Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 48

WAƘA TA 97 Kalmar Allah Za Ta Sa Mu Rayu

Me Muka Koya Daga Yadda Yesu Ya Ciyar da Mutane da Burodi?

Me Muka Koya Daga Yadda Yesu Ya Ciyar da Mutane da Burodi?

“Ni ne abinci mai ba da rai, wanda ya zo wurina ba zai ƙara jin yunwa ba.”YOH. 6:35.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga darussan da za mu koya daga Yohanna sura 6. A wurin, Yesu ya ciyar da duban mutane da burodi biyar da kifi biyu kawai.

1. Yaya mutane a zamanin dā suke ɗaukan burodi?

 LITTAFI MAI TSARKI ya nuna cewa burodi abinci ne da mutane suke ci sosai a zamanin dā. (Far. 14:18; Luk. 4:4) Burodi yana da muhimmanci sosai a lokacin har ma a wasu lokuta idan ana so a ce abinci, sai a ce burodi kawai. (Mat. 6:11) A muꞌujizai biyu da Yesu ya yi da aka fi sani, ya yi amfani da burodi. (Mat. 16:9, 10) Ɗaya daga cikinsu yana Yohanna sura 6. Yayin da muke bincika wannan labarin, za mu koyi wasu darussa da za su amfane mu a yau.

2. Wane yanayi ne ya sa dubban mutane suka bukaci abinci?

2 Bayan da mazannin Yesu suka gama waꞌazi, sai Yesu ya sa sun shiga kwalekwale tare da shi, suka kama hanya za su haye Tekun Galili, don su je su huta. (Mar. 6:7, 30-32; Luk. 9:10) Da suka haye, sai suka je wani wuri kusa da Betsaida, inda ba kowa. Amma ba da daɗewa ba, dubban mutane suka zo wurin suka same su. Yesu ya ƙi kula su ne? Aꞌa. Ya soma koya musu game da Mulkin Allah, kuma ya warkar da waɗanda ba su da lafiya. Da yake yamma ta yi sosai, almajiransa sun soma tunanin inda za a sami abin da za a ba mutanen su ci. Mai yiwuwa wasunsu suna da ɗan abin da za su ci, amma yawancinsu suna bukatar su nemi abin da za su ci. (Mat. 14:15; Yoh. 6:4, 5) Me Yesu zai yi?

YESU YA YI ABIN BAN MAMAKI

3. Mene ne Yesu ya gaya wa manzanninsa su yi wa mutanen? (Ka kuma duba hoton.)

3 Yesu ya gaya wa manzanninsa cewa: “Ba lallai su tafi ba, ku ba su wani abu su ci.” (Mat. 14:16) Yin hakan bai da sauƙi domin mazajen da suke wurin kawai ma 5,000 ne. Kuma idan aka haɗa da mata da yara, wataƙila za su kai mutane 15,000. (Mat. 14:21) Andarawus ya ce: “Ga wani ɗan yaro nan da dunƙulen burodi biyar na garin bale da kuma kifi biyu. Amma me waɗannan za su yi wa mutane masu yawa haka?” (Yoh. 6:9) A lokacin, mutane suna yawan cin burodi da aka yi da garin wani hatsi mai suna bale, kuma wataƙila ƙananan kifi biyun irin wanda ake barbaɗa masa gishiri ne a busar. Amma burodi da kifi na wurin yaron ba za su ishe mutane da yawa haka ba!

Bayan da Yesu ya koya wa mutanen game da Jehobah, ya ba su abinci su ci (Ka duba sakin layi na 3)


4. Me za mu iya koya daga Yohanna 6:11-13? (Ka kuma duba hotunan.)

4 Yesu ya so ya yi wa mutanen alheri, saboda haka ya gaya musu su zauna ƙungiya-ƙungiya a kan ciyawa. (Mar. 6:39, 40; karanta Yohanna 6:11-13.) Bayan haka, Yesu ya gode wa Ubansa don burodin da kifin. Yadda Yesu ya gode wa Allah ya dace, domin shi ne Tushin abincin. Hakan ya koya mana cewa yana da muhimmanci mu yi adduꞌa kafin mu ci abinci, ko da a ina ne muke. Bayan da Yesu ya yi adduꞌa, sai ya gaya wa almajiransa su ba wa mutanen abincin. Dukan mutanen sun ci sun ƙoshi, har ma ya rage. Yesu bai so a zubar da abincin da ya rage ba domin za a iya cinsa daga baya. Sai ya gaya wa almajiransa su tattara shi. Wannan misali mai kyau ne Yesu ya kafa. Idan ku iyaye ne, za ku iya yin amfani da wannan labarin ku koya wa yaranku muhimmancin yin adduꞌa kafin a ci abinci, da yi wa mutane alheri, da kuma bayarwa hannu sake kamar Yesu.

Ka tambayi kanka, ‘Ina adduꞌa kafin in ci abinci kamar yadda Yesu ya yi?’ (Ka duba sakin layi na 4)


5. Mene ne mutanen suka so su yi da suka ga abin ban mamaki da Yesu ya yi, kuma mene ne Yesu ya yi?

5 Yadda Yesu ya koyar da mutanen da abubuwan ban mamaki da ya yi, ya burge su sosai. Wataƙila sun ɗauka cewa Yesu ne annabi na musamman da Musa ya ce Allah zai turo musu. (M. Sha. 18:15-18) Hakan ya sa sun ga kamar idan Yesu ya zama sarkinsu, zai sa dukan mutane a Israꞌila su sami abinci. Saboda haka, mutanen suka soma shirin “ɗauke [Yesu] ƙarfi da yaji su naɗa shi sarki.” (Yoh. 6:14, 15) Da a ce hakan ya faru, da Yesu zai saka hannu a siyasar Yahudawa da ke ƙarƙashin mulkin Roma. To me ya yi? Littafi Mai Tsarki ya ce Yesu “ya sāke komawa kan babban tudu shi kaɗai.” Duk da cewa mutane sun matsa masa, Yesu ya ƙi ya saka hannu a harkokin siyasa. Me hakan ya koya mana?

6. Ta yaya za mu yi koyi da Yesu? (Ka kuma duba hoton.)

6 A yau ƙila mutane ba za su ce mana mu ciyar da su a hanya mai ban mamaki, ko mu warkar da marasa lafiya, ko kuma su ce mu zama sarki ba. Amma za su iya cewa mu zaɓi wani mai mulki da suke ganin zai kawo sauƙin abubuwa, ko su ce mu goyi bayansa. A irin wannan yanayi, zai dace mu bi misalin Yesu. Ya ƙi ya saka hannu a harkokin siyasa, kuma daga baya ya ce: “Mulkina ba iri na duniya ba ne.” (Yoh. 17:14; 18:36) A yau, muna bukatar mu bi misalin Yesu ta wajen goyon bayan Mulkin Allah, da yin waꞌazinsa, da kuma yin adduꞌa cewa Mulkin ya zo. (Mat. 6:10) Amma labarin bai ƙare ba! Akwai wasu darussa kuma da za mu iya koya daga abin ban mamaki da Yesu ya yi na ciyar da mutane da burodi.

Yesu bai saka hannu a siyasa ba, mu ma kada mu yi hakan (Ka duba sakin layi na 6)


“MAꞌANAR CIYAR DA MUTANE DUBU BIYAR NAN”

7. Wane abin ban mamaki ne Yesu ya yi, kuma yaya almajiransa suka ji da suka ga haka? (Yohanna 6:16-20)

7 Bayan da Yesu ya ciyar da mutanen, ya gaya wa almajiransa su shiga kwalekwale su bar wurin su koma Kafarnahum. Saꞌan nan shi ya je kan dutse don kada mutanen su gan shi kuma su naɗa shi sarki. (Karanta Yohanna 6:16-20.) Da almajiransa suke kan tafiya, sai aka soma guguwa. Ana haka, sai Yesu ya zo wurin da suke, yana tafiya a kan ruwa. Ya kuma gaya wa manzo Bitrus shi ma ya yi tafiya a kan ruwan. (Mat. 14:22-31) Da zarar Yesu ya shiga kwalekwalen, sai guguwar ta tsaya. Hakan ya ba wa almajiransa mamaki. Sai suka ce: “Gaskiya, kai Ɗan Allah ne.” a (Mat. 14:33) Ka lura cewa lokacin da Yesu ya ciyar da dubban jamaꞌa da burodi, ba su yi irin wannan furucin ba. Sai bayan da suka gan shi ya yi tafiya a kan ruwa. Markus ya ce: “Mamaki ya kama [almajiransa] ƙwarai. Saboda ba su san mene ne maꞌanar ciyar da mutane dubu biyar nan ba, gama zuciyarsu ba ta fahimci maꞌanar ba.” (Mar. 6:50-52) Almajiransa ba su fahimci cewa Jehobah ya ba wa Yesu ikon yin abubuwan ban mamaki sosai ba. Bayan haka, sai Yesu ya sake yin zancen lokacin da ya ciyar da dubban mutane. Wane darasi ya koya mana a wannan karo?

8-9. Me ya sa mutanen suke neman Yesu? (Yohanna 6:26, 27)

8 Abin da ya fi muhimmanci a gun mutanen nan da Yesu ya ciyar da su, shi ne yadda za su sami biyan bukatunsu. Me ya nuna hakan? Washegari, sun ga cewa Yesu da almajiransa sun tafi. Sai suka shiga jiragen ruwa da suka zo daga Tibariya, suka kama hanya zuwa Kafarnahum domin su nemi Yesu. (Yoh. 6:22-24) Me ya sa? Suna so su ƙara koya game da Mulkin Allah ne? Aꞌa. Suna son Yesu ya sake ciyar da su ne. Ta yaya muka san haka?

9 Da suka sami Yesu kusa da Kafarnahum, sai Yesu ya gaya musu cewa suna nemansa ne kawai domin ya sake ciyar da su. Yesu ya ƙara da cewa ko da yake sun ‘ci burodi nan sun ƙoshi,’ abinci ne “mai lalacewa.” Saboda haka ya gaya musu su yi “aiki a kan abincin da zai dawwama zuwa ga rai na har abada.” (Karanta Yohanna 6:26, 27.) Mutanen sun yi mamaki sosai da suka ji cewa akwai abincin da zai iya ba su rai na har abada! Wane irin abinci ne ke nan, kuma ta yaya za su sami abincin?

10. Mene ne mutanen suke bukatar su yi don su sami rai na har abada?

10 Mutanen sun so su san abin da za su yi don su sami irin wannan abincin. Wataƙila sun zata Yesu zai ce musu su bi Dokar Musa. Amma sai Yesu ya gaya musu cewa: “Wannan shi ne abin da Allah yake so ku yi, wato ba da gaskiya ga wanda ya aiko.” (Yoh. 6:28, 29) Hakika, idan suna so su “sami rai na har abada,” suna bukatar su ba da gaskiya ga wanda Allah ya aiko, kuma su nuna hakan ta ayyukansu. Yesu ya taɓa gaya musu hakan. (Yoh. 3:16-18, 36) Kuma wannan ba shi ne karo na ƙarshe da ya yi wannan zancen ba.—Yoh. 17:3.

11. Ta yaya mutanen suka nuna cewa sun fi damuwa ne da abinci? (Zabura 78:24, 25)

11 Mutanen ba su yarda cewa wajibi ne su ba da gaskiya ga Yesu ba. Sun ce: “Wace alamar ban mamaki ce za ka yi domin mu gani mu ba da gaskiya gare ka?” (Yoh. 6:30) Sun kuma ce a zamanin Musa, Allah ya ba kakaninsu manna, kuma abincin da suka ci kullum ke nan. (Neh. 9:15; karanta Zabura 78:24, 25.) Bayaninsu ya nuna cewa yadda za su sami abinci ne damuwarsu. Kuma saꞌad da Yesu ya yi magana game da “abinci na gaskiya daga sama,” wato wanda zai ba su rai na har abada, ba su ma nemi su san ainihin abin da yake nufi ba. (Yoh. 6:32) Sun mai da hankali gabaki ɗaya a kan abinci, har ma da Yesu yake ƙoƙarin gaya musu yadda za su sami rai na har abada, ba su saurare shi ba. Mene ne wannan labarin ya koya mana?

ABIN DA YA FI MUHIMMANCI

12. Mene ne abu mafi muhimmanci a rayuwarmu, kuma ta yaya Yesu ya nuna hakan?

12 Darasi na musamman da muka koya a Yohanna sura 6 shi ne cewa: Yin biyayya da kuma kasancewa da dagantaka mai kyau da Allah ne abu mafi muhimmanci a rayuwarmu. Yesu ya nuna cewa hakan gaskiya ne a lokacin da Shaiɗan ya jarabce shi. Ya ce: “Ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga wurin Allah.” (Mat. 4:3, 4) Kuma a koyarwar da ya yi a kan dutse, ya faɗi amfanin zama aminin Jehobah. (Mat. 5:3) Saboda haka, zai dace mu tambayi kanmu, ‘Yadda nake rayuwa ya nuna cewa na fi mai da hankali ga kasancewa da dangantaka mai kyau da Allah ne, ko ga biyan bukatuna ne?’

13. (a) Me ya sa ba laifi ba ne mu ci abinci mu ji daɗi? (b) Wane gargaɗi ne Bulus ya bayar? (1 Korintiyawa 10:6, 7, 11)

13 Ba laifi ba ne mu yi adduꞌa game da abubuwan da muke bukata kuma mu ji daɗinsu idan muka samu. (Luk. 11:3) Yin aiki tuƙuru yana sa ‘mu ci, mu sha,’ mu ji daɗi, domin “daga wurin Allah” ne. (M. Wa. 2:24; 8:15; Yak. 1:17) Duk da haka, wajibi ne mu kula don kada neman abin duniya ya zama abu mafi muhimmanci a rayuwarmu. Manzo Bulus ma ya yi wa Kiristoci wannan gargaɗin. Ya ambaci abubuwa marar kyau da Israꞌilawa suka yi a daji, har da abin da ya faru a lokacin da suke kusa da Tudun Sinai. Ya ce ma Kiristocin kada su so mugayen abubuwa yadda Israꞌilawa suka yi. (Karanta 1 Korintiyawa 10:6, 7, 11.) Jehobah ya yi wa Israꞌilawan tanadin abinci a hanya mai ban mamaki. Amma da yake abin da za su ci ne kawai damuwarsu, abincin ya zama mugun abu a gare su, wato ya zama musu dalilin yin zunubi. (L. Ƙid. 11:4-6, 31-34) Ban da haka ma, a lokacin da suka bauta wa wani siffar ɗan bijimi, sun nuna cewa sun fi damuwa ne da abin da za su ci su sha. Kuma jin daɗin rayuwarsu ne suke so, ba yin biyayya ga Jehobah ba. (Fit. 32:4-6) Bulus ya ambaci wannan labarin ne don ya zama kashedi ga Kiristoci da suke rayuwa kusa da lokacin da za a halaka Urushalima da haikalinta a shekara ta 70 bayan haihuwar Yesu. Mu ma muna rayuwa kusa da ƙarshen wannan zamanin. Don haka yana da muhimmanci mu bi gargaɗin Bulus.

14. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da abinci a aljanna?

14 Saꞌad da Yesu ya koya mana mu roƙi Allah ya “ba mu abincin yau da kullum,” ya kuma ce mu yi adduꞌa ‘a yi nufinsa a cikin duniya, kamar yadda ake yinsa a cikin sama.’ (Mat. 6:9-11) Yaya rayuwa za ta kasance a lokacin? Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa nufin Allah ne a sami abinci mai kyau a duniya. Ishaya 25:6-8, sun ce mutane za su ji daɗin cin abinci mafi kyau a ƙarƙashin Mulkin Allah. Kuma Zabura 72:16 ta ce za a “sami hatsi a yalwace a ƙasar,” har “amfanin gona ya rufe kan tuddai.” Wataƙila kana marmarin ganin lokacin da za ka yi amfani da hatsin nan ka yi irin burodin da ka fi so, ko ka gwada dafa irin abincin da ba ka taɓa dafawa ba? Ƙari ga haka, za ka iya shuka naka gonar inabi, kuma ka ci moriyar ꞌyaꞌyan inabin. (Isha. 65:21, 22) Ba kai kaɗai ba ne za ka mori wannan albarkar, dukan mutane da ke rayuwa a lokacin ne.

15. Me za a koya wa waɗanda aka tayar daga mutuwa? (Yohanna 6:35)

15 Karanta Yohanna 6:35. Ka kuma sake yin tunani game da mutanen nan da Yesu ya ciyar da su da kifi da burodi. Ko da yake da yawa daga cikinsu ba su ba da gaskiya ga Yesu ba, mai yiwuwa za ka haɗu da wasu daga cikinsu a lokacin da za a ta da matattu. (Yoh. 5:28, 29) A lokacin za su bukaci su koyi maꞌanar abin da Yesu ya faɗa saꞌad da ya ce: “Ni ne abinci mai ba da rai, wanda ya zo wurina ba zai ƙara jin yunwa ba.” Kuma za su bukaci su ba da gaskiya cewa Yesu ya ba da ransa dominsu. A lokacin, za a koyar da dukan waɗanda aka tayar daga mutuwa, da yaran da za a haifa, game da Jehobah da kuma nufinsa. Koyar da mutanen nan zai sa mu farin ciki sosai! Babu shakka, taimaka wa mutane su kasance da dagantaka mai kyau da Jehobah zai sa mu farin ciki fiye da duk wani abinci da za mu ci a sabuwar duniya.

16. Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

16 Mun ɗan tattauna labarin da ke Yohanna sura 6, amma akwai abubuwa da dama da Yesu ya koyar game da “rai na har abada.” Fahimtar abin da Yesu ya faɗa yana da muhimmanci ga Yahudawan da yake magana da su, har da mu ma. Shi ya sa a talifi na gaba, za mu ci-gaba da tattauna Yohanna sura 6.

WAƘA TA 20 Ka Ba da Ɗanka Mai Daraja

a Don samun ƙarin bayani game da wannan labari mai daɗi, ka duba littattafan nan, Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu, shafi na 185, da kuma Jesus—The Way, the Truth, the Life, shafi na 131.