai buguwa yakan yi da kuma matsalolin da hakan yake jawo masa. a Wani dattijo mai suna Daniel da ke zama a Turai ya tuna rayuwarsa a dā kafin ya zama Kirista. Ya ce: “A dā, ina shan giya sosai kuma hakan ya sa na yanke shawarwari marasa kyau. Na shiga matsaloli da dama, kuma har yau nakan yi baƙin ciki idan na tuna da hakan.”

Ta yaya Kirista zai iya yanke shawarar da ta dace kuma ya guji munanan sakamakon da yawan shan giya yake jawowa? Abin da zai taimaka masa ya yi hakan shi ne, ya bi raꞌayin Allah game da giya.

Yanzu bari mu tattauna abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da shan giya da kuma dalilan da suka sa wasu suke shan giya.

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA FAƊA GAME DA SHAN GIYA

Kalmar Allah ba ta haramta shan giya daidai kima ba. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa shan giya zai iya sa mutum farin ciki. Ya ce: “Ka ji daɗin abincinka, ka sha ruwan inabinka da farin ciki.” (M. Wa. 9:7) Akwai lokutan da Yesu, da wasu bayin Allah masu aminci suka sha giya.— Mat. 26:​27-29; Luk. 7:34; 1 Tim. 5:23.

Amma ko da yake Littafi Mai Tsarki bai haramta shan giya ba, ya haramta buguwa. Ya faɗa dalla-dalla cewa: “Kada kuma ku bugu da ruwan inabi.” (Afis. 5:18) Ya kuma nuna cewa “masu buguwa” ba za su “shiga mulkin Allah” ba. (1 Kor. 6:10) Hakika, Jehobah ya haramta buguwa da kuma yawan shan giya. Maimakon mu bar raꞌayin mutane ko kuma alꞌadarmu ta shafi shawarar da muke yankewa game da giya, zai dace mu bi raꞌayin Allah.

Wasu suna gani cewa za su iya shan giya da yawa ba tare da sun bugu ba. Amma yin hakan yana da haɗari sosai. Littafi Mai Tsarki ya ce, ‘zama bawa ga ruwan inabi,’ zai iya sa mutum ya yi babban kuskure kuma ya ɓata dangantakarsa da Allah. (Tit. 2:3; K. Mag. 20:1) Yesu ma ya gargaɗe mu cewa “yawan shaye-shaye” zai iya hana mutum shiga Mulkin Allah. (Luk. 21:​34-36, Mai Makamantu[n] Ayoyi) To, mene ne zai taimaka wa mutum ya guji matsalolin da shan giya yake iya jawowa?

KA YI TUNANI A KAN YAWAN GIYA DA KAKE SHA DA ABIN DA YA SA KAKE SHA

Idan mutum ya bar alꞌadarsa ta shafi raꞌayinsa game da giya, hakan zai iya kasance da haɗari sosai. Kiristoci suna yanke shawarar da za ta faranta wa Allah rai idan ya zo ga batun abinci da kuma abin sha. Littafi Mai Tsarki ya tuna mana da cewa: “Duk abin da kuke yi, ko kuke ci, ko kuke sha, ku yi kome saboda ɗaukakar Allah.” (1 Kor. 10:31) Ga wasu tambayoyi da ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da za mu iya yin tunani a kai:

Shin ina shan giya don kada wasu su zolaye ni ne? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba za ka bi bayan taron jamaꞌa” ba. (Fit. 23:​2, MMA) A nan, Jehobah yana ja wa Israꞌilawa kunne cewa su daina bin mutanen da ba sa faranta masa rai. Wannan gargaɗin yana da muhimmanci ga Kiristoci a yau. Idan mun bar raꞌayin mutane ya shafi yadda muke shan giya, hakan zai sa mu ɓata dangantakarmu da Jehobah.—Rom. 12:2.

Shin ina shan giya don in nuna cewa ni jarumi ne ko kuma ina da ƙarfi? A wasu alꞌadu, ba laifi ba ne mutum ya sha giya da yawa kusan kullum. (1 Bit. 4:3) Amma ka ga shawara mai kyau da ke 1 Korintiyawa 16:​13, ta ce: “Ku zauna da shiri, ku tsaya sosai cikin bangaskiyarku, ku zama da ƙarfafawa, kuma da ƙarfi.” Shin shan giya zai iya sa mutum ya zama jarumi ko mai ƙarfi ne? Aꞌa. Idan mutum ya sha giya, ba zai iya yin tunani da kyau kuma ya yanke shawarar da ta dace ba. Don haka, shan giya da yawa ba ya nuna cewa mutum jarumi ne ko mai ƙarfi. A maimakon haka, yana nuna cewa shi marar tunani ne da kuma wawa. Ishaya 28:7 ta nuna cewa waɗanda suka bugu da giya sukan yi tangaɗi kuma su yi tuntuɓe.

Jehobah ne yake ba mu ƙarfi na gaskiya. Amma don mu samu ƙarfin, muna bukatar mu zauna da shiri kuma mu tsaya sosai cikin bangaskiyarmu. (Zab. 18:32) Muna yin hakan ta wajen guje wa abubuwan da suke da haɗari da yanke shawarar da za ta ɓata dangantakarmu da Jehobah. Yesu yana da dangantaka mai kyau da Jehobah, kuma mutane da yawa sun daraja shi don yana da ƙarfin zuciya da niyyar yin abin da ya dace.

Shin ina shan giya don in manta da damuwata ne? Wani marubucin zabura ya rubuta cewa: ‘Saꞌad da damuwoyi sukan yi mini yawa, taꞌaziyyarka [Jehobah] takan ƙarfafa raina.’ (Zab. 94:19) Idan damuwoyi sun yi maka yawa, ka roƙi Jehobah ya taimaka maka, maimakon ka sha giya. Abu ɗaya da za ka iya yi don ka rage yawan damuwa shi ne adduꞌa ga Jehobah a-kai-a-kai. Ban da haka, wasu ꞌyanꞌuwa sun lura cewa neman shawara daga wurin ꞌyanꞌuwa da suka manyanta a ikilisiya yana da amfani. Gaskiyar ita ce, idan mutum ya sha giya domin ya manta da damuwarsa, ba zai kasance da niyyar yin abin da ya dace ba. (Hos. 4:11) Daniel da muka ambata a baya ya ce: “Na yi ta damuwa da kuma nadama. Na sha giya don in daina damuwa amma matsalar ta ƙaru. Hakan ya sa na rasa abokaina da kuma mutuncina.” Mene ne ya taimaka wa Daniel? Daniel ya ce: “Daga baya, na gano cewa taimakon Jehobah ne nake bukata, ba giya ba. A ƙarshe, na iya na magance matsalolina kuma na shawo kansu.” Gaskiyar ita ce, a kullum Jehobah yana a shirye ya taimaka mana ko da muna ganin cewa matsalolinmu sun yi yawa kuma babu mafita.—Filib. 4:​6, 7; 1 Bit. 5:7.

Idan kana shan giya a wasu lokuta, za ka iya bincika ka ga ko kana bukatar ka rage yawan giya da kake sha ta wajen yi wa kanka tambayoyin nan: ‘Shin wani a iyalina ko kuma abokina ya taɓa nuna damuwa game da yadda nake shan giya?’ Idan amsar e ce, hakan na nuna cewa ka soma koyan hali marar kyau ko kuma ka soma shiga wata matsala ba tare da saninka ba. ‘Shin ina shan giya yanzu fiye da yadda na saba?’ Hakan yana iya nuna cewa shan giya yana so ya zama maka jaraba. ‘Shin yana min wuya in yi kwana biyu ba tare da na sha giya ba?’ Idan haka ne, shan giya ya zama maka jaraba ke nan. Yana iya nufin cewa kana bukatar taimako daga ƙwararrun likitoci.

Saboda haɗari da kuma matsaloli da ke tattare da shan giya, wasu Kiristoci sun yanke shawara cewa ba za su sha giya ba. Wasu kuma ba sa sha saboda ɗanɗanonsa. Idan wani abokinka ya ce ba zai sha giya ba, za ka iya yi masa alheri ta wajen daraja shawarar da ya yanke, kuma ka guji yi masa dariya.

Ƙila ka ga cewa zai dace ka rage yawan giyar da kake sha ko kuma ka rage lokutan da za ka riƙa shan giya. Kana iya ragewa zuwa sau ɗaya a mako, ko kuma ka sha kaɗan saꞌad da kake cin abinci. Wasu Kiristoci kuma, sun yanke shawarar cewa za su sha giya, amma ba za su sha giya da ke da ƙarfi sosai ba. Idan Kirista ya riga ya yanke shawara a kan irin giyar da zai sha da yawanta, kuma ya ce ba zai sha fiye da hakan ba, zai yi masa sauƙi ya bi shawarar da ya yanke. Bai kamata Kirista ya ji kunya ba idan har ya yanke wannan shawarar kuma yana iya ƙoƙarinsa ya bi ta.

Yana da kyau kuma mu yi laꞌakari da raꞌayin mutane yayin da muke yanke shawara. Romawa 14:21 ta ce: “Ya fi kyau kada ka ci nama, ko ka sha ruwan inabi, ko ka aikata kowane irin abu idan zai sa ɗanꞌuwanka ya faɗi.” Ta yaya za ka bi wannan shawarar? Ka nuna wa ɗanꞌuwanka ƙauna. Idan ka ga cewa shan giya zai sa ɗanꞌuwanka tuntuɓe, ƙauna za ta sa ka sadaukar da ꞌyancinka na shan giya. Yin hakan zai nuna cewa kana daraja raꞌayin wasu kuma ba ka mai da hankali ga abin da zai amfane ka kawai.—1 Kor. 10:24.

Ƙari ga haka, gwamnati za ta iya kafa doka game da giya kuma dole ne Kirista ya bi dokar. Dokar tana iya nuna shekarun da mutum yake bukatar ya kai kafin ya sha giya, ko ta hana mutum shan giya saꞌad da yake tuƙi ko kuma amfani da wasu injuna.—Rom. 13:​1-5.

Jehobah ya ba mu ꞌyancin more kyaututtuka da yawa da ya ba mu. Ɗaya daga cikinsu shi ne ꞌyancin zaɓan irin abinci da abin sha da muke so. Bari zaɓin da muke yi ya nuna cewa muna daraja wannan ꞌyancin da Jehobah ya ba mu, kuma mu yi amfani da shi mu faranta masa rai.

a Wata Cibiyar Kiwon Lafiya a Amurka ta ce wasu matsalolin da shan giya yake jawowa su ne, kisan gilla, da kisan kai, da cin zarafi, da cin zalin miji ko mata, da yin jimaꞌi da ke sa a yi cikin da ba a shirya ba, da kamuwa da cututtuka, da kuma ɓarin ciki.