Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Labari

Labari

Tausaya wa Kowa

Wata ꞌyarꞌuwa a Niyu Zilan ta kalli bidiyon nan Mu Nuna Tausayi ga Juna.” Bidiyon ya nuna yadda tausayi yake sa Jehobah ya taimaka wa mutane. (Isha. 63:​7-9) Ta koyi darasi daga bidiyon kuma ta nemi zarafin taimaka wa mutane. Bayan da ta kalli bidiyon, sai ta je yin cefane kuma ta haɗu da wata mata da ba ta da wurin kwana. Ta gaya wa matar cewa za ta so ta saya mata abinci, sai matar ta amince. Da take ba wa matar abincin, ta yi mata waꞌazi kuma ta nuna mata warƙar nan Wahala Za Ta Ƙare Kuwa?

Sai matar ta fashe da kuka. Ta bayyana cewa an koyar da ita game da Jehobah tun tana ƙarama, amma yanzu ta yi shekaru da yawa ba ta bin abin da ta koya. A kwana-kwanan nan ta yi ta adduꞌa ga Jehobah ya taimaka mata ta dawo ƙungiyarsa. ꞌYarꞌuwar ta ba matar Littafi Mai Tsarki kuma matar ta yarda a yi nazari da ita. a

Kamar Jehobah, mu ma za mu iya jin tausayin dukan mutane. Hakan ya haɗa da iyalinmu da ꞌyanꞌuwanmu a ikilisiya. Za mu kuma iya nuna cewa muna jin tausayin mutane ta wajen neman zarafi mu yi musu waꞌazi.

a Don ka san yadda za ka taimaka wa waɗanda suka daina zuwa taro da yin waꞌazi, ka duba talifin nan “Ku Juyo Gare Ni” a Hasumiyar Tsaro ta Yuni, 2020.