Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Tuna?

Ka Tuna?

Ka karanta duka Hasumiyar Tsaro da aka fitar a shekarar nan da kyau? Ka ga ko za ka iya amsa tambayoyi na gaba:

Wane misali ne Jehobah ya kafa a kan yadda ya kamata a bi da mata?

Ba ya nuna musu bambanci, kuma ba ya son maza fiye da mata. Yana saurarar su, ya damu da su, kuma yana so ya san yadda suke ji da kuma matsalar da suke fuskanta. Ƙari ga haka, ba ya shakka cewa za su iya yin aikin da ya ba su.—w24.01, shafi na 15-16.

Ta yaya za mu bi abin da ke Afisawa 5:7, da ta ce: “Kada ku haɗa kai da su”?

Manzo Bulus yana mana gargaɗi ne cewa mu guji mutanen da za su sa ya yi mana wuya mu bi ƙaꞌidodin Jehobah. Wato mu guji yin abokantaka da su, ko a zahiri ko a dandalin sada zumunta.—w24.03, shafi na 22-23.

Waɗanne labaran ƙarya ne muke bukatar mu guje musu?

Wani lokaci abokanmu za su iya gaya mana labarin da ba su tabbatar da shi ba. Kuma wasu da ba mu san su ba za su iya tura mana irin wannan saƙo ta waya haka kawai. Akwai kuma ꞌyan ridda da sukan yi kamar suna so su ji waꞌazinmu ne.—w24.04, shafi na 12.

Mene ne ba mu sani ba game da yadda Jehobah zai shariꞌanta Sarki Sulemanu, da mutanen da ya hallaka a Saduma da Gwamarata da kuma zamanin Nuhu, kuma mene ne muka sani?

Ba mu da tabbaci cewa hukuncin da Jehobah ya yi musu shi ne hallaka ta har abada. Abin da muka sani shi ne cewa Jehobah ya san kome, kuma shi mai jinkai ne sosai.—w24.05, shafi na 3-4.

Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah “Dutse ne,” wane tabbaci ne hakan ya ba mu? (M. Sha. 32:4)

Za mu iya mai da Jehobah wurin ɓuyanmu. Za mu iya dogara da shi domin a koyaushe yana cika alkawarinsa. Kuma ba ya canjawa. Ba ya taɓa canja halinsa da kuma nufinsa.—w24.06, shafi na 26-28.

Me zai taimaka maka idan ka canja ikilisiya?

Ka dogara ga Jehobah, zai taimake ka kamar yadda ya taimaki bayinsa a dā. Ka daina kwatanta sabuwar ikilisiyarku da ta dā. Ka riƙa yin abubuwa tare da ꞌyanꞌuwa a sabuwar ikilisiyarku, kuma ka yi sabbin abokai.—w24.07, shafi na 26-28.

Waɗanne darussa ne aka koya mana a misalai uku da suke littafin Matiyu sura 25?

Misalin tumaki da awaki ya nuna muhimmancin kasancewa da aminci. Misalin ꞌyan mata masu hikima da wawaye ya nuna muhimmancin zama a shirye har ƙarshe. Misalin talanti kuma ya nuna muhimmancin kasancewa da ƙwazo.—w24.09, shafi na 20-24.

Yaya tsayin zauren da ke gaban haikalin da Sulemanu ya gina?

A 2 Tarihi 3:4, waɗansu kofi na rubuce-rubucen hannu na dā sun ce “kamu 120” ne, wato mita 53 (ko kafa 175). Amma akwai wasu kofi na rubuce-rubucen hannu na dā da aka yarda da su, da suka ce “kamu 20” ne, (wato kafa 30). Kuma masu bincike sun ce kamu 20 ne ya fi dacewa da kaurin bangon haikalin.—w24.10, shafi na 31.

Me ake nufi da cewa bawa mai hidima “ya kasance da mace ɗaya”? (1 Tim. 3:12)

Ana nufin cewa mace ɗaya kaɗai zai aura, kuma kada ya yi lalata. Ƙari ga haka, dole ya guji yin duk wani abin da zai nuna cewa yana shaꞌawar wata da ba matarsa ba.—w24.11, shafi na 19.

Me ya nuna cewa abin da Yesu ya faɗa a Yohanna 6:53 ba game da Jibin Maraice na Ubangiji ba ne?

A Yohanna 6:53 Yesu ya ce mutane suna bukatar su ci naman jikinsa kuma su sha jininsa. A shekara ta 32 bayan haihuwarsa ne ya yi wannan maganar, a yankin Galili. Kuma da Yahudawan da ba su gaskata da shi ba ne yake. Shekara ɗaya bayan haka ne ya yi taron cin Jibin Maraice na Ubangiji, kuma maganar da ya yi a wurin da waɗanda za su yi mulki da shi a sama ne.—w24.12, shafi na 10-11.