Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

SHAWARA A KAN YIN NAZARI

Yin Zane Zai Taimake Ka Ka Tuna da Darasin

Yin Zane Zai Taimake Ka Ka Tuna da Darasin

Bayan mun gama yin nazari, wani lokaci yana mana wuya mu tuna da abin da muka koya. Amma ba ya mana wuya mu tuna da abubuwan da Yesu ya koyar domin a yawancin lokaci, yakan yi misali da abin da an saba gani. Idan ka yi tunani a kan misalin da ya bayar, da abin da ya yi misalin da shi, za ka yi saurin tuna darasin. Mu ma idan muna nazari kuma mun yi tunani a kan yadda abin ya faru, ko yadda yake a zahiri, za mu yi saurin tuna darasin. Me zai taimaka mana mu yi hakan? Yin zane-zane a lokacin da muke nazari ne zai taimaka.

Waɗanda suke zana abin da suka koya sun fi tunawa da shi. Zanen yana sa su tuna da abin da aka faɗa, har ma da darasin da ake so a koyar. Ba sai ka zana abin ya fita da kyau ba, zane mai sauƙi kawai ya isa. An kuma lura cewa yin irin zanen nan yana taimaka wa tsofaffi sosai su tuna da abin da suka koya.

Don haka a nazarinka na gaba, ka gwada yin wasu zane-zane a kan abin da ka koya. Ƙila hakan ya sa ka tuna da darussan sosai har ya ba ka mamaki!