TALIFIN NAZARI NA 13
WAƘA TA 127 Irin Mutumin da Ya Kamata In Zama
Jehobah Ya Amince da Kai?
“Ina jin daɗinka ƙwarai.”—LUK. 3:22.
ABIN DA ZA MU KOYA
Yadda za mu daina yin shakkar cewa Jehobah ya amince da mu.
1. Wane irin tunani ne wasu bayin Allah masu aminci suke fama da shi?
SANIN cewa Jehobah ya amince da bayinsa yana da ban ƙarfafa! Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yahweh yakan ji daɗin mutanensa.” (Zab. 149:4) Amma a wasu lokuta, Kirista zai iya yin sanyin gwiwa kuma ya soma shakkar ko Jehobah ya amince da shi. Akwai bayin Allah masu aminci da yawa a Littafi Mai Tsarki da su ma sun yi fama da irin wannan tunani.—1 Sam. 1:6-10; Ayu. 29:2, 4; Zab. 51:11.
2. Wane ne zai iya samun amincewar Allah?
2 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ꞌyan Adam ajizai za su iya samun amincewar Allah. Ta yaya? Ta wurin ba da gaskiya ga Yesu Kristi da kuma yin baftisma. (Yoh. 3:16) Ta yin hakan, za mu nuna wa mutane cewa mun tuba daga zunubanmu kuma mun yi alkawarin yin nufin Jehobah. (A. M. 2:38; 3:19) Jehobah zai yi farin ciki sosai idan muka ɗau matakan nan don mu zama abokansa. Idan muka ci-gaba da cika alkawarin da muka yi cewa za mu yi nufin Jehobah, Jehobah zai amince da mu kuma zai ɗauke mu a matsayin abokansa.—Zab. 25:14.
3. Waɗanne abubuwa ne za mu tattauna yanzu?
3 To me ya sa a wasu lokuta Kirista yakan ji kamar Jehobah bai amince da shi ba? Ta yaya Jehobah yake nuna cewa ya amince da mu? Kuma ta yaya Kirista zai kasance da tabbaci cewa Jehobah ya amince da shi?
DALILAN DA ZA SU IYA SA WASU SU GA KAMAR JEHOBAH BAI AMINCE DA SU BA
4-5. Ko da a wasu lokuta muna ji kamar ba mu da muhimmanci, wane tabbaci ne za mu iya kasancewa da shi?
4 Tun muna ƙanana, da yawa daga cikinmu muna ganin ba mu da muhimmanci. (Zab. 88:15) Wani ɗanꞌuwa mai suna Adrián ya ce: “Tun ina ƙarami nakan ji kamar ba ni da muhimmanci. Na tuna saꞌad da nake ƙarami nakan yi adduꞌa domin iyalinmu su shiga aljanna, ko da yake a ganina ban cancanci in shiga aljanna ba.” Tony, wanda iyayensa ba Shaidun Jehobah ba ne, ya ce: “Iyayena ba su taɓa gaya min cewa suna ƙauna ta ko kuma suna alfahari da ni ba. Hakan ya sa na ji kamar ba zan taɓa yin abin da zai gamshe su ba.”
5 Mu ma idan a wasu lokuta mun ji kamar ba mu da muhimmanci, zai dace mu tuna cewa Jehobah da kansa ne ya jawo mu wurinsa. (Yoh. 6:44) Ya ma fi mu sanin halaye masu kyau da muke da su, kuma ya san tunanin zuciyarmu. (1 Sam. 16:7; 2 Tar. 6:30) Don haka, idan ya ce muna da daraja, ya kamata mu yarda da shi.—1 Yoh. 3:19, 20.
6. Yaya manzo Bulus ya ji game da zunuban da ya yi a dā?
6 Kafin mu koyi gaskiya, mai yiwuwa wasunmu mun yi abubuwa marasa kyau, kuma hakan ya sa zuciyarmu tana damin mu. (1 Bit. 4:3) Wasu Kiristoci kuma sun daɗe suna bauta ma Jehobah da aminci, amma har yanzu suna fama da wata kasawa kuma hakan na sa zuciyarsu ta dame su. Kai kuma fa, shin haka kake ji? Idan haka ne, kada ka yi sanyin gwiwa domin akwai bayin Allah masu aminci da su ma suka yi fama da tunani kamar haka. Alal misali, saꞌad da manzo Bulus ya yi tunani a kan kurakuren da ya yi, sai ya ce shi abin tausayi ne. (Rom. 7:24) Bulus ya riga ya tuba daga zunubansa kuma ya yi baftisma. Amma ya kira kansa “mafi ƙanƙanta a cikin manzannin Yesu,” kuma ya ce shi ne “mafi zunubi.”—1 Kor. 15:9; 1 Tim. 1:15.
7. Me ya kamata mu tuna game da zunuban da muka yi a dā?
7 Ubanmu na sama ya yi alkawari cewa zai yafe mana idan muka tuba. (Zab. 86:5) Don haka, ya kamata mu tuna cewa idan mun tuba da gaske, Jehobah ya gafarta mana, kamar yadda ya yi alkawari.—Kol. 2:13.
8-9. Me zai taimaka mana mu daina tunani cewa Jehobah bai amince da mu ba?
8 Dukanmu muna so mu bauta ma Jehobah da dukan ƙarfinmu. Amma, wasu suna ji kamar ba za su taɓa iya yin abin da zai sa ya amince da su ba. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Amanda ta ce: “A tunanina, bauta ma Jehobah da iya ƙarfina yana nufin in riƙa yin abubuwa fiye da yadda nake yi a yanzu. Don haka, nakan yi ƙoƙarin yin abubuwan da suka fi ƙarfina. Kuma idan na ‘gagara’ yin su, sai in yi baƙin ciki kuma in ji kamar na ɓata ma Jehobah rai.”
9 Ta yaya za mu daina tunanin nan cewa ba za mu iya yin abin da zai faranta ran Jehobah ba? Ka tuna cewa Jehobah mai sanin yakamata ne. Ba zai taɓa gaya mana mu yi abin da ya fi ƙarfinmu ba. Yana jin daɗi idan ya ga yadda muke bauta masa iya gwargwadon ƙarfinmu. Ban da haka, ka yi tunani a kan bayin Allah da suka bauta ma Jehobah da dukan zuciyarsu. Alal misali, ka tuna yadda Bulus ya yi shekaru da yawa yana waꞌazi da ƙwazo sosai. Ya yi tafiya zuwa wurare masu nisa sosai kuma ya kafa ikilisiyoyi da yawa. Amma da yanayinsa ya canja kuma ya ƙasa bauta ma Jehobah yadda yake yi a dā, shin Jehobah ya daina amincewa da shi ne? Aꞌa. Ya ci-gaba da yin iya ƙoƙarinsa kuma Jehobah ya albarkace shi. (A. M. 28:30, 31) Mu ma, a wasu lokuta ba za mu iya bauta ma Jehobah kamar yadda muke yi a dā ba, amma abin da yake faranta wa Jehobah rai shi ne dalilin da ya sa muke bauta masa. Yanzu bari mu tattauna wasu hanyoyi da Jehobah yake nuna mana cewa ya amince da mu.
TA YAYA JEHOBAH YAKE NUNA CEWA YA AMINCE DA MU?
10. Ta yaya za mu ji yadda Jehobah yake gaya mana cewa ya amince da mu? (Yohanna 16:27)
10 Ta wurin Littafi Mai Tsarki. Jehobah yana neman hanyar da zai nuna wa mutanensa cewa ya amince da su. A cikin Littafi Mai Tsarki, sau biyu Jehobah ya gaya wa Yesu cewa shi Ɗansa ne da yake ƙauna kuma Ya amince da shi. (Mat. 3:17; 17:5) Za ka so ka ji cewa Jehobah yana ƙaunar ka kuma ya amince da kai? Jehobah ba ya magana da mu daga sama, amma yana magana da mu ta wurin Kalmarsa. Idan muka karanta abubuwa masu ban ƙarfafa da Yesu ya gaya wa mabiyansa, kamar Jehobah ne yake magana da mu. (Karanta Yohanna 16:27.) Yesu yana da halaye daidai irin na Ubansa. Don haka, a duk lokacin da muka karanta yadda Yesu ya gaya wa almajiransa cewa ya amince da su, mu ɗauka cewa Jehobah ne yake magana da mu.—Yoh. 15:9, 15.
11. Me ya nuna cewa matsalolin da muke fuskanta ba sa nufin cewa Jehobah yana fushi da mu? (Yakub 1:12)
11 Ta wurin ayyukansa. Jehobah yana marmarin taimaka mana kuma yana hakan ta wajen ba mu abubuwan da muke bukata. A wasu lokuta, Jehobah yana barin munanan abubuwa su faru da mu kamar yadda ya bari su faru da Ayuba. (Ayu. 1:8-11) Idan muna fuskantar matsaloli, hakan ba ya nufin cewa Jehobah ya daina amincewa da mu. A maimakon haka, matsaloli suna ba mu damar nuna wa Jehobah yadda muke ƙaunar sa da kuma yadda muka dogara gare shi. (Karanta Yakub 1:12.) Kuma saꞌad da muka fuskanci matsaloli, za mu ga yadda yake kula da mu da kuma taimaka mana mu jimre.
12. Wane darasi ne za mu iya koya daga labarin Dmitrii?
12 Ka yi laꞌakari da misalin wani ɗanꞌuwa a Asiya mai suna Dmitrii. An sallame shi daga wurin aiki kuma ya yi watanni bai sami wani aiki ba. Don haka, ya yanke shawarar yin waꞌazi fiye da yadda yake yi a dā don ya nuna cewa da Jehobah ya dogara. Watanni da yawa bayan haka, ya ƙasa samun aiki, kuma ya soma rashin lafiya mai tsanani har ya ƙasa tashi daga kan gado. Sai ya soma tunani cewa shi ba mijin kirki ba ne kuma Jehobah yana fushi da shi. Wata rana, sai ꞌyarsa ta rubuta abin da ke Ishaya 30:15 a takarda. Ayar ta ce: “Cikin kwanciyar hankali da dogara gare ni za ku sami ƙarfi.” Ta zo ta same shi a kan gado kuma ta nuna masa. Sai ta ce: “Baba, a duk lokacin da ka soma baƙin ciki, ka tuna da nassin nan.” Dmitrii ya gano cewa saboda taimakon Jehobah ne suke da isasshen abinci da kayan sakawa da kuma wurin kwana. Ya ce: “Abin da nake bukatar in yi shi ne in kwantar da hankalina kuma in dogara ga Jehobah.” Idan kai ma kana fuskantar irin matsalar nan, ka kasance da tabbaci cewa Jehobah ya damu da kai kuma zai taimaka maka ka iya jimrewa.
13. Su wane ne Jehobah yake amfani da su don ya nuna mana cewa ya amince da mu, kuma ta yaya yake yin hakan?
13 Ta wurin ꞌyanꞌuwanmu masu bi. Jehobah yana amfani da ꞌyanꞌuwanmu masu bi don ya nuna mana cewa ya amince da mu. Alal misali, zai iya sa ꞌyanꞌuwanmu su ƙarfafa mu a lokacin da muke bukata. Abin da ya faru da wata ꞌyarꞌuwa a Asiya ke nan saꞌad da take fuskantar matsaloli. An sallame ta daga aiki, kuma bayan haka ta kamu da rashin lafiya mai tsanani. Sai maigidanta ya yi zunubi mai tsanani kuma aka dakatar da shi daga zama dattijo. Ta ce: “Na kasa gane dalilin da ya sa abubuwan nan suke faruwa da ni. Na yi tunani cewa mai yiwuwa akwai laifin da na yi kuma Jehobah yana fushi da ni.” ꞌYarꞌuwar ta roƙi Jehobah ya sake tabbatar mata cewa ya amince da ita! Ta yaya Jehobah ya yi hakan? Ta ce, “Dattawan ikilisiyarmu sun tattauna da ni kuma sun taimaka min in fahimci cewa har yanzu Jehobah yana ƙauna ta.” Bayan wasu lokuta, ta sake roƙan Jehobah ya tabbatar mata da cewa yana ƙaunar ta. Ta ce: “A rana-ranar na sami wasiƙa daga wasu ꞌyanꞌuwa a ikilisiyarmu. Yayin da nake karanta kalmomi masu ban ƙarfafa da ke wasiƙun, sai na gaya wa kaina cewa Jehobah ne ya amsa adduꞌata.” Hakika, Jehobah yana tuna mana cewa yana ƙaunar mu ta wurin kalmomi masu ban ƙarfafa daga ꞌyanꞌuwanmu.—Zab. 10:17.
14. Ta wace hanya ce kuma Jehobah yake nuna mana cewa ya amince da mu?
14 Jehobah yana kuma nuna mana cewa yana ƙaunar mu ta wajen sa ꞌyanꞌuwanmu su yi mana gargaɗi. Alal misali a ƙarni na farko, Jehobah ya sa Bulus ya rubuta littattafai 14 ga ꞌyanꞌuwansa Kiristoci. A wasiƙun, Bulus ya yi wa ꞌyanꞌuwansa gargaɗi ba tare da ɓoye-ɓoye ba, amma ya yi hakan a hanyar da ta nuna cewa yana ƙaunar su. To don me Jehobah ya sa Bulus ya rubuta irin wannan gargaɗin? Domin Jehobah Uba ne mai kirki, kuma yaransa da “yake ƙauna” ne yake yi wa horo. (K. Mag. 3:11, 12) Idan wani ya yi amfani da Littafi Mai Tsarki ya yi mana gargaɗi, hakan ba ya nufin cewa Jehobah yana fushi da mu, amma tabbaci ne cewa har yanzu Jehobah yana amincewa da mu. (Ibran. 12:6) Waɗanne abubuwa ne kuma suke nuna mana cewa Jehobah ya amince da mu?
WASU ABUBUWA DA SUN NUNA CEWA JEHOBAH YA AMINCE DA MU
15. Su wane ne Jehobah yake ba wa ruhu mai tsarki, kuma wane tabbaci ne hakan yake ba mu?
15 Jehobah yana ba da ruhu mai tsarki ga waɗanda ya amince da su. (Mat. 12:18) Za mu iya yi wa kanmu tambayar nan, ‘Shin ina da wasu halaye da ruhu mai tsarki yake taimaka mana mu kasance da su?’ Shin ka lura cewa kana haƙuri da mutane fiye da yadda kake yi kafin ka fara bauta ma Jehobah? Gaskiyar ita ce, yayin da kake daɗa koyan halaye da ruhu mai tsarki yake taimaka mana mu kasance da su, hakan zai tabbatar maka cewa Jehobah ya amince da kai!—Ka duba akwatin nan, “ Halin da Ruhun Allah Yake Haifar Shi Ne . . . ”
16. Su wane ne Jehobah ya ba su hakkin yin waꞌazi, kuma yaya hakan yake sa ka ji? (1 Tasalonikawa 2:4)
16 Jehobah ya ba da hakkin yin waꞌazin labari mai daɗi ga waɗanda ya amince da su. (Karanta 1 Tasalonikawa 2:4.) Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Jocelyn ta ga tabbacin hakan yayin da take yin waꞌazin Mulkin Allah. Wata rana Jocelyn ta tashi da baƙin ciki. Ta ce: “Na ji kamar ba ni da ƙarfi kuma hakan ya sa na ga kamar ba ni da amfani. A lokacin ni majagaba ce, kuma ranar ce nake zuwa waꞌazi. Sai na yi adduꞌa kuma na fita waꞌazi.” A safiyar, Jocelyn ta haɗu da wata mata mai suna Mary. Matar tana da kirki kuma ta yarda Jocelyn ta yi nazari da ita. Bayan wasu watanni, Mary ta ce dā ma tana roƙon Allah ya taimaka mata, sai ga Jocelyn ta zo ta ƙwanƙwasa ƙofarta. Mene ne Jocelyn ta koya daga abin da ya faru? Ta ce: “Na ji kamar Jehobah yana gaya min cewa, ‘Ina jin daɗin ki sosai.’” Gaskiya ne cewa ba kowa ne zai saurari waꞌazinmu ba. Amma mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai yi farin ciki idan muka yi iya ƙoƙarinmu mu yi wa mutane waꞌazi.
17. Mene ne ka koya daga abin da Vicky ta faɗa game da fansar Yesu Kristi? (Zabura 5:12)
17 Waɗanda Jehobah ya amince da su ne suke amfana daga fansar Yesu. (1 Tim. 2:5, 6) Amma me zai faru idan mun ci-gaba da ji kamar Jehobah bai amince da mu ba duk da cewa mun ba da gaskiya ga fansar Yesu kuma mun yi baftisma? Mu tuna cewa zuciyarmu za ta iya ruɗin mu. Amma Jehobah ba ya kuskure, don haka za mu iya yarda da shi. A gunsa, waɗanda suka ba da gaskiya ga fansar Yesu Kristi masu adalci ne, kuma ya yi alkawarin yi musu albarka. (Karanta Zabura 5:12; Rom. 3:26) Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Vicky ta amfana sosai daga yin tunani mai zurfi a kan fansar Yesu. Bayan da ta yi tunani a kan fansar wata rana, sai ta ce: “Jehobah ya daɗe yana haƙuri da ni. . . . Duk da haka, kamar dai ina ce masa: ‘Ba za ka taɓa ƙaunar irina ba. Zunubaina sun yi yawa da har hadayar Ɗanka ba za ta iya wanke su ba.’” Tunani da ta yi game da fansar Yesu Kristi ya sa ta soma ganin yadda Jehobah yake ƙaunar ta. Mu ma za mu fahimci yadda Jehobah yake ƙaunar mu da kuma yadda ya amince da mu, idan mun yi tunani sosai a kan fansar Yesu.
18. Wane tabbaci ne za mu iya kasancewa da shi idan mun ci-gaba da ƙaunar Ubanmu na sama?
18 Duk da cewa za mu yi iya ƙoƙarinmu mu bi darussa da muka koya daga wannan talifin, a wasu lokuta za mu iya yin sanyin gwiwa kuma mu soma shakkar ko Jehobah ya amince da mu. Idan hakan ya faru da mu, mu tuna cewa Jehobah yana amincewa da “masu ƙaunarsa.” (Yak. 1:12) Don haka, ka ci-gaba da yin kusa da Jehobah, kuma ka lura da hanyoyin da Jehobah yake amfani da su don ya nuna maka cewa ya amince da kai. A kullum ka riƙa tuna cewa Jehobah ba ya “nesa da kowannenmu.”—A. M. 17:27.
MECE CE AMSARKA?
-
Me ya sa wasu suke ji kamar Jehobah bai amince da su ba?
-
Waɗanne hanyoyi ne Jehobah yake amfani da su don ya nuna mana cewa ya amince da mu?
-
Me ya sa za mu iya gaskata cewa Jehobah ya amince da mu?
WAƘA TA 88 Ka Koya Mini Hanyoyinka