Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 6

WAƘA TA 18 Muna Godiya Domin Mutuwar Yesu

Muna Godiya don Jehobah Yana Gafarta Mana

Muna Godiya don Jehobah Yana Gafarta Mana

“Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da makaɗaicin Ɗansa.”YOH. 3:16.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga abubuwan da Jehobah ya yi don ya iya gafarta mana zunubanmu. Hakan zai sa mu ƙara yin godiya don wannan alheri da ya yi mana.

1-2. Ta yaya yanayinmu ya yi kama da na saurayin da aka ambata a sakin layi na 1?

 A CE wani saurayi yana da iyaye masu kuɗi, sai wata rana iyayensa suka yi hatsari suka mutu. Abin da ya faru ya sa shi cikin damuwa sosai. Amma ana wani sai ga wata. An gaya masa cewa iyayensa sun cinye dukan kuɗin da suke da shi har ma sun ci bashi mai yawa. Hakika wannan ba ƙaramin balaꞌi ba ne. Maimakon ya gāji dukiyarsu, bashi ne suka bar masa. Waɗanda suke bin su bashin kuma sun nace ya biya su da wuri. Ga shi ba zai taɓa iya biyan duka basussukan ba. Lallai wannan saurayin yana cikin babbar matsala, ko ba haka ba?

2 Yanayinmu ya yi kama da na wannan saurayin. Domin da aka halicci iyayenmu na farko, Adamu da Hauwaꞌu, ba su da zunubi, kuma suna zama a aljanna. (Far. 1:27; 2:7-9) Za su iya yin rayuwa har abada cikin jin daɗi. Amma da suka yi zunubi, sai kome ya canja. An kore su daga Aljannar, kuma ba zai yiwu su rayu har abada ba. Wane gādo ne suka bar wa yaransu? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya [Adamu], zunubin nan kuwa shi ya jawo mutuwa, ta haka mutuwa ta bi ta shiga dukan ꞌyan Adam, gama kowa ya yi zunubi.” (Rom. 5:12) Mun gāji zunubi daga wurin Adamu, kuma shi ya sa muke mutuwa. Wannan zunubi da muka gāda yana kama da bashi mai yawa, da ba za mu taɓa iya biya ba.—Zab. 49:8.

3. Me ya sa idan muka yi zunubi, kamar mun ci bashi ne?

3 Yesu ya ce zunubanmu kamar basussuka suke. (Mat. 18:32-35) Wato idan muka yi zunubi, za mu iya cewa Jehobah yana bin mu bashi. Dole ne mu biya wannan bashin. In ba haka ba, mutuwa ce kaɗai za ta raɓa mu da bashin.—Rom. 6:7, 23.

4. (a) In ba an taimaka mana ba, me zai faru da mu? (Zabura 49:7-9) (b) Me ake nufi da Kalmar nan “zunubi” a Littafi Mai Tsarki? (Ka duba akwatin da ya ce, “ Zunubi.”)

4 Shin, mu da kanmu za mu iya sake samun dukan abubuwan da Adamu da Hauwaꞌu suka rasa? Sam! Ba zai yiwu ba. (Karanta Zabura 49:7-9.) In ba an taimaka mana ba, ba mu da begen yin rayuwa har abada ko begen tashiwa idan muka mutu. Hakan yana nufin cewa kamar dabbobi, idan muka mutu, ta mu ta ƙare ke nan.—M. Wa. 3:19; 2 Bit. 2:12.

5. Ta yaya Ubanmu na sama ya taimaka mana da zunubin da muka gāda? (Ka duba hoton.)

5 Ka ɗan yi tunani game da saurayin da muka ambata ɗazu. A ganinka, yaya zai ji idan wani mai kuɗi ya ce zai biya dukan basussukan da ake bin iyayensa? Ba shakka, saurayin zai yi godiya sosai kuma zai amince da wannan taimakon. Irin abin da Jehobah, Ubanmu mai ƙauna, ya yi mana ke nan. Ya ba mu abin da zai biya bashin zunubin da muka gāda daga wurin Adamu. Yesu ya ce: “Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin dukan wanda ya ba da gaskiya gare shi kada ya halaka, amma ya sami rai na har abada.” (Yoh. 3:16) Ƙari ga haka, wannan kyautar da Jehobah ya yi mana ya buɗe mana hanyar zama aminansa.

Yesu ya yi waꞌazi game da yadda Jehobah yake gafarta mana don fansar da aka bayar. (Yoh. 3:16) Saꞌan nan ya ba da ransa da yardar rai don a biya fansar (Ka duba sakin layi na 5)


6. Me za mu tattauna a talifin nan, kuma me ya sa?

6 Me za mu yi don mu amfana daga wannan babbar kyauta da Allah ya yi mana, kuma a yafe mana zunubanmu? Don mu amsa wannan tambayar, za mu tattauna wasu furuci daga Littafi Mai Tsarki da maꞌanarsu. Hakan zai ba mu damar yin tunani mai zurfi a kan abin da Jehobah ya yi don ya gafarta zunubanmu, kuma zai sa mu ƙara gode masa.

JEHOBAH YANA SO MU ZAMA AMINANSA

7. (a) Ta yaya zunubin da Adamu da Hauwaꞌu suka yi ya shafi dangantakarsu da Jehobah? (b) Da yake mu ꞌyaꞌyan Adamu da Hauwaꞌu ne, me muke bukata a yi mana? (Romawa 5:10, 11)

7 Ban da cewa Adamu da Hauwaꞌu sun yi hasarar rai na har abada, sun ɓata dangantakarsu da Jehobah. Kafin su yi zunubi, suna cikin iyalin Jehobah. (Luk. 3:38) Amma da suka yi zunubi, Jehobah ya kore su daga cikin iyalinsa, tun kafin su soma haihuwa. (Far. 3:23, 24; 4:1) Da yake mu ꞌyaꞌyansu ne, mu kamar maƙiyan Allah ne, kuma muna bukatar a shirya tsakaninmu da shi. (Karanta Romawa 5:10, 11.) Hakan yana nufin cewa muna bukatar mu daina zama maƙiyansa kamar Adamu da Hauwaꞌu, kuma mu zama aminansa. Abin farin cikin shi ne, Jehobah ne ya ɗauki mataki don ya sa hakan ya yiwu. Me ya yi?

ALLAH YA BUƊE MANA HANYAR ZAMA AMINANSA

8. Mene ne Jehobah ya yi?

8 Jehobah ya shirya yadda mutane masu zunubi za su iya zama aminansa. Ya yi hakan ne ta wurin buɗe wata hanya da wani zai iya ba da abin da ya yi daidai da abin da Adamu ya rasa. Nassosin Helenanci ma sun yi magana game da wannan tanadi da Jehobah ya yi, don mutane masu zunubi su iya zama aminansa.—Rom. 3:25.

9. Mene ne Jehobah ya ce Israꞌilawa su yi don ya gafarta musu zunubansu?

9 A dā, Jehobah ya yi wani tanadi don ya iya gafarta wa Israꞌilawa zunubansu kuma su zama aminansa. Israꞌilawa sukan yi bikin Ranar Ɗaukar Alhakin Zunubi sau ɗaya kowace shekara. A ranar, babban firist yakan yi hadaya da dabbobi don zunuban jamaꞌar. Gaskiyar ita ce, hadayar dabbobi ba za ta iya share zunubin mutum ba, domin dabbobi ba su kai mutane daraja ba. Amma Jehobah ya yarda ya yafe ma Israꞌilawan zunubansu, muddin sun tuba kuma sun yi hadayar da ya ce su yi. (Ibran. 10:1-4) Ƙari ga haka, hadayun neman gafara da Israꞌilawa suke yi a lokacin, sun riƙa tuna musu cewa su masu zunubi ne kuma suna bukatar abin da zai share musu wannan zunubin gabaki ɗaya.

10. Mene ne Jehobah ya yi don a iya gafarta wa ꞌyan Adam zunubansu gabaki ɗaya?

10 Mene ne Jehobah ya yi don a iya gafarta wa ꞌyan Adam zunubansu? Ya shirya yadda zai miƙa Ɗansa “sau ɗaya domin ya ɗauki zunuban mutane da yawa.” (Ibran. 9:28) Yesu kuma ya “ba da ransa domin ceton mutane da yawa.” (Mat. 20:28) Ta yaya hakan ya yiwu?

ABIN DA AKA BIYA DON MU IYA ZAMA AMINAN ALLAH

11. (a) Bisa ga Littafi Mai Tsarki, me ya sa ake bukatar a biya fansa? (b) Me ake bukata don a iya biyan fansar?

11 Bisa ga Littafi Mai Tsarki, Jehobah ya tsai da shawara cewa za a biya fansa don a iya gafarta mana, kuma mu zama aminansa. a Me ake bukatar a biya domin ꞌyan Adam su sami abin da Adamu ya rasa? Ana bukatar a biya abin da ya yi daidai da wanda aka rasa. (1 Tim. 2:6) Ka tuna cewa Adamu da Hauwaꞌu sun rasa gatan yin rayuwa har abada, kuma sun zama masu zunubi. Mene ne zai yi daidai da abin da suka rasa? Ana bukatar mutum, wanda (1) bai da zunubi; (2) zai iya yin rayuwa har abada a duniya; kuma (3) zai yarda ya ba da ransa a madadinmu. Ran irin wannan mutumin ne zai yi daidai da wanda Adamu ya rasa.

12. Me ya sa Yesu ya iya biyan fansar da ake bukata?

12 Me ya sa Yesu ne zai iya biyan wannan fansar? Ga dalilai uku: (1) An haife shi bai da zunubi, kuma “bai taɓa yin laifi ba ko kaɗan.” (1 Bit. 2:22) (2) Zai iya yin rayuwa har abada a duniya don bai da zunubi. (3) Ya yarda ya ba da ransa a madadinmu. (Ibran. 10:9, 10) Yesu marar laifi ne, kamar yadda Adamu yake kafin ya yi zunubi. (1 Kor. 15:45) Shi ya sa da Yesu ya mutu, ya biya alhakin zunubin Adamu, wato daidai abin da Adamu ya rasa. (Rom. 5:19) Ta haka, Yesu ya zama ‘Adamu na ƙarshe.’ Ba a bukatar wani ya sake biyan abin da Adamu ya rasa, domin da Yesu ya mutu, “ya miƙa hadaya ɗaya ta har abada.”—Ibran. 7:27; 10:12.

13. Me ya taimaka mana mu iya kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah?

13 Me ya taimaka mana mu iya kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah? Jehobah ya buɗe hanyar da za a ba da fansa don a iya gafarta mana zunubanmu. Saꞌan nan, Yesu ya ba da ransa marar zunubi don ya biya daidai abin da Adamu ya ɓatar.—Afis. 1:7; Ibran. 9:14.

ꞌYANCI DAGA ZUNUBI DA MUTUWA, DA KUMA ZAMA MARASA LAIFI

14. Me za mu bincika yanzu, kuma me ya sa?

14 Ta yaya muke amfana daga wannan abin da Jehobah ya yi mana? Don mu amsa wannan tambayar, za mu bincika maꞌanar wasu furuci biyu da aka yi a Littafi Mai Tsarki. Furuci biyun nan sun bayyana yadda muke amfana sosai don Jehobah yana gafarta mana zunubanmu.

15-16. (a) Mene ne za mu iya samuwa don fansar Yesu? (b) Yaya muke ji don wannan ꞌyanci da muka samu?

15 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa da yake an biya fansar, an ꞌyantar da mu. Manzo Bitrus ya ce: “Kun sani cewa an fanshe ku [an ꞌyantar da ku] ne daga alꞌadun banza waɗanda kakanninku suka bar muku gādo. Ba a kuwa fanshe ku da abubuwa masu lalacewa kamar azurfa da zinariya ba, amma da jinin nan mai daraja na Almasihu, wanda ya zama kamar ɗan rago na hadaya marar tabo, marar ciwo.”—1 Bit. 1:18, 19.

16 Saboda fansar Yesu, za mu iya samun ꞌyanci daga zunubi da mutuwa da suke jawo mana wahala ba kaɗan ba. (Rom. 5:21) Muna matukar godiya ga Jehobah da Ɗansa Yesu, don yadda suka ꞌyantar da mu ta wurin jinin Yesu mai daraja.—1 Kor. 15:22.

17-18. (a) Ta yaya samun zama marasa laifi a gaban Allah yake amfanarmu? (b) Yaya hakan yake sa mu ji?

17 Littafi Mai Tsarki ya kuma ce bayin Allah sun sami zaman marasa laifi a gabansa. Hakan yana nufin cewa idan mun tuba, Allah ba zai sake tuhumarmu a kan zunuban da muka yi ba. Duk da haka, Jehobah yana yin adalci. Me ya sa muka ce haka? Domin Jehobah ba ya amincewa da zunubi. Ƙari ga haka, ba don ƙoƙarinmu ne muka sami zama marasa laifi a gabansa ba. To me ya sa Jehobah yake mana gafara? Domin mun gaskata da abin da Shi da Yesu suka yi don su ꞌyantar da mu daga zunubi da mutuwa.—Rom. 3:24; Gal. 2:16.

18 Ta yaya samun zama marasa laifi a gaban Allah yake amfanarmu? An zaɓi wasu daga cikinmu su yi mulki tare da Yesu a sama, kuma sun zama ꞌyaꞌyan Allah. (Tit. 3:7; 1 Yoh. 3:1) Jehobah ya yafe musu zunubansu kuma ya mai da su marasa laifi kamar ba su taɓa yin zunubi ba. Don haka, sun cancanci su yi mulki tare da Yesu. (Rom. 8:1, 2, 30) Sauran bayin Allah da suka sami zama marasa laifi a gabansa za su yi rayuwa har abada a nan duniya. Jehobah ya gafarta musu zunubansu kuma sun zama aminansa. (Yak. 2:21-23) Taro mai-girma da za su tsira a yaƙin Armageddon ba za su taɓa mutuwa ba idan suka riƙe amincinsu. (Yoh. 11:26) Kuma za a ta da “masu adalci” da “marasa adalci” da suka mutu. (A. M. 24:15; Yoh. 5:28, 29) A ƙarshe, duk bayin Jehobah a duniya da suka yi biyayya, za su “sami ꞌyancin nan na ɗaukakar da za a yi wa ꞌyaꞌyan Allah.” (Rom. 8:21) Muna marmarin ganin wannan lokacin da za mu zama marasa zunubi, da kuma ꞌyaꞌyan Jehobah, Ubanmu na sama!

19. Ta yaya yanayinmu ya canja don alherin da Jehobah da Yesu suka yi mana? (Ka kuma duba akwatin nan, “ Gafarar da Jehobah Yake Mana.”)

19 Hakika a dā ba mu da bege, kamar saurayin da muka ambata a farkon talifin nan, wanda ya yi hasarar kome kuma ya gāji bashi mai yawa da ba zai iya biya ba. Amma Jehobah ya taimake mu. Yanzu mun sami ceto domin Jehobah ya buɗe hanyar da za a iya fanshe mu, kuma Yesu ya ba da abin da ake bukata don a ꞌyantar da mu. Za mu iya samun ꞌyanci daga zunubi da mutuwa da yake mun ba da gaskiya ga Yesu Kristi. Ƙari ga haka, idan Jehobah ya yafe mana zunubanmu, zai mai da mu marasa laifi kamar ba mu taɓa yin zunubi ba. Mafi muhimmanci ma, za mu iya zama aminan Jehobah, Ubanmu na sama mai ƙauna.

20. Me za mu tattauna a talifi na gaba?

20 Muna matukar godiya idan muka yi tunani mai zurfi a kan abin da Jehobah da Yesu suka yi mana. (2 Kor. 5:15) Da ba don taimakon da suka yi mana ba, da ba mu da wani bege! A talifi na gaba, za mu tattauna misalai da dama da suka nuna cewa idan Jehobah ya yafe mana, bai kamata mu bar zuciyarmu ta ci-gaba da daminmu ba.

WAƘA TA 10 Mu Yabi Jehobah Allahnmu!

a A wasu yaruka, fassarar kalmar nan “fansa” ita ce: “darajar rai,” ko “abin da aka biya.”