Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Kada Ka Zama Mai Son Kai Kamar Mutane da Yawa a Yau

Kada Ka Zama Mai Son Kai Kamar Mutane da Yawa a Yau

SHIN ka lura cewa mutane da yawa a yau suna ganin sun fi kowa muhimmanci? Hakan yana sa su ga kamar sun cancanci a ba su gata, da daraja, da kuma kulawa fiye da sauran mutane. Ko da mene ne aka yi musu, ba sa taɓa gamsuwa. Irin waɗannan mutanen masu son kansu ne, kuma marasa godiya. Amma ba abin mamaki ba ne, domin Littafi Mai Tsarki ya ce mutane za su kasance da irin halin nan a kwanakin ƙarshe.—2 Tim. 3:2.

Gaskiyar ita ce, ba yau ne aka soma nuna irin halin nan ba. Alal misali, Adamu da Hauwaꞌu sun so su sami ꞌyancin zaɓan abin da suke so, mai kyau ko marar kyau, kuma hakan ya jawo mummunar sakamako. Ɗarurruwan shekaru bayan haka, Uzziya Sarkin Yahuda ya ga kamar ya cancanci ya kona turare a haikali, amma yin hakan ba aikinsa ba ne. (2 Tar. 26:18, 19) Ƙari ga haka, Farisiyawa da Sadukiyawa sun ga kamar ya kamata Allah ya nuna musu alheri fiye da sauran mutane, da yake su daga zuriyar Ibrahim ne.—Mat. 3:9.

Mu ma a yau, muna kewaye da mutane masu son kai, kuma halinsu zai iya shafan mu. (Gal. 5:26) Za mu iya soma ganin cewa mun cancanci samun wata gata ko kulawa ta musamman. Me zai taimaka mana kada mu riƙa yin irin tunanin nan? Muna bukatar mu san raꞌayin Jehobah game da batun. Akwai ƙaꞌidodi biyu a Littafi Mai Tsarki da za su taimaka.

Jehobah ya faɗi abin da kowannenmu ya cancanci ya samu. Ga wasu misalai.

  • A iyali, namiji ya cancanci matarsa ta daraja shi, kuma matar ta cancanci mijinta ya ƙaunace ta. (Afis. 5:33) Maꞌaurata suna bukatar su riƙa nuna wa junansu kaɗai soyayya. (1 Kor. 7:3) Iyaye kuma sun cancanci yaransu su yi musu biyayya, yara kuma suna bukatar ƙauna da kulawa daga wurin iyayensu.—2 Kor. 12:14; Afis. 6:2.

  • A ikilisiya, ya kamata mu riƙa daraja dattawa don aikin da suke yi da ƙwazo. (1 Tas. 5:12) Amma, ba a ba su izinin nuna iko a kan ꞌyanꞌuwa ba.—1 Bit. 5:2, 3.

  • Allah ya ce mu daraja shugabannin gwamnati, kuma ya ba su damar karɓan haraji daga wurinmu.—Rom. 13:1, 6, 7.

Jehobah yana ba mu abubuwa fiye da yadda muka cancanta. Da yake mu masu zunubi ne, mun cancanci mu mutu ne kawai. (Rom. 6:23) Duk da haka, Jehobah yana mana alheri sosai don yana ƙaunar mu. (Zab. 103:10, 11) Saboda haka, duk wani gata ko wata albarka da muka samu a rayuwa, alheri ne daga Allah, ba don mun cancanta ba.—Rom. 12:6-8; Afis. 2:8.

ME ZAI TAIMAKA MANA MU GUJI SON KAI KO KUMA TUNANI CEWA MUN FI MUTANE DARAJA?

Mu guji yin tunani irin na mutanen duniya. Idan ba mu mai da hankali ba, za mu soma ji kamar mun cancanci samun wasu abubuwa fiye da sauran mutane. A misalin da Yesu ya bayar na maꞌaikatan da aka biya su dinari guda, ya nuna mana yadda za mu iya soma irin tunanin nan. Wasu maꞌaikatan sun yi aiki daga safe har yamma a cikin rana; wasu kuma sun yi aiki na awa ɗaya ne kawai. Waɗanda suka soma aiki tun da safe sun ga kamar sun cancanci a biya su fiye da sauran, domin irin aikin da suka yi. (Mat. 20:1-16) Yesu ya ba da wannan misalin ne don ya nuna cewa mabiyansa suna bukatar su gamsu da duk abin da Jehobah ya ba su.

Mutanen da suka yini suna aiki sun ga kamar sun cancanci a biya su fiye da sauran

Mu zama masu godiya, kuma kada mu riƙa ganin cewa mu ne ya kamata mu riƙa samun abubuwa. (1 Tas. 5:18) Abin da manzo Bulus ya yi ke nan. Ko da yake ya cancanci ya gaya wa ꞌyanꞌuwan da ke Korinti su ba shi abubuwan da yake bukata, bai yi hakan ba. (1 Kor. 9:11-14) Zai dace mu riƙa nuna godiya ko da mene ne aka ba mu, kuma kada mu ɗauka cewa mun cancanci a ba mu fiye da hakan.

Manzo Bulus bai nemi mutane su tallafa masa da kuɗi ba

Mu kasance da sauƙin kai. Idan mutum yana ji da kansa, zai iya soma ganin kamar ya cancanci ya samu fiye da abin da yake da shi. Amma idan mu masu sauƙin kai ne, hakan zai sa ba za mu yi wannan tunani marar kyau ba.

Jehobah ya daraja annabi Daniyel sosai don shi mai sauƙin kai ne

Annabi Daniyel ya kafa mana misali mai kyau na nuna sauƙin kai. Duk da cewa shi daga gidan manyan mutane ne, kuma yana da kyau, da ilimi, da kuma baiwa iri-iri, bai ga kamar ya cancanci gata da daraja da ya samu ba. (Dan. 1:3, 4, 19, 20) A maimakon haka, Daniyel ya kasance da sauƙin kai kuma hakan ya sa Jehobah ya daraja shi.—Dan. 2:30; 10:11, 12.

Bari mu guji son kai ko kuma yin tunani cewa mun fi sauran mutane daraja, don wannan halin duniya ne. Mu kuma ci-gaba da nuna godiya don albarkun da Jehobah yake mana, da yake shi mai yawan alheri ne.