TARIHI
“Ban Taɓa Kasancewa Ni Kaɗai Ba”
YANAYOYI da dama za su iya sa mu ji kamar mun kaɗaita. Alal misali, idan wani na kusa da mu ya mutu, ko mun ƙaura zuwa wurin da ba mu taɓa zuwa ba, ko kuma muna zama mu kaɗai. A rayuwata, na yi fama da dukan waɗannan yanayoyin. Duk da haka, idan na yi tunani game da rayuwata, sai in ga cewa ban taɓa kasancewa ni kaɗai ba. Ga abin da ya sa na ce hakan.
MISALIN DA IYAYENA SUKA KAFA
Iyayena ꞌyan Katolika ne. Amma da suka koyi cewa sunan Allah Jehobah ne daga Littafi Mai Tsarki, sai suka zama Shaidun Jehobah. Mahaifina kafinta ne kuma yana yin siffofin Yesu da katakai, amma da ya koyi gaskiya, ya daina. Da yake ya iya aiki sosai, ya mai da wani wuri a gidanmu ya zama Majamiꞌar Mulki na farko a San Juan del Monte, wani unguwa a Manila, babban birnin Filipin.
An haife ni a 1952, kuma iyayena sun soma koya mini game da Jehobah kamar yadda suka yi wa ꞌyanꞌuwana maza huɗu da mata uku. Da nake girma, babana ya gaya min in riƙa karanta sura ɗaya na Littafi Mai Tsarki kowace rana. Kuma ya yi nazari da ni da littattafanmu dabam-dabam. Iyayena suna gayyatar masu kula da daꞌira da kuma wakilan rashen ofishinmu su zauna a gidanmu jifa-jifa. Dukanmu a iyali mukan amfana daga labaransu, kuma hakan ya taimaka mana mu sa bautar Jehobah farko a rayuwarmu.
Na koyi abubuwa da yawa daga wurin iyayena don sun bauta wa Jehobah da aminci. Bayan da mahaifiyata ta yi fama da rashin lafiya kuma ta mutu, sai ni da mahaifina muka soma hidimar majagaba a 1971. Amma saꞌad da nake shekara 20 a 1973, mahaifina ma ya mutu. Mutuwar iyayena ta sa na ji kamar na rasa kome kuma ban da kowa. Amma tabbatacciyar alkawarin da ke Littafi Mai Tsarki ya sa na kasance da bege, na daina yawan damuwa kuma na ci-gaba da kusantar Jehobah. (Ibran. 6:19) Jim kaɗan bayan mutuwar mahaifina, na soma hidimar majagaba na musamman a tsibirin Coron, a jihar Palawan.
YIN HIDIMA MAI WUYA NI KAƊAI
Shekaruna 21 a lokacin da na soma hidima a Coron. Da yake a birni ne na yi girma, na yi mamaki sosai da na ga cewa ba wutan lantarki ko ruwan famfo sosai a tsibirin, kuma motoci da mashuna kaɗan ne. Ko da yake akwai ꞌyanꞌuwa kaɗan a wurin, a wasu lokuta ni kaɗai ne nake fita waꞌazi. A wata na farko da na yi a wurin, na yi kewar
ꞌyanꞌuwana da abokaina sosai. Da dare, ina zama ina zub da hawaye ina kallon taurari a sama. Na ji kamar in daina hidimar da nake yi, kuma in koma gida.A waɗannan lokutan, nakan yi adduꞌa ga Jehobah kuma in gaya masa duk abin da ke damu na. Nakan tuna wasu abubuwan da ke Littafi Mai Tsarki da littattafanmu masu ban-ƙarfafa da na taɓa karantawa. Ayar da ke yawan zuwa zuciyata ita ce, Zabura 19:14. Na gano cewa idan na ci-gaba da yin tunani a kan abubuwan da za su faranta ran Jehobah, kamar ayyukansa da halayensa, zai zama “Dutsen ɓuyana da Mai fansata.” Ƙari ga haka, talifin da ke Hasumiyar Tsaro mai jigo, “You Are Never Alone” a ya taimaka min sosai. Na karanta shi sau da sau. A waɗannan lokutan, na ji kamar ina tare da Jehobah ne. Ba zan taɓa manta da waɗannan lokutan ba domin sun ba ni damar yin adduꞌa da nazari da kuma yin tunani mai zurfi.
Jim kaɗan bayan na isa Coron, an naɗa ni dattijo. Da yake ni kaɗai ne dattijo, na soma gudanar da Makarantar Hidima ta Allah, da Taron Hidima, da Nazarin Littafi na Ikilisiya, da kuma Nazarin Hasumiyar Tsaro. Kuma kowane mako ni nake yin jawabi ga jamaꞌa. A gaskiya, ban ji kaɗaici kuma ba don ina da ayyuka da yawa!
Na ji daɗin hidimata a Coron, kuma wasu daga cikin ɗalibaina sun yi baftisma. Amma duk da haka, na fuskanci matsaloli. A wasu lokuta, nakan taka da kafa daga safe har rana kafin in isa wurin da zan yi waꞌazi. Kuma ba na ma sanin inda zan kwana idan na isa. Akwai ƙananan tsibirai da yawa a yankin da muke waꞌazi. Don haka, a yawancin lokuta nakan je wuraren a kwalekwale mai inji, cikin guguwa kuma ban iya iyo ba! A dukan matsalolin nan, Jehobah ya taimaka mini kuma ya kāre ni. Daga baya na gano cewa, ashe Jehobah yana shirya ni ne don matsalolin da zan fuskanta a nan gaba.
PAPUA NEW GUINEA
A shekara ta 1978, an tura ni hidima a Papua New Guinea, da ke arewacin Ostireliya. A wurin akwai duwatsu sosai, kuma girmar ƙasar ta kusan kai girmar Sifen. Na yi mamaki da na ga cewa mutane wajen miliyan uku da suke ƙasar, suna da yaruka fiye da 800. Amma abin farin cikin shi ne, yawancin mutane suna yin yaren da ake kira Tok Pisin.
An tura ni hidima a wata ikilisiyar Turanci na ɗan lokaci da ke birnin tarayyar, wato Port Moresby. Amma daga baya na koma ikilisiya da ake yin Tok Pisin kuma na soma koyan yaren. Nakan yi amfani da abin da nake koya a waꞌazi, kuma hakan ya taimaka min in koyi yaren da wuri. Ba da daɗewa ba, sai na soma ba da jawabai a Tok Pisin. Na yi mamaki sosai da aka ce in soma hidimar mai kula da daꞌira a ikilisiyoyin Tok Pisin, duk da cewa ban kai shekara ɗaya da zuwa Papua New Guinea ba.
Da yake ikilisiyoyin suna da nisa da juna, nakan shirya taron daꞌira da yawa, kuma nakan yi tafiye-tafiye da dama. Da farko, na ji kamar ni kaɗai ne, ga shi ina sabuwar ƙasa, kuma yare da alꞌadun mutanen sun yi dabam da waɗanda na saba da su. Ba na iya bin ta hanya in je inda ikilisiyoyin suke domin akwai hawa da yawa a wurin, kuma hanyoyin ba sa nan sumul. Saboda haka, kusan kowane mako, jirgin sama ne nake shiga. A wasu lokuta, ni kaɗai ne fasinja da ke zama a wani
ɗan ƙaramin jirgin sama da bai da kyau sosai. A duk lokacin da nake irin wannan tafiyar, hankalina na tashiwa kamar yadda yake idan ina tafiya a jirgin ruwa!Ƙari ga haka, mutane kaɗan ne suke da waya a wurin, don haka nakan tura wa ikilisiyoyin saƙo ta wasiƙa. A yawancin lokuta, nakan isa wuraren kafin wasiƙun su isa, sai in tambayi mutanen garin inda ꞌyanꞌuwa suke. Amma duk lokacin da na haɗu da ꞌyanꞌuwan, suna farin ciki sosai kuma irin ƙaunar da suke nuna mini, yana sa in ga cewa ƙoƙarina ba a banza ba ne. Na ga yadda Jehobah ya taimaka min a hanyoyi da yawa kuma na daɗa kusantar sa.
A taro na farko da na je a wani tsibiri da ake kira Bougainville, wasu maꞌaurata sun same ni suna murmushi suka ce mini, “Ka tuna da mu?” Sai na tuna cewa ni ne na fara nazari da su lokacin da nake Port Moresby. Amma daga baya, na gaya wa wani ɗanꞌuwa ya ci-gaba da nazarin. Yanzu su biyun sun yi baftisma! Wannan ɗaya ne daga cikin albarkun da na samu a shekaru uku da na yi a Papua New Guinea.
ƘARAMIN IYALI MASU ƘWAZO
Kafin in bar Coron a 1978, na haɗu da wata kyakkyawar ꞌyarꞌuwa mai yin sadaukarwa sosai, sunanta Adel. Tana hidimar majagaba yayin da take kula da yaranta biyu, Samuel da Shirley. Ƙari ga haka, ita ce take kula da mahaifiyarta da ta tsufa. A Mayu 1981, na koma Filipin kuma na auri Adel. Bayan aurenmu, mun ci-gaba da hidimar majagaba da kuma kula da iyalin.
Ko da yake muna da yara, a 1983, an sake naɗa ni majagaba na musamman kuma an ce in yi hidima a tsibirin Linapacan, a jihar Palawan. Dukanmu a iyali mun ƙaura zuwa wannan wurin kuma babu Shaidu a wurin. Bayan wajen shekara ɗaya, sai mahaifiyar Adel ta rasu. Duk da haka mun ci-gaba da waꞌazi da ƙwazo kuma abin da ya taimaka mana ke nan mu iya jimrewa. Ba da daɗewa ba, mun soma nazari da mutane da yawa a Linapacan da suka sami ci-gaba sosai, har mun bukaci ɗan ƙaramin Majamiꞌar Mulki. Don haka, mun gina wani ɗan ƙaramin majamiꞌa da kanmu. Bayan da muka yi shekaru uku a wurin, mun yi farin ciki sosai da muka ga mutane 110 sun halarci Taron Tunawa da Mutuwar Yesu. Kuma da yawa daga cikinsu sun yi baftisma bayan mun bar wurin.
A shekara ta 1986, na soma hidima a wani tsibiri mai suna, Culion. Kuma a wurin ne aka ce Adel ta soma hidima a matsayin majagaba na musamman. Akwai wani wuri a tsibirin inda mutane da yawa suke fama da ciwon kuturta. Da farko mun ji tsoron yin waꞌazi ga mutanen da cutar ta riga ta canja musu kamanni. Amma ꞌyanꞌuwa da ke wurin sun gaya mana cewa zai yi wuya mutum ya kamu da cutar don an riga an ba su magani. Wasu daga cikinsu ma suna halartar taro da ake yi a gidan wata ꞌyarꞌuwa. Ba da daɗewa ba, mu ma mun saba da su, kuma mun ji daɗin yin waꞌazi ga mutanen nan da suke ganin kamar Allah ya ƙi su, mutane ma sun ƙi su. Abin farin ciki ne ganin yadda mutanen nan da suka yi fama da irin wannan cutar, suke murna don sun koyi cewa a-kwana-a-tashi, za su kasance da koshin lafiya.—Luk. 5:12, 13.
Yaranmu kuma fa, me ya taimaka musu saꞌad da muke Culion? Ni da matata Adel mun gayyaci wasu ꞌyanꞌuwa mata biyu daga Coron su zo su zauna tare da mu. Hakan ya taimaka wa yaranmu su sami abokan kirki. Samuel da Shirley da kuma ꞌyanꞌuwa mata biyun, su ma sun taimaka wa yara da yawa su koyi gaskiya. Yayin da suke nazari da yaran, ni da matata mukan yi nazari da iyayensu. Akwai lokacin da muke nazari da iyalai 11. Ba da daɗewa ba, ɗalibanmu da yawa sun sami ci-gaba, kuma hakan ya sa an kafa wata sabuwar ikilisiya!
Da farko ni kaɗai ne dattijo a wurin. Don haka, ofishinmu ya ce in riƙa gudanar da taro kowane mako da masu shela guda takwas da ke Culion, kuma in yi hakan da masu shela guda tara da ke wani ƙauye da ake kira Marily. Amma sai an yi tafiya na awa uku a jirgin ruwa kafin a kai ƙauyen. Bayan taro a ƙauyen, dukanmu a iyali mukan yi saꞌoꞌi da yawa muna hawa da sauka a kan tuddai da kafa, don mu je mu yi nazari da ɗalibanmu a wani ƙauye da ake kira Halsey.
Da shigewar lokaci, mutane da yawa sun soma bauta wa Jehobah har ya sa muka gina Majamiꞌun Mulki a Marily da kuma Halsey. Kamar yadda aka yi a Linapacan, ꞌyanꞌuwa da ɗalibansu ne suka kawo yawancin abubuwan da ake bukata a yi ginin, kuma su ne suka yi yawancin aikin. Majamiꞌar da aka gina a Marily zai iya ɗaukan mutane 200 kuma ana iya kara girmansa. Hakan ya sa muna iya gudanar da taron daꞌira a ciki.
NA YI BAƘIN CIKI KUMA NA JI KAƊAICI, AMMA NA SAKE YIN FARIN CIKI
Saꞌad da yaranmu suka yi girma a shekara ta 1993, ni da Adel mun soma hidimar mai kula da daꞌira a ƙasar Filipin. Saꞌan nan a shekara ta 2000, na halarci Makarantar Koyar da Masu Hidima don in sami horarwa na zama malamin makarantar. Na ji kamar ba zan iya ba, amma matata Adel ta ƙarfafa ni kamar yadda ta saba. Ta tuna mini cewa Jehobah zai taimaka mini in yi wannan aikin. (Filib. 4:13) Adel ta iya ƙarfafa ni ne domin ta ga yadda Jehobah ya taimaka mata ta ci-gaba da hidimarta, duk da cewa tana fama da rashin lafiya.
A shekara ta 2006, na zama malamin makarantar, kuma a lokacin ne aka gano cewa matata
Adel tana da cutar karkarwar jiki ta Parkinson. Mun yi mamaki sosai! Da na gaya wa Adel cewa zan dakatar da hidimata don in kula da ita, sai ta ce, “Don Allah, ka nema min likitan da zai taimaka mini, na san cewa Jehobah zai taimaka mana mu ci-gaba da hidimarmu.” Adel ta ci-gaba da hidimarta har wajen shekara shida ba tare da wani gunaguni ba. Saꞌad da ba ta iya tafiya da ƙafanta, tana waꞌazi da keken guragunta. Saꞌad da ba ta iya magana da kyau, takan yi amfanin da kalma ɗaya ko biyu ta ba da amsa a taro. ꞌYanꞌuwa da yawa sun yi ta tura wa Adel saƙon godiya don irin jimirin da ta kasance da shi, har lokacin da ta mutu a 2013. Na yi shekaru 30 da matata mai ƙauna da aminci, amma yanzu kamar na koma gidan jiya. Na soma baƙin ciki sosai kuma na ji kamar ba ni da kowa.Matata Adel ta so in ci-gaba a hidimata, kuma abin da na yi ke nan. Na ci-gaba da yin hidimata da ƙwazo kuma hakan ya taimaka mini in jimre. Daga 2014 zuwa 2017, an ce in ziyarci ikilisiyoyi da suke yaren Tagalog a ƙasashen da ꞌyanꞌuwanmu ba sa iya yin ibada a sake. Bayan hakan, na ziyarci wasu ikilisiyoyin da ake yin Tagalog a Taiwan, da Amurka, da kuma Kanada. A shekara ta 2019, na gudanar da Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki da Turanci a ƙasar Indiya da kuma Tailan. Na ji daɗin dukan hidimomin nan da na yi. Nakan yi farin ciki sosai idan na duƙufa a yin hidimata ga Jehobah.
ZA MU SAMI TAIMAKON DA MUKE BUKATA A KOYAUSHE
A duk lokacin da na soma wata hidima, ꞌyanꞌuwan da nake haɗuwa da su sukan zama abokaina, kuma barin su bai da sauƙi. Amma idan lokaci ya zo da za mu rabu, abin da na koya shi ne, in dogara ga Jehobah da dukan zuciyata. Na sha ganin yadda yake taimaka mini, kuma hakan ya sa yana mini sauƙi in amince da duk wani canjin da na samu a rayuwa. A yanzu haka, ina hidimar majagaba na musamman a ƙasar Filipin. Na saba da ꞌyanꞌuwan da ke sabuwar ikilisiyar, kuma suna kula, da taimaka mini kamar ꞌyan iyalina. Ƙari ga haka, ina alfahari da Samuel da Shirley don yadda suke da bangaskiya kamar mahaifiyarsu.—3 Yoh. 4.
A gaskiya, na yi fama da matsaloli da yawa a rayuwata. Na sami kaina a yanayoyi dabam-dabam, kuma a idona matata ta yi fama da cuta mai tsanani har ta mutu. Duk da haka, na ga cewa Jehobah bai da “nesa da kowannenmu.” (A. M. 17:27) Hannun Jehobah “bai kāsa ba, har da ba zai iya miƙa shi” ya taimaka wa bayinsa a duk inda suke ba. (Isha. 59:1) Jehobah, wanda shi ne Dutsen ɓuyana, ya kasance da ni dukan rayuwata kuma ina gode masa sosai. Ban taɓa kasancewa ni kaɗai ba.
a Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Satumba, 1972, shafi na 521-527.