Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 5

WAƘA TA 108 Ƙauna ta Gaskiya Daga Allah

Yadda Muke Amfana Daga Ƙaunar da Jehobah Ya Nuna Mana

Yadda Muke Amfana Daga Ƙaunar da Jehobah Ya Nuna Mana

“Almasihu Yesu ya zo duniya domin ceton masu zunubi.”1 TIM. 1:15.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga yadda muke amfana daga fansar, da kuma yadda za mu nuna godiyarmu ga Jehobah.

1. Me za mu yi don mu sa Jehobah ya ji daɗi?

 A CE KA yi wa mutum kyautar wani abu mai kyau, kuma abin zai amfane shi sosai, amma sai mutumin ya ajiye abin a durowa ya manta da shi, yaya za ka ji? Ba za ka ji daɗi ba. Za ka so a ce mutumin ya gode maka kuma ya yi amfani da abin, ko ba haka ba? Mu ma Jehobah ya ba mu Ɗansa. Ba ka ganin zai ji daɗi sosai idan mun nuna godiya don wannan kyauta mai daraja da ya ba mu?—Yoh. 3:16; Rom. 5:​7, 8.

2. Me za mu tattauna a talifin nan?

2 In ba mu yi hankali ba, da shigewar lokaci za mu daina ganin muhimmancin fansar nan da Jehobah ya bayar dominmu. Zai zama kamar mun sa wannan kyauta mai muhimmanci a durowa ne, inda ba ma ganinsa, kuma mun manta da shi. Me za mu yi domin kada hakan ya faru? Muna bukatar mu dinga yin tunani a-kai-a-kai a kan abin da Jehobah da Yesu suka yi mana. Kuma talifin nan zai taimaka mana mu yi hakan. Za mu tattauna yadda muke amfana daga fansar yanzu, da kuma yadda za mu amfana a nan gaba. Bayan haka, za mu ga abin da za mu iya yi don mu nuna ma Jehobah cewa muna godiya, musamman a lokacin Taron Tunawa da Mutuwar Yesu.

YADDA MUKE AMFANA A YANZU

3. A wace hanya ce muke amfana daga fansar yanzu?

3 Muna amfana daga fansar Yesu sosai a yau. Alal misali, saboda fansar, Jehobah yana yafe mana zunubanmu, ko da yake ba dole ba ne. Amma yana yin hakan da son ransa. Da Dauda ya yi tunani a kan yadda Jehobah yake yafe mana zunubanmu, abin ya burge shi sosai. Ya ce: “Gama kai, ya Ubangiji, mai alheri ne kuma mai yin gafara.”—Zab. 86:5; 103:​3, 10-13.

4. Domin su waye ne Jehobah ya ba da fansar? (Luka 5:32; 1 Timoti 1:15)

4 Wasu sukan ga kamar ba su isa a ce Jehobah ya yafe musu ba, don yawan zunubansu. A gaskiya babu waninmu da ya cancanci a yafe masa zunubansa. Manzo Bulus ma ya ce ‘bai isa a ce da shi manzo ba.’ Ya ƙara da cewa: “Amma saboda alherin Allah ne na zama yadda nake.” (1 Kor. 15:​9, 10) Jehobah yana yafe mana zunubanmu idan mun tuba. Me ya sa yake hakan? Domin yana ƙaunarmu, ba don mun cancanta ba. Saboda haka, idan kana ganin kamar bai kamata Jehobah ya yafe maka ba don zunubanka sun yi yawa, ka tuna cewa Jehobah ya ba da fansar nan ne domin masu zunubi da suka tuba, ba don marasa zunubi ba.—Karanta Luka 5:32; 1 Timoti 1:15.

5. A cikinmu, akwai wanda ya isa ya ce ya kamata Jehobah ya yafe masa zunubansa? Ka bayyana.

5 Bai kamata wani a cikinmu ya ɗauka cewa ai ya kamata Jehobah ya yafe masa zunubansa domin ya daɗe yana bauta masa ba. Ba shakka, Jehobah yakan tuna da dukan abubuwan da muka yi a bautarsa. (Ibran. 6:10) Amma saꞌad da ya ba da Ɗansa, kyauta ne ya yi mana, ba biyan mu ya yi don bautar da muka yi masa ba. Idan muka ɗauka cewa mun cancanta, ko kuma ya kamata Jehobah ya yafe mana domin mun yi abubuwa da yawa a bautarsa, muna nufin cewa a banza ne Yesu ya mutu ke nan, domin ba ma bukatar fansarsa.—Ka kuma duba Galatiyawa 2:21.

6. Me ya sa Bulus ya yi ƙwazo sosai a hidimarsa?

6 Bulus ya san cewa komen yawan aikin da ya yi ma Jehobah, yana bukatar Jehobah ya yi masa jinkai. To me ya sa ya yi ƙwazo sosai a hidimarsa? Ya yi hakan ne don ya nuna godiyarsa ga Jehobah, don yawan alherin da ya yi masa. (Afis. 3:7) Mu ma za mu ci-gaba da bauta ma Jehobah da ƙwazo don mu nuna cewa mun gode da alherin da ya yi mana, ba don mu nuna cewa mun isa ya gafarta mana ba.

7. Mece ce hanya ta biyu da muke amfana daga fansar Yesu? (Romawa 5:1; Yakub 2:23)

7 Hanya ta biyu da muke amfana daga fansar ita ce, fansar ta ba wa kowannenmu damar yin kusa da Jehobah har mu zama abokansa. a Kamar yadda aka ambata a talifin da ya shige, lokacin da aka haife mu, babu dangantaka tsakaninmu da Jehobah don ba ma cikin iyalinsa. Amma yanzu saboda fansar Yesu, za mu iya more “salama da Allah” har ma mu zama abokansa.—Karanta Romawa 5:1; Yakub 2:23.

8. Me ya sa ya kamata mu gode ma Jehobah da ya ba mu damar yin adduꞌa?

8 Wani babban abin da muke jin daɗin yi domin abokantakar da ke tsakaninmu da Jehobah shi ne, yin adduꞌa. Ban da adduꞌar da muke yi a taro, Jehobah yana jin adduꞌar da kowannenmu yake yi. Idan muna cikin damuwa kuma muka yi adduꞌa, hankalinmu yakan kwanta. Ban da haka, yin adduꞌa yana ƙara danƙon zumuncin da ke tsakaninmu da Allahnmu. (Zab. 65:2; Yak. 4:8; 1 Yoh. 5:14) Lokacin da Yesu yake duniya, ya yi ta yin adduꞌa don ya san cewa Jehobah yana jin sa, kuma ya san cewa yin adduꞌa zai sa ya ci-gaba da zama aminin Jehobah. (Luk. 5:16) Ba shakka, muna godiya sosai don yadda fansar Yesu ta ba mu gatan yin adduꞌa da zama abokan Jehobah!

YADDA ZA MU AMFANA A NAN GABA

9. Ta yaya bayin Jehobah masu aminci za su amfana daga fansar Yesu a nan gaba?

9 Ta yaya bayin Jehobah masu aminci za su amfana daga fansar Yesu a nan gaba? Jehobah zai ba su rai na har abada. Mutane da yawa suna ganin ba zai yiwu mutum ya rayu har abada ba, domin an daɗe ana mutuwa. Amma tun dā ma Jehobah ya halicci mutane don su yi ta rayuwa har abada ne. Da a ce Adamu bai yi zunubi ba, da ba mu san mutuwa ba, kuma da kowa zai rayu har abada. Ko da yake yanzu yana mana wuya mu gane yadda yin rayuwa har abada zai kasance, mun san zai faru, domin irin sadaukarwar da Jehobah ya yi. Ya ba da Ɗansa da yake ƙauna don mu sami rai.—Rom. 8:32.

10. Wane lada ne Jehobah zai ba wa shafaffun Kiristoci da waɗansu tumaki?

10 Yayin da muke jiran lokacin da za mu sami rai na har abada, Jehobah yana so mu yi ta marmarinsa. Shafaffun Kiristoci za su ji daɗin rayuwa a sama kuma za su yi mulkin duniyar nan tare da Yesu. (R. Yar. 20:6) Waɗansu tumaki kuma za su yi rayuwa a aljanna a duniya, inda babu wahala da baƙin ciki. (R. Yar. 21:​3, 4) Kana cikin waɗanda suke sa ran yin rayuwa har abada a duniya? Idan haka ne, kar ka ɗauka cewa ladan yin rayuwa a sama ne ya fi, don tun dā ma Jehobah ya yi mu mu yi rayuwa a duniya ne. Don haka, babu irin jin daɗin da ba za mu ji ba a lokacin.

11-12. Waɗanne abubuwa masu burgewa ne za mu yi a Aljanna? (Ka kuma duba hotunan.)

11 Ka yi tunanin yadda rayuwarka za ta kasance a cikin Aljanna. Babu ruwanka da rashin lafiya ko mutuwa. (Isha. 25:8; 33:24) Jehobah zai ba ka duk wani abu mai kyau da kake so. Akwai abubuwan da za ka so ka koya a aljanna? Za ka so ka yi bincike a kan dabbobi ne? Ko za ka so ka koyi yin waƙa da kiɗa ne? Ko dai yin zane ne ka fi so? A aljanna, za a bukaci masu zana gine-gine da masu ginawa. Za a kuma bukaci masu noma da masu dafuwa, da masu ƙera kayan aiki, da masu shuka furanni da kuma kula da su. (Isha. 35:1; 65:21) Kar ka damu, da yake za ka rayu har abada, za ka sami lokacin yin dukan abubuwan da kake so.

12 Ba shakka za mu yi farin ciki sosai lokacin da za mu ga mutanenmu da suka mutu! (A. M. 24:15) Ka yi tunanin yadda za ka ji daɗin koyan sabbin abubuwa game da halittun Jehobah. (Zab. 104:24; Isha. 11:9) Abu mafi kyau ma shi ne, ba za ka taɓa yin zunubi ba, balle ma zuciyarka ta dame ka! Za ka yarda ka rasa aljannar nan don kawai ka yi abin da zai gamshe ka a yau? (Ibran. 11:25) Kar ka yarda! Ko da me za mu samu a duniyar nan yanzu, ba zai kai abin da za mu mora a Aljanna ba. Ka tuna cewa ba har abada ne za mu yi ta jiran aljannar ba. A-kwana-a-tashi zai zama inda muka saba zama. Kuma fansar da Jehobah ya bayar saboda ƙaunar da yake mana ce ta sa dukan abubuwan nan za su yiwu!

Waɗanne abubuwa ne za ka so ka yi a aljanna? (Ka duba sakin layi na 11-12)


KA NUNA MA JEHOBAH CEWA KANA GODIYA

13. Ta yaya za mu nuna godiyarmu ga Jehobah don ƙaunar da ya nuna mana? (2 Korintiyawa 6:1)

13 Ta yaya za mu nuna godiyarmu ga Jehobah don ƙaunar da ya nuna mana? Ta wajen sa bautarsa a kan gaba a rayuwarmu. (Mat. 6:33) Ka tuna cewa Yesu ya mutu ne “domin waɗanda suke da rai, kada su yi zaman ganin dama nan gaba, sai dai su yi zama saboda wanda ya mutu dominsu, aka kuma tashe shi saboda su.” (2 Kor. 5:15) Jehobah ya yi mana alheri sosai, don haka zai dace mu yi duk wani abin da za mu iya yi a bautarsa. Hakan zai nuna cewa da gaske muna godiya.—Karanta 2 Korintiyawa 6:1.

14. Ta yaya za mu nuna cewa mun yarda da Jehobah kuma muna bin ja-gorancinsa?

14 Wata hanya kuma da za mu nuna cewa muna godiya ita ce, mu yarda da Jehobah kuma mu bi ja-gorancinsa. Ta yaya? Ta wurin yin tunani a kan abin da Jehobah zai so mu yi a duk lokacin da muke so mu zaɓi abin da za mu yi. Alal misali, idan aka zo batun yawan karatun boko da za mu yi ko irin aikin da za mu yi. (1 Kor. 10:31; 2 Kor. 5:7) Idan muka yi zaɓin da ya nuna cewa ba ma shakkar Jehobah, bangaskiyarmu za ta ƙaru kuma dangantakarmu da shi za ta ƙara danƙo. Kuma za mu ƙara samun tabbaci cewa zai ba mu rai na har abada.—Rom. 5:​3-5; Yak. 2:​21, 22.

15. Ta yaya za mu nuna cewa muna godiya don fansar a lokacin Taron Tunawa da Mutuwar Yesu?

15 Hanya ta uku da za mu iya nuna cewa muna godiya don fansar ita ce, ta wurin yin iya ƙoƙarinmu a hidimarmu makonni kafin Taron Tunawa da Mutuwar Yesu, da kuma bayan taron. Mu shirya yadda za mu je taron, kuma mu gayyaci mutane su zo. (1 Tim. 2:4) Mu bayyana musu abubuwan da za a yi a taron. Za ka iya yin amfani da bidiyoyin nan, Me Ya Sa Yesu Ya Mutu? da, Ka Tuna da Mutuwar Yesu, don suna taimakawa sosai. Dattawa su tabbata sun gayyaci waɗanda suka daina zuwa taro. Ba shakka, za a yi farin ciki sosai a sama, da nan duniya idan wani ya dawo ya ci-gaba da bauta wa Jehobah! (Luk. 15:​4-7) Idan muka je taron, mu tabbata cewa mun gai da juna, da sabbin mutanen suka zo, da kuma waɗanda suka daɗe ba su zo taro ba. Mu sa su ji cewa an karɓe su hannu bibbiyu!—Rom. 12:13.

16. Me ya sa zai dace mu ƙara ƙwazo a hidimarmu a lokacin Taron Tunawa da Mutuwar Yesu?

16 Shin, za ka iya ƙara ƙwazo a hidimarka makonni kafin Taron Tunawa da Mutuwar Yesu, da kuma bayan taron? Yin haka, hanya ce mai kyau da za ka nuna godiyar ka don abin da Jehobah da Yesu suka yi mana. Idan muna waꞌazi sosai, za mu ƙara ganin yadda Jehobah yake taimakonmu, kuma hakan zai sa mu ƙara yarda da shi. (1 Kor. 3:9) Ƙari ga haka, ka tabbata ka bi karatun Littafi Mai Tsarki na Taron Tunawa da Mutuwar Yesu da ke littafin nan, Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana, ko wanda yake littafin taronmu na tsakiyar mako. Za ka iya yin nazari a kan nassosin nan.

17. Me yake faranta wa Jehobah rai? (Ka kuma duba akwatin nan, “ Hanyoyin Nuna Godiyarmu.”)

17 Wataƙila ba za ka iya ƙara yawan abubuwan da kake yi a hidimarka ba don yanayin da kake ciki. Idan haka ne, ka tuna cewa Jehobah ba ya gwada abin da kake yi da wanda wasu suke yi. Ya san cewa kana ƙaunarsa sosai. Ya kuma san cewa kana godiya sosai don fansar da ya bayar a madadinmu. Kuma hakan yana faranta masa rai.—1 Sam. 16:7; Mar. 12:​41-44.

18. Me ya sa muke gode wa Jehobah da Yesu Kristi?

18 Da ba don fansar nan ba, da ba zai yiwu a yafe mana zunubanmu, ko mu zama abokan Jehobah har mu sa ran yin rayuwa har abada ba. Amma yanzu muna moran abubuwan nan don Jehobah ya ƙaunace mu kuma ya ba da fansar. Bari mu ci-gaba da nuna masa cewa muna godiya. (1 Yoh. 4:19) Bari mu kuma nuna godiyarmu ga Yesu, wanda ya yarda ya ba da ransa dominmu!—Yoh. 15:13.

WAƘA TA 154 Ƙauna Ba Ta Ƙarewa

a Tun kafin Yesu ya ba da fansar, Jehobah yana yafe wa bayinsa. Me ya sa? Domin Jehobah ya san cewa Yesu zai riƙe aminci kuma zai ba da ransa. Don haka a gun Jehobah, kamar an riga an ba da fansar ne.—Rom. 3:25.