Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Su waye ne “malaꞌikun da aka zaɓa” da aka ambata a 1 Timoti 5:21?

Manzo Bulus ya rubuta wa Timoti, wanda shi ma dattijo ne, cewa: “A gaban Allah, da Almasihu Yesu, da kuma malaꞌikun da aka zaɓa, ina maka gargaɗi ka bi waɗannan umarnai ban da nuna bambanci ko nuna cewa ka fi son wani fiye da sauran.”—1 Tim. 5:21.

Su waye ne waɗannan “malaꞌikun da aka zaɓa”? Bari mu soma da waɗanda ba sa cikin malaꞌikun nan da aka zaɓa. Shafaffu 144,000 ba sa cikin malaꞌikun nan. Me ya sa muka ce haka? A lokacin da Bulus ya rubuta wa Timoti wannan wasiƙar, babu wani cikin shafaffu da yake sama. Manzanni da shafaffun Kiristoci ba su riga sun zama malaꞌiku a lokacin ba. Don haka, ba su ba ne waɗannan “malaꞌikun da aka zaɓa.”—1 Kor. 15:50-54; 1 Tas. 4:13-17; 1 Yoh. 3:2.

Ƙari ga haka, malaꞌikun da suka yi tawaye a lokacin Nuhu ba sa cikin “malaꞌikun da aka zaɓa.” Waɗannan malaꞌikun sun zama aljanu domin sun bi Shaiɗan, kuma su maƙiyan Yesu ne. (Far. 6:2; Luk. 8:30, 31; 2 Bit. 2:4) A nan gaba, Yesu zai jefar da su cikin rami mai zurfin nan, kuma za su yi shekaru 1,000, a ciki. Bayan haka, za a hallaka su tare da Shaiɗan.—Yahu. 6; R. Yar. 20:1-3, 10.

Saboda haka, “malaꞌikun da aka zaɓa” da Bulus ya ambata, malaꞌiku ne a sama da suke goyon bayan “Allah, da Almasihu Yesu.”

Akwai duban malaꞌiku masu aminci. (Ibran. 12:22, 23) Kuma ba dukan malaꞌiku ne Jehobah yake ba wa aiki iri ɗaya ba. (R. Yar. 14:17, 18) Alal misali, Jehobah ya ba wa malaꞌika ɗaya aikin halaka sojojin Assuriya 185,000. (2 Sar. 19:35) Amma malaꞌiku da yawa ne za su “tara dukan abubuwan da suka sa mutane su yi zunubi, da kuma duk masu yin mugayen ayyuka, su fitar da su daga Mulkin [Yesu].” (Mat. 13:39-41) Wasu kuma za su tattaro shafaffu “waɗanda aka zaɓa” zuwa sama. (Mat. 24:31) Wasu malaꞌiku kuma suna kiyaye mu cikin dukan hanyoyinmu.—Zab. 91:11; Mat. 18:10; ka kuma duba abin da ke Matiyu 4:11; Luka 22:43.

“Malaꞌikun da aka zaɓa” da aka ambata a 1 Timoti 5:21, mai yiwuwa malaꞌiku ne da suke da aikin kula da ikilisiyoyi. Me ya sa muka ce haka? Domin kafin Bulus ya faɗi abin da ke ayar nan, ya yi magana game da yadda ya kamata dattawa su yi aikinsu, kuma ya ce ꞌyanꞌuwa a ikilisiya su yi musu biyayya. Ya ce kada dattawa su “nuna bambanci,” ko su nuna cewa sun “fi son wani fiye da sauran” ꞌyanꞌuwa. Ya kuma ce kada su yanke shawara ba tare da yin tunani da kyau ba. Saꞌan nan ya gaya musu abin da ya sa yin hakan yake da muhimmanci. Ya ce suna aiki ne a “gaban Allah, da Yesu Almasihu, da kuma malaꞌikun da aka zaɓa.” Hakan ya nuna cewa an ba wasu malaꞌiku aikin ƙare bayin Allah, da taimaka musu a waꞌazi, da kuma gaya wa Jehobah abin da suka lura da shi.—Mat. 18:10; R. Yar. 14:6.