ABUBUWAN DA ZA KU IYA YIN NAZARI A KAI
Ka Kasance da Ƙarfin Zuciya ko da Ana Tsananta Maka
Ka karanta Irmiya 38:1-13 don ka ga abin da za ka iya koya daga yadda annabi Irmiya da Ebedmelek suka kasance da ƙarfin zuciya.
Ka bincika labarin sosai. Me ya sa Irmiya yake bukatar ƙarfin zuciya don ya gaya wa mutane saƙon da Allah ya ba shi? (Irm. 27:12-14; 28:15-17; 37:6-10) Da mutanen suka ji saƙon, mene ne suka yi?—Irm. 37:15, 16.
Ka nemi ƙarin bayani. Mene ne mutanen suke ganin Irmiya zai yi? (jr-E 26-27 sakin layi na 20-22) Ka yi bincike don ga yadda rijiya marar ruwa yake a dā, da kuma amfaninsu. (it-1-E 471) Yaya kake ganin Irmiya ya ji saꞌad da aka jefa shi cikin rijiya marar ruwa kuma ya soma lumewa cikin taɓo? Waɗanne abubuwa ne mai yiwuwa da za su sa Ebedmelek ya ji tsoro?—w12 5/1 31 sakin layi na 2-3.
Ka yi tunani a kan abubuwan da ka koya. Ka tambayi kanka:
-
‘Mene ne wannan labarin ya koya mini game da yadda Jehobah yake kāre bayinsa masu aminci?’ (Zab. 97:10; Irm. 39:15-18)
-
‘A waɗanne yanayoyi ne nake bukatar in muna ƙarfin zuciya?’
-
‘Ta yaya zan nuna ƙarfin zuciya kuma in yi abin da ya dace ko da ana tsananta mini?’ (w11 3/1 30) a
a Don ƙarin bayani game da abubuwan da za ka iya yin nazari a kai, ka duba talifin nan “Shawara a Kan Yin Nazari” da ke Hasumiyar Tsaro ta Yuli 2023.