TARIHI
Ban Taba Daina Koyan Abubuwa Ba
NA GODE wa Jehobah don damar da ya ba ni in zama ɗalibinsa. (Isha. 30:20) Yana koyar da bayinsa ta wurin Littafi Mai Tsarki, da halittunsa masu ban mamaki, da kuma ƙungiyarsa. Kuma yana amfani da ꞌyanꞌuwanmu maza da mata wajen koya mana abubuwa. Ko da yake na kusan shekaru 100 yanzu, ina amfana sosai daga koyarwa da Jehobah yake mini a hanyoyin nan. Bari in gaya muku abin da ya sa na ce hakan.
An haife ni a shekara ta 1927, a wani ƙaramin gari da ke kusa da Chicago, Illinois, a ƙasar Amurka. Mu biyar ne iyayenmu suka haifa. Na farko ita ce Jetha, sai Don, sai ni, sai Karl, sai kuma Joy. Dukanmu mun ƙudiri niyar bauta wa Jehobah. Jetha ta halarci aji na biyu na makarantar Gilead a shekara ta 1943. Ɗanꞌuwana Don ya soma hidima a Bethel da ke Brooklyn, New York, a shekara ta 1944, Karl a shekara ta 1947, Joy kuma a shakara ta 1951. Misali mai kyau da su da iyayena suka kafa, ya sa na ƙara ƙwazo a hidimata ga Jehobah.
YADDA IYALINMU TA KOYI GASKIYA
Babana da Mamata suna son karanta Littafi Mai Tsarki kuma suna ƙaunar Allah. Kuma sun sa yaransu ma su ƙaunace shi. Amma da mahaifina ya dawo daga Yaƙin Duniya na 1 da ya je a ƙasashen Turai, sai ya daina ganin darajar coci. Mahaifiyata ta yi farin ciki don ya dawo da ransa. Ana nan sai ta ce masa: “Zo mu tafi coci kamar yadda muka saba yi.” Sai mahaifina ya ce: “Zan raka ki, amma ba zan shiga cikin cocin ba.” Sai mahaifiyata ta ce: “Me ya sa?” Sai ya ce mata: “A lokacin da ake yaƙin, na ga limamai da addininsu ɗaya ne amma ƙasarsu ba ɗaya ba, kowannensu yana yi wa sojojin ƙasarsa adduꞌa su yi nasara a kan ɗayan ƙasar! Adduꞌar wa kike gani Allah zai ji?”
Bayan mahaifiyata ta je coci, sai Shaidu biyu suka zo gidanmu. Sun ba wa mahaifina wasu littattafai biyu masu jigo Light, wato Haske. Littattafan sun bayyana abin da ke littafin Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna. Mahaifina ya so littattafan kuma ya karɓa. Da mahaifiyata ta ga littattafan, sai ta soma karanta su. Wata rana da mahaifiyata tana karanta wata jarida, sai ta ga an rubuta a ciki cewa ana gayyatar mutane zuwa nazarin Littafi Mai Tsarki, kuma da littattafan nan ne za a yi nazarin. Sai ta je. Da ta isa wurin, sai wata tsohuwa ta buɗe kofa. Mahaifiyata ta ɗaga ɗaya daga cikin littattafan ta ce: “Kuna nazarin wannan littafin a nan?” Sai matar ta amsa da cewa, “E, ki shigo.” A mako na gaba, mahaifiyata ta kai dukanmu wurin. Bayan haka, mun soma zuwa wannan taron kowane mako.
Wata rana da muka je, sai ɗanꞌuwan da yake gudanar da taron ya ce mini in karanta Zabura 144:15, da ta nuna cewa masu bauta wa Jehobah suna farin ciki. Da na karanta, na ji daɗin abin da ayar ta ce. Wasu ayoyi kuma da suka burge ni su ne 1 Timoti 1:11 (NWT), da ta ce Jehobah “Allah mai farin ciki” ne, da kuma Afisawa 5:1, da ta ƙarfafa mu mu zama masu koyi da Allah. Nassosin nan sun sa na gane cewa ina bukatar in bauta wa Mahaliccina da farin ciki, kuma in gode masa don wannan gata da ya ba ni. Abin da na yi ke nan.
Ikilisiya da ta fi kusa da inda muke tana da nisan kilomita 32 (mil 20) a birnin Chicago. Duk da haka muna zuwa taro, kuma na yi ta ƙara fahimtar abin da ke Littafi Mai Tsarki. Na tuna ranar da yayata Jetha ta ɗaga hannu kuma an kira ta ta ba da amsa. Da na ji abin da ta faɗa, sai na ce: ‘Ai ni ma na san wannan amsar. Da-na-sani, da na ɗaga hannu.’ Daga ranar, na soma yin shiri da kuma ba da amsa a taro. Mafi muhimmanci ma, na ƙara kusantar Jehobah kamar ꞌyanꞌuwana. Kuma a 1941 na yi baftisma.
JEHOBAH YA KOYAR DA NI A BABBAN TARONMU
Ba zan manta da babban taro da aka yi a 1942, a birnin Cleveland da ke jihar Ohio ba. A tenti ne iyalai da dama suka kwana, kusa da inda aka yi taron. Mu ma abin da muka yi ke nan. ꞌYanꞌuwa sun taru a wasu wurare fiye da 50 a Amurka, kuma sun saurari taron ta tarho. A lokacin ana kan Yaƙin Duniya na 2, kuma ana tsananta wa Shaidun Jehobah sosai. Ranar da yamma, na lura cewa wasu ꞌyanꞌuwa sun faka motocinsu yadda za su fuskanci waje. Na rasa me ya sa suka yi hakan. Ashe sun shirya ne cewa mutum ɗaya zai kwana a kowane mota, yana gadi. Idan masu gadin suka ga cewa maƙiya sun zo su cutar da ꞌyanꞌuwa, sai kowa ya danna hon kuma ya kunna wutar motarsa don su kashe wa maƙiyan ido. Saꞌan nan wasu ꞌyanꞌuwa za su zo su taimaka. Da na gano hakan, sai na ce, ‘Lallai mutanen Jehobah suna yin shiri don kome da zai iya faruwa!’ Don haka na yi barcina hankali kwance. Mun gode wa Allah cewa ba abin da ya faru.
Shekaru da yawa bayan haka, idan na tuna da wannan taron, nakan kuma tuna cewa mahaifiyata ba ta ji tsoro ba ko kaɗan. Ta san cewa Jehobah da ƙungiyarsa za su kula da mu. Ta kafa mana misali mai kyau da ba zan taɓa mantawa ba.
Da daɗewa kafin taron, Mahaifiyata ta soma hidimar majagaba na kullum. Hakan ya sa ta mai da hankali sosai saꞌad da ake jawabai game da hidima ta cikakken lokaci. Da muke komawa gida, ta ce mana: “Ina so in ci-gaba da yin hidimar majagaba na kullum, amma ba zan iya yinsa kuma in kula da ayyukan gidanmu yadda ya kamata ba.” Sai ta tambaye mu ko za mu iya taimakawa. Sai muka ce, “E.” Sai ta rarraba mana ɗakunan da za mu riƙa sharewa kafin mu karya da safe. Idan muka gama kuma muka tafi makaranta, sai ta je ta duba ta tabbata cewa kome ya yi daidai, saꞌan nan ta tafi waꞌazi. Ko da yake tana da ayyuka da yawa, ta ci-gaba kula da yaranta. Idan muka tashi daga makaranta mukan zo mu same ta ta riga ta dafa abincin rana tana jiranmu. Kuma a wasu lokuta bayan mun ci abincin, sai mu bi ta yin waꞌazi. Hakan ya taimaka mana mu fahimci aikin da majagaba suke yi.
NA SOMA HIDIMAR MAJAGABA
Na soma hidimar majagaba na kullum saꞌad da nake shekara 16. A wannan lokacin mahaifina bai zama Mashaidi ba, amma a kullum yakan tambaye ni yaya hidimata. Wata rana da yamma, na gaya masa cewa har yanzu ban sami wanda ya yarda in yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi ba. Sai na dakata
kaɗan, kuma na tambaye shi cewa, “Za ka so mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki tare?” Sai ya ɗan yi tunani kuma ya yarda. Don haka babana ne ya zama ɗalibina na farko. Hakika, wannan babban gata ne gare ni!Mun yi nazarin da littafin nan, “The Truth Shall Make You Free,” wato Gaskiya Za Ta Sa Ka Sami ꞌYanci. Da muka ci-gaba da nazarin, na ga cewa mahaifina yana taimaka mini in inganta yadda nake nazari da koyarwa. Alal misali, wata rana da muka karanta wani sakin layi, ya ce: “Na ji abin da littafin ya ce. Amma me ya tabbatar maka cewa gaskiya ne?” Ban yi shirin amsa wannan tambayar ba, don haka na gaya masa cewa: “Yanzu haka ba zan iya amsa tambayar nan ba, amma zan ba ka amsa a nazarinmu na gaba.” Kuma abin da na yi ke nan. Na samo ayoyi da suka nuna cewa abin da muke tattaunawa gaskiya ne. Tun daga lokacin, na soma yin bincike sosai don in kasance a shirye kafin nazarinmu. Yin hakan ya taimaka mini da mahaifina mu ƙara fahimtar abin da ke Littafi Mai Tsarki. Ya bi abin da ya koya kuma ya yi baftisma a 1952.
NA CI-GABA DA KOYAN ABUBUWA A BETHEL
Na bar gida saꞌad da nake shekara 17. Kuma a lokacin ne, yayata Jetha a ta zama mai wa’azi a ƙasar waje, Ɗanꞌuwana Don kuma ya soma hidima a Bethel. Su biyu sun so hidimarsu sosai, kuma hakan ya ƙarfafa ni. Hakan ya sa na cika fom na zuwa Bethel da na Makarantar Gilead kuma na bar kome a hannun Jehobah. Ana nan sai aka gayyace ni zuwa Bethel a 1946.
A shekaru 75 da na yi a Bethel, na yi aiki a wurare dabam-dabam. Hakan ya sa na koyi abubuwa da dama. Na koyi yadda ake buga littattafai da kuma kula da kuɗaɗe. Na kuma koyi yadda ake sayan abubuwan da ake bukata a Bethel, da kuma yadda ake aika kaya zuwa ƙasar waje. Mafi muhimmanci ma, ina jin daɗin koyarwar da ake mana a Bethel a lokacin ibadar safiya da dai sauransu.
Ban da haka, na koyi abubuwa daga wurin ƙanina Karl, wanda ya zo Bethel a 1947. Ya kware wajen yin nazari da koyar da Littafi Mai Tsarki. Akwai lokacin da aka ba ni wani jawabi, sai na gaya masa ya taimaka mini in san yadda zan shirya jawabin da kyau. Na gaya masa cewa na samo bayanai da yawa amma ban san yadda zan yi amfani da su ba. Sai ya yi mini wata tambaya, ya ce, “Joel, mene ne jigon jawabin nan naka?” Tambayarsa ta taimaka mini in gane cewa ba dukan bayanan da na samo nake bukata ba. Sai dai waɗanda za su taimaka mini in bayyana jigon jawabin da kyau. Ba zan taɓa manta da wannan abin da ya koya mini ba.
Idan mutum yana so ya kasance da farin ciki a Bethel, yana bukatar ya sa ƙwazo wajen yin waꞌazi. Yin hakan zai sa mu sami labarai masu ban-ƙarfafa. Na tuna wani abin da ya faru wata rana da yamma a birnin New York. Ni da wani ɗanꞌuwa mun ziyarci wata mata da ta karɓi Hasumiyar Tsaro da Awake! Da muka isa, mun gai da ita, sai muka ce, “Muna nuna wa mutane abubuwa masu ban ƙarfafa a Littafi Mai Tsarki ne da yammar nan.” Sai ta ce, “Idan game da Littafi Mai Tsarki ne ku shigo.” Mun karanta ayoyi da dama game da Mulkin Allah da aljanna kuma mun tattauna su. Matar ta ji daɗin bayanin da muka yi mata har ta ce wa abokanta da yawa su ma su zo mako na gaba. Daga baya, ita da mijinta sun soma bauta wa Jehobah.
NA KOYI ABUBUWA DAGA WURIN MATATA
Kafin in yi aure, na yi shekaru 10 ina neman wadda zan aura. Abin da ya taimaka min in sami macen kirki shi ne adduꞌa. Na roƙi Jehobah ya taimaka mini, kuma na yi tunani a kan irin rayuwar da nake so in yi da wadda zan aura.
Sai a babban taro da aka yi a Yankee Stadium a 1953, na haɗu da wata ꞌyarꞌuwa mai suna Mary Aniol. Ita da ꞌyarꞌuwata sun je aji na biyu na Makarantar Gilead tare, kuma sun yi waꞌazi a ƙasar waje tare. Mary ta ba ni labarin yadda take jin daɗin hidimarta, da mutanen da ta yi nazari da su. Hirar da muka yi ta sa mun ga cewa dukanmu muna so mu ci-gaba da yin hidima ta cikakken lokaci. Mun ƙara son juna, kuma a-kwana-a-tashi muka yi aure, a watan Afrilu 1955. Mary ta zama mini albarka sosai a rayuwata, kuma halinta abin koyi ne. Ko da wane aiki ne aka ba ta, tana yinsa da farin ciki. Tana aiki da ƙwazo, ta damu da mutane sosai, kuma a koyaushe alꞌamuran Mulkin Allah ne take sa a kan gaba. (Mat. 6:33) Mun yi shekaru uku muna hidimar mai kula da daꞌira tare. Sai a 1958 aka gayyace mu mu zo Bethel.
Na koyi abubuwa da yawa daga wurin matata. Alal misali, ba da daɗewa ba bayan aurenmu, mun soma karanta Littafi Mai Tsarki tare. Mukan karanta wajen ayoyi 15 kowace rana. Bayan mutum ɗaya ya karanta wasu ayoyi, sai mu dakata kuma kowa ya faɗi abin da ya koya da yadda za mu bi shi a rayuwarmu. Idan muna hakan, Mary tana yawan gaya mini abubuwan da ta koya a Makarantar Gilead ko saꞌad da take waꞌazi a ƙasar waje. Abubuwan da na koya daga wurinta sun taimaka mini na inganta jawabaina da yadda nake ƙarfafa ꞌyanꞌuwa mata.—K. Mag. 25:11.
Matata Mary ta mutu a 2013. Ina marmarin sake ganin ta a sabuwar duniya! Kafin nan, burina shi ne in ci-gaba da koyan abubuwa kuma in dogara ga Jehobah da dukan zuciyata. (K. Mag. 3:5, 6) Ina jin daɗi sosai idan na yi tunani a kan abubuwan da bayin Jehobah za su yi a aljanna, kuma hakan yana ƙarfafa ni. Babu shakka Allah, wanda shi ne Malaminmu, zai koya mana sabbin abubuwa kuma za mu ƙara saninsa! Ba zan iya kwatanta irin godiyar da nake masa ba, don yawan alherinsa a gare ni da kuma abubuwan da ya koya mini.
a Ka ga tarihin ꞌyarꞌuwa Jetha Sunal a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Maris 2003, shafi na 23-29.