TALIFIN NAZARI NA 49
WAƘA TA 147 Alkawarin Rai Na Har Abada
Me Za Ka Yi don Ka Sami Rai na har Abada?
“Duk wanda yake duban Ɗan, yake kuma gaskatawa da shi [zai sami] rai na har abada.”—YOH. 6:40.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga yadda shafaffu da kuma waɗansu tumaki za su amfana daga hadayar da Yesu ya yi.
1. Me ya sa wasu suke gani kamar ba zai yiwu mutane su rayu har abada ba?
MUTANE da yawa suna lura da irin abincin da suke ci kuma suna motsa jiki a-kai-a-kai don su kula da lafiyarsu. Duk da haka, sun san cewa a-kwana-a-tashi, za su tsufa kuma su mutu. Don haka, suna ganin ba zai yiwu mutum ya ci-gaba da rayuwa har abada ba. Amma Yesu ya ce zai yiwu mutane su rayu “har abada,” kamar yadda aka ambata a Yohanna 3:16 da sura 5:24.
2. Mene ne Yesu ya ce game da rai na har abada a Yohanna sura 6? (Yohanna 6:39, 40)
2 Akwai ranar da Yesu ya yi wani abin ban mamaki, ya ciyar da dubban mutane da burodi da kifi. a Abin da ya yi ya burge mutanen, amma abin da ya gaya wa waɗanda suka biyo shi zuwa Kafarnahum washegari ne ya fi burgewa. A wannan wurin, kusa da bakin Tekun Galili, Yesu ya gaya musu cewa zai ta da waɗanda suka mutu kuma za su iya rayuwa har abada. (Karanta Yohanna 6:39, 40.) Wannan tabbaci ne cewa za a ta da mutane da yawa da suka mutu, kuma da kai da waɗanda kake ƙauna za ku iya rayuwa har abada. Abokanka da danginka da suka mutu ma za su amfana daga wannan abin da Yesu ya ce zai yi. Amma akwai abin da Yesu ya faɗa a Yohanna sura 6 da ya yi wa mutane wuyar ganewa. Bari mu bincika abin da ya ce.
3. Bisa ga Yohanna 6:51, mene ne Yesu ya ce game da kansa?
3 Burodin da Yesu ya ciyar da jamaꞌar da shi ya sa sun tuna da yadda Jehobah ya ciyar da kakanninsu da manna. Littafi Mai Tsarki ma ya ce mannar abinci ne ko burodi “daga sama.” (Zab. 105:40; Yoh. 6:31) Sai Yesu ya yi amfani da mannar don ya koya musu wani abu mai muhimmanci. Ya gaya musu cewa kakanninsu sun ci manna amma duk da haka sun mutu. (Yoh. 6:49) Sai ya ce shi ne “abinci na gaskiya daga sama,” da “abincin Allah,” da kuma “abinci mai ba da rai.” (Yoh. 6:32, 33, 35) Bayan haka sai ya gaya musu yadda shi ya fi mannar da kakanninsu suka ci. Ya ce: “Ni ne abincin rai da ya sauko daga sama. Duk wanda ya ci wannan abinci, zai rayu har abada.” (Karanta Yohanna 6:51.) Abin da Yesu ya faɗa ya ɓata wa Yahudawan rai. Sun kasa fahimtar abin da ya sa Yesu ya ce shi “abinci” ne daga sama, har ma cewa ya fi mannar da Allah ya ba wa kakanninsu. Sai Yesu ya ƙara da cewa: “Wannan abinci naman jikina ne.” Me Yesu yake nufi? Yana da muhimmanci mu fahimci wannan batun, domin shi ne ya nuna yadda mu da waɗanda muke ƙauna za mu sami rai na har abada. Yanzu bari mu ga abin da yake nufi.
ABINCI MAI BA DA RAI DA KUMA NAMAN JIKINSA
4. Me ya sa abin da Yesu ya faɗa ya ba wa wasu mutane mamaki?
4 Wasu mutanen sun yi mamaki sosai da Yesu ya ce naman jikinsa ne abincin da ya kamata su ci, kuma shi ne zai “bayar domin duniya ta sami rai.” Me ya sa? Domin a ganinsu, Yesu yana so ya ba su naman jikinsa ne su ci. (Yoh. 6:52) Sai Yesu ya faɗi abin da ya ƙara ba su mamaki. Ya ce: “In ba kun ci naman jikin Ɗan Mutum kun kuma sha jininsa ba, ba ku da rai a cikinku ke nan.”—Yoh. 6:53.
5. Me ya tabbatar mana cewa ba naman jikinsa da jininsa ne Yesu yake so Yahudawan su ci su sha ba?
5 Tun zamanin Nuhu, Allah ya haramta cin jini. (Far. 9:3, 4) Kuma Jehobah ya sake maimaita wannan dokar ga Israꞌilawa. Ya ce duk wanda ya ci jini, “za a kawar da shi,” wato za a kashe shi. (L. Fir. 7:27) Yesu ya ce bin dukan dokokin Allah yana da muhimmanci. (Mat. 5:17-19) Saboda haka, ba zai yiwu ya ba ma Yahudawan naman jikinsa da kuma jininsa su ci kuma su sha ba. Ba shakka, wani abu dabam ne Yesu yake so ya koya musu a kan yadda za su sami “rai na har abada.”—Yoh. 6:54.
6. Ta yaya muka san cewa abin da Yesu ya faɗa a Yohanna 6:53 misali ne?
6 Hakika misali ne Yesu yake yi a nan, kamar yadda ya gaya wa ꞌyar Samariyar nan cewa: “Duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi, ba zai ƙara jin ƙishi ba har abada. Ruwan da zan ba shi zai zama masa maɓuɓɓugar ruwa wadda take ɓulɓullowa zuwa ga rai na har abada.” (Yoh. 4:7, 14) b Yesu ba ya nufin cewa zai ba ta wani ruwa ta sha don ta sami rai na har abada. Misali ne kawai yake yi. Haka ma yake da lokacin nan da ya gaya wa mutane a Kafarnahum cewa za su rayu har abada idan suka ci naman jikinsa kuma suka sha jininsa.
BAMBANCIN DA KE TSAKANIN KALMOMIN YESU
7. Mene ne wasu suke cewa game da abin da Yesu ya faɗa a Yohanna 6:53?
7 Wasu mutane suna cewa ya kamata a bi abin da Yesu ya faɗa a Yohanna 6:53 a lokacin Jibin Maraice na Ubangiji, domin kalmomin da ya yi amfani da su a wuraren nan kusan ɗaya ne. (Mat. 26:26-28) Sun ce ya kamata duk wanda ya halarci Jibin Maraice na Ubangiji ya ci burodin kuma ya sha ruwan inabin. Hakan gaskiya ne? Mu ma muna yin wannan taron kowace shekara, kuma miliyoyin mutane suna zuwa taron. Don haka yana da muhimmanci mu san gaskiyar wannan batun. Bari mu ga bambancin da ke tsakanin abin da Yesu ya faɗa a Yohanna 6:53 da abin da ya faɗa a lokacin Jibin Maraice na Ubangiji.
8. Mene ne bambancin abin da Yesu ya faɗa a Yohanna 6:53 da wanda ya faɗa a lokacin Jibin Maraice na Ubangiji? (Ka kuma duba hotunan.)
8 Akwai bambanci tsakanin abin da Yesu ya faɗa a Yohanna 6:53 da wanda ya faɗa a lokacin Jibin Maraice na Ubangiji. Na ɗaya, lokaci da kuma wurin da ya yi maganar ba ɗaya ba ne. Maganar da ya yi a Yohanna 6:53-56, a Kafarnahum ne a yankin Galili, a shekara ta 32 bayan haihuwarsa. Kuma shekara ɗaya ke nan kafin Jibin Maraice na Ubangiji na farko da aka ci a Urushalima. Na biyu, mutanen da ya yi wa magana ba ɗaya ba ne. Yawancin mutanen da yake magana da su a yankin Galili sun mai da hankalinsu ga yadda za su sami abinci, fiye da koya game da Jehobah da Mulkinsa. (Yoh. 6:26) Shi ya sa da Yesu ya faɗi abin da ba su fahimta ba, sai suka daina sauraron sa. Har ma wasu almajiransa sun daina binsa. (Yoh. 6:14, 36, 42, 60, 64, 66) Amma waɗanda Yesu ya yi magana da su a lokacin Jibin Maraice na Ubangiji a shekara ta 33, manzaninsa 11 ne. Duk da cewa ba su fahimci abin da yake koya musu da kyau ba, ba su daina binsa ba. Ƙari ga haka, manzannin Yesu ba su taɓa yin shakka cewa shi ne Ɗan Allah wanda ya zo daga sama ba. (Mat. 16:16) Shi ya sa ya ce musu: “Ku ne kuka tsaya da aminci tare da ni a duk gwaje-gwajen da na sha.” (Luk. 22:28) Abubuwa biyun nan da muka tattauna kawai ma, sun nuna cewa abin da Yesu ya faɗa a Yohanna 6:53 ba game da Jibin Maraice na Ubangiji ba ne. Bari mu ga wasu dalilai kuma.
YADDA KAI MA ZA KA AMFANA
9. Da su wa Yesu yake magana a lokacin Jibin Maraice na Ubangiji?
9 A lokacin Jibin Maraice na Ubangiji, Yesu ya raba wa manzanninsa burodi marar yisti, kuma ya ce musu burodin yana wakiltar jikinsa. Saꞌan nan ya ba su ruwan inabi kuma ya ce yana wakiltar “jini na cikar yarjejeniyar” ko alkawari. (Mar. 14:22-25; Luk. 22:20; 1 Kor. 11:24) Maganar da ya yi game da alkawari tana da muhimmanci sosai. Me ya sa? Domin Yesu ya ce sabon alkawari ne, kuma an yi wa waɗanda za su yi mulki tare da shi ne wannan alkawarin, ba dukan mutane ba. (Ibran. 8:6, 10; 9:15) A lokacin, an kusa a shafe manzanninsa da ruhu mai tsarki don su shiga sabon alkawarin kuma su sami damar yin mulki tare da shi a sama, amma ba su fahimci abin da yake nufi sosai ba.—Yoh. 14:2, 3.
10. Wane bambanci ne kuma yake tsakanin abin da Yesu ya faɗa a lokacin Jibin Maraice na Ubangiji da kuma yankin Galili? (Ka kuma duba hoton.)
10 A lokacin Jibin Maraice na Ubangiji Yesu yana magana ne da waɗanda ake kira, “ƙaramin garke.” Manzanninsa 11 da suke tare da shi a wannan lokacin ne aka fara tattarawa cikin wannan garken. (Luk. 12:32) Su da sauran mutanen da za su shiga wannan garken za su ci burodin kuma su sha ruwan inabin. Su ne za su yi mulki tare da Yesu a sama. Hakika, wani bambanci da ke tsakanin abin da ya faɗa wa manzanninsa a lokacin Jibin Maraice na Ubangiji da kuma yankin Galili, shi ne cewa: Abin da Yesu ya faɗa a lokacin Jibin Maraice na Ubangiji game da mutane kaɗan ne, amma abin da ya faɗa a yankin Galili game da mutane da yawa ne.
11. Mene ne Yesu ya faɗa a yankin Galili da ya nuna cewa ba da mutane kaɗan yake ba?
11 Yawancin mutane da Yesu yake magana da su a yankin Galili a shekara ta 32, Yahudawa ne da suke so ya ba su abinci. Amma sai Yesu ya yi ƙoƙari ya taimaka musu su fahimci wani abin da ya fi abinci muhimmanci. Ya ambaci wani abin da zai ba su rai na har abada. Har Yesu ya gaya musu cewa a rana ta ƙarshe, za a ta da waɗanda suka mutu kuma za su iya rayuwa har abada. Ba game da mutane kaɗan ne Yesu yake magana a nan ba, akasin yadda ya yi a lokacin Jibin Maraice na Ubangiji. A maimakon haka, yana magana ne game da albarkun da dukan mutane za su iya samuwa. Shi ya sa ya ce: “Duk wanda ya ci wannan abinci, zai rayu har abada. Wannan abinci naman jikina ne, wanda zan bayar domin duniya ta sami rai.”—Yoh. 6:51. c
12. Su wane ne kaɗai za su sami rai na har abada?
12 Yesu ba ya nufin cewa kowa da kowa zai sami rai na har abada. Waɗanda suka “ci wannan abinci,” wato waɗanda suka nuna bangaskiyarsu gare shi ne kaɗai za su sami albarkar nan. Mutane da yawa a yau suna cewa sun ba da gaskiya ga Yesu kuma shi ne mai cetonsu. (Yoh. 6:29) Amma yin hakan bai isa ba, domin akwai waɗanda suka ba da gaskiya ga Yesu a yankin Galili kuma daga baya suka daina binsa. Me ya sa?
13. Mene ne mutum yake bukatar ya yi don ya zama mabiyin Yesu na gaske?
13 Yawancin mutanen nan a yankin Galili sun bi Yesu ne domin su sami abin da suke so. Suna so Yesu ya yi ta ba su abinci, ya warkar da su in suna rashin lafiya, kuma ya gaya musu abin da suke so su ji. Amma Yesu ya nuna musu cewa ba abin da ya kawo shi duniya ke nan ba. Abin da ya kawo shi duniya shi ne ya koya musu yadda za su zama mabiyansa na gaske. Suna bukatar su zo wurinsa, wato su saurare shi kuma su bi maganarsa.—Yoh. 5:40; 6:44.
14. Me za mu yi don mu amfana daga hadayar da Yesu ya yi da jikinsa da jininsa?
14 Yesu ya gaya wa jamaꞌar cewa zai ba da jikinsa da jininsa hadaya, kuma zai ba su damar yin rayuwa har abada. Amma don su sami wannan albarkar, yana da muhimmanci su gaskata da Yesu da hadayarsa, kuma su nuna hakan. Mu ma muna bukatar mu kasance da irin bangaskiyar nan. (Yoh. 6:40) Abin da Yesu ya faɗa a Yohanna 6:53 yana nufin cewa bangaskiyarmu ga hadayarsa ita ce za ta sa mu sami rai na har abada. Kuma duk wanda ya ba da gaskiya zai sami wannan ladar.—Afis. 1:7.
15-16. Waɗanne abubuwa masu muhimmanci ne muka koya a Yohanna sura 6?
15 A Yohanna sura 6, mun koyi abubuwa da yawa masu muhimmanci da kuma ban-ƙarfafa. Surar ta nuna cewa Yesu yana ƙaunar mutane sosai. Shi ya sa da yake yankin Galili, ya warkar da marasa lafiya, ya koya musu game da Mulkin Allah, kuma ya ba su abinci. (Luk. 9:11; Yoh. 6:2, 11, 12) Mafi muhimmanci ma, ya bayyana cewa shi ne “abinci mai ba da rai.”—Yoh. 6:35, 48.
16 Bai kamata waɗanda Yesu ya kira su “waɗansu tumaki” su ci burodi ko su sha ruwan inabi da ake bayarwa a lokacin Jibin Maraice na Ubangiji ba. (Yoh. 10:16) Amma duk da haka, su ma suna cin “abinci mai ba da rai.” Ta yaya? Ta wurin nuna bangaskiyarsu ga hadayar Yesu da albarkun da zai kawo mana. (Yoh. 6:53) Waɗanda suke cin burodin kuma suke shan ruwan inabin, suna nuna cewa da su aka yi sabon alkawari, kuma za su yi mulki tare da Yesu a sama. Don haka, ko da mu shafaffu ne ko waɗansu tumaki, za mu amfana sosai idan muka bi abin da ke Yohanna sura 6. Surar ta bayana muhimmancin nuna bangaskiyarmu ga hadayar Yesu, don ita ce za ta sa mu sami rai na har abada.
WAƘA TA 150 Mu Bi Allah Don Mu Sami Ceto
a An tattauna Yohanna 6:5-35 a talifin da ya gabata.
b Abin da Yesu yake nufi da ruwa a nan shi ne, tanadodin da Jehobah yake mana don mu sami rai na har abada.
c A Yohanna sura 6, an yi ta amfani da kalmomi kamar “duk wanda,” kuma hakan ya nuna cewa kowa ne zai iya samun rai na har abada.—Yoh. 6:35, 40, 47, 54, 56-58.