Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 1

WAƘA TA 2 Jehobah Ne Sunanka

Mu Daukaka Jehobah

Mu Daukaka Jehobah

JIGON SHEKARARMU NA 2025: Ku miƙa wa Jehobah ɗaukakar da ta cancanci sunansa.ZAB. 96:8.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga yadda za mu ba wa Jehobah ɗaukakar da ta cancance shi.

1. Mene ne mutane da yawa suka fi so su yi?

 MUTANE da yawa a yau, sun fi so su ɗaukaka kansu. Alal misali, a dandalin sada zumunta, wasu suna iya ƙoƙarinsu wajen jan hankalin mutane zuwa kansu da kuma abubuwan da suke yi. Mutane kaɗan ne suke ɗaukaka Jehobah. A wannan talifin, za mu tattauna abin da ake nufi da cewa mu ɗaukaka Jehobah, da abin da zai sa mu yi hakan. Ƙari ga haka, za mu ga yadda za mu miƙa wa Jehobah ɗaukakar da ta cancance shi, da kuma yadda zai ɗaukaka sunansa a nan gaba.

ME AKE NUFI DA CEWA MU ƊAUKAKA JEHOBAH?

2. Ta yaya Jehobah ya nuna wa Israꞌilawa ɗaukakarsa a Babban Tudun Sinai? (Ka kuma duba hoton.)

2 Mene ne ɗaukaka? A Littafi Mai Tsarki, idan aka ce a “ɗaukaka” mutum, ana nufin a sa kowa ya gan shi da daraja. Jehobah ya nuna cewa shi mai ɗaukaka ne sosai bayan da ya ceci Israꞌilawa daga ƙasar Masar. Ya sa miliyoyin Israꞌilawa sun taru kusa da Babban Tudun Sinai don su ji abin da zai gaya musu. Sai Jehobah ya sa hayaƙi mai duhu ya rufe tudun. Dukan tudun ya soma girgiza sosai, ana ta walƙiya, ga tsawa da kuma babbar ƙarar ƙaho. (Fit. 19:​16-18; 24:17; Zab. 68:8) Babu shakka, yadda Jehobah ya nuna musu ɗaukakarsa ya burge su ba kaɗan ba.

Jehobah ya nuna wa Israꞌilawa ɗaukakarsa a hanya mai ban mamaki a Tudun Sinai (Ka duba sakin layi na 2)


3. Ta yaya za mu ɗaukaka Jehobah?

3 Mu ꞌyan Adam za mu iya ɗaukaka Jehobah kuwa? Ƙwarai da gaske. Za mu ɗaukaka Jehobah idan muna gaya wa mutane game da yawan ikonsa da kuma halayensa masu kyau. Kuma za mu sa a ɗaukaka shi idan mun miƙa masa yabo don abubuwan da muka yi da taimakon sa. (Isha. 26:12) Wani da ya ɗaukaka Jehobah sosai shi ne Sarki Dauda. Akwai lokacin da ya yi adduꞌa a gaban jamaꞌar Israꞌila kuma ya ce wa Allah: “Ya Yahweh, girma da iko naka ne! Ɗaukaka da kuma daraja da nasara naka ne gama kome a sama da ƙasa naka ne.” Da ya kammala adduꞌar, “sai dukan jamaꞌa suka yabi Yahweh.”—1 Tar. 29:​11, 20.

4. Ta yaya Yesu ya ɗaukaka Jehobah?

4 A lokacin da Yesu yake duniya, ya ɗaukaka Jehobah ta wajen sanar da cewa Jehobah ya ba shi ikon yin abubuwan ban mamaki. (Mar. 5:​18-20) Yesu ya kuma sa an ɗaukaka Jehobah ta wajen maganganun da ya yi game da shi, da kuma yadda ya kula da mutane. Akwai ranar da Yesu yake koyar da mutane a wata majamiꞌa. Kuma wata mata da aljani ya sa ta yi shekaru 18 tana rashin lafiya tana wurin. Aljanin ya sa ta tanƙware, ba ta iya miƙewa. Matar ta wahala sosai. Da Yesu ya gan ta, ya tausaya mata kuma ya ce: “Uwargida, an warkar da ke daga rashin lafiyarki.” Sai ya sa hannunsa a kanta, nan-da-nan sai ta miƙe tsab kuma “ta yabi Allah.” Ta gode wa Jehobah sosai don yadda ya ba ta lafiya. (Luk. 13:​10-13) Hakika, ya dace da ta ɗaukaka Jehobah, kuma mu ma muna da dalilai masu kyau na yabonsa.

ME YA SA MUKE ƊAUKAKA JEHOBAH?

5. Waɗanne dalilai ne muke da su na ɗaukaka Jehobah?

5 Muna ɗaukaka Jehobah domin muna daraja shi sosai. Jehobah ya cancanci mu daraja shi, domin shi mai iko duka ne, ikonsa babu iyaka. (Zab. 96:​4-7) Halittunsa sun nuna cewa shi mai hikima ne sosai. Shi ne ya ba mu rai da dukan abubuwan da muke bukata. (R. Yar. 4:11) Shi mai aminci ne. (R. Yar. 15:​4, NWT) Yana yin nasara a koyaushe kuma idan ya yi alkawari, yana cika shi. (Yosh. 23:14) Shi ya sa annabi Irmiya ya ce: “Cikin dukan masu hikima na alꞌummai, kuma cikin dukan mulkokinsu, babu wani kamarka.” (Irm. 10:​6, 7) Ba shakka muna da dalilai masu kyau da za su sa mu ɗaukaka Ubanmu na sama. Amma ba ɗaukaka shi kawai muke yi ba, muna ƙaunar sa sosai.

6. Me ya sa muke ƙaunar Jehobah?

6 Muna ɗaukaka Jehobah domin muna ƙaunarsa sosai. Muna ƙaunar Jehobah domin yana da halaye masu kyau. Shi mai jinƙai ne kuma mai tausayi. (Zab. 103:13; Isha. 49:15) Kuma idan abu ya dame mu, shi ma yakan dame shi. (Zak. 2:8) Yana jawo mu kusa da shi don mu zama abokansa. (Zab. 25:14; A. M. 17:27) Kuma shi mai sauƙin kai ne. Littafi Mai Tsarki ya ce, ‘Yakan sunkuya daga can bisa yana kallon sammai da duniya. Yakan ta da talakawa daga ƙura.’ (Zab. 113:​6, 7) Shi ya sa muke so mu ci-gaba da ɗaukaka Allahnmu.—Zab. 86:12.

7. Da yake mun san gaskiya game da Jehobah, me za mu iya yi?

7 Muna ɗaukaka Jehobah domin muna son mutane su san shi. Mutane da yawa ba su san Jehobah ba. Me ya sa? Domin Shaiɗan ya sa ana faɗan abubuwa da yawa game da Shi da ba gaskiya ba ne. (2 Kor. 4:4) Shaiɗan ya sa mutane suna gani kamar Jehobah mai fushi ne sosai, bai damu da mu ba kuma shi ne ya sa muke shan wahala. Amma mun san gaskiyar! Don haka, za mu iya fahimtar da mutane har su zo su yabi Jehobah. (Isha. 43:10) Zabura ta 96 ta nuna muhimmancin ɗaukaka Jehobah. Bari mu tattauna wannan zaburar. Yayin da muke haka, ka yi tunanin yadda za ka miƙa wa Jehobah ɗaukakar da ta cancance shi.

TA YAYA ZA MU MIƘA WA JEHOBAH ƊAUKAKAR DA TA CANCANCE SHI?

8. Ta yaya za mu ɗaukaka Jehobah? (Zabura 96:​1-3)

8 Karanta Zabura 96:​1-3. Za mu iya ɗaukaka Jehobah ta wajen abin da muke faɗa. Ayoyin nan sun ce mu “rera [waƙa] ga Yahweh,” mu “yabi Sunansa,” mu “yi shelar cetonsa,” kuma mu “yi shelar ɗaukakarsa cikin alꞌummai.” Duk waɗannan hanyoyi ne da za mu ɗaukaka Ubanmu na sama. Bayin Jehobah a dā sun yi ta gaya wa mutane game Jehobah, da alheran da ya yi musu. (Dan. 3:​16-18; A. M. 4:29) Ta yaya mu ma za mu yi hakan a yau?

9-10. Mene ne ka koya daga labarin Angelena? (Ka kuma duba hoton.)

9 Akwai wata ꞌyarꞌuwa mai suna Angelena, a a ƙasar Amirka. ꞌYarꞌuwar ta ɗaukaka sunan Jehobah a inda take aiki ba tsoro. Kamfaninsu ta yi taro da dukan sabbin maꞌaikatanta kuma Angelena tana cikinsu. A irin taron nan, akan ba wa sabbin maꞌaikata dama su gaya wa sauran maꞌaikatan wani abu game da rayuwarsu. Don haka, Angelena ta shirya hotuna da za ta nuna musu kuma ta gaya musu yadda take farin ciki don tana bauta wa Jehobah. Amma kafin a zo kanta, wani da ya gabatar da kansa ya ce iyayensa Shaidun Jehobah ne, sai ya soma faɗin abubuwa marasa kyau game da mu da kuma imaninmu. Angelena ta ce: “Zuciyata ta soma bugawa don tsoro. Amma sai na ce: ‘Gaskiya ba zan yi shiru ba. Dole in gaya musu gaskiya game da Jehobah.’”

10 Da mutumin ya gama magana, nan-da-nan sai Angelena ta yi adduꞌa a zuciyarta. Kuma cikin natsuwa ta ce masa: “Ni ma iyayena Shaidun Jehobah ne, na zaɓi in zama Mashaidiyar Jehobah, kuma ban daina ba har wa yau.” Duk da cewa Angelena ta ji tsoro, ta natsu ta nuna wa abokan aikinta hotunan da ta ɗauka da abokanta, da suka nuna irin farin cikin da take yi don tana bauta ma Jehobah. Ta kuma bayyana musu imaninta cikin basira. (1 Bit. 3:15) Wane sakamako aka samu? Da Angelena ta gama bayaninta, mutumin shi ma ya canja raꞌayinsa. Har ya faɗi wasu kyawawan abubuwa da ya shaida lokacin da yake tarayya da Shaidun Jehobah saꞌad da yake ƙarami. Angelena ta ce: “Jehobah ya cancanci a ɗaukaka shi. Kuma babban gata ne a gare ni in gaya wa mutane gaskiya game da shi.” Mu ma babban gata ne a gare mu mu yabi Jehobah kuma mu ɗaukaka shi, ko da wasu suna ƙoƙarin ɓata masa suna.

Za mu iya ɗaukaka Jehobah ta abin da muke faɗa game da shi, da dukiyarmu, da kuma halinmu (Ka duba sakin layi na 9-10) b


11. Tun daga zamanin dā har wa yau, ta yaya bayin Allah suke bin abin da ke Zabura 96:8?

11 Karanta Zabura 96:8. Za mu iya ɗaukaka Jehobah da dukiyarmu. Bayin Jehobah sun daɗe suna haka. (K. Mag. 3:9) Alal misali, Israꞌilawa sun ba da abin da suke da shi don a gina haikalin Jehobah kuma a kula da shi. (2 Sar. 12:​4, 5; 1 Tar. 29:​3-9) Wasu mabiyan Yesu su ma sun yi amfani da dukiyarsu wajen kula da Yesu da kuma manzanninsa. (Luk. 8:​1-3) Kiristoci a lokacin manzannin Yesu ma sun aika kuɗi don su taimaka wa ꞌyanꞌuwansu da suke fama da yunwa. (A. M. 11:​27-29) A yau, mu ma za mu iya ɗaukaka Jehobah ta wajen ba da gudummawa da son rai.

12. Ta yaya gudummawarmu take sa a ɗaukaka Jehobah? (Ka kuma duba hoton.)

12 Ga wani labari da ya nuna yadda gudummawarmu ta sa an ɗaukaka Jehobah. An yi ƙarancin ruwan sama sosai a shekara ta 2020 a Zimbabwe. Yunwa ya kusan kashe mutane da yawa, har da wata ꞌyarꞌuwa mai suna Prisca. Duk da haka, Prisca ba ta daina fita waꞌazi ran Laraba da Jummaꞌa kamar yadda ta saba ba, har a lokacin damuna. Maƙwabtanta sun yi ta mata dariya cewa tana zuwa waꞌazi maimakon ta je gona, kuma sun yi ta cewa, “Ai yunwa zai kashe ki.” Sai Prisca ta ce, “Jehobah ba zai taɓa barin bayinsa ba.” Ana nan, ba da daɗewa ba sai ƙungiyarmu ta tura kayan agaji wurinsu. Kuɗaɗen da muke bayarwa ne suka sa aka iya tura musu kayan agaji. Abin ya burge maƙwabtan Prisca har sun ce mata, “Allah bai bar ki ba. Mu ma muna so mu koya game da shi.” Hakan ya sa maƙwabtanta bakwai sun soma zuwa taro.

Za mu iya yin amfani da dukiyarmu mu ɗaukaka Jehobah (Ka duba sakin layi na 12) c


13. Me za mu yi don halinmu ya ɗaukaka Jehobah? (Zabura 96:9)

13 Karanta Zabura 96:9. Za mu iya ɗaukaka Jehobah ta halinmu. Jehobah ya gaya wa firistoci su tsabtace jikinsu kafin su yi hidima a haikalinsa. (Fit. 40:​30-32) Mu ma ya kamata mu tsabtace jikinmu, amma abin da ya fi muhimmanci shi ne mu guji yin abin da Jehobah ba ya so, don hakan ƙazanta ne. (Zab. 24:​3, 4; 1 Bit. 1:​15, 16) Littafi Mai Tsarki ya ce mu yar da ‘halinmu na dā,’ kuma mu ɗauki “sabon hali.” Abin da hakan yake nufi shi ne, mu yi iya ƙoƙarinmu mu guje wa tunani da hali marasa kyau. Ƙari ga haka, ya kamata mu koyi yin tunani mai kyau da kuma halayen da za su faranta wa Allah rai. (Kol. 3:​9, 10) Da taimakon Jehobah, mugayen mutanen ma, za su iya canja halinsu kuma su soma faranta ran Jehobah.

14. Me ka koya daga labarin Jack? (Ka kuma duba hoton.)

14 Alal misali, akwai wani mugun mutum mai suna Jack, har wasu suna kiransa The Demon, wato Aljani. Tsananin laifuffukan da ya aikata, an yanke masa hukuncin kisa. Amma kafin a kashe shi, wani ɗanꞌuwan ya je waꞌazi a gidan yarin da yake kuma Jack ya yarda a soma nazari da shi. Duk da cewa shi mugu ne sosai, a-kwana-a-tashi Jack ya canja rayuwarsa har ya yi baftisma. Jack ya canja halinsa sosai har a ranar da za a kashe shi, wasu masu gadin gidan yarin sun yi kuka. Wani sajent da yake aiki a wurin ya ce: “A dā, Jack ya fi kowa mugunta a gidan yarin nan. Amma yanzu yana cikin masu halin kirki sosai.” Bayan mutuwar Jack, da ꞌyanꞌuwa suka zo za su yi taro a gidan yarin, sai suka ga wani da bai taɓa zuwa ba, ya zo taron. Me ya sa ya zo? Yadda Jack ya canja halinsa ne ya burge shi. Don haka, ya ce yana so a koya masa yadda zai bauta wa Jehobah. Babu shakka, halinmu zai iya sa a ɗaukaka Jehobah!—1 Bit. 2:12.

Za mu iya ɗaukaka Jehobah ta halinmu (Ka duba sakin layi na 14) d


NAN BA DA DAƊEWA BA, JEHOBAH ZAI ƊAUKAKA SUNANSA

15. Ta yaya Jehobah zai nuna wa kowa cewa shi ne ya cancanci ɗaukaka? (Zabura 96:​10-13)

15 Karanta Zabura 96:​10-13. A ayoyin nan, Zabura 96 ta kammala da cewa Jehobah Sarki ne da yake yin shariꞌar gaskiya. Nan ba da daɗewa ba, Jehobah zai ɗaukaka sunansa. Ta yaya zai yi hakan? Ta wurin hukuncin da zai yi. Nan ba da daɗewa ba, zai halaka Babila Babba domin yadda take ɓata sunansa. (R. Yar. 17:​5, 16; 19:​1, 2) Wataƙila idan wasu suka ga halakar Babila Babba, za su soma bauta wa Jehobah tare da mu. A ƙarshe kuma, Jehobah zai halaka dukan mugayen mutane a lokacin yaƙin Armageddon. Ta haka, zai kawar da dukan maƙiyansa da suke ɓata sunansa. Saꞌan nan ya ceci masu ƙaunarsa, wato waɗanda suke son ɗaukaka sunansa. (Mar. 8:38; 2 Tas. 1:​6-10) Bayan Sarautar Yesu na Shekara Dubu kuma an yi gwaji na ƙarshe, Jehobah zai tsarkake sunansa gabaki ɗaya. (R. Yar. 20:​7-10) A wannan lokacin, “duniya za ta cika da sanin ɗaukakar Yahweh, kamar yadda ruwaye sun cika teku.”—Hab. 2:14.

16. Me za ka so ka yi wa Jehobah? (Ka kuma duba hoton.)

16 Muna marmarin ganin lokacin da kowa da kowa zai ɗaukaka Jehobah yadda ya kamata! Amma kafin nan, za mu iya yin amfani da duk wata dama da muka samu mu ɗaukaka Allahnmu Jehobah. Yin hakan yana da muhimmanci sosai, shi ya sa Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta zaɓi Zabura 96:8 ta zama jigon shekara ta 2025 inda ya ce: “Ku miƙa wa Jehobah ɗaukakar da ta cancanci sunansa.”

A ƙarshe, kowa da kowa zai ɗaukaka Jehobah yadda ya kamata! (Ka duba sakin layi na 16)

WAƘA TA 12 Jehobah, Allah Mafi Iko

a An canja wasu sunayen.

b BAYANI A KAN HOTUNA: Kwaikwayon abin da ya faru da Angelena.

c BAYANI A KAN HOTO: Kwaikwayon abin da ya faru da Prisca.

d BAYANI A KAN HOTO: Kwaikwayon abin da ya faru da Jack.