Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 2

WAƘA TA 132 Yanzu Mun Zama Ɗaya

Maza, Ku Girmama Matanku

Maza, Ku Girmama Matanku

“Ku maza, sai ku . . . girmama su.”1 BIT. 3:7.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga yadda maza za su girmama matansu ta maganganunsu da kuma ayyukansu.

1. Mene ne ɗaya cikin dalilan da suka sa Jehobah ya ce mutane su yi aure?

 JEHOBAH “Allah mai farin ciki” ne, kuma yana so mu ma mu kasance da farin ciki. (1 Tim. 1:11) Ya ba mu abubuwa da dama da za su sa mu ji daɗin rayuwa. (Yak. 1:17) Wani abin da ya ba mu kyauta shi ne aure, kuma yana so maꞌaurata su yi farin ciki. A ranar aure, mata da miji sukan yi alkawari cewa za su ƙaunaci juna kuma su girmama juna. Idan mata da miji suka ƙaunaci juna, za su ji daɗin zaman aurensu.—K. Mag. 5:18.

2. Wane hali ne maza da yawa suke nuna wa matansu a yau?

2 Abin baƙin cikin shi ne, a yau mutane da yawa da suka yi aure, sun manta da alkawarin nan da suka yi ma junansu. Don haka ba sa farin ciki. Kwana-kwanan nan, Hukumar Lafiya ta Duniya ta ba da rahoto cewa maza da yawa suna dūkan matansu, suna zaginsu, kuma suna wulaƙanta su a hanyoyi dabam-dabam. Wasu maza suna girmama matansu idan suna gaban jamaꞌa, amma suna wulaƙanta su a gida. Ƙari ga haka, maza da yawa suna kallon batsa. Wannan ma yana sa mata baƙin ciki kuma su ji kamar ba su da daraja.

3. Me ya sa wasu maza suke wulaƙanta matansu?

3 Me ya sa wasu maza suke wulaƙanta matansu? Wataƙila don mahaifinsu shi ma azzalumi ne. Hakan zai iya sa su ɗauka cewa wulaƙanta mace ba kome ba ne. Wasu kuma suna wulaƙanta matansu ne domin haka ake yi a inda suke. Irin mazan nan suna ganin kamar wulaƙanta matansu ne zai nuna cewa su jarumai ne. Wasu mazan kuma ba a koya musu cewa yana da kyau mutum ya zama mai kamun kai kuma ya riƙa danne fushinsa ba. Ƙari ga haka, kallon batsa yana sa maza su zama da raꞌayi marar kyau game da mata da kuma jimaꞌi. Masana sun kuma ce a lokacin korona, maza da yawa sun soma wulaƙanta matansu. Amma wulaƙanta mace abu ne da bai kamata ba, ko da mene ne dalilin mutum.

4. Me ya kamata mazan da suke bauta ma Jehobah su guje wa, kuma me ya sa?

4 Ya kamata mazan da suke bauta ma Jehobah su yi hankali don kar su bi raꞌayin mutanen duniya game da mata. a Me ya sa? Wani dalili shi ne domin raꞌayin mutum ko tunaninsa ne yake sa ya yi wani abu. Manzo Bulus ya gaya ma shafaffun Kiristoci da suke Roma cewa ‘kada su yarda tunani irin na zamanin nan ya bi da hankalinsu.’ (Rom. 12:​1, 2) Waɗanda Bulus ya yi wa wannan maganar ba sabbin Kiristoci ba ne, sun yi kwan biyu suna bauta ma Jehobah. Amma abin da ya faɗa ya nuna cewa har ila, wasu daga cikinsu ba su daina bin raꞌayin mutanen duniya ba. Shi ya sa ya ƙarfafa su su canja tunaninsu da halinsu. A yau ma, ya kamata bayin Jehobah su bi wannan gargaɗi. Abin baƙin ciki ne cewa wasu maza a ikilisiya suna bin raꞌayin mutanen duniya har suna wulaƙanta matansu. b Yaya Allah yake so maza su bi da matansu? Nassin da aka ɗauko jigon talifin nan ya ba mu amsar wannan tambayar.

5. Bisa ga 1 Bitrus 3:​7, yaya ya kamata miji ya bi da matarsa?

5 Karanta 1 Bitrus 3:7. Jehobah ya umarci maza su girmama matansu. Mijin da yake girmama matarsa zai dinga nuna mata ƙauna da kuma alheri. A talifin nan, za mu tattauna yadda mutum zai nuna wa matarsa cewa yana girmama ta. Amma kafin nan, bari mu tattauna wasu abubuwa da idan mutum yana yin su, zai zubar da mutuncin matarsa.

KA GUJI YIN DUK WANI ABIN DA ZAI ZUBAR DA MUTUNCINTA

6. Yaya Jehobah yake ɗaukan mazan da suke cin zalin matansu? (Kolosiyawa 3:19)

6 Kada ka ci zalin matarka. Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah yana ƙin mai son ta da hankali. (Zab. 11:5) Kuma ya tsani mazan da suke yi wa matansu mugunta. (Mal. 2:16; karanta Kolosiyawa 3:19.) Nassin da muke tattaunawa a talifin nan, wato 1 Bitrus 3:7 ta nuna cewa idan mutum yana yi wa matarsa mugunta, Jehobah zai yi fushi da shi. Adduꞌarsa ma ayar ta ce Jehobah ba zai ji ba.

7. Bisa ga Afisawa 4:​31, 32, wane irin magana ne bai kamata maza su yi ba? (Ka kuma duba “Maꞌanar Wasu Kalmomi.”)

7 Kar ka yi mata tsawa ko maganar da zai dame ta. Wasu suna wa matansu magana da fushi, kuma suna gaya musu maganganun da ba su dace ba. Amma Jehobah ba ya son mai “haushi, da fushi, da faɗa, da ɓata suna,” c ko kaɗan. (Karanta Afisawa 4:​31, 32.) Jehobah yana jin duk wani abin da mutum yake gaya wa matarsa, kuma ba ya so miji ya yi wa matarsa baƙar magana ko da a gida ne inda ba kowa. Idan mutum yana wa matarsa maganar da zai ɓata mata rai, hakan zai ɓata zaman aurensu, kuma zai ɓata dangantakarsa da Jehobah.—Yak. 1:26.

8. Mene ne raꞌayin Jehobah game da abubuwan batsa, kuma me ya sa?

8 Kada ka kalli abubuwan batsa. Mene ne raꞌayin Jehobah game da abubuwan batsa? Ya tsane su. Don haka idan mutum yana kallon hotunan batsa, Jehobah zai yi fushi da shi, kuma mutuncin matarsa zai zube. d Jehobah yana son miji ya zama mai riƙon amana. Miji mai riƙon amana ba zai yi lalata da wata ba ko ya yi tunanin hakan. Kuma Yesu ya ce idan mutum ya yi wa mace kallon shaꞌawa, ya riga ya yi zina ke nan da ita “a zuciyarsa.” eMat. 5:​28, 29.

9. Me ya sa Jehobah ba ya son ganin miji yana zub da mutuncin matarsa a lokacin jimaꞌi?

9 A lokacin jimaꞌi, kar ka sa ta yin abin da zai zub da mutuncinta. A lokacin jimaꞌi, wasu maza sukan sa matansu su yi abin da zai dame su ko ya sa su ji kamar ba su da daraja. Jehobah ya tsani irin halin nan. Yana so maza su ƙaunaci matansu, su daraja su, kuma kar su yi abin da zai dame su. (Afis. 5:​28, 29) Idan wanda yake bauta ma Jehobah yana yin abubuwan da matarsa ba ta so, ko yana kallon batsa kuma fa? Me zai taimaka masa ya canja halinsa?

YADDA ZA KA DAINA YIN ABIN DA YAKE ZUB DA MUTUNCINTA

10. Me ya sa zai dace maza su yi ƙoƙari su bi halin Yesu?

10 Me zai taimaka wa mutum ya daina yin abin da yake cutar da matarsa ko zub da mutuncinta? Ya yi ƙoƙari ya bi halin Yesu. Me ya sa? Domin ko da yake Yesu bai yi aure ba, yadda ya bi da mabiyansa ya nuna yadda ya kamata maza su bi da matansu. (Afis. 5:25) Yanzu bari mu tattauna abin da maza za su iya koya daga yadda Yesu ya bi da almajiransa, da yadda ya yi musu magana.

11. Yaya Yesu ya bi da manzanninsa?

11 Yesu ya yi wa manzanninsa alheri a kullum, kuma ya girmama su. Bai yi musu tsawa ba, kuma bai nuna musu iko ba. Duk da cewa shi ne Ubangijinsu da kuma Shugabansu, bai rena su ko ya sa su ji tsoronsa ba. A maimako, ya ƙasƙantar da kansa har ya yi musu hidima. (Yoh. 13:​12-17) Ya ce wa mabiyansa: “Ku … koya daga wurina, domin ni mai tawaliꞌu ne, mai sauƙin kai, kuma za ku sami hutu a zuciyarku.” (Mat. 11:​28-30) Yesu mai tawaliꞌu ne. Mai tawaliꞌu ba rago ba ne. Amma halin nan yana nuna cewa shi jarumi ne, domin yana iya kame kansa. Ko an ɓata masa rai, yakan natsu kuma ya yi tunani kafin ya yi wani abu.

12. Yaya Yesu ya yi magana da mutane?

12 Yesu ya ƙarfafa mutane da maganganunsa. Bai yi wa mabiyansa magana da tsawa ba. (Luk. 8:​47, 48) Akwai lokutan da maƙiyansa suka zage shi kuma suka yi ta ƙoƙarin ɓata masa rai, duk da haka “bai mai da zagin ba.” (1 Bit. 2:​21-23) A wasu lokuta, Yesu yakan yi shiru maimakon ya ba su amsa da fushi. (Mat. 27:​12-14) Wannan abin koyi ne sosai ga maza!

13. Ta yaya miji zai “manne wa matarsa” kamar yadda aka ce a Matiyu 19:​4-6? (Ka kuma duba hoton.)

13 Yesu ya umurci maza su zama masu riƙon amana. Har ya maimaita abin da Ubansa ya faɗa cewa miji “ya manne wa matarsa.” (Karanta Matiyu 19:​4-6.) Asalin kalmar da aka yi amfani da ita a ayar nan tana nufin ya manne wa matarsa yadda ake manne abu da gam mai ƙarfi. Wato ya kamata ƙaunar da ke tsakanin mata da miji ta yi ƙarfi sosai har ya zama kamar an manne su biyun ne da gam. Idan wani abu ya yi ƙoƙarin raba su, su biyun za su ji zafi. Duk mijin da yake ƙaunar matarsa haka, ba zai kalli wani abin batsa ba. Zai kawar da idanunsa nan-da-nan “daga abubuwan banza.” (Zab. 119:37) Kamar Ayuba, zai yi niyya sosai a zuciyarsa cewa ba zai yi wa wata mace kallon shaꞌawa ba, sai dai matarsa.—Ayu. 31:1.

Wani ɗanꞌuwa da yake ƙaunar matarsa ya ƙi ya kalli hotunan batsa (Ka duba sakin layi na 13) g


14. Waɗanne abubuwa ne wanda yake wulaƙanta matarsa yake bukatar ya yi?

14 Idan mutum yana yi wa matarsa mugunta, ko yana mata baƙar magana, akwai abubuwa da yake bukatar ya yi don ya gyara dangantakarsa da Jehobah da kuma matarsa. Na ɗaya, ya yarda cewa yana da babbar matsala, kuma Jehobah yana ganin duk wani abin da yake yi. (Zab. 44:21; M. Wa. 12:14; Ibran. 4:13) Na biyu, ya daina wulaƙanta matarsa kuma ya canja halinsa. (K. Mag. 28:13) Na uku, ya ba wa matarsa haƙuri kuma ya nemi gafararta, saꞌan nan ya roƙi Jehobah ya yafe masa. (A. M. 3:19) Ya kuma roƙi Jehobah ya taimaka masa ya yi niyyar canja halinsa. Kuma ya roƙe shi ya taimaka masa ya riƙa tunani, da magana, da kuma yin abubuwa yadda ya dace. (Zab. 51:​10-12; 2 Kor. 10:5; Filib. 2:13) Na huɗu, ya koyi yadda zai ƙi kowane irin mugunta. Hakan zai nuna cewa yana taimakon kansa kamar yadda yake roƙon Allah ya taimake shi. (Zab. 97:10) Na biyar, ya je ya gaya wa dattawa abin da yake yi don su taimaka masa. (Yak. 5:​14-16) Na shida, ya shirya abubuwan da zai kiyaye don kar ya maimaita kuskurensa. Mijin da yake kallon batsa ma yana bukatar ya ɗauki duka matakan nan. Idan ya yi ƙoƙari ya canja halinsa, Jehobah zai taimake shi. (Zab. 37:5) Ya kamata mutum ya daina yin duk wani abin da yake zub da mutuncin matarsa, amma ba shi ke nan ba. Yana kuma bukatar ya koyi yadda zai girmama ta. Ta yaya zai yi hakan?

YADDA ZA KA GIRMAMA TA

15. Ta yaya miji zai nuna wa matarsa cewa yana ƙaunarta?

15 Ka nuna mata cewa kana ƙaunarta. Wani abin da ya sa wasu maza suke jin daɗin zaman aurensu shi ne, suna yin wani abu kowace rana don su nuna wa matansu yadda suke ƙaunarsu. (1 Yoh. 3:18) Miji zai iya nuna wa matarsa ƙauna ta wurin yin ƙananan abubuwa kamar riƙe hannunta ko rungumarta. Zai kuma iya tura mata saƙo a waya ya ce, “Ina kewarki,” ko ya ce, “Yaya kike?” Bayan wani lokaci kuma, zai iya yin rubutu a kan takarda ya bayyana mata irin son da yake mata ko ya saya mata wani abu. Idan miji yana yin irin abubuwan nan, zai nuna cewa yana girmama matarsa, kuma zai ƙara danƙon zumunci tsakaninsu.

16. Me ya sa yake da kyau miji ya gaya wa matarsa yadda yake ji da ita?

16 Ka gaya mata yadda kake ji da ita. Wanda yake girmama matarsa zai riƙa gaya mata abin da ya sa take da muhimmanci a gare shi, kuma zai ƙarfafa ta. Wani abin da zai taimaka shi ne, ya dinga gode mata don abubuwan da take yi. (Kol. 3:15) Idan miji yana gaya wa matarsa yadda abubuwan da take yi suke burge shi, hakan zai sa hankalinta ya kwanta. Kuma za ta ji cewa yana ƙaunarta da kuma girmama ta.—K. Mag. 31:28.

17. Ta yaya mutum zai nuna wa matarsa cewa yana daraja ta?

17 Ka riƙa mata alheri kuma ka daraja ta. Wanda yake ƙaunar matarsa zai ɗauke ta da muhimmanci sosai. Zai riƙa ganinta a matsayin kyauta mai daraja sosai da Jehobah ya ba shi. (K. Mag. 18:22; 31:10) Don haka zai riƙa mata alheri kuma zai daraja ta, har a lokacin yin jimaꞌi. Alal misali, ba zai matsa mata ta yi abin da zai sa ta ji wani iri, ko ta yi abin da zai sa zuciyarta ta dame ta, ko ta ji kamar ba ya daraja ta ba. f Shi ma bai kamata ya yi abin da zai dami zuciyarsa ba.—A. M. 24:16.

18. Me ya kamata maza su yi niyyar yi? (Ka kuma duba akwatin nan, “ Hanyoyi Huɗu da Za Ka Iya Daraja Matarka.”)

18 Maza, Jehobah yana farin ciki sosai a duk lokacin da ya ga kuna ƙoƙari ku girmama matanku a kome da kuke yi. Ku yi niyya sosai cewa za ku girmama su ta wurin yi musu alheri, da daraja su, da nuna musu cewa kuna ƙaunarsu, da kuma guje wa duk wani abin da zai zub da mutuncinsu. Idan kuna haka, za su ga cewa kuna ƙaunarsu, kuma suna da muhimmanci a gare ku. Ku girmama matanku, hakan zai sa ku ci-gaba da zama abokan Jehobah, kuma wannan ita ce dangantakar da ta fi muhimmanci.—Zab. 25:14.

WAƘA TA 131 ‘Abin da Allah Ya Haɗa’

a Ya kamata mazaje su karanta talifin nan mai jigo, “Kana Daraja Mata Yadda Jehobah Yake Yi?” da ke Hasumiyar Tsaro ta Janairu 2024.

b Idan mijinki yana wulaƙanta ki, za ki amfana sosai idan kika karanta talifin nan mai jigo, “Abin da Zai Taimaka wa Wadanda Ake Cin Zarafinsu a Gida.” Yana a cikin jerin talifofi da ake kira “Karin Batutuwa” a jw.org/ha ko a manhajar JW Library®.

c MAꞌANAR WASU KALMOMI: Ko da yake an yi amfani da “ɓata suna” ne a nan, ainihin abin da ake nufi shi ne baƙar magana. Hakan ya haɗa da kiran mutum da sunan da ke nuna cewa an rena shi, da zaginsa, da kuma gaya masa maganganun da za su yi masa zafi a rai.

d Ka ga talifin nan mai jigo, Pornography Can Shatter Your Marriage,” a jw.org ko a manhajar JW Library.

e Idan maigidanki yana kallon hotunan batsa, za ki amfana sosai idan kika karanta talifin nan mai jigo, “Me Za Ki Yi Idan Maigidanki Yana Kallon Batsa? da ke Hasumiyar Tsaro ta Agusta 2023.

f Littafi Mai Tsarki bai gaya mana abin da ya kamata, da wanda bai kamata mata da miji su yi a lokacin jimaꞌi ba. Kowane mutum da matarsa ne za su zaɓi yadda za su yi shi don su girmama Jehobah, su gamsar da juna, kuma kar zuciyarsu ta dame su. Wannan ba abin da mata da miji za su tattauna da wani ba ne.

g BAYANI A KAN HOTO: Abokan aikin wani ɗanꞌuwa sun kawo wata takarda da ke ɗauke da hotunan batsa suna so su nuna masa.