TALIFIN NAZARI NA 7
WAƘA TA 15 Mu Yabi Ɗan Allah!
Yadda Muke Amfana Idan Jehobah Ya Gafarta Mana
“A wurinka akwai gafara [ta gaske, NWT].”—ZAB. 130:4.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu bincika wasu misalai da ke Littafi Mai Tsarki da suka nuna yadda Jehobah yake gafartawa. Talifin nan zai sa mu ƙara gode wa Jehobah don gafartawarsa.
1. Me ya sa yake da wuya a san abin da mutum yake nufi idan ya ce ya yafe?
IDAN ka yi wa mutum laifi kuma ka ba shi haƙuri, sai ya ce: “Na yafe maka,” babu shakka za ka ji hankalinka ya kwanta! Amma zai yarda ku sake yin zumunci kamar dā kuwa? Ƙila ya yafe da gaske kuma yana so abokantakarku ta ci-gaba. Wataƙila kuma ba ya so ku sake magana a kan batun ne kawai. Idan mutane suka ce sun yafe, da wuya ka san abin da ke zuciyarsu.
2. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da yadda Jehobah yake gafartawa? (Ka kuma duba ƙarin bayani.)
2 Yadda Jehobah yake gafartawa ya yi dabam sosai da yadda ꞌyan Adam suke gafartawa. Babu mai gafartawa irinsa. Mai zabura ya yi magana game da Jehobah cewa: “A wurinka akwai gafara [ta gaske, NWT] domin a ji tsoronka.” a (Zab. 130:4) Idan Jehobah ya gafarta wa mutum, da “gaske” yake. Shi ne yake nuna mana yadda ya kamata mu gafarta wa mutane. A wasu lokuta, kalmar Ibrananci da marubutan Littafi Mai Tsarki suka yi amfani da ita wajen kwatanta yadda Jehobah yake gafartawa ta yi dabam da na ꞌyan Adam.
3. Mene ne bambancin yadda Jehobah yake gafartawa da yadda mutane suke gafartawa? (Ishaya 55:6, 7)
3 Idan Jehobah ya yafe wa mutum, ya goge zunubansa ke nan. Mutumin zai sake zama amininsa. A duk lokacin da mutum ya yi zunubi kuma ya tuba, Jehobah yakan yafe masa kwata-kwata. Hakan abin godiya ne sosai!—Karanta Ishaya 55:6, 7.
4. Mene ne Jehobah ya yi don ya taimaka mana mu fahimci yadda yake gafartawa?
4 Da yake yadda Jehobah yake gafartawa ya yi dabam da namu, zai yiwu mu fahimci yadda yake gafartawa kuwa? Ƙwarai kuwa! Jehobah ya yi amfani da misalai da dama don ya taimaka mana mu fahinci yadda yake gafartawa. A talifin nan, za mu tattauna wasu daga cikinsu. Waɗannan misalan za su nuna mana yadda Jehobah yake goge zunubin mutum kuma ya jawo mutumin kusa da shi. Wannan binciken zai sa mu ƙara gode wa Ubanmu mai ƙauna da yake gafarta mana a hanyoyi da dama.
JEHOBAH YAKAN KAWAR DA ZUNUBANMU
5. Da yake zunubi kamar kaya mai nauyi ne, me ke faruwa idan Jehobah ya gafarta wa mutum?
5 A Littafi Mai Tsarki, ana yawan kwatanta zunubin mutum da kaya mai nauyi. Alal misali, Sarki Dauda ya ce: “Zunubaina sun sha kaina, kamar kaya mai nauyi sun fi ƙarfina.” (Zab. 38:4) Amma idan mutum ya tuba, Jehobah zai gafarta masa zunubin da ya yi. (Zab. 25:18; 32:5) Kalmar Ibrananci da aka fassara zuwa “gafarta” a Zabura 25:18 da kuma Zabura 32:5 tana nufin a “ɗauke” wani abu. Saboda haka, idan Jehobah ya gafarta wa mutum zunubinsa, kamar ya ɗauke wa mutumin kaya mai nauyi ne.
6. Yaya nisan inda Jehobah yakan kai zunubin mutum idan ya yafe masa?
6 Akwai wani misali kuma da ya nuna cewa Jehobah yakan ɗauki zunubanmu ya kai su da nisa sosai. Zabura 103:12 ta ce: “Kamar yadda gabas take nesa da yamma, haka ne ya sa zunuban gangancinmu sun yi nesa da mu.” Gabas ce ta fi nisa daga yamma. Idan wani mutum ya nufi gabas, wani kuma ya nufi yamma, ba za su taɓa haɗuwa ba. Hakan yana nufin cewa, idan Jehobah ya gafarta mana, yana ɗaukan zunubanmu ne ya kai su da nisa sosai inda ba za a sake ganinsu ba. Wannan tabbaci ne cewa Jehobah yakan yafe mana gabaki ɗaya!
7. Mene ne Jehobah yake yi da zunubanmu bayan ya gafarta mana? (Mika 7:18, 19)
7 Amma Jehobah yakan ajiye zunubanmu a wani wuri ne? Aꞌa. Sarki Hezekiya ya ce: “Ka kawar da dukan zunubaina daga gabanka.” (Isha. 38:9, 17) Hakan ya nuna cewa idan mutum ya tuba, Jehobah yakan ɗauki zunubinsa ya yar domin kada ya sake ganin sa. Wani littafin da ke bayyana abin da ke Littafi Mai Tsarki ya ce abin da Hezekiya ya faɗa, yana nufin cewa Allah zai mai da zunubansa kamar ba su taɓa faruwa ba. A littafin Mika 7:18, 19, (karanta) an yi amfani da wani misali kuma don a nuna abin da Jehobah yake yi idan ya gafarta mana. Ayoyin sun ce Jehobah yakan jefar da zunubanmu a cikin teku mai zurfi. A zamanin dā, idan aka jefar da wani abu a cikin teku, ba za a sake samunsa ba.
8. Mene ne muka koya daga misalan da muka tattauna?
8 Misalan da muka tattauna sun koya mana cewa idan Jehobah ya gafarta mana, mun rabu da zunubanmu ke nan. Dauda ya ce: “Mai albarka ne mutumin da aka gafarta masa zunuban gangancinsa, wanda aka yafe masa zunubansa. Mai albarka ne mutumin da Ubangiji bai lissafta laifofinsa ba.” (Rom. 4:6-8) Abin da gafara ta gaske take nufi ke nan!
JEHOBAH YAKAN GOGE ZUNUBANMU
9. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah yana gafarta mana kwata-kwata?
9 Saboda fansar Yesu ne Jehobah yake goge zunuban mutanen da suka tuba. Bari mu tattauna wasu misalan da suka nuna yadda Jehobah yake yin hakan. Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah yakan wanke mu kuma ya tsabtace mu daga zunubanmu, sai mu zama marasa laifi. (Zab. 51:7; Isha. 4:4; Irm. 33:8) Jehobah da kansa ya kwatanta abin da yake yi da zunubanmu saꞌad da ya ce: “Ko da kun yi ja wur da zunubi, za ku yi fari fat kamar auduga. Ko da laifofinku sun sa kun yi ja kamar jini, za ku koma fari kamar farin ulu.” (Isha. 1:18) Idan wani abu mai jan kala ya zuba a farin riga, yana wuya sosai a wanke rigar. Amma, Jehobah ya ce ko da zunubanmu sun sa mun yi ja wur, zai wanke mu tsab yadda ba za a sake ganin ko alamar su ba.
10. Mene ne kuma aka kwatanta zunubanmu da shi don a taimaka mana mu fahimci yadda Jehobah yake gafartawa?
10 Kamar yadda muka gani a talifi da ya wuce, zunubi yana kama da bashi. (Mat. 18:32-35) Saboda haka, a duk lokacin da muka yi zunubi, kamar muna sake cin wani bashi ne. Gaskiyar ita ce, Jehobah yana bin mu bashi mai yawa sosai! Amma idan Jehobah ya yafe mana, kamar ya ce kada mu biya bashin da yake bin mu ne. Ba ya sake ce mu biya hakkin zunubin da ya riga ya gafarta mana. Hakan yana sa mu farin ciki sosai kamar wanda aka yafe masa bashin da ake binsa!
11. Wane misali ne kuma ya nuna yadda Jehobah yake gafarta mana? (Ayyukan Manzanni 3:19)
11 Ba yafe basussuka ko zunubanmu ne kawai Jehobah yake yi ba, yana kuma wanke su ne. (Karanta Ayyukan Manzanni 3:19.) Alal misali, a ce an ja layi a kan takarda da aka rubuta bashin da ake bin wani mutum, don a nuna cewa an yafe masa bashin, hakan ba zai hana ganin abin da aka rubuta kafin a ja layin ba. Amma idan aka ce an wanke abu, dabam ne. Don mu fahimci abin da ake nufi a nan, muna bukatar mu tuna cewa abin da mutane a dā suke rubutu da shi bai da wuyar wankewa. Mutum zai iya yin amfani da tsumma da aka jika a ruwa ya wanke abin da aka rubuta. Saboda haka, idan aka ce an “wanke” bashin da ake bin mutum, hakan yana nufin cewa, ba za a sake ganin sa ba. Mutane ba za su iya ganin bashin da aka rubuta a dā ba. Kamar dai ba a taɓa karɓan bashin ba. Sanin cewa idan Jehobah ya gafarta mana kamar ba mu taɓa yin zunubin ba ne, abin farin ciki ne!—Zab. 51:9.
12. Bisa ga Ishaya 44:22, mene ne ke faruwa idan Jehobah ya yafe mana?
12 Jehobah ya yi amfani da wani misali kuma don ya nuna yadda yake kawar da zunubanmu gabaki ɗaya. Ya ce: “Zan goge laifofinka, in kuma rufe zunubanka kamar da gajimare.” (Isha. 44:22, NWT) Idan Jehobah ya yafe mana, kamar ya yi amfani da gajimare ko girgije ya rufe laifofinmu ne, domin kada a sake ganin su.
13. Idan Jehobah ya gafarta mana, mene ne bai kamata mu yi ba?
13 Mene ne misalan nan suka koya mana? Idan Jehobah ya riga ya gafarta mana, bai kamata mu bar zuciyarmu ta ci-gaba da damunmu ba. Hadayar da Yesu ya yi tana sa a yafe zunubanmu. Kuma idan Jehobah ya yafe mana, kamar ba mu taɓa yin zunubin ba ne. Yadda Jehobah yake gafarta wa mutane ke nan idan sun tuba daga zunubansu.
JEHOBAH YANA SAKE ƊAUKAN MU A MATSAYIN AMINANSA
14. Me ya sa bai kamata mu yi shakka ba idan Jehobah ya yafe mana? (Ka kuma duba hotunan.)
14 Idan Jehobah ya gafarta mana, ba shakka mun sake zama aminansa ke nan. Sanin hakan zai taimaka mana kada zuciyarmu ta ci-gaba da damunmu. Ba za mu ji tsoro cewa Jehobah yana fushi da mu, ko yana neman damar hukunta mu ba. Jehobah ba zai taɓa yin hakan ba. Me ya sa bai kamata mu yi shakka ba idan Jehobah ya yafe mana? Jehobah ya gaya wa annabi Irmiya cewa: “Zan gafarta musu laifofinsu, ba kuwa zan sāke tunawa da zunubansu ba.” (Irm. 31:34) Waɗannan kalmomin ne manzo Bulus ya maimaita saꞌad da ya ce: “Ba zan kuwa ƙara tuna da zunubansu ba.” (Ibran. 8:12) Mene ne hakan yake nufi?
15. Me ake nufi da cewa Jehobah ba ya tuna da zunubanmu?
15 A Littafi Mai Tsarki, ba kowane lokaci ne kalmar nan “tunawa” take nufi mutum ya yi tunani ko ya tuna da wani abu ba. Amma, yana iya nufin mutum ya ɗau matakin yin wani abu. Alal misali, ɗaya daga cikin mutane da aka rataya a kan gungume kusa da Yesu ya ce: “Ya Yesu, ka tuna da ni saꞌad da ka shiga mulkinka!” (Luk. 23:42, 43) Me mutumin yake nufi da ya ce Yesu ya tuna da shi? Yana roƙon Yesu ya yi masa wani abu ne, ba wai ya tuna da shi kawai ba. Kuma abin da Yesu ya faɗa ya nuna cewa zai ta da shi daga mutuwa. Saboda haka, idan Jehobah ya ce ba zai sake tuna da zunubanmu ba, hakan yana nufin cewa ba zai ɗauki mataki a kan zunuban kuma ba. Ba zai hukunta mu a nan gaba don zunuban da ya riga ya gafarta mana ba.
16. Da yake mu kamar bayin zunubi ne, me yake faruwa idan Jehobah ya gafarta mana?
16 Idan Jehobah ya yafe mana, mun sami ꞌyanci ke nan. Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da wani misali don ya taimaka mana mu fahimci hakan. Ya ce da yake mu ajizai ne, mu kamar “bayin zunubi ne.” Amma idan Jehobah ya gafarta mana, yakan “ꞌyantar” da mu daga zunubin. (Rom. 6:17, 18; R. Yar. 1:5) A gaskiya, sanin cewa Jehobah ya gafarta mana yana sa mu yi farin ciki kamar bayin da suka sami ꞌyanci.
17. Idan Jehobah ya gafarta mana, ta yaya hakan yake sa mu warke? (Ishaya 53:5)
17 Karanta Ishaya 53:5. Littafi Mai Tsarki ya ce da yake mu masu zunubi ne, muna kama da mutanen da suke fama da muguwar cuta da take kashe mutane. Amma yadda Yesu ya ba da ransa a madadinmu yana sa Jehobah ya warkar da mu. (1 Bit. 2:24) Ta yaya? Zunubi yakan ɓata dangantakarmu da Jehobah. Amma saboda fansar Yesu, Jehobah zai iya gafarta mana zunubanmu kuma mu sake zama aminansa. Idan hakan ya faru, kamar ya warkar da mu ne daga muguwar cuta. Kuma kamar yadda wanda ya warke daga cuta mai tsanani yake farin ciki, mu ma muna farin ciki sosai idan Jehobah ya amince da mu kuma mun zama aminansa.
YADDA MUKE AMFANA IDAN JEHOBAH YA GAFARTA MANA
18. Mene ne muka koya daga misalan da muka tattauna game da yadda Jehobah yake gafartawa? (Ka kuma duba akwatin nan, “Yadda Jehobah Yake Gafarta Mana.”)
18 Mene ne muka koya daga misalan da muka tattauna game da yadda Jehobah yake gafartawa? Idan Jehobah ya gafarta mana, kamar ba mu taɓa yin zunubin ba ne, kuma ba zai hukunta mu don zunubin ba. Hakan zai sa mu zama aminan Ubanmu na sama. Ƙari ga haka, mun ga cewa gafartawa da Jehobah yake mana alheri ne domin yana ƙaunar mu.—Rom. 3:24.
19. (a) Me ya sa ya kamata mu gode ma Jehobah sosai? (Romawa 4:8) (b) Me za mu tattauna a talifi na gaba?
19 Karanta Romawa 4:8. Ya kamata kowannenmu ya gode ma Jehobah sosai don yadda yake gafarta mana zunubanmu. (Zab. 130:4) Amma, idan muna so Jehobah ya gafarta mana, muna bukatar mu yi wani abu. Yesu ya ce: “Idan . . . ba ku gafarta wa mutane ba, haka ma Ubanku ba zai gafarta muku laifofinku ba.” (Mat. 6:14, 15) Hakan ya nuna cewa yana da muhimmanci mu zama masu gafartawa kamar Jehobah. Ta yaya za mu yi hakan? Abin da za mu tattauna a talifi na gaba ke nan.
WAƘA TA 46 Muna Godiya, Ya Jehobah
a A Ibrananci, furuci da aka yi amfani da shi a Zabura 130:4 yana nufin gafara ta gaske, ba irin gafartawa da yawancin mutane suke yi ba. Juyin Littafi Mai Tsarki da dama ba su nuna wannan bambancin a yadda suka fassara ayar nan ba.