TALIFIN NAZARI NA 51
WAƘA TA 3 Ƙarfinmu, Begenmu da Makiyayinmu
Jehobah Yana Ganin Kukan da Kake Yi Kuma Ya Damu da Kai
“Ka auna yawan hawayena. Ba a rubuce suke a cikin littafinka ba?”—ZAB. 56:8.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga cewa idan muna cikin damuwa sosai, Jehobah ya san ainihin yadda muke ji kuma zai ƙarfafa mu.
1-2. Waɗanne yanayoyi ne za su iya sa mutum ya zub da hawaye?
BABU wanda bai taɓa zub da hawaye ba. Wasu sukan zub da hawaye don tsananin farin ciki, ƙila a lokacin da wani abu mai muhimmanci ya faru a rayuwarsu. Alal misali, idan sun haifi ɗa, ko sun tuna da wani abu da ya burge su sosai, ko kuma sun haɗu da wani abokinsu da suka yi shekaru ba su haɗu ba.
2 Amma a yawancin lokuta, wahala da kuma damuwar da muke ciki ne suke sa mu zub da hawaye. Alal misali, mukan zub da hawaye idan aka ci amanarmu, ko muna fama da wata cuta da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa, ko mun rasa wani da muke ƙauna. Irin wannan yanayin zai iya sa mu ji yadda annabi Irmiya ya ji saꞌad da aka halaka Urushalima. Ya ce: “Hawaye suna zubowa kamar ruwan kogi . . . Hawayena za su yi ta zubowa, ba tsayawa, ba hutawa.”—Mak. 3:48, 49.
3. Yaya Jehobah yake ji idan ya ga bayinsa suna shan wahala? (Ishaya 63:9)
3 Jehobah ya san yawan lokutan da muka yi kuka don matsalolinmu. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa ya san lokacin da kowannenmu yake cikin damuwa, kuma idan muka roƙe shi zai taimaka mana. (Zab. 34:15) Amma ba ganinmu da jinmu ne kawai Jehobah yake yi ba. Shi ne Ubanmu kuma yana ƙaunarmu sosai. Don haka idan ya gan mu muna kuka, abin yakan dame shi, kuma hakan yakan sa ya ɗauki mataki nan-da-nan don ya taimaka mana.—Karanta Ishaya 63:9.
4. Mene ne labaran wasu bayin Allah suka nuna mana game da shi?
4 Labaran bayin Allah sun nuna mana yadda yake ji idan ya ga bayinsa suna kuka, da yadda yake taimaka musu. Labarin Hannatu da Dauda da kuma Sarki Hezekiya ya nuna haka. Bari mu bincika labarinsu mu ga mene ne ya sa su kuka? Ta yaya Jehobah ya taimaka musu? Kuma ta yaya labarinsu zai taimaka mana idan muna cikin damuwa, ko an ci amanarmu, ko kuma muna ganin kamar ba mu da mafita?
HAWAYE DON TSANANIN DAMUWA
5. Yaya matsalolin Hannatu suka sa ta ji?
5 Hannatu ta yi fama da matsalolin da suka sa ta cikin damuwa sosai har ta yi ta kuka. Ɗaya daga ciki matsalolin shi ne, Hannatu tana da kishiya mai suna Feninna kuma ta tsani Hannatu sosai. Ban da haka, Hannatu ba ta haifuwa, amma kishiyar tana da yara da yawa. (1 Sam. 1:1, 2) Feninna ta yi ta tsokanarta don ba ta haifuwa. Babu wanda zai ji daɗi idan ya shiga irin halin da Hannatu ta shiga. Abin ya dame ta sosai har “ta yi ta kuka ta ƙi cin abinci,” don tsananin “ɓacin zuciya.”—1 Sam. 1:6, 7, 10.
6. Mene ne Hannatu ta yi don ta ji sauƙi?
6 Mene ne Hannatu ta yi don ta ji sauƙi? Wani abin da ta yi shi ne, ta je ta bauta ma Jehobah a tentinsa. Da ta isa wurin, sai ta soma yin “adduꞌa tana kuka mai zafi,” wataƙila kusa da kofar tentin ne ta yi hakan. Ta roƙi Jehobah cewa: “Ka dubi wahalar baiwarka … ka tuna da ni.” (1 Sam. 1:10b, 11) Hannatu ta gaya wa Jehobah dukan damuwarta a cikin adduꞌa. Da Jehobah ya ji kukanta, shi ma ya damu, domin yana ƙaunarta sosai kuma yana so ya taimake ta!
7. Ta yaya Hannatu ta amfana da ta gaya wa Jehobah damuwarta?
7 Bayan da Hannatu ta gaya wa Jehobah abin da ke damunta kuma Eli Babban Firist ya tabbatar mata cewa Jehobah zai biya bukatarta, yaya ta ji? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sai ta tafi ta ci abinci, ba ta sāke yin baƙin ciki kuma ba.” (1 Sam. 1:17, 18) Ko da yake yanayinta bai canja ba, ta ji sauƙi. Tana da tabbaci cewa Jehobah ya fahimce ta da matsalolinta kuma zai taimaka mata. Abin da Jehobah ya yi ke nan. Ya ji kukanta kuma ya taimaka mata ta haifi ɗa.—1 Sam. 1:19, 20; 2:21.
8-9. Bisa ga Ibraniyawa 10:24, 25, me ya sa zai dace mu yi iya ƙoƙarinmu mu je taro? (Ka kuma duba hoton.)
8 Darasin. Mai yiwuwa kai ma kana fama da matsalolin da suke sa ka damuwa sosai. Wataƙila wani danginka ko abokinka ne ya rasu. Irin abin nan yakan sa mutum ya so kasancewa shi kaɗai. Amma ka tuna cewa da Hannatu ta je inda ake bauta ma Jehobah, Jehobah ya ƙarfafa ta. Kai ma idan ka yi ƙoƙari ka je taro, Jehobah zai ƙarfafa ka. (Karanta Ibraniyawa 10:24, 25.) A taronmu akan bayyana mana nassosin da suke ƙarfafa mu. Ta hakan ne Jehobah yake taimaka mana mu daina tunani a kan abubuwan da suke sa mu baƙin ciki. Hakan zai sa mu ji sauƙi, ko da yanayinmu bai canja ba nan tāke.
9 Ƙari ga haka, idan muka je taro za mu yi cuɗanya da ꞌyanꞌuwan da suke ƙaunarmu, kuma kalamansu da ke nuna cewa suna tausaya mana za su iya ƙarfafa mu. (1 Tas. 5:11, 14) Abin da ya faru da wani majagaba na musamman ke nan da matarsa ta rasu. Ɗanꞌuwan ya ce: “Wani lokaci nakan yi kuka sosai, don haka nakan je inda babu kowa. Amma nakan sami ƙarfafa idan na je taro. Maganganun alheri da ꞌyanꞌuwa suke gaya min suna sa hankalina ya kwanta. Ko da na damu sosai, ina jin sauƙi idan na halarci taro.” Jehobah yana ƙarfafa mu ta wurin ꞌyanꞌuwanmu maza da mata a taronmu.
10. Ta yaya za mu bi misalin Hannatu idan muna cikin damuwa?
10 Da Hannatu ta yi adduꞌa kuma ta gaya wa Jehobah damuwarta, ta ji sauƙi. Kai ma ka danƙa ma Jehobah dukan damuwarka cikin adduꞌa, da tabbacin cewa zai ji ka. (1 Bit. 5:7) Akwai wata ꞌyarꞌuwa da ꞌyan fashi da makami suka kashe maigidanta. ꞌYarꞌuwar ta ce: “Abin ya dame ni sosai, har na ji kamar ba zan sake yin farin ciki a rayuwata ba. Amma duk saꞌad da na yi adduꞌa ga Jehobah nakan ji sauƙi. Shi Ubana ne kuma yana ƙaunata sosai. Wani lokaci nakan rasa yadda zan gaya masa yadda nake ji, amma yakan fahimce ni. Idan na damu sosai kuma ina jin tsoro, nakan roƙe shi ya ba ni salama. Sai in ji hankalina ya kwanta kuma na sami ƙarfin jimrewa.” Duk saꞌad da ka gaya wa Jehobah damuwarka, shi ma zai damu don ya san irin zafin da kake ji a ranka. Ko da matsalar ba ta ƙare ba, Jehobah zai ƙarfafa ka kuma zai ba ka kwanciyar hankali. (Zab. 94:19; Filib. 4:6, 7) Yana ganin duk ƙoƙarin da kake yi don ka bauta masa, kuma zai ba ka lada.—Ibran. 11:6.
HAWAYE DON AN CI AMANANRMU
11. Yaya Dauda ya ji sakamakon muguntar da wasu suka yi masa?
11 Akwai abubuwa da yawa da suka faru a rayuwar Dauda da suka sa shi kuka. Mutane da yawa sun tsane shi, kuma wasu da suke kusa da shi sun ci amanarsa. (1 Sam. 19:10, 11; 2 Sam. 15:10-14, 30) Akwai lokacin da ya ce: “Na gaji tilis saboda baƙin ciki, kowane dare gadona yakan jiƙe saboda kukana, matashin kaina yakan jiƙe sharaf da hawaye.” Me ya sa shi cikin wannan halin? Ya ce: “Saboda … kukan da abokan gābana suka sa ni.” (Zab. 6:6, 7) Muguntar da mutane suka yi masa ce ta sa ya damu, har ya yi ta kuka.
12. Bisa ga Zabura 56:8, wane tabbaci Dauda yake da shi?
12 Dauda ya sha wahala sosai, amma duk da haka ya san cewa Jehobah yana ƙaunarsa. Ya ce: “Yahweh ya riga ya ji kukana.” (Zab. 6:8) Akwai wani lokaci kuma da ya faɗi wani abin ban-ƙarfafa. Kalmomin nan suna rubuce a Zabura 56:8. (Karanta.) Abin da ya faɗa ya nuna cewa Jehobah yana ƙaunarmu sosai kuma ya damu da mu. Dauda ya ce kamar Jehobah yana auna hawayensa ne yana ajiyewa, ko yana rubuta su a wani littafi. Dauda bai yi shakkar cewa Jehobah yana ganin damuwarsa kuma yana tunawa da shi ba. Dauda ya tabbata cewa Jehobah ya san matsalar da yake ciki kuma ya san yadda abin yake damunsa.
13. Idan aka ci amanarmu, me ya kamata mu tuna? (Ka kuma duba hoton.)
13 Darasin. An taɓa cin amanarka kuma hakan ya dame ka? Wataƙila kana baƙin ciki domin wadda ko wanda kike so ki aura ya rabu da ke. Ko mijinki ko matarka ta bar ka, ko kuma wani da kake ƙauna ya daina bauta wa Jehobah. Akwai wani Ɗanꞌuwa da matarsa ta yi zina kuma ta bar shi. Ɗanꞌuwan ya ce: “Na ɗauka mafarki nake yi. Na ji kamar ba ni da wani amfani, kuma na dinga fushi da baƙin ciki.” Idan kai ma kana fama don wani ya ci amanarka ko ya yi abin da ba ka zata zai yi ba, ka tuna cewa Jehobah yana tare da kai. Ɗanꞌuwan da muka ambata dazu ya ce: “Mutane za su iya cin amanarmu, amma Jehobah ba zai taɓa barin mu ba. Ko da me ya faru, yana tare da mu muddin mun riƙe amincinmu.” (Zab. 37:28) Ƙari ga haka, ka tuna cewa babu wanda yake ƙaunarmu kamar Jehobah. Idan aka ci amanarka, za ka ji zafi sosai kam, amma hakan ba ya rage darajarka a gun Jehobah. (Rom. 8:38, 39) Gaskiyar ita ce, ko da mene ne wani ko wata ta yi maka, Ubanmu na sama yana ƙaunar ka.
14. Wane abin ƙarfafa ne yake Zabura 34:18?
14 Idan an ci amanarmu, abin da ke Zabura 34:18 (Karanta) zai ƙarfafa mu. Wani littafin bincike ya ce “waɗanda an karya musu ƙarfin gwiwa” sukan ji kamar tasu ta ƙare. Ta yaya Jehobah yake taimaka wa irin mutanen nan? Jehobah yakan kusace su. Yakan riƙe su kamar yadda uba ko uwa takan riƙe ɗanta idan yana kuka kuma ta rarrashe shi. Da zarar an ɓata mana rai ko muna ganin ba mu da amfani, yana marmarin taimaka mana. Ban da haka ma, ya yi mana alkawura da dama da idan muka tuna da su, za mu sami ƙarfin jimrewa.—Isha. 65:17.
HAWAYE DON MUNA GANIN BA MU DA MAFITA
15. Wane yanayi ne Sarki Hezekiya ya shiga da ya sa shi kuka?
15 Da Sarki Hezekiya yake shekara 39, ya yi rashin lafiya sosai, kuma annabi Ishaya ya gaya masa cewa zai mutu sakamakon rashin lafiyar. (2 Sar. 20:1) Abin ya yi kamar Sarki Hezekiya bai da mafita. Ya damu sosai kuma ya yi ta kuka. Sai ya roƙi Jehobah ya taimake shi.—2 Sar. 20:2, 3.
16. Mene ne Jehobah ya yi da ya ji kukan Hezekiya?
16 Jehobah ya ji kukan Hezekiya, ya tausaya masa, kuma ya ce: “Na ji adduꞌarka, na kuma ga hawayenka. Hakika zan warkar da kai.” Jehobah ya sa annabi Ishaya ya gaya masa cewa zai ƙara masa tsawon kwanaki, kuma zai ceci Urushalima daga hannun Assuriyawa.—2 Sar. 20:4-6.
17. Ta yaya Jehobah zai taimaka mana idan muna fama da rashin lafiya? (Zabura 41:3) (Ka kuma duba hoton.)
17 Darasin. Idan kana fama da wani rashin lafiya da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, ka gaya wa Jehobah kome. Zai saurare ka ko da kana kuka ne. Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana da cewa “Uba mai yawan tausayi, Allah wanda yake yi mana kowace irin taꞌaziyya,” zai ƙarfafa mu ko da wane hali muke ciki. (2 Kor. 1:3, 4) A yau, mun san cewa Jehobah ba zai cire dukan matsalolinmu ba, amma a koyaushe zai taimake mu. (Karanta Zabura 41:3.) Zai yi amfani da ruhunsa ya ba mu ƙarfin jimrewa, da hikima, da kuma kwanciyar hankali. (K. Mag. 18:14; Filib. 4:13) Ya kuma ce a-kwana-a-tashi, ba wanda zai ce yana ciwo. Haka ma abin ban-ƙarfafa ne.—Isha. 33:24.
18. Wace aya ce ta taɓa ƙarfafa ka saꞌad da kake cikin hali mai wuya sosai? (Ka duba akwatin nan, “ Kalmomi Masu Sanyaya Zuciya da Za Su Ƙarfafa Mu.”)
18 Abin da Jehobah ya gaya wa Hezekiya ya ƙarfafa shi. Mu ma idan muka karanta Kalmar Allah, za ta ƙarfafa mu. Jehobah ya sa an rubuta kalmomi masu sanyaya zuciya a Kalmarsa don amfaninmu a lokacin da muke damuwa. (Rom. 15:4) Wata ꞌyarꞌuwa a Afirka ta Yamma tana yawan kuka domin famar da take yi da cutar kansa. Ta ce: “Wani nassin da ke ƙarfafa ni shi ne Ishaya 26:3. Wani lokaci ba za mu iya magance matsalolinmu ba, amma ayar nan ta tabbatar min da cewa Jehobah zai ba ni kwanciyar hankali da ƙarfin jimrewa.” Akwai wata ayar da ta taɓa ƙarfafa ka saꞌad da ka shiga halin da ya yi kamar babu mafita?
19. Wane alkawari ne Jehobah ya yi mana?
19 Abubuwan da za su sa mu kuka za su yi ta ƙaruwa ne, domin ƙarshen duniyar nan ta yi kusa. Amma kamar yadda muka gani a labarin Hannatu, da Dauda, da kuma Sarki Hezekiya, Jehobah yana ganin kukan da muke yi kuma abin yana damunsa. Yana ƙaunar mu don ƙoƙarin da muke yi mu bauta masa, kuma ba zai manta da wahalarmu ba. Don haka, idan muka shiga hali mai wuya, mu gaya masa kome cikin adduꞌa. Kada mu bar wani abu ya hana mu kusantar ꞌyanꞌuwanmu a ikilisiya, domin suna ƙaunarmu. Kuma bari kalmomi masu sanyaya zuciya da ke Kalmar Allah su ƙarfafa mu. Ba shakka idan muka jimre kuma muka yi nufin Jehobah, zai albarkace mu. Wani alkawari mai ban-shaꞌawa da ya yi mana shi ne cewa, ba da daɗewa ba zai share mana dukan hawaye da muke yi domin tsananin damuwa, ko cin amana, ko kuma yanayi mai wuya da muka rasa mafita. (R. Yar. 21:4) A lokacin ba za mu sake zub da hawaye don baƙin ciki ba, sai dai don farin ciki.
WAƘA TA 4 “Jehobah Makiyayina Ne”