Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ABUBUWAN DA ZA KU IYA YIN NAZARI A KAI

Idan Mai Aminci Ya Yi Alkawari, Yana Cika Shi

Idan Mai Aminci Ya Yi Alkawari, Yana Cika Shi

Ku karanta Alƙalai 11:30-40 don ku koyi darasi daga wurin Jephthah da ꞌyarsa a kan muhimmancin cika alkawari.

Ku bincika labarin sosai. Idan mutumin Israꞌila mai aminci ya yi ma Jehobah alkawari, yaya yake ɗaukan alkawarin? (L. Ƙid. 30:2) Yaya Jephthah da ꞌyarsa suka nuna cewa su masu bangaskiya ne?—Alƙa. 11:9-11, 19-24, 36.

Ku nemi ƙarin bayani. A lokacin da Jephthah ya yi alkawarin nan, me yake a zuciyarsa? (w16.04 5 sakin layi na 12) Waɗanne abubuwa ne Jephthah da ꞌyarsa suka saɗaukar don su cika alkawarin? (w16.04 6-7 sakin layi na 14-16) Waɗanne alkawura ne bayin Jehobah suke masa a yau?—w17.04 5-8 sakin layi na 10-19.

Ku yi tunani a kan abubuwan da kuka koya. Kowa ya tambayi kansa:

  • ‘Mene ne zai taimake ni in cika alkawarin da na yi cewa zan bauta ma Jehobah a dukan rayuwata?’ (w20.03 13 sakin layi na 20)

  • ‘Waɗanne abubuwa ne zan iya sadaukarwa don in ƙara himma a bautar Jehobah?’

  • ‘Me zai taimake ni in cika alkawarin da na yi wa matata ko maigidana a ranar da muka yi aure?’ (Mat. 19:5, 6; Afis. 5:28-33)