Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 4

WAƘA TA 18 Muna Godiya Domin Mutuwar Yesu

Mene ne Fansar Yesu Ta Nuna Mana?

Mene ne Fansar Yesu Ta Nuna Mana?

“Ga yadda Allah ya nuna mana ƙaunarsa.”1 YOH. 4:9.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga abin da mutuwar Yesu ta nuna mana game da halin Jehobah da Yesu Kristi.

1. Me ya sa yake da muhimmanci mu dinga zuwa Taron Tunawa da Mutuwar Yesu kowace shekara?

 A GASKIYA, Jehobah ya ba mu kyauta na musamman saꞌad da ya turo Ɗansa ya mutu dominmu! (2 Kor. 9:15) Mutuwar Yesu ce ta sa muke iya zama abokan Jehobah. Kuma ita ce ta buɗe mana hanyar samun rai na har abada. Hakika ya kamata mu gode wa Jehobah sosai da ya ƙaunace mu haka, har ya ba da Ɗansa dominmu! (Rom. 5:8) Yesu yana so mu ɗauki wannan hadayar da muhimmanci sosai, kuma mu ci-gaba da nuna godiyarmu, shi ya sa ya ce mu dinga zuwa Taron Tunawa da Mutuwarsa kowace shekara.—Luk. 22:​19, 20.

2. Me za mu tattauna a talifin nan?

2 A shekarar nan, ran Asabar 12 ga Afrilu, 2025 ne za mu yi Taron Tunawa da Mutuwar Yesu. Ba shakka dukanmu muna marmarin zuwa taron. A makonni kafin taron da kuma bayan taron, zai yi kyau mu nemi lokaci mu yi tunani mai zurfi a kan wannan abin da Jehobah da Yesu suka yi mana. A talifin nan, za a tattauna abin da fansar Yesu ta nuna mana game da Jehobah da Ɗansa. A talifi na gaba kuma, za a bayyana yadda za mu amfana daga fansar, da yadda za mu nuna godiyarmu.

ABIN DA FANSAR TA NUNA MANA GAME DA JEHOBAH

3. Ta yaya mutuwar mutum ɗaya zai ceci miliyoyin mutane? (Ka kuma duba hoton.)

3 Fansar ta nuna mana cewa Jehobah mai adalci ne. (M. Sha. 32:4) Ta yaya? Saꞌad da Adamu ya yi rashin biyayya, ya zama mai zunubi kuma daga baya ya mutu. Da yake mu ꞌyaꞌyansa ne, mu ma masu zunubi ne kuma muna mutuwa. (Rom. 5:12) Jehobah yana so ya cire mana wannan zunubi da mutuwa, shi ya sa ya aiko da Yesu ya ba da ransa a madadinmu. Amma ta yaya mutuwar mutum ɗaya zai ceci miliyoyin mutane? Manzo Bulus ya ce: “Kamar yadda mutane da yawa suka zama masu zunubi ta wurin rashin biyayyar mutum ɗaya [wato Adamu], haka kuma mutane da yawa za su zama masu adalci ta wurin biyayyar mutum ɗaya [wato Yesu].” (Rom. 5:19; 1 Tim. 2:6) Mutum ɗaya marar zunubi ne ya yi rashin biyayya. Shi ya sa dukan mutane suka zama masu zunubi kuma suna mutuwa. Don haka ya dace a ce idan mutum ɗaya marar zunubi ya yi biyayya ga Allah, zai iya ceton dukan mutane daga zunubi da mutuwa.

Ta wurin mutum ɗaya ne muka zama masu zunubi kuma muna mutuwa. Haka ma ta wurin mutum ɗaya ne za mu sami ceto (Ka duba sakin layi na 3)


4. Me ya sa Jehobah bai bar ꞌyaꞌyan Adamu masu halin kirki su ci-gaba da rayuwa har abada kawai ba?

4 Amma dole ne Yesu ya mutu kafin a cece mu? Me ya sa Jehobah bai bar ꞌyaꞌyan Adamu masu halin kirki su ci-gaba da rayuwa har abada kawai ba? Wasu suna ganin cewa da Jehobah ya yi hakan, da ya magance matsalar cikin sauƙi. Amma a gun Jehobah, yin hakan ba adalci ba ne. Me ya sa? Domin idan ya yi hakan, abin zai yi kamar Adamu bai yi babban zunubi ba, kuma kamar ꞌyaꞌyansa ba su zama masu zunubi ba.

5. Me ya tabbatar mana da cewa Jehobah zai yi abin da ya dace a koyaushe?

5 Ƙari ga haka, da a ce Jehobah ya bar ꞌyaꞌyan Adamu sun ci-gaba da rayuwa har abada kuma bai ba da fansar ba, da hakan zai nuna cewa shi da kansa ba ya bin ƙaꞌidodin da ya kafa. Kuma ƙila hakan zai sa mutane su soma shakkarsa, har su ce ba zai yi abin da ya ce zai yi a nan gaba ba. Amma tun da Jehobah ya ba da Ɗansa hadaya don ya tabbatar da cewa an yi abin da ya dace, ba shakka zai yi abin da ya dace a koyaushe.

6. Wane abu ne kuma ya sa Jehobah ya turo Yesu ya zo ya mutu? (1 Yohanna 4:​9, 10)

6 Akwai wani abu kuma na musamman da ya sa Jehobah ya turo Yesu ya zo ya mutu dominmu. Me ke nan? Ƙaunar da yake mana. (Yoh. 3:16; karanta 1 Yohanna 4:​9, 10.) Jehobah yana so mu rayu har abada kuma mu zama ꞌyan iyalinsa, shi ya sa ya turo Ɗansa ya mutu dominmu. Lokacin da Adamu ya yi zunubi, Jehobah ya cire shi daga iyalinsa. Don haka, dukanmu ba a haife mu a cikin iyalin Jehobah ba. Amma da yake an ba da fansa, dukan waɗanda suka gaskata da Allah kuma suka yi masa biyayya za su zama ꞌyan iyalinsa. Ko a yanzu ma, za mu iya kusantar sa, kuma mu bauta masa tare da ꞌyanꞌuwanmu kamar iyali ɗaya. Babu shakka, Jehobah yana ƙaunarmu sosai!—Rom. 5:​10, 11.

7. Ta yaya za mu fahimci irin ƙaunar da Jehobah yake mana?

7 Za mu iya fahimtar irin ƙaunar da Jehobah yake mana idan muka yi tunani a kan irin zafin da ya ji a ransa lokacin da ya ga Yesu yana shan wahala. Shaiɗan ya ce idan bawan Allah ya sha wahala, ba zai riƙe amincinsa ba. Shi ya sa Jehobah ya bar Yesu ya sha wahala kafin ya mutu, don ya nuna cewa hakan ƙarya ne. (Ayu. 2:​1-5; 1 Bit. 2:21) Jehobah ya ga lokacin da maƙiyan Yesu suka yi masa dariya, sojoji suka yi masa dūkan tsiya, kuma suka rataya shi a kan gungume. Kuma Jehobah ya ga yadda suka bar Ɗansa ya yi ta fama da zafi mai tsanani, har lokacin da ya mutu. (Mat. 27:​28-31, 39) Yana da ikon hana abubuwan nan faruwa. Alal misali, da maƙiyan Yesu suka ce: “Bari Allah ya cece shi yanzu, idan yana so.” Da Jehobah yana so, da ya ceci Yesu. (Mat. 27:​42, 43) Amma idan Jehobah ya yi hakan a lokacin, ba za a ba da fansar ba, kuma da ta mu ta ƙare ke nan. Shi ya sa Jehobah ya bar Ɗansa ya sha wahala har ya mutu.

8. Me ya tabbatar da cewa Jehobah ya damu sosai da ya ga yadda aka azabtar da Ɗansa? (Ka kuma duba hoton.)

8 Kada mu ɗauka cewa da yake Jehobah mai iko duka ne, abu ba ya damunsa. Littafi Mai Tsarki ya ce ya halicce mu a kamanninsa. Da yake muna damuwa idan muka ga abu marar daɗi, babu shakka shi ma yana damuwa. Zabura 78:​40, 41 sun ce Jehobah ya yi “baƙin ciki” da ya ga halin Israꞌilawa. Ka kuma tuna labarin Ibrahim da Ishaƙu. Jehobah ya gaya wa Ibrahim ya yi hadaya da Ishaku, wanda shi ne kaɗai Ɗansa. (Far. 22:​9-12; Ibran. 11:​17-19) Ba ka ganin Ibrahim ya damu sosai lokacin da yake shirin kashe ɗansa? Ba shakka, baƙin cikin da Jehobah ya ji da ya ga mugayen mutane suna azabtar da Ɗansa har mutuwa ya ma fi na Ibrahim!—Ka kalli bidiyon nan, Ku Yi Koyi da Bangaskiyarsu—Ibrahim, Kashi na 2, a jw.org/ha.

Jehobah ya ji zafi sosai da ya ga Ɗansa yana shan wahala (Ka duba sakin layi na 8)


9. Mene ne Romawa 8:​32, 38, 39 suka nuna maka game da ƙaunar da Jehobah yake ma kowannenmu?

9 Yadda Jehobah ya ba da Ɗansa ya nuna cewa babu wanda ya kai shi ƙaunarmu. Danginmu ko abokinmu da ya fi ƙaunarmu ma, bai kai Jehobah ƙaunarmu ba. (Karanta Romawa 8:​32, 38, 39.) Duk ƙaunar da muke yi wa kanmu ma, bai kai yadda Jehobah yake ƙaunarmu ba. Kana so ka rayu har abada? Ka san cewa Jehobah ya fi ka son hakan. Kana so a yafe maka zunubanka? To ka san cewa Jehobah ya fi ka son hakan. Abin da yake so ka yi kawai shi ne, ka nuna godiyarka ta wurin ba da gaskiya ga fansar da kuma bin maganarsa. Ba shakka, fansar kyauta ce babba, da ta nuna cewa Jehobah yana ƙaunarmu ba kaɗan ba. Kuma a aljanna, za mu koyi abubuwa da dama da Jehobah ya yi mana don yana ƙaunarmu.—M. Wa. 3:11.

ABIN DA FANSAR TA NUNA MANA GAME DA YESU

10. (a) Me ya fi damun Yesu game da yadda za a kashe shi? (b) Ta yaya Yesu ya tsarkake sunan Jehobah? (Ka kuma duba akwatin nan, “ Yesu Ya Tsarkake Sunan Jehobah Ta Wurin Riƙe Amincinsa.”)

10 Yesu ba ya so ya ji an ɓata suna Jehobah, ko kaɗan. (Yoh. 14:31) Yesu ya yi baƙin ciki sosai don mutane za su ɓata sunan Ubansa. Ta yaya za su yi hakan? Za su ce ya yi saɓo har su kashe shi. Shi ya sa ya yi adduꞌa ya ce: “Ubana, idan zai yiwu, ka ɗauke mini kwaf na wahalar nan.” (Mat. 26:39) Amma da yake Yesu ya riƙe amincinsa ga Jehobah har mutuwa, ya nuna cewa duk abin da Shaiɗan ya faɗa game da Jehobah ƙarya ne.

11. Ta yaya Yesu ya nuna cewa yana ƙaunar mutane sosai? (Yohanna 13:1)

11 Yadda Yesu ya ba da ransa ya nuna mana cewa yana ƙaunar mutane sosai, musamman mabiyansa. (K. Mag. 8:31; karanta Yohanna 13:1.) Alal misali, Yesu ya san cewa abin da zai zo ya yi a duniya ba sauƙi, musamman irin mutuwar da zai yi. Duk da haka, ya zo kuma ya yi dukan abubuwan nan da zuciya ɗaya, domin yana ƙaunar mutane. Yesu ya nuna wa mutane ƙauna sosai ta wurin yi musu waꞌazi, da koyar da su, da kuma taimaka musu. Har a ranar da aka kashe shi, Yesu ya ɗauki lokaci ya wanke ƙafafun manzanninsa, ya koyar da su, kuma ya ƙarfafa su. (Yoh. 13:​12-15) Ƙari ga haka, duk da zafin da yake ji a lokacin da aka rataya shi, ya ba wa wani mai laifi bege cewa zai shiga aljanna, kuma ya ce wa Yohanna ya kula da mahaifiyarsa. (Luk. 23:​42, 43; Yoh. 19:​26, 27) A gaskiya, ban da mutuwar da ya yi dominmu, Yesu ya nuna wa mutane ƙauna sosai a dukan rayuwarsa a duniya.

12. Waɗanne abubuwa ne Yesu yake mana a yau?

12 Duk da cewa Yesu ya mutu ne “sau ɗaya tak ba ƙari,” akwai abubuwa da yawa da yake mana har wa yau. (Rom. 6:10) Me yake yi? Fansar ta buɗe mana hanyar samun abubuwa da yawa, kuma Yesu yana iya ƙoƙarinsa ya ga cewa mun sami abubuwan nan. A yanzu haka, Yesu yana aiki sosai a matsayin Sarki, da Babban Firist, da kuma shugaban ikilisiyar Kirista. (1 Kor. 15:25; Afis. 5:23; Ibran. 2:17) Shi ne yake ja-gorantar aikin tattara shafaffun Kiristoci da taro mai girma, kuma zai kammala wannan aikin kafin ƙarshen ƙunci mai girma. a (Mat. 25:32; Mar. 13:27) Ƙari ga haka, yana ba mu abubuwan da muke bukata don mu bauta wa Jehobah da kyau babu fashi a waɗannan kwanakin ƙarshe. Kuma yana hakan ne ta wurin bawan nan mai aminci. (Mat. 24:45) Ban da haka ma, a lokacin da zai yi Sarauta na Shekara Dubu, zai ci-gaba da yin hidima don amfaninmu. Tabbas, lokacin da Jehobah ya ba da Ɗansa dominmu, ya ba da shi ne don ya yi mana abubuwa da yawa, ba don ya mutu a madadinmu kawai ba!

KA CI-GABA DA KOYAN SABBIN ABUBUWA

13. Ta yaya za ka ƙara fahimtar irin ƙaunar da Allahnmu Jehobah da Yesu Kristi suke mana?

13 Za ka ƙara fahimtar irin ƙaunar da Allahnmu Jehobah da Yesu Kristi suke mana, idan ka ci-gaba da yin tunani mai zurfi a kan abin da suka yi mana. Za ka iya karanta ɗaya daga cikin littattafan Linjila ko fiye da hakan a lokacin Tunawa da Mutuwar Yesu. Ka yi karatun cikin natsuwa, kar ka ce sai ka karanta surori da yawa a rana guda. A maimakon haka, ka yi karatun a hankali, don ka ga wasu abubuwan da suke nuna cewa Jehobah da Yesu suna ƙaunarmu sosai. Bayan haka, ka yi ƙoƙari ka gaya ma wasu abin da ka gano.

14. Ta yaya yin bincike zai taimaka mana mu ci-gaba da koyan abubuwa game da fansar Yesu da dai sauransu? (Zabura 119:97; ka kuma duba hoton.)

14 Idan ka daɗe sosai a ƙungiyar Jehobah, wataƙila ka ga kamar ba wani sabon abin da za ka koya kuma a batun adalcin Jehobah, da ƙaunarsa, da kuma fansa. Amma gaskiyar ita ce, ba za mu taɓa gama fahimtar abubuwan nan da ma wasu abubuwa game da Jehobah ba. Me zai taimaka maka ka ci-gaba da koyo? Ka yi ta karanta bayanan da ake yi a littattafanmu kuma ka yi nazarinsu. Idan ka ga wani abin da ba ka gane sosai ba, ka yi bincike. Bayan haka, ka yi ta tunani a kan abin da ka gano, da kuma abin da hakan ya nuna maka game da Jehobah, da Ɗansa, da irin ƙaunar da suke maka.—Karanta Zabura 119:97.

Ko da mun daɗe sosai a ƙungiyar Jehobah, akwai sabbin abubuwan da za mu iya koya a batun fansa kuma mu nuna godiyarmu (Ka duba sakin layi na 14)


15. Me ya sa yake da kyau mu ci-gaba da ƙoƙarin koyan sabbin abubuwa daga Littafi Mai Tsarki?

15 Idan ka yi bincike amma ba ka gano wani sabon abu ko wani abin da ya burge ka ba, kar ka damu. Me ya sa? Domin idan kana nazari, kamar kana neman gwal ne. Kana bukatar haƙuri. Masu neman gwal za su iya yin awoyi da yawa ko kwanaki suna nema. Duk da haka, sukan ci-gaba da nema, don sun san cewa ko da ƙarami ne suka samu, yana da daraja sosai. Gaskiyar ita ce, duk wani sabon abin da ka koya a Littafi Mai Tsarki ya fi gwal daraja! (Zab. 119:127; K. Mag. 8:10) Saboda haka, ka ci-gaba da karanta Littafi Mai Tsarki da yin bincike, don ka koyi sabbin abubuwa.—Zab. 1:2.

16. Ta yaya za mu nuna cewa muna yin koyi da Jehobah da Yesu?

16 Idan kana nazari, ka yi tunani a kan yadda za ka bi abin da ka koya. Alal misali, da yake Jehobah mai adalci ne sosai, kai ma kada ka nuna wa mutane bambanci. Kamar Yesu, ka nuna cewa kana ƙaunar Jehobah da mutane sosai, ta wurin yin abin da Jehobah yake so da kuma taimaka wa mutane, ko da hakan zai sa ka sha wahala. Ƙari ga haka, ka yi wa mutane waꞌazi kamar yadda Yesu ya yi, don su ma su zo su amfana daga alherin da Jehobah ya yi mana.

17. Me za mu tattauna a talifi na gaba?

17 Idan muka ci-gaba da yin nazari da tunani mai zurfi a kan fansar, za mu ƙara ƙaunar Jehobah da Yesu. Kuma su ma za su ƙara ƙaunarmu. (Yoh. 14:21; Yak. 4:8) Don haka, bari mu yi amfani da dukan abubuwan da Jehobah ya ba mu, mu ci-gaba da yin nazari game da fansar nan. A talifi na gaba, za mu ga yadda fansar take amfanarmu, da kuma yadda za mu nuna godiyarmu don ƙaunar da Jehobah ya nuna mana.

WAƘA TA 107 Mu Yi Koyi da Allah a Nuna Ƙauna

a A Afisawa 1:​10, manzo Bulus ya ce za a tattaro “abubuwan da suke a sama.” A Matiyu 24:31 da Markus 13:27 kuma, Yesu ya ce za a tattaro “waɗanda aka zaɓa.” Amma abin da suke nufi ba ɗaya ba ne. Bulus yana magana ne a kan lokacin da Jehobah yake zaɓan waɗanda za su yi mulki tare da Yesu. Yesu kuma yana magana ne a kan lokacin da za a tattara sauran shafaffu da suka rage a duniya a kai su sama, wato a lokacin ƙunci mai girma.