Yadda Za Ka Zama Aboki na Ƙwarai
KA TAƁA fuskantar wata matsala kuma ka ji kamar ba ka da wanda zai taimaka maka? Babu shakka, hakan zai iya sa mutum sanyin gwiwa kuma ya ji kamar ya kaɗaita. Littafi Mai Tsarki ya ce a “kwanakin ƙarshe za a sha wahala sosai.” (2 Tim. 3:1) Amma, idan muna fama da matsaloli, abokanmu za su taimaka mana. Littafi Mai Tsarki ya ce abokai na ƙwarai za su taimaka mana sosai “a kwanakin masifa.”—K. Mag. 17:17.
YADDA ABOKAI NA ƘWARAI SUKE TAIMAKAWA
Saꞌad da manzo Bulus yake zuwa wurare dabam-dabam yana waꞌazi, ya je ne tare da abokansa kuma sun taimaka masa sosai. (Kol. 4:7-11) Da aka sa Bulus a kurkuku a Roma, abokansa sun taya shi yin ayyukan da ba zai iya yi da kansa ba. Alal misali, Abafroditus ya kawo wa Bulus wasu abubuwa da ꞌyanꞌuwa da ke Filibi suka tara. (Filib. 4:18) Tikikus kuma ya kai wa ikilisiyoyi dabam-dabam wasiƙun da Bulus ya rubuta. Da taimakon abokansa, Bulus ya ci-gaba da ƙarfafa ikilisiyoyi a lokacin da aka tsare shi a gida, da kuma lokacin da yake kurkuku. Ta yaya kai ma za ka zama aboki na ƙwarai a yau?
Akwai misalan ꞌyanꞌuwanmu Kiristoci a yau da suka nuna yadda abokai suke kula da juna. Alal misali, wata ꞌyarꞌuwa majagaba a Sifen mai suna Elisabet ta faɗi yadda wata ꞌyarꞌuwa ta taimaka mata a lokacin da take cikin matsala. ꞌYarꞌuwar ta turo mata saƙonni da yawa masu ban ƙarfafa daga Littafi Mai Tsarki a lokacin da mahaifiyarta take fama da cutar kansa. ꞌYarꞌuwa Elisabet ta ce: “Idan na ga saƙonta, nakan yi farin ciki sosai don na san cewa akwai wanda ya damu da ni, kuma hakan yana ba ni ƙarfin da nake bukata.”—K. Mag. 18:24.
Za mu iya ƙara danƙon zumuncin da ke tsakanin mu da ꞌyanꞌuwa a ikilisiya ta wajen taimaka musu su iya halartar taro da kuma fita waꞌazi. Alal misali, za ka iya taimaka wa ꞌyanꞌuwa tsofaffi ta wajen kai su taro ko waꞌazi. Kuma idan ka yi hakan, za ka ƙarfafa su, kuma su ma za su ƙarfafa ka. (Rom. 1:12) Amma akwai wasu ꞌyanꞌuwa da ba sa iya barin gidajensu sanadiyyar tsufa ko rashin lafiya da dai sauransu. Ta yaya za mu iya taimaka musu?
KU TAIMAKI WAƊANDA BA SA IYA BARIN GIDAJENSU
Wasu ꞌyanꞌuwanmu maza da mata ba sa iya zuwa taro a Majamiꞌar Mulki sanadiyyar rashin lafiya mai tsanani ko wasu yanayoyi dabam. Abin da ya faru da wani ɗanꞌuwa mai suna David ke nan. An gano cewa yana da cutar kansa, kuma ya yi wata shida yana jinya. Da yake jinyar, Ɗanꞌuwa David da matarsa Lidia sun ci-gaba da halartar taro ta bidiyo.
Ta yaya ꞌyanꞌuwa a ikilisiya suka ƙarfafa su? Da zarar an gama taro, ꞌyanꞌuwa da suka halarci taron a Majami’ar Mulki sukan yi ƙoƙari su yi magana da
David da matarsa ta bidiyo. Ƙari ga haka, idan David da matarsa suka ba da amsa a taro, ꞌyanꞌuwa sukan tura musu saƙonni masu ban ƙarfafa bayan taron. Hakan ya sa David da matarsa suka ƙara kusantar ꞌyanꞌuwan sosai.Game da waꞌazi kuma fa? Ta yaya za mu iya taimaka wa ꞌyanꞌuwa da ba sa iya barin gidajensu? Ta wajen yin wasu canje-canje don mu iya yin waꞌazi da su. Hakan zai nuna musu cewa ba mu manta da su ba. (K. Mag. 3:27) Za mu iya rubuta wasiƙu ko kuma mu yi waꞌazi ta waya tare. Dattawa za su iya yin shiri don waɗanda ba sa iya barin gidajensu su shiga taron fita waꞌazi ta naꞌurarsu. Ɗanꞌuwa David da matarsa sun yi farin ciki da yake an yi irin wannan shirin a ikilisiyarsu. Ɗanꞌuwa David ya ce, “Kasancewa na ɗan lokaci da ꞌyanꞌuwa maza da mata saꞌad da ake taron fita waꞌazi da kuma yin adduꞌa tare da su yana ƙarfafa mu sosai.” Ƙari ga haka, idan zai yiwu, za mu iya kai ɗalibinmu gidan wani ɗanꞌuwa ko ꞌyarꞌuwa da ba ta iya barin gida don mu yi nazari a wurin. Amma kafin mu yi hakan, zai dace mu nemi izinin ɗanꞌuwan ko ꞌyarꞌuwar.
Kasancewa tare da ꞌyanꞌuwanmu da ba sa iya barin gidajensu zai taimaka mana mu ƙara kusantar su, ta haka za mu ga halayensu masu kyau da za mu iya yin koyi da su. Alal misali, idan ka yi waꞌazi tare da irin waɗannan ꞌyanꞌuwan kuma ka ga yadda suke amfani da Kalmar Allah wajen taimaka wa mutane, hakan zai sa ka ƙara daraja su. Ban da haka ma, idan kana taimaka wa ꞌyanꞌuwa maza da mata su iya halartar taro ko fita waꞌazi, za ka sami sabbin abokai.—2 Kor. 6:13.
A lokacin da Bulus yake fama da matsaloli, abokinsa Titus ya je wurinsa kuma hakan ya ƙarfafa shi sosai. (2 Kor. 7:5-7) Wannan ya nuna mana cewa, yana da kyau mu ƙarfafa ꞌyanꞌuwanmu da kalamanmu. Amma ba shi ke nan ba, zai dace mu je wurinsu kuma mu taimaka musu da duk wani aiki da suke da shi.—1 Yoh. 3:18.
KU TAIMAKA WA ABOKANKU IDAN ANA TSANANTA MUSU
ꞌYanꞌuwanmu maza da mata a Rasha sun kafa misali mai kyau wajen taimaka wa juna. Alal misali, bayan da ꞌyan sanda suka bincika gidan Ɗanꞌuwa Sergey da matarsa Tatyana, sun tafi da su don su yi musu tambayoyi. Ɗanꞌuwa Sergey ya ce da aka saki matarsa kuma ta isa gida, nan da nan wata ꞌyarꞌuwa ta ziyarce ta. Ba da daɗewa ba, wasu ꞌyanꞌuwa maza da mata suka zo kuma suka taya su shirya abubuwan da ꞌyan sandan suka watsar.
Sergey ya daɗa da cewa: “Tun da daɗewa ina son abin da ke Karin Magana 17:17, da ta ce: ‘Aboki na ƙwarai yana nuna ƙauna a koyaushe, kuma shi ɗanꞌuwa ne da ke ba da taimako a lokacin damuwa.’ (K. Mag. 17:17, NWT) A lokacin nan da muke fama da tsanantawa, na daɗa gani cewa abin da ke wannan ayar gaskiya ce domin mun bukaci taimakon abokanmu sosai. Jehobah ya ba mu abokai masu ƙarfin zuciya da suka taimaka mana.” a
Yayin da muke fama da matsaloli, muna bukatar abokan da za su taimaka mana. Kuma za mu fi bukatar taimakonsu a lokacin ƙunci mai girma. Saboda haka, bari mu yi iya ƙoƙarinmu yanzu don mu zama abokai na ƙwarai!—1 Bit. 4:7, 8.
a Ka duba talifin nan mai jigo “Jehovah Has Provided Friends Who Are Fearlessly at My Side,” a jw.org.