Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 3

WAƘA TA 35 Mu Riƙa Yin “Abin da Ya Fi Kyau”

Ka Tsai da Shawarwari da Ke Faranta wa Jehobah Rai

Ka Tsai da Shawarwari da Ke Faranta wa Jehobah Rai

“Tsoron Yahweh shi ne mafarin hikima, sanin Mai Tsarkin nan kuwa ganewa ne.”K. MAG. 9:10.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga yadda sani da kuma fahimtar wani batu zai taimaka mana mu tsai da shawarwari masu kyau.

1. Wane abu mai wuya ne muke bukatar mu yi kowace rana?

 KOWACE RANA, muna bukatar mu tsai da shawarwari. Wasu shawarwarin ba su da wuya, kamar zaɓan abin da za mu ci da safe ko kuma lokacin da za mu yi barci da dare. Amma wasu suna da wuya. Domin za su iya shafan lafiyarmu, ko danginmu, ko ibadarmu ko kuma farin cikinmu. Burinmu shi ne mu tsai da shawarwari da za su amfane mu da iyalinmu. Mafi muhimmanci ma shi ne, mu tsai da shawarwari da za su sa Jehobah farin ciki.—Rom. 12:​1, 2.

2. Me zai taimaka maka ka tsai da shawarwari masu kyau?

2 Za ka tsai da shawarwari masu kyau idan (1) ka san gaskiyar batun, (2) ka yi ƙoƙarin sanin raꞌayin Jehobah game da batun, kuma (3) ka yi tunanin wasu abubuwan da za ka iya yi. A wannan talifin, za mu tattauna waɗannan abubuwa uku, kuma za mu ga abubuwan da za su taimaka mana mu riƙa tsai da shawarwari masu kyau.—K. Mag. 2:11.

KA SAN GASKIYAR BATUN

3. Ka ba da misalin da ya nuna amfanin sanin gaskiyar batu kafin ka tsai da shawara.

3 Abu na farko da zai taimaka maka ka tsai da shawara mai kyau shi ne sanin gaskiyar batun. Me ya sa hakan yake da muhimmanci? Ga wani misali. A ce wani mai ciwo mai tsanani ya je wurin likita. Shin, likitan zai ba shi magani ba tare da ya duba shi ko yi masa wasu tambayoyi ba? Likitan da ya ƙware ba zai yi hakan ba. Kai ma za ka tsai da shawarwari masu kyau idan ka yi tunani sosai kuma ka san gaskiyar batun. Ta yaya za ka yi hakan?

4. Bisa ga Karin Magana 18:​13, me za ka yi don ka san gaskiyar batun? (Ka kuma duba hoton.)

4 A yawancin lokuta, za ka san gaskiyar batu idan ka yi tambaya. A ce an gayyace ka zuwa wani biki. Yaya za ka san ko zai dace ka je? Idan ba ka san wanda ya shirya bikin da abubuwan da za a yi a wurin ba, zai dace ka yi ma wanda ya gayyace ka tambayoyi kamar: “A ina ne za a yi bikin kuma wane lokaci ne za a yi? Mutane nawa ne za su zo bikin? Waye ne uban bikin? Su waye ne za su zo bikin? Me da me za a yi a wurin? Za a raba giya a bikin?” Amsoshin tambayoyin nan za su taimaka maka ka tsai da shawarar da ta dace.—Karanta Karin Magana 18:13.

Ka san gaskiyar batun ta wurin yin tambayoyi (Ka duba sakin layi na 4) a


5. Me ya kamata ka yi bayan ka gane gaskiyar batun?

5 Bayan ka gane gaskiyar batun, ka yi tunani a kan yanayin gabaki ɗaya. A ce ka ji cewa mutanen da ba sa bin ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki za su zo bikin. Ko cewa za a ba da giya a wurin kuma za ka iya shan yadda kake so ba tare da wani ya hana ka ba. Ba ka ganin cewa mutane za su yi yadda suka ga dama a wannan bikin? (1 Bit. 4:3) Wani abu kuma shi ne, a ce zuwa bikin zai hana ka zuwa taro ko waꞌazi, me za ka yi? Idan ka fahimci batun ciki da waje kuma ka yi tunani a kansa, zai yi maka sauƙi ka tsai da shawarar da ta dace. Amma akwai wani abu kuma da kake bukatar ka yi. Kana bukatar ka san raꞌayin Jehobah game da batun.—K. Mag. 2:6.

KA SAN RAꞌAYIN JEHOBAH

6. Bisa ga Yakub 1:​5, me ya sa ya dace mu roƙi Jehobah ya taimaka mana?

6 Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka san raꞌayinsa. Jehobah ya ce zai ba mu hikimar sanin abin da zai faranta masa rai. Kuma yana ba da wannan hikimar “hannu sake ba tare da gori ba.”—Karanta Yakub 1:5.

7. Ta yaya za ka san raꞌayin Jehobah game da wani batu? Ka ba da misali.

7 Bayan ka roƙi Jehobah ya taimake ka ka san abin da yake so ka yi, ka lura ka ga yadda zai amsa adduꞌarka. A ce kana tafiya sai ka ɓata hanya, kuma ka tambayi wani ya gaya maka inda za ka bi, za ka tafi tun ba ka ji abin da zai faɗa ba? Aꞌa. Za ka natsu ka ji abin da zai gaya maka. Mu ma idan muka roƙi Jehobah ya taimake mu mu san abin yake so mu yi, zai dace mu natsu kuma mu yi ƙoƙarin gane abin da yake gaya mana, ta wurin bincika dokokinsa da ƙaꞌidodinsa da suka shafi batun a Littafi Mai Tsarki. A ce kana tunanin ko za ka je bikin da aka ambata ɗazu, zai yi kyau ka duba abin da Littafi Mai Tsarki ya ce a kan bukukuwan shaye-shaye, da abokan banza, da amfanin sa alꞌamuran Mulkin Allah a kan gaba maimakon jin daɗin kanmu.—Mat. 6:33; Rom. 13:13; 1 Kor. 15:33.

8. Me za ka yi idan kana bukatar a taimaka maka da wasu bayanai? (Ka kuma duba hoton.)

8 A wasu lokuta za ka bukaci a taimaka maka da wasu bayanai. Wataƙila ka nemi shawarar wani ɗanꞌuwa ko ꞌyarꞌuwa da ta manyanta. Amma za ka kuma amfana idan ka yi bincike da kanka. Za ka sami bayanai da za su taimaka maka sosai idan ka yi amfani da Littafin Bincike Don Shaidun Jehobah da kuma littafin nan, Scriptures for Christian Living. Ka tuna cewa burinka shi ne ka yi zaɓin da zai faranta wa Jehobah rai.

Ka san raꞌayin Jehobah (Ka duba sakin layi na 8) b


9. Me zai tabbatar mana da cewa zaɓin da muka yi zai faranta wa Jehobah rai? (Afisawa 5:17)

9 Me zai tabbatar mana da cewa zaɓin da muka yi zai faranta wa Jehobah rai? Da farko muna bukatar mu san Jehobah sosai. Littafi Mai Tsarki ya ce, “Sanin Mai Tsarkin nan kuwa ganewa ne.” (K. Mag. 9:10) Hakika za mu faranta wa Jehobah rai idan muka san halayensa, da nufinsa da kuma abin da yake so da wanda ya tsana. Ka tambayi kanka, ‘Bisa ga abin da na sani game da Jehobah, wane zaɓi ne idan na yi zai faranta masa rai?’—Karanta Afisawa 5:17.

10. Me ya sa bin ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki ya fi bin alꞌadarmu ko raꞌayin iyalinmu?

10 A wasu lokuta, idan muna so mu sa Jehobah farin ciki, dole mu yi abin da wasu na kusa da mu ba sa so. Alal misali, wasu iyaye za su iya ce lallai sai ꞌyarsu ta auri mai kuɗi ko da mutumin bai damu da dangantakarsa da Jehobah ba. Ba laifi ba ne iyaye su ga cewa ꞌyarsu ta auri wanda zai kula da ita, amma zai yi kyau ꞌyar ta tambaye kanta: “Mutumin nan zai taimaka min in kusaci Jehobah kuwa? Mene ne raꞌayin Jehobah?” Amsar tana Matiyu 6:33. A ayar Yesu ya ce, “Muhimmin abu na farko shi ne ku miƙa kanku ga alꞌamuran mulkin.” Ko da yake muna daraja iyayenmu da kuma mutanen garinmu, mun fi so mu yi abin da zai faranta wa Jehobah rai.

KA YI TUNANIN WASU ABUBUWAN DA ZA KA IYA YI

11. Bisa ga Filibiyawa 1:​9, 10, me zai taimaka mana mu iya zaɓan abin da ya fi kyau?

11 Bayan ka bincika ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da suka shafi batun, kana bukatar ka yi tunani a kan abubuwa dabam-dabam da za ka iya yi. (Karanta Filibiyawa 1:​9, 10.) Yin hakan zai sa ka zama mai ganewa, wato za ka dubi kowane zaɓi kuma ka gane abin da zai iya faruwa idan ka yi shi. Ƙila yin zaɓin ya zo maka da sauƙi. Amma fa a wasu lokuta, sanin zaɓin da zai fi kyau bai da sauƙi. Duk da haka, yin tunani sosai zai sa ka gane zaɓin da idan ka yi, ba za ka ɓata wa Jehobah rai ba.

12-13. A batun neman aiki, ta yaya yin tunani a kan sakamakon kowane zaɓi zai taimaka maka?

12 Ga wani misali. A ce kana neman aiki don ka ciyar da iyalinka. Kuma ka sami wurare biyu da suka yarda cewa za su ɗauke ka aiki. Sai ka yi tunani a kan kowannensu. Alal misali ka yi tunani a kan irin aikin da za su ba ka, da yawan lokaci da zai ci, da nisan wurin aikin da dai sauransu. Kowannensu aiki ne da Kirista zai iya yi. Wataƙila ma ka fi son ɗaya daga cikinsu domin irin aikin ko kuma albashin ya fi yawa. Duk da haka, akwai wasu abubuwan da ya kamata ka duba kafin ka zaɓi wanda za ka yi.

13 Alal misali, zai yi kyau ka san ko wanne ne a cikinsu zai hana ka zuwa taro. Ƙari ga haka, akwai wani a cikinsu da zai hana ka kasancewa tare da iyalinka da kuma taimaka musu su kusaci Jehobah? Irin wannan tunanin zai taimaka maka ka fi mai da hankali ga abin da ya fi muhimmanci, wato ibadarka da bukatun iyalinka maimakon neman kuɗi. Hakan zai sa ka yi zaɓin da zai sa Jehobah farin ciki kuma ya yi maka albarka.

14. Ta yaya ƙauna da yin tunani a kan sakamakon zaɓinmu zai taimaka mana kada mu sa wasu tuntuɓe?

14 Yin tunani a kan sakamakon zaɓinmu zai sa mu lura da yadda abin da muka zaɓa zai shafi mutane, don kada mu sa wani ya yi “tuntuɓe.” (Filib. 1:​10, NWT) Zai dace mu yi hakan saꞌad da muke zaɓan irin kayan da za mu sa, ko irin adon da za mu yi. Alal misali, mai yiwuwa akwai irin kaya ko adon da muka fi so. Amma idan mun san cewa wasu a ikilisiya ko mutanen yankinmu ba za su so shi ba fa? Zai dace mu nuna cewa mun damu da su. Ƙauna za ta sa mu yi abin da zai sa mutane su ji daɗi ba abin da zai gamshe mu kawai ba. (1 Kor. 10:​23, 24, 32; 1 Tim. 2:​9, 10) Yin irin wannan tunanin zai sa mu yi zaɓin da zai nuna cewa muna ƙaunar mutane kuma muna daraja su.

15. Idan kana so ka tsai da wata shawara mai muhimmanci, me kake bukatar ka yi?

15 Idan kana so ka tsai da wata shawara mai muhimmanci, zai dace ka yi tunani a kan abubuwan da kake bukatar ka yi. Yesu ya koya mana cewa ya kamata mu riƙa yin lissafi kafin mu ɗauki mataki. (Luk. 14:28) Saboda haka, kafin ka ce, ga abin da za ka yi, zai yi kyau ka lura da yawan lokacin da zai ci, da abubuwan da za ka yi amfani da su, da dai sauransu. Ban da haka ma, a wasu lokuta zai dace ka tattauna da iyalinka don kowa ya san yadda zai taimaka a sami nasara. Me ya sa yin hakan yake da muhimmanci? Domin wataƙila zai sa ka ga cewa kana bukatar ka yi gyara a matakin da za ka ɗauka ko kuma ka yi wani zaɓi dabam. Ƙari ga haka, idan ka gaya wa iyalinka kuma ka ji raꞌayin kowa, hakan zai sa su goyi bayan zaɓin da ka yi da zuciya ɗaya don a sami nasara.—K. Mag. 15:22.

KA TSAI DA SHAWARA DA ZA TA YI NASARA

16. Waɗanne abubuwa ne za su taimaka maka ka yi zaɓi mai kyau? (Ka kuma duba akwatin nan, “ Yadda Za Ka Yi Zaɓi Mai Kyau.”)

16 Za ka yi zaɓi mai kyau idan ka bi shawarwarin da aka ambata a baya. Domin ka san gaskiyar batun, kuma ka bincika ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da za su sa ka yi zaɓin da zai faranta wa Jehobah rai. Abin da za ka yi yanzu shi ne ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka yi nasara.

17. Mene ne zai taimaka maka ka tsai da shawarwari masu kyau?

17 Ko da ka tsai da shawarwari masu kyau a dā, ka tuna cewa ainihin abin da zai sa ka tsai da shawara mai kyau shi ne idan ka dogara ga Jehobah, ba iliminka ba. Jehobah ne kaɗai zai iya ba ka sani da ganewa. Kuma sani da ganewa ne suke sa mutum ya zama mai hikima. (K. Mag. 2:​1-5) Da taimakon Jehobah za ka tsai da shawarwarin da za su faranta masa rai.—Zab. 23:​2, 3.

WAƘA TA 28 Yadda Za Mu Zama Abokan Jehobah

a BAYANI A KAN HOTUNA: Wasu ꞌyanꞌuwa matasa suna magana a kan wani biki da aka gayyace su. Kowannensu na da saƙon gayyatar a wayarsa.

b BAYANI A KAN HOTO: Ɗaya daga cikinsu yana yin bincike don ya san ko zai je, ko ba zai je ba.